Showing 6001 words to 9000 words out of 131263 words

Chapter 3 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt

Ayshatuu   

20 Dec 2024

5191

ba at this tender age ace ba tada Uwa bare Uba. A hankali ta kifa kanta kan gadon Tana sauke ajiyar zuciya a hankali bacci ya dauketa, cikin baccin taji ringing din wayarta hakan yasa a firgice ta tashi se taga sunan Junaid hakan yasa ta Mike zuwa gaban dressing mirror tana kallon fuskarta ko yaro ya kalleta yasan Tasha kuka Balle Junaid, khol ta murza a idon ta dauki shade ta saka ta fito. Tunda ta fito ya maida dukkan hankalinshi kanta, Abun da yafi burgeshi da Sulaim shi ne tafiyar ta yadda take tafiya a hankali Cikeda nutsuwa babu hargowa a ciki shi yake burgeshi.


_Your gaze Junaid it's Haram!_


Inner self dinshi ya fada mishi hakan yasa yayi kasa da kanshi, itama shade din da ta saka shi ya bata damar kare mishi kallo, as usual kananan kaya ne jikinshi short sleeve top se denim jeans da wrist watch me kyau da ya dace da fatar Hannunsa yayi masa kyau, Tana zuwa gabanshi ya Mike ta biyo bayanshi har mota babu Wanda yace uffan, seda ya hau titi sannan yace


Remove those shade zasu hanaki ganin hanya.


Babu musu ta ciresu cikin sa'a ya sauke idanunsa a kanta, take gabanshi ya fadi ganin yadda idanunta sukai swollen, gangarawa yayi gefen titi yace


Meye samu fuskarki? Me ya sakaki kuka.


Ai kukan da ya ambata se ta kuma sakin wani she's missing them shekaru biyar kenan amma kullum tana jin mutuwar sabuwa a ranta. Gaba daya hankalin Junaid ya tashi yayi juyin duniya taki magana, yayi lallashin har ya gaji amma taki tayi shiru hakan yasa yayi dialing number Mami, Tana dagawa ya fada mata Abinda yake faruwa aikuwa tace ya hadata da Sulaim din, jin muryar Mami ya kara tada mata hankali hakan yasa abinda ta Fara cewa


Mami I'm missing you!


Murmushi Mami tayi tace


Shiyasa kike kuka? Idan nayi miki aure kuma fa? Shima kuka zaki dinga yi idan kina son ganina? Kiyi hakuri next week zanzo gaisuwa kanon nida Babanki, is that OK?


Kanta ta gyada taji dadi kuma hawayen suka dauke Allah ya mata replacing Mummy da Mami , Daddy kuma da Baba. Seda ta tabbatar ta daina kukan kafin tayi magana da Junaid, haka suka cigaba da tafiya jefi jefi yana mata tambayoyi dukda yawanci akan makaranta ne. Acan kuwa Mami tana tunanin dalilin kukan Sulaim don tasan tana missing dinsu amma bazaiyiwu ace shi ne yasa take Wannan kukan ba kuma daga muryarta kasan ta jima tana yi. A haka dai ta hakura akan koma Menene idan tazo zata gani. Ranar Junaid da Sulaim sun Sha yawo se maghariba ya maida ta gida Har lokancin subay'a bata dawo ba.


