Showing 45001 words to 48000 words out of 131263 words
Chapter 16 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt
Kara missing call din nashi. Junaid ta Fara kira bai dade yana ringing ba yayi picking
Wayan a silent yake ne
Ko kuma kina ta surutu ba
Ya fada Yana kallon Ahmad dake gefenshi. Murmushi tayi tace
A'a ne fa.
Shima murmushin yayi yace
Anyways, ga sako nan ki basu ki gaishesu ni na fita
Kallon envelope din tayi tace
Mungode Allah ya saka da alkhairi Zasuji, a dawo lapiya.
Kai ya gyada yace
Akwai Abinda kike so na taho miki dashi?
Kai ta girgixa tace
A'a, se kun dawo.
Daga haka sukai sallama ta dauki envelopes din batareda ta buda ba ta mimika musu tace
Yaya yace a baku
Duka sukai godiya suka zura cikin handbags dinsu nan hirar ta koma kan Junaid wanda Aimana ce kawai tasan shi amma su basu taba ganin shi ba
To Sulaim ki aureshi mana kiga yadda yake kula dake Yana kaffa kaffa da ke.
Khulthum ta fada , Sulaim Baki bude tace
A gidanshi muke fa matarshi tana nan, wayace muku wai soyayya muke.
Tsaki Khairi tayi tace
Ki cigaba da denying abin ai a bayyane yake, ko tone din muryarki ansan akwai magana.
Haka sukai ta yi mata se ta sharesu kawai, ana La'asar aka cire kunshi yayi kyau sosae suka dinga mamakin dama haka Khulthum take dama tanada wannan talent din amma take neman tsayawa dogara da namiji. Wajen 5pm aka zo daukarsu Khairi zata bi Khulthum Hu zai sauke ta a BUK, yayinda Nu'uman yazo daukar Aimana. Suna fitowa tace
Muje kui sallama da Anty.
Parlonta suka nufa Sede Tun kafin su bude kofar muryoyi Ke tashi Wanda ya tabbatar musu tayi baki, da sallama suka shiga yan uwanta ne dukda wannan ne Karon farko da Sulaim ta gansu dukkansu Amma tana ganinsu jefi jefi suna Zuwa, mutane ne yan rainin hankali da suke ganin kowa bai iya ba su kadai suka iya to haka suke, ga kallon wulakanci. To tunda suka shigo suke binsu da ido suma su Khulthum haka, tare suka gaishesu Subay'a dake zaune tace
Ya akai?
Sulaim ta kalleta saboda taji haushin tambayar, se ta kyaleta tace
Zasu tafi ne.
To
Kawai tace takaici kamar me haka Sulaim taji suna fitowa Surayya tace
Subay'a wannan yarinyar ce kanwar Junaid din?
Subay'a ta dago tareda fadin
Ita ce fa
Kan babban bala'i! Kika barta take Zaune a gidanki
Sulma tayi saurin fadin
Me yasa kuke haka itada gidan dan uwanta.
Samina tace
Yaya Sulma dan Allah Kiyi shiru, Amma Yaya Subay'a this is carelessness, how sure are yarinyar ba spy bace.
Tsaki Suhaila tayi tace
Ke ta spy kike, taje tayi ta leken asirinta who cares? What matters kada ta juyawa Junaid kwakwalwar kanshi, kinga kyau kamar Aljana.
Didim!!! Gaban Subay'a ya fadi kada fa hakan ta kasance, kada fa turo ta akai don a aura mishi ita!
A'a Kada kui haka, Sister kada ki manta maganar da mukai dake, babu wani alaka tsakaninsu amma idan kinji shawarata kenan kada ki tada hankalin ki a banza kuma yazo baida niyya yaga Abinda ake gani a tare da ita.
Samiha tace
Gaskiya kika fada Sulma sede ina ganin kiyi watching yarinyar, saboda kallon da take miki kadai Irin na baki gabana haka take miki.
Dakyar Subay'a ta hadiyi mugun yawu tace
Kallon da takeyi min kenan Tun zuwanta gidannan, akwai wasu abubuwa tattare da yarinyar na rasa Meye kawai idan na ganta gabana faduwa yake, Wallahi tsoro take bani.
Wata ashar Samina tayi tace
Haba Yaya Subay'a Kada ki badamu dan Allah wannan yarinyar? Da Ummin Yaya Safina I'm sure ta gurmeta zata na fadar miki gaba, idan ta kawo miki raini Kici ubanta shi ne kawai.
Haka sukai ta zugata ita kuma baki daya ta duburburce taki fada musu ainahin signs din data gani saboda gaskiya hankalinta ya kasa kwanciya da Junaid.
