Showing 72001 words to 75000 words out of 131263 words
Chapter 25 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt
wardrobe ya bude important kayanta duka basu gurin, Dayan bedroom din ya tafi nanma same case. Da sauri ya fito ya nufi kitchen for the first time, Atika na hada salad taji kamshin turare hakan yasa ta juo da sauri se ganin Junaid tayi, gaba daya ta duburburce don Bata taba ganinshi a kitchen ba,
Me zaa baka?
Ta tambaya gabanta na faduwa, kallonta yayi yace
Ina Subay'a taje?
Kanta ta girgixa tace
Nima bansani ba amma sun fita da kaya itada yayarta amma gashi.
Ta ciro paper daga Apron din jikinta ta mika mishi, cikin hanzari ya karba sannan ya fice Zuwa parlor, Baki daya yasan raini kam subay'a ta gama ko bai karanta abinda Ke cikin paper ba yasan ta tafi Tunda yaga dakinta a haka.
_Dear, I'm sorry da Abinda zaka tarar amma babu yadda zanyi tafiyar ta zama dole. Ka yafe min zan kula maka da kaina sannan zan dawo gareka. I missed you. Subay'a_
Daga haka ya dafe kanshi wanda ke barazanar tsagewa saboda yadda kwakwalwar shi ta cunkushe, hannunsa ya saka ya rufe fuskarsa wadda tayi jawur saboda tsananin bacin rai. Yana nan Zaune Muhammad yazo yana kukan Mimi. Wannan ya kara daga mishi hankali ga har lokancin uku batayi ba Balle yasa ran dawowar Sulaim. Atika ce Taxo ta daukeshi Cikeda mamakin halin da ta samu Junaid.
Shima dakinshi ya koma ya kwanta bayan ya samu Muhammad yayi shiru Ahmad kuma yayi bacci, ya dade yana tunanin abinda zaiyi Amma ya kasa tuno Abinda ya dace yayi saboda baya son yanke hukunci cikin fushi amma Wallahi yasan har Subay'a ta koma ga Allah bazata manta wannan abin da zai mata ba.
Wasa wasa haka Junaid ya zauna a daki shi daya zuciyarshi na tafarfasa a haka akai sallar laasar ya fita zuwa massallaci kafin ya dawo Sulaim ta dawo, Tana shigowa Tajiyo kukan Muhammad, da sauri ta nufi kitchen dan can ta jiyo kukan, Tana zuwa ta karbe shi daga hannun laraba tana girgiza shi tace
Waye ya taba min babyna?
Mimi
Ya fada Yana kara Sautin kukan shi, kallon Atika tayi tace
Ina Mamansu ne?
Atika tace
Tun safe akazo aka dauketa.
Juyawa tayi ta fita tana mamakin Subay'a she's never a good mother neither a good wife. Komawa tayi parlor tare da Lallashin shi Sega Junaid da Ahmad sun shigo, kallonshi tayi taga wani tashin hankali kwance a Fuskarshi wai a hakan ma ya ragu kusan 70cent Bayan yayi sallah tareda kai kukanshi ga Allah, se taji gaba daya ranta ya baci har Seda ta saki tsaki. Zama tayi shima ya shigo ya zauna ya kalli Muhammad dake jikinta yace
Kin dawo kenan?
Kanta ta gyada tana patting bayan Muhammad se yaji inama ya zama Muhammad ko ya samu wannan care din shima.
Na dawo Yaya, ya gidan?
Dan murmushi yayi mata yace
Alhamdulillah, gobe zanje kaduna akwai sako?
Kanta ta dago da sauri tace
Zanje nima
Murmushi yayi a ranshi Yana ganin wannan yarinyar will kill him tamkar bashi bane dazu ya rasa inda zai tsoma ranshi amma daga ganinta har ya fara dawowa hayyacinsa.
A'a kiyi hakuri next week zan kaiku kinji?
Turo mishi Baki tayi tana bubbuga kafa hakan yasa ya tsira mata ido kamar bazai dauke idonsa ba, ganin haka yasa tayi saurin daidaita kanta ta Mike zuwa dakinta tana jin tamkar tafi kowa saa a rayuwarta.