Shatuuu ♥️
[6/21, 8:05 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU!*


✍️Shatuuu ♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


Birnin kudu local government ce a jigawa state kuma tana karkashin Dutse emirate, yawancin mazauna garin Fulani ne se kuma hausawa, garin suna da duwatsu da kuma Nono. Malam Muhammadu shi ne sakataren local government a wannan lokacin don haka yanada rufin asiri sosae, matarshi kwaya daya Maryamu se yaransu biyar Lukman, Fatima, Aminu, Sauda da Hafsa. Baki dayansu babu Wanda baiyi karatu ba hatta matan saboda shi yayi karatu yasan dadin karatun hakan yasa duk yadda ake tsegumin shi seda yasa sukai karatun. Lukman shi ne soja a cikinsu kuma yana rike da matakin General , Umma Fatima classroom teacher ce Tana aure da yaranta a Ningi, Mama Sauda kuma Nurse ce Tana FMC birnin kudu tana aiki sannan Tana auren wani Barrister shima dan garin ne, se Anty Hafsa Itace take aure a Niamey kasar Niger. General Lukman soja ne mijin Hajiya Nafi wadda asalinta yar kebbi ce sun hadu da ita a saudiyya sunje aikin hajji anan Bayan sun dawo aka Yi dukkan wasu formalities sannan sukai aure. A maiduguri suka Fara zama sannan suka koma Abekuta anan ta haifi Junaid me tsananin Kama da Uncle Aminu tamkar shi ya haifeshi. Baiyi shekaru uku ba aka maida Baba aiki Minna hakan yasa Mami wadda Barrister ce kawai tabar aiki da Gwamnati Sede private Tace idan sukai settling ta samu tayi joining wani abun sannan ta dakko kanwarta Zahra ta rike wadda ta auri uncle Aminu daga baya. Seda Junaid yayi kusan shekaru biyar kafin Mami ta haifi Jabir, Bayan shekara uku ta haifi Ja'afar, har ta fitar da rai da haihuwa wajen shekaru Tara sannan ta haifi Auta Jawad. Junaid shi ya gado Mami shi yayi Law a university of Nsukka yayi serving a Niger sannan ya dawo gida lokacin sun koma baki daya kaduna anan cikin Jaji, a high court yayi practicing na shekara biyu sannan ya koma ABU yayi masters sanann yayi academician anan ya hadu da Subay'a ita kuma tana banking and finance, asalin Subay'a yan Kano ne mahaifinta dan Rano ne mahaifiyarta yar Bichi suna da kudi sosae kuma yan Boko ne gashi basuda namiji ko daya baki dayansu mata ne hakan yasa sukeda zumunci Don haka idan Kaje gidajensu zakaga haka suke tafiyar da rayuwar su iri daya a cewarsu uwarsu batada da namiji so babu Wanda zaiyi disrespecting dinta Shiyasa ya kasance basu girmama dangin miji. Danshi na farko Ahmad Wanda Keda shekaru shida se na biyu me shekaru uku Muhammad. Yanzu haka he's a lecturer a faculty of Law cikin BUK. Jabir shi ne na biyu his father's son, sosae yake kama da baba kuma shi ne soja me rank din Conel Yana Delta shida matarshi Imratu yar jigawa ce a garin Babura ta social media suka hadu, tana level 3 akai Auren a UDUS haka dai aka samu ta kammalla karatun suka tattara Zuwa delta. Tana da kirki tasan mutuncin mutane sede basu taba haihuwa ba hakan yasa suka daga hankalinsu Amma Baba da kanshi yayi musu nasiha akan komai na rayuwa MUQQADARI NE, kada su manta hakan wannan yasa suka Kwantar da hankalunsu, tsakanin subay'a da Imratu babu wani kyakyawan muamala saboda Imratu bata son raini itakuma kullum kallon kaskanci take mata hakan yasa Basa shiri ko kadan haka nan Jabir basu shiri da subay'a wanda ya kuma shafar ita Imratun. Ja'afar shi ne na uku pharmacist ne Yana aiki a cikin kaduna bashida aure, shima kusan halinsu daya da Jabir sede shi mutum ne me kulekulen yan mata shi kanshi bazai iya irga yan matanshi ba saboda yawansu, gaba daya ya fisu kyau hakan yasa yake ganin jin yakai, ko Baibi yan mata ba definitely Za'a bishi. Amma Duk Wannan yan matan yana son Sulaim Yana ganin Ita kadai ce taste dinsa Don currently tare suke, yana ganin ita reserve dinshi ce Sede besan hakan kuskure ba ne Don duk Abinda yake Sulaim na sane dashi . Jawad shekara daya kawae ya bawa Sulaim shi ne abokinta wanda ko abu ya sameta shi take Fara fadawa yana ABU yana engineering.