A waje kuwa Hu ya fara isowa suka gaisa sannan ya dauki gimbiya da khairi se BUK, suna nan tsaye Aimana tana Bata labari Nu'uman ya iso, yana parking ya fito ya zo inda suke tsaye suka gaisheshi ya amsa kafin yace
Sulaim nace ina sonki kawar ki ta Hana ta kankane ko ina.
Dariya sukai saboda yadda yayi maganar tamkar irin kana son Abu an hanaka, Sulaim tace
Kayi hakuri I'm already taken!
Aimana ta kalleta da sauri amma se ta kawar da kanta saboda tasan karya tayi amma a yanxun tana ganin har Yaushe zata cigaba da Tara samari kuma batajin son su a ranta, don ita tana ganin zuciyarta..... Se kuma tayi shiru yayinda Nu'uman yayi murmushi me ciwo yace
Ban fidda rai ba, ban hakura ba amma inason na zama admirer from the side, in karba number ki?
Kanta ta gyada kawai she can't say no, yayan Aimana ne dole tace
Babu damuwa, Aimana ki bashi.
Murmushi sukayi sannan sukai sallama suka barta a gurin har kewarsu ta Fara damunta. Tadan jima a tsaye kafin ta shiga ciki bata bi takan kowa ba ta wuce dakinta ta gyara sannan ta yi tilawa.
Karfe Sha daya da Rabi na dare daidai lokacin Sulaim ta dade da yin bacci wayarta ta Fara ringing, da kyar ta janyo wayar ta kara a kunnenta Sede muryar Salim tasa ta bude idonta da kyau
Princess Nayi laifi ne?
A hankali cikin bacci tace
Bacci nake fa!
Seda muryar ta ratsashi hakan yasa yace
Ooops sorry Yi baccinki.
Bata jira ba kuwan ta koma ta kwanta se bacci abinta. Washegari akai last paper kuma babu laifi tayi dadi, suna fitowa Khairi ta wuce Jalingo itama Aimana ta wuce gida ya rage se Sulaim da Khulthum the bussoms kenan.
Yawwa Khulthum akan maganar Ashir ne ya kuke ciki.
Tsaki Khulthum tayi tace
Rabu da wawa, wai yaki hakura
Kince ya hakura ne?
Eh mana, baya cikin type dina Sulaim so kike na yaudareshi? Na fada mishi gaskiya ni bazan aureshi ba.
Haba Khulthum yace yakai kudin me kuke cewa abin?
Sulaim ta fada Tana son taunawa
Na gani ina so, Twenty thousand ce fa! Yazo ya karba abarahi .
Khulthum ni kawar ki ce, ke kinfi karfin kawa gurina you the sister I never had, ki nutsu ki Daidaita kanki rayuwar duniya batada tabbas a wannan zamanin har kika samu kamar Ashir kike wulakantawa mutum me bright future ahead? A'a fa ki guji dana sani.
Bazan taba yi ba, Dan Allah Sulaim ki kyaleni da zancen Ashir hakanan kodai asiri yayi miki ne?
Dariya sosae Sulaim tayi tace
Ina ganin kamar ya cancanci ya zama mijinki ne Shiyasa na dameki, to ki fitar da Yusuf kui aure mana
Tsaki Khulthum tayi tace
Baida arzikin mijin da nake burin aura, wayeshi? Wa ya sani? Waye ya sanshi? Kin gane kuma ni yanzun babu aure a tsarina.
Kai Sulaim ta girgixa tace
Wanne irin miji kike so
Murmushi me kyau tayi tace
Me kudi, shekarunshi kamar talatin bai taba aure ba haka bayada yan mata, bayason mata ma baki daya, kyakyawa wanda yan uwanshi basa zaman kasar Balle su saka mana ido, me hadadden gida da mota. In takaice miki Handsome in a flashy car and a top rich Man..... Shi ne burina.
Shatuuu ♥️
[7/17, 10:44 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
20
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*Where are all the fantastic, fabulous, awesome and gorgeous Damsels of SHATUUU's KINGDOM and Damsels of Maman Mama novels..... Take This page as a token of appreciation.... Thank you very much ladies for always having my back, for always being there for me..... You're such a darlings*
Idanunshi a kulle tamkar wanda yake bacci amma kwatakwata ba baccin bane cikin idanunshi hasalima baya tunanin a Wannan Daren akwai possibility shi din yayi bacci saboda yana cikin mawuyacin hali, Yana cikin tsananin tsukun rayuwa wanda soyayya ta jefashi a ciki, soyayya me zafi wadda take neman tayyar mishi da hankalinshi take neman wargatsa mishi Duk wani karfi da a da yake tunanin yana dashi to Amma soyayyar Sulaim ta nuna mishi shidin ba kowa bane ba kuma komai bane. Idan zai iya tunawa jibi ne Sulaim zata cika eighteen years da haihuwa he remember vividly lokacinda aka haifeta lokacin baifi lokacin shekarunsa wajen sha shida don ya Kare secondary school dinshi, through out rayuwarshi yayi tane akan bata kulawa ta kanwa bai ko taba tunanin zai rikeda ya zama wannan zazzafan son ba, gashi wadda yake dan ita bata masan halinda yake ciki ba sha'aninta kawai take abinta babu wata damuwa a tattare da ita amma shi gashi nan walwala da sukuninshi gaba daya soyayyar Sulaim tayi tafiyar ruwa dasu. Kwanciya ya gyara ya kalli agogon dake jikin bango karfe takwas da rabi ba wani Dare bane yayi hakan yasa ya janyo wayarshi ya fara kiran Mami, lokacin Mami tana zaune itada Imratu wanda suka dawo jiya daga Saudia, likitoci sun tabbatar musu lokacin haihuwa ne baiyi ba amma babu wani abu dake damunsu dukda haka se suka basu guidelines da zai boosting fertility din nasu, to Sede ayi fatan Allah ya sa a dace.