Washegari Seda ya kaisu makaranta kafin yayi mata sallama yace
Gobe Inshaaa Allah zan dawo, kinji?
Kanta ta gyada tace
Tohm Allah kaemu, safest journey a gaida su Mami.
Zasuji dear, kuma haka zan tafi babu ko kallon da zan na tunawa dashi, babu something sweet?
Hannunta tasa ta rufe fuskar ta tana dariya, a hankali kamar me rada tace
I will miss you.
Matso da kunnenshi yayi saitin bakinta yace
Kikace me?
I'll miss you.....
Wata kayatarciyar dariya ya saki yace
I'll miss you more *my Dove*
Jin yace dove yasa ta kalleshi se yayi dariya yace
Se munyi waya.
Fitowa tayi tana jin farin ciki na ratsa zuciyata tamkar ta tashi sama, Yaya Junaid!
Karfe goma na safe ya isa kaduna seda ya gama dukkan abinda zaiyi sannan ya nufi gida, luckily Mami da Baba suna gida. Mami ta kasa boye murnar da take ciki tare sukai breakfast sannan suka zauna hira dukkansu. Junaid ya rasa ta ina zai fara se can cikin damuwa ya sanar dasu halin da ake ciki, Baba couldn't say a word se Mami ce ta Fara salati tace
Wani hukuncin ka yanke?
Sakk
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
33
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Da sauri Ja'afar ya juya don komawa dakinshi saboda maganar da yaji Junaid ya furta tamkar kibiya haka ta sokar mishi zuciya, bai taba kawowa zaiji Irin wannan mummunar maganar ba kenan yayi wasa da damarshi, kenan Abinda Sulaim ta dade tana fada mishi akan Watarana yana gani zata zabi wani over him. Hannunsa ya cusa kanshi wanda yake Cikeda gashi da ake bashi kulawa tamkar na mace. Me yayiwa rayuwar shi kenan? Me ya amfana a rayuwarshi. Ya sani yana da 'yanmata amma son gaskiya na Sulaim ne itakadai take da features da yake bukata Daga gurin matar da zai aura se gashi ya luza akan fushinshi na banza wanda ya sani laifinshi ne amma yaki waiwayar ta Yana takamar tana mishi son da bazata jure rashin shi ba.
Kujerar dake kusa dashi ya fada kamar me shirin kuka saboda yadda zuciya take tafarfasa, yasan ko Yana hauka bai isa karawa da Junaid ba a fagen neman mace, Abu daya zai nunawa Junaid shi ne yarinta Amma Bayan haka bai da komai ba kuma da Abinda zai tunkara Sulaim dashi. Ya tuno lokutan da take yawan ce mishi *If you love someone, make sure you hold that person tight but if you didn't, others will surely do!* ga maganarta ta tabbata, ta samu Wanda ya fishi shi kuma ya tashi a tutar babu, he has completely messed up! Se muce Ja'afar ayi hakuri!
Baba ya bude Baki da niyyar magana farin ciki fal zuciyarshi har ya gagara boyewa seda ya bayyana kan Fuskarshi, Mami tayi saurin fadin
Aure kace Junaid?
Seda gabanshi ya fadi Don Mami hardly ta kirashi da Junaid, idan ta furta to tabbas abu yayi tsamari. Kanshi a kasa yace
Eh Mami aurenta nake son Yi.
Saboda 'yar gaban goshi bata nan, saboda kana son amfani da ita ka hukunta matarka, ai Junaid har yanzun Kai ba namiji bane, bakayi wayon rike mata biyu ba Tunda har ka kasa controlling mace daya, se biyu.
Kanta ta girgixa ta cigaba da fadin
'Yata Sulaim ba wadda zaayi auren huce haushi da ita bane, don haka ka manta da maganar auren ka jira matarka ta dawo.
Ita kanta Mami ta tsorata da yadda idanun Junaid suka koma amma ta dake, ta dauke idanunta kar ma tausayinshi ya rinjaye ta, bawai tana kin abin bane tafi kowa farin ciki amma dole ta nunawa Junaid laifinshi saboda ya sakar ma Subay'a da yawa, idan Jabir ne bazai taba haka ba.