Uncle Aminu neurosurgeon ne matarshi Anty Zahra, daga Zuwa wani course Germany shi kenan suka retaining dinshi yake musu serving acan. Duk wata Niima da Allah yake bawa mutum sun samu haihuwa ce kawai Allah bai kawo ba, sunje asibitin Amma shiru har suka hakura Se kuma kwatsam Sega Anty Zahra da ciki, murna kam ba'a magana haka suka ta murna suda danginsu. Wata Yana kaiwa lokacin shi ta haifi yarta mace me Kama da ita sosae sede Bayan ta haihu ta Fara wani Irin bleeding na fitar hankali, Duk yadda akaaso tsayar dashi abu ya faskara hakan yasa Uncle Aminu signing aka cire mahaifar baki daya, hakan yasa Bata kuma haihuwa ba Daga kan Sulaim. Baki daya suka dawo Nigeria a gidan Mami suka zauna akai suna Yarinya aka saka mata Ummu_Sulaim Daga nan suka tafi birnin kudu inda tayi watanni uku kafin suka koma Germany. Kowa nasan Sulaim musamman yaran Mami Tunda basuda mace a gidan Tun lokacin Baba yaso karbarta amma ganin kamar itakadai ce abinda suka mallaka yasa ya hakura. A Kwana a tashi Bbu wuya gurin ubangiji haka Sulaim tayi ta girma har ta shiga secondary school dinta, sun sota ta sosu sun bata dukkan abinda Allah ya wajabta iyaye su bayar to babu abinda Sulaim ta rasa, sun mata gata kuma sunyi mata tarbiyya.


On the fateful day, Tana tashi Daga school taki bin school bus don tayi da Mummy da Daddy dinta akan da kansu zasu zo daukarta sede kafin nan ma Sega mota daga office din Daddy anzo tafiya da ita, duk tunaninta basu samu dama zuwa bane Shiyasa, sede tana Zuwa compound dinsu taga an taru ga reporters, police, Nigerian Ambassador da sauran mutanen embassy, se gawarwaki guda biyu an rufesu da farin likafani, Tunda ta zo gurin kawai taja ta tsaya bata yi gaba Balle tayi baya Tanan dai a tsaye ta kusan Mintina goma kafin aka fahimci zuwanta, Alhaji Salisu shi ne Ambassador din, riko hannunta yayi ya isa da ita inda gawarwakin suke ya bude fuskokinsu, Mummy's ce da Daddy tamkar suna raye babu digon ciwo jikinsu, itadai kawai shiru tayi tana ta kallonsu amma ta kasa furta komai, addu'ar da aka saka ta tayi ma take kasa tana nan har aka zo tafiya dasu don musu sallah saboda Baba general ya wakilta Ambassador yayi duka necessary saboda bazasu samu tasowa ba se Washegari. Haka Sulaim na kallo aka tafi dasu amma hawaye ko dis bai digo mata ba, akai musu sallah aka binne su sannan aka tafi da Ita Nigerian embassy dake kasar, Tunda taje Matar Alhaji Salisu take ce mata


Sulaim Mummy ta rasu Daddy ma haka, bazaki kara ganinsu ba kiyi kuka kinji


Amma ko dis ta kasa gashi ko uhm bata furta ba itadai ta zama gata nan gata nan dai ita kamar statue haka ta zama. Har su Mami suka iso Sulaim Batayi ba duk yadda taga ana kuka Tana son Yi Amma ta kasa, seda aka gama komai aka taho da ita Nigeria anan ta Fara wani Irin kuka me Cikeda tashin hankali, shi kenan se ta dawo musu da mutuwar sabuwa aka Fara wani mourning din. Tasha kuka Sulaim kamar bazata taba dariya ba, don seda aka Fara hadata da therapist kafin aka samo kanta. Hakan yasa ta bata shekara daya bata fara school ba. Jawad shi ne abokinta na farko Bayan Mami kullum suna tare se Ja'afar Wanda ya nuna mata soyayya me tsayawa a zuciya, shikam Junaid ba a gari yake ba amma yanada matsayi cikin zuciyarta saboda duk lokacinda ta ganshi se Daddy ya fado mata kuma dake farkon tafiyar Daddy Germany da Junaid yayi hakan yasa sukeda abubuwa da yawa ita dashi in common.