Mami barka da dare
Barka dae Uban Sulaim
Dama Duk lokacinda ta yanke abu akan Sulaim din shikuma ya nuna rashin amincewar shi haka take ce masa, kowa yasan Mami tace ayiwa Sulaim booking jirgi ta tafi Kebbi to yau ya kamata a gama komai se aiki ya rike Junaid bai samu yaje ba ya kirata akan ta tafi wani satin Tace dashi ya Bari ta turo Ja'afar ya kaita a mota, aikuwa Junaid yayi tsalle ya dire yace babu Wannan maganar zai bar Duk Abinda yake ya kaita da kanshi, to kafin su gama magana tayi Baki tayi mishi sallama akan zasui magana da daddare. Murmushi yayi kayatacce yace
Kai Mami wai Baban Sulaim
Baban Sulaim mana, yanzun ni na rigada na turo Ja'afar Don Tun shida na yamma ya iso kano, gobe da safe zasu wuce.
Kanshi ya dafe yana tunanin me zaiyi kuma shifa tafiyar ce baki daya baya so Sulaim tayi ita da Ja'afar amma Mami ta kasa fahimta bai sani ba Mamin tun dadewa ta harbo jirginsu ta rigada tasan cewar akwai kakkarfar soyayya tsakanin Junaid da Sulaim dukda a farko Junaid ne kadai amma daga baya se ta fahimci Sulaim ta afka, tayi farin ciki sosae tunda tasan waye Junaid ita ta haifeshi Duk cikin 'ya'yanta babu mutum me tsananin hakuri, kauda kai da juriya Irin Junaid tasan idan har ace Jabir Ke auren Subay'a da tuni gayyar ta watse amma daidai da rana daya bai taba mata complain akan zamansu da ita ba dukda tasan cewar a takure yake sede tayi alkawari kwaya daya duk ranar da ya kawo wata zai aura zata Goya mishi baya Sede a yanzun tana tantamar idan zata yarda da wannan abin kasancewar su biyu Junaid da Ja'afar sunyi tarayya akan son Sulaim
To Mami Allah ya kaimu goben.
Sanyin halin Junaid na Kara masa matsayi cikin zuciyar ta Mamin, tasan baya so amma bazai mata musu ba.
Ina sulaim din take.
Dan dariya yayi yace
Mami tana dakinta ina nawa sede ko idan za'akai mata wayar ne?
Itama murmushin tayi tace
Zan kirata kawai a gaida Subay'a da yara.
Daga haka sukai sallama ya kifar da wayar shima ya kifar da kanshi, Baki daya yau ranar Bata masa dadi ba ya yini cikin aiki a office ga wannan ya kunno kai, ya zaiyi kenan? Zuwa zaiyi ya tunkare ta da zancen? What if it happens tanason Ja'afar? Se ya zama me son kanshi bayan yasan idan Ja'afar ne zai iya dedicating mishi ba Sulaim ba ko Abinda yafi Sulaim dinne? To shi Yana babba me yasa yake son kanshi da Yawa? Tambayoyi barkatai wanda babu amsarsu kuma suke neman tarwatsa kwakwalwar kanshi saboda kanshi ya fara Sara mishi, Sede wata zuciyar tace babu yadda xa'ayi ta sadaukarwa da Ja'afar abar kaunarta idan kuma hakan ta kasance bazata taba hutawa ba kuma bazata yafewa Junaid din ba kuma se Allah yayi musu hisabi on the resurrection day!