Idanunshi jajur tamkar jini haka cikin wani tashin hankali wanda ya baibaye zuciyarshi Lokaci daya saboda jin furucin Mami, amma ya sani shi yake nema dole ya Dukar da Kai, cikin nitsuwa da kwantar da murya yace
Mami Wallahi bazaki taba kamani da wofantar da 'yarki ba, kinsani mutumin da Daddy Aminu da Anty Zahra suka nuna suna so ma bazan bari a cutar dasu ba Balle gudan jininsu Sulaim kiyi hakuri.
Kanta ta kawar gefe tana jin yadda zuciyarta Ke tausayawa Junaid,
Ka bar maganar kawai.
Juyawa yayi ya dubi Baba with pleading eyes akan ya saka baki amma ya Kaudar da kanshi don suna yara idan Mami ta hana abu gurin Baba suke zuwa haka shima idan ya hana amma yau abin Yana neman juyewa. Ko cikin tunaninshi bai taba tunanin cewar zai kawo proposal din auren Sulaim ayi declining amma gashi yayi. Mikewa yayi saboda Baba yace mishi yaje ya huta. Babu musu ya Mike ya nufi masaukinshi dake cikin gidan, Tun zuwanshi aka gyara hakan yasa ya wuce bayi Don yin wanka. Gaba daya zuciyarshi tamkar ana gobara haka yakeji , kenan rayuwarshi ta koma idan yana neman abu bazai samu ba a wannan lokacin.
Ana gama lectures suka fito kamar Koda Yaushe dukda yanzun sun zama su uku don tuni Khulthum ta cire kanta daga garesu, to ba kullum take Zuwa ba ma yanzun a sha ruwan tsuntsaye take wa Zuwa makarantar.
Aimana tace da Sulaim Bayan sun Yi sallama da Khairi ta wuce hostel.
Kwana biu duk kin zama wata iri, Meye ne Ke damunki dan Allah?
Kallonta Sulaim tayi tace
Babu komai Aimana, kawai Kwana biyu Bana jin dadi ne.
Dama tasan bawai zata fada mata bane amma dole Tunda tare suke.
Kodai Salim dinne har yanzun?
Wata muguwar harara ta maka mata tace
Lallai ke dinnan, Salim kuma ni Sulaim ce ba Khulthum ba.
Dariya tayi tace
Haka ne kam, kinga muyi sauri saboda Yaya Nu'uman bazai zo ba.
Hakane kinga Yaya Yaje kaduna gashi bai ma kira yace min yaje ba.
Sulaim ta fada fuskarta dauke da damuwa. Kallonta Aimana tayi amma batace komai ba har suka samu napep suka shiga zuwa gida. Koda Sulaim taje gida duk tunaninta zata tarar Subay'a ta dawo amma ga mamakinta kofar parlonta a kulle, yaran suna zaune suna kallo suna jiyo sallamar ta suka taho tarar ta. Rungumarsu tayi tana shafa kansu tareda tambayar kowa school kafin suka raka ta daki Don yin wanka. Tana fitowa taga kiran Imratu ita Duk tunaninta Junaid ne Tunda call dinsa take ta expecting amma shiru, dauka tayi ta placing wayar a speaker saboda tana shiryawa. Da wasa da dariya kamar yadda suka Saba suka gaisa sannan Imratu tace
Ke ashe Hajiyar gidanku Cyprus ta tafi karatu?
Cikin rashin fahimta Sulaim tace
Wace hajiyar gidanmu kuma?
Dallah, Subay'a nake nufi.
Idanu a waje Sulaim Cikeda mamaki tace Cy what? Dan Allah da gaske.
Wallahi, yanzun ya kira Soja yake fada mishi wai ya hanata Bayan ya tafi office ta tafi.
Innalillahi wa Inna ilahil rajiun! Yaya Imratu Nikam a rayuwata I've never seen a bad mother and wife kamar Subay'a ba. Ayya Shiyasa Yaya jiya Tunda na dawo gidan daga school naga akwai damuwa tattare dashi.
Ba dole ba Sulaim, bari kiji abinda yasa na kiraki, kinga a yanzun babu Abinda Papan Ahmad ke bukata Irin support, inason as much as u can kiyi supporting dinshi ki bashi kulawar da ya rasa, ina son ki zame mishi sanyin idanuya Kina jina?