A haka ta dangana ta Fara school inda ta karasa secondary dinta shi ne ta Fara law..... Sulaim kenan.


Khulthum Itace yar Mama (Hadiza) ta farko , mahaifin Khulthum malamin wata islamiyya ne a wani kauye a malumfashi, shi ne mijin Mama na farko wanda uwar miji da danginshi suka hanata sakat Seda ya saketa da cikin Khulthum haka ta koma gida a Kano babu dadewa ta haifi Ummu_Khulthum shi kuma Malam Sule Allah yayi masa rasuwa. Bayan ta yaye Khulthum tayi wani auren shi ne ta haifi Amir, A'isha, Maryam, Amira da auta Osama. Mahaifinsu aikinshi shi ne hada guga da dinkewa Dan haka se ranar da Allah ya kawo ciniki akeyi da Wannan Za'a kukuta ayi cefane, to yanzun anzo era da kwatakwata kusan a birni guga bashida amfani shi kuma sanaar da ya iya kenan. Hakan yasa suke cikin bakin talauci. Dadi daya se Khulthum ta iya kunshi takeyi, Idan akace sallah tazo to gidannan ba'a rufeshi saboda mutane, se ya zamana Yarinya Tana da abin batarwa to most lokuta ita ke bada kudin cefane hakan yasa ta raina su, raini na fitar hankali kuwa, dakuna biyu ne a gidan amma kayanta ne kawai a ciki yaran nasu na gurin iyayensu idan ka shiga gidan tunani zakayi cewar Khulthum ce yar gidan sauran su ne agola. A haka aka Fara daukarta tana zuwa gidajen masu kudi tayi lalle wannan shi ya fara bude mata ido taji tabbas bazata iya cigaba da zama a wannan halin ba.


Ashir shi ne saurayin ta na karfen kusan kowa tare ya sansu dukda itadin tana kula wasu amma a zuciyarta Ashir shi ne reserve dinta, to kuma se ta shiga makaranta ta Fara ganin kankarrrun masu kudi, yan karya hakan yasa akalar Rayuwarta ta Fara juyawa. Wannan kenan.


To people of Allah kunji asalin kowa! Ya kuke ganin xa'ayi? Yanzu zamu shiga cikin labarin sosae.




Shatuuu ♥️
[6/23, 10:17 AM] Heedaya Bunu: *MACE A YAU*
5
✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


Sulaim! Sulaim!! Sulaim!!!


Mtsssss


Sulaim ta buga tsaki jin yadda ake kwala mata Kira, ita a karan kanta bazata iya tuna Yaushe taji ana kiranta irin haka ba, gyara zamanta tayi babu alamun ko niyyar zataje kiran da Subay'a ke yi mata, haka ta cigaba da revising books dinta don Bata fiye son barin karatu ya tarar mata ba. Tana nan Zaune se ga Atika ta shigo ko bata fada ba tasan aiko ta akai hakan yasa tace


Kije ki ce mata gani nan.


Ba tareda Atika tayi magana ba ta fice sannan Sulaim ta Mike ta fito fuskarta babu walwala, Subay'a na zaune kan daya daga cikin cushion din da suka kawata parlour, Tana cikin abaya baka kasancewar Friday ce basu saka suit, dawowarta kenan daga office don ko kaya bata canza ba. Kafarta daya kan daya tana ta girgixa ta ga fuskar nan a murtuke.


Ance Kina kirana?


Sulaim ta tambaya lokacinda ta tsaya akan Subay'a bawai Sulaim tana da rashin kunya bane no, idan kaja girmanka tafi kowa girmamaka amma idan ka nuna mata Kai Bakada mutunci zata saka wannan rigar don ku daidaita differences dinku.


Bakiji tun dazu Inata kwala miki kira ba.


Subay'a ta fada a kufule, zama Sulaim tayi tace


Na jiki mana kawai naga kiran yayi yawa ne.....


Yimin shiru fitsararriya..... Tashi kije na fasa fada.