Baki Sulaim ta turo tace
Kai! Ni kuma a wa? Se kace matarshi.
Tsaki Imratu tayi tace
Matsala ta dake kenan taurin Kai, ai ya fadawa soja cewar yayi miki proposing kuma bana son ki yaudare kanki kina son Papan Ahmad....
Ni kuma? Shi ya fada miki? Lallai ma Wallahi ba wani.
Seda Imratu tayi dariya yadda take so sannan tace
Hakan da kikayi ya tabbatar min zargin mu, Papan Ahmad bai san Kina son shi ba amma shi Yana miki so me suna so, me tsanani wanda ya gaza boyuwa. Inason Kiyi amfani da damar da Allah ya baki, ki bashi Abinda ya rasa cikin rayuwarsa.....
Kenan zan aureshi ba don so ba sedan Maye gurbin wata? Dama shi yasa yace Yana sona jiya saboda matarshi ba Tanan?
Kai Imratu ta dafe saboda batai tsamannin abin zaizo haka ba.
Shekarunki Nawa sulaim?
Last month nake nineteen.
Ke Yarinya ce har yanzun, kiyi tunani sosae akan maganar mu, kuma inason Kisa a ranki ko da Subay'a ko babu ita Junaid na sonki, he proposed jiya without knowing ta tafi, ki sani ke kadai ce hope dinshi a wannan lokacin idan kika barshi then Bana tunanin Kinyi mishi da kanki adalci.
Kafin Sulaim ta bata amsa ta katse call din, kasa tashi tayi daga gurin ta xurfafa tunanin maganganun Imratu, tabbas ko haka bata faru ba Tana jin tausayin Junaid tausayi me tsanani na gasken gaske wanda hakan shi ne Abinda ya fara saka sonshi cikin zuciyar ta, to yanzun bazata iya ba kenan? Abubuwa nawa Junaid yayi mata, wani Irin sacrifice ne bai mata ba, wannan kadai ya isa ya tabbatar mata Son gaske yake mata. Tun rasuwar Daddy dinta komai nata shi ke daukar nauyinsa, cin ta, sha, sutura da karatun ta. Ita kuma se ta kasa bashi farin ciki, ta kasa amsar soyayyarshi. Da sauri ta girgixa kanta, ta Mike jiki a matukar sanyaye ta nemi shirt da dogon wando ta saka sannan ta rufe kanta da hula.
Wayarta ta dauka ta kira Imratu tana picking murya a sanyaye tace
Yaya Ya zanyi to ?
Murmushi Imratu tayi tace
Kada kice mishi kin amince a baki, ki kyaleshi amma ki bashi kulawa yadda ya kamata. Kin gane?
Kanta ta gyada tace
Inshaaa Allah.
Daga haka sukai sallama ta koma ta zauna ta Fara neman layin Junaid, cikin sa'a ta shiga Sede yana kallon "Dove" kamar yadda ya saka mata tana kira amma ya kasa picking saboda har lokancin Samasama yake jin kanshi kuma muryarshi da yayi magana zata nuna halin da yake ciki. Ganin baiyi picking ba yasa ta hakura kawai Amma hankalinta yana gunshi. A haka har dare yayi baiyi returning call din ba. Seda su Ahmad sukai bacci sannan ta tuna da safe Jawad yace mata yana kaduna Don haka ta Fara kiranshi.
Friend Yaya Junaid Yana nan?
Ta tambaya yana picking,
Kya Bari mu gaisa ai, Yana dakinshi na kai mishi ne?
Da sauri tace
Yes please!
Kashewa yayi ya nufi dakin da Junaid yake, Yana zaune kan carpet ya kurawa screen din system dinshi ido ga abinci Kan tray an jera Amma bashida appetite din ci. Dago idonshi yayi Wanda ya fara washewa Daga jan da yayi ya dubi Jawad da ya zauna gefenshi yace
Sulaim tace na kawo maka waya zatai maka magana.
Kanshi ya gyada cikin sanyin murya yace
I'll call her. Seda safe.
Sallama yayi mishi ya tafi shi kuma ya kashe system din ya koma gado don kiranta, har ta gaji da jira ta Fara chatting kiranshi ya shigo, wani sanyi taji ya mamaye dukkan jikinta babu shiri ta saki murmushi sannan tayi picking.