Batace da ita komai ba ta Mike kuwa ta koma dakinta ta cigaba da bitar ta sede tayi murmushi idan ta tuna karonsu da Subay'a. Ta dan jima a zaune taji zaman ya isheta hakan yasa ta Mike ta fito hannunta rikeda wayar ta, babu kowa a parlor hakan yasa ta samu dogon cushion ta kwanta kafin ta Fara neman layin Ja'afar, a iya lissafinta Kwana biu kenan basui waya ba kullum ya kira tayi bacci ita kuma Bata samu damar returning masa call din ba.


Hello Sweetm


Shi ne Abinda ya fara fada Yana amsa call din, murmushinta me kyau tayi wanda wushiryar dake bakinta ta bayyana se ta Fara rikidewa zuwa fuskar Junaid, Don ita da babanta take kama kuma Junaid photocopy Uncle Aminu ne.


Hi Luff


Ajiyar zuciya duka suka sauke, shima daidaita kwanciyarshi yayi tareda rike wayar da kyau yace


Kinsan yadda Nayi missing dinki kuwa, gaskiya kano zanzo na ganki.


Dariya ta saki a hankali daidai bude kofar parlour amma saboda yadda ta shagala Bama tasan an shigo ba.


Kai da Yaushe nazo har zaka dinga ihun kayi missing dina, though I missed you too


Se yayi dariya yace


Kaji ta Ashe Kema Kinaji, to ya komai hope babu Wanda yake hunting life dinki?


Haba dai waye ya isa bayan ka kankane ko ina, Sulaim is for Ja'afar babu wani.


Tarin da taji yasa ta dago a hankali ta dubi gurin, Junaid ne a tsaye da dukkan alamu ya jima da shigowa, idanunsa da suke farare sun Dan canja kadan, gaba daya ya zuba su akanta, yadda yake kallonta yasa ta duburburce ta Yi saurin kashe wayar tareda mikewa Sede kafin ta tako inda yake har yayi gaba ya nufi inda kofar parlour shi take. Komawa tayi ta zauna tayi shiru a ranta tana fadin me yasa yake min irin kallon nan kamar Nayi masa laifi? Ko dai wani abunne? Gaba daya se ta kasa sakewa hakan yasa ta koma daki Tana ta jujjuya abin, a saka Ja'afar ya kara kira amma se taji bata bukatar sake magana dashi haka tayi ta ringing Batayi picking ba Daga karshe Tayi picking Daga muryarta ya fahimci bata mood din hakan yasa yayi mata sallama donshi ma aikinsa yake.


Junaid kam a parlonshi ya cire takalman kafarshi tare da Adana su cikin rack dake gefe, cikin bedroom dinshi ya shiga wanka yayi, haka Yake neat tamkar na mace, Junaid Nada tsafta kuma yanada kula baya tarayya da kazanta hakan yasa ko baa gyara mishi ba zaiyi sparing Lokaci ya gyara da kanshi. Komai da ya cire seda ya maida shi inda ya dace, towel ya daura ya shiga bayi ba tareda ya Bari abinda ya faru tsakaninshi da Sulaim ya dawo masa ba. Haka yayi wanka yayi Alwala sannan ya fito a tunaninshi Subay'a ta shigo amma har lokancin babu Wanda ya shigo kuma sunsan ya dawo. Jallabiya yasa Fara tas hade da hularta, ya jika jikinshi da turarenahi wanda ko kudi ya baka indai daga jikinshi ya fito to Seka ji wannan kamshin saboda yadda ya kama jikinshi.


A parlor yayi tunanin zaiga Sulaim nan ma Bata nan haka ya wuce massallaci akai maghrib sukai meeting na magidantan unguwa sannan akai isha'i kafin ya dawo gida. Ko dining bai kalla ba ya wuce parlonshi yayi kusan Mintina ashirin Subay'a bata zo ba, hakan ya kara dagula masa lissafi ta barshi da abinda yake ji mana, inda tasan yadda zuciyarshi take ciwo a halin yanxu baya tunanin zata barshi shi daya, kuma wannan halinta ne ba wai yau ta Fara ba yayi maganar har ya gaji amma bata fasa ba but yau Yana ganin xa'ayi sabon zama.


Yana nan Zaunen Sega ta shigo, tayi kyau babu karya, lace ne jikinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login