My Dove, I'm sorry
Dukda bata san dalilin da yasa yake kiranta da Dove ba, amma she have already fallen for the name! Bakinta ta turo tace
Bakaga call dina ba tun dazu? Baka kira kace kaje lapiya ba, Muhammad suna ta tambayarka.
Murmushi yayi me sauti Wanda seda Tajiyo hakan yasa ta sake fadin
Murmushi kakeyi ma ko?
Hannunsa ya rufe bakinsa dashi yace
Come-on Dove nace I'm sorry ko, nazo na samu abubuwan da suka cushe min Shiyasa. Duk yaran sunyi bacci?
Kanta ta gyada tace
sunyi bacci, ina Mami
Mami tayi bacci, smile mana
A'a
Ta fada Tana bata fuska, hakan yasa yayi dariya a hankali wadda ta ratsa sulaim har Seda ta sauke ajiyar zuciya. Haka sukai taba hira kafin yace
Kiyi bacci, nayi magana Za'a zo daukarku gobe Inshaaa Allah. Nima very early zan dawo. Good night?
Kanta ta gyada kamar yana kallonta tace
OK, night.
Daga haka sukai hanging kowanne zuciyarshi fes, musamman Junaid da yaji hankalinshi ya Dan kwanta Don Yana ganin bazai samu matsala da ita ba, Mami ce damuwarshi.
Washegari bakwai ya fito cikin shirin tafiya, a parlor Baba ya samesu suna kallon news din safe a Aljazira, seda suka gaisa yace
Zan koma Kano.
Baba ne yace
Da wurwuri haka? Abinci fa?
Kanshi ya girgixa yace
Se naje zanci.
Kai Mami ta girgixa tace
Zauna yanzun Za'a kawo breakfast.
Bai musa mata ba haka ya tankwashe kafafunsa Yana kallon news dukda hankalinshi Yana kan maganar da sukai jiya amma su kuwa hirarsu suke tamkar basu san dashi a gurin ba. Ba a jima ba aka kawo breakfast babu musu yaci sannan ya Mike yace
Zan wuce se next week zan kawo su duka.
Baba yace
Allah ya tsare
Mami tace
Ayi tuki a hankali, ka kula da kanka.
Murmushin jin dadi yayi sannan ya aje musu envelope ya kara musu sallama a ranshi Yana fadin
Mami is using son da nake yiwa Sulaim ta hukunta ni akan tafiyar Subay'a.
Unexpected right? Mami ta bamu mamaki har ni kaina? Na aza zata amince Amma taki ga Baba yaki magana. So Wacce shawara zaku bawa Junaid? Yana jira.......see you later
Team #Junaid and Sulaim#
Shatuuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
34
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
CYPRUS
Kwanaki bakwai kenan da saukarsu Subay'a birnin na Cyprus, tuntuni aka kama musu Dan apartment me dakuna uku dake Sulma itada mijinta sukaje shima zaiyi wani course a can. Se apartment din da take yana facing nasu, kuma bashida Nisa zuwa makarantar da suke. Tunda suka sauka a garin gaba daya hankalin Subay'a ba'a kwance yake ba, Dama da safe jirginsu ya sauka Don haka suna zuwa suka Yi 'yan gyare gyare suka kwanta dan huce gajiya amma Subay'a se juyi kawai take ta kasa baccin, hankalinta ya tafi akan Junaid, ko me zai yi bayan ya tarar ta tafi, ko ina yaranta suke. Haka dai tayi tayi har bacci ya samu ya dauketa. Se dare suka fita dan ganin gari, to a Wannan ne ma zamu ce ta saki jikinta Don garin ya burgeta Sosae da sosae, se eleven suka dawo nan suka baje a parlor suka ci abincin kowacce ta kira mijinta ganin haka yasa Subay'a sulalaewa zuwa dakinta Don nufin kiran Junaid sede tsoro ya hanata yin hakan.
Washegari suka shirya kowacce ta nufi department dinta don Fara daukar lectures amma Subay'a babu Abinda take ganewa bata fahimtar komai dukkan hankalinta yana Nigeria, ga wani ciwon mara da takeyi me