Cikin hakane Subay'a ta shigo tayi kwaliyya bawai iya ta fuska ba har a jikinta, tayi kyau har ta gaji da yinshi, babu Abinda Ke tashi jikinta banda kamshi me mutsar da kwantar da zuciya Sede a yau babu Abinda Ke bakanta ma Junaid rai Irin ganin Subay'a saboda yana ganin rashin kulawar ta gareshi yasa shi cikin wani hali, saboda lokacin ai son baiyi karfi ba Tunda har idan yana tareda Subay'a yakan manta da Sulaim amma saboda rashin bashi muhimmanci se Wannan implantation na kaunar Sulaim wanda aka dasa shi can kan Septum na zuciyarshi seda yayi yado ya taba Ventricles, Atrium, bundle of hiss, inferior and superior Vena cava, Aorta da dukkan wasu jijiyoyin dake zuciyarshi har yakan ga Subay'a ta rikide mishi ta koma Sulaim.
Gefenshi ta zauna ta Daura hannunta Kan hannunshi ta zuba idanunta cikin nashi tana karanto halinda idanun ke ciki, taga So me karfi wanda ba mallakin ta ba, taga fear na kar na rasa Wannan abin, taga haushi na wannan ta watsar dani, idanunshi masu haske sunyi ja alamar yana cikin wani hali.
Better half!
Ta kira cikin wani salo wanda duk karfin zuciyarka se ka jishi har kwakwalwar ka, Balle Junaid that's helpless wanda bashida makoma soyayyar Yarinya mitsitiya tana neman maida shi rago. Ya kalli Subay'a wadda idanunta suka Fara maiko alamun taruwar kwalla
Better half Meye ke damunka? Meye matsalar ka? Yaushe rabon naga kayimim murmushi? Baka nemana, ka daena cin abinci. Dan Allah ka fadamin ni matarka ce Bakada kamata.
Sosae yake kallonta saboda yaso abinda take fada gaskiya ne, amma karya take, ina ya zama better half dinta ta ina? Da ta bashi muhimmanci da bazai shiga Wannan halin ba. Baice ko uffan ya Mike ya fada bayi kamar five minutes ya fito Fuskarshi da kanshi na digar da ruwa, seda ya goge kafin yace
Abinci kikazo ki kirani mu ci ko? Let's go
Haka ya fice ya barta a gurin, hawayen suka samu damar sakkowa daga idanunta. Waye ya maida mata miji haka? Wayake so har haka? Ko dai waccan yarinyar yake so? Da Wallahi ko ta tsiya ko ta arziki se ta bar gidan. Hawayen ta goge tabi Bayan Junaid wanda har ya zauna yayi serving yaran dashi kanshi, Sulaim Bata gurin bai kirata ba bai kuma damu ba a cewarshi kenan amma baki daya hankalinshi Yana kan me takeyi?!
Tana kwance ta tasa system a gabanta tana kallo, ita bata kallon Korean dramas Amma Tunda ta dawo Nigeria Jawad ya kwadaita mata su gashi yanzu batada abin kalla se su, yanzun ma wani Empresski take kalla ko nace maimaici Don ta jima da kallonshi amma yadda yayi kyau yasa take maimatawa, ta Gama shirinta tsaf gobe kawai take jira ga dokin ganin dangin uwa ga dadin sun shirya da Ja'afar zaayi tafiya tare Sede acan kasan zuciyarta akwai wani abu da take ji Marar dadi, Ta rasa ko meye abin amma Lokaci guda har yana son yayi overcoming baki daya farincikin da take ciki, lokuta da dama takanji inama ace itada Babban yaya zasu tafi, wannan murmushin nashi, wannan muryar very deep amma me dadin saurare, me kuma mutsar da Mai laifi, wannan idanun masu haske tamkar an disa musu abu a ciki, wannnan sharp and piercing looks din nashi masu maidata jin she's helpless! Kai everything about Junaid is just perfect.... Ta jima tana mafarkin inama ace shi ne Ja'afar, Ja'afar ne shi, Tasha ayyana idan ace Itace Subay'a she will never ever mess up kamar yadda Subay'a ke barin damarta. Tamkar karfe da magnet haka Sulaim taji mummunan force of attraction haka cilak ta Mike ta doshi kofa sede Allah ya taimaka tayi assessing kanta Ashe half gown ce jikinta da sauri ta dawo ta cire rigar ta dauki abaya ash ta saka ta yafa mayafin ta fito batareda sanin meye dalilin fitowar ba ashe she wants to see him, she wants to see all Abinda ta lissafa akanshi. Almighty Allah so kind, da idanun ta Fara tozali Bata jira ba ta sakar mishi tattausan murmushi wanda for life ba zai taba manta wannan murmushin ba, shima bai bata lokaci ba ya mayar mata da wanda ya fiahi Lokaci daya suka runtse idanunsu gam! Wani Irin chemical reactions, chemical bondings ya fara taking place, within seconds magnesium ya hadu da sulphate, hydrogen da oxygen, sodium da chlorine and many more. Ina Subay'a? Ta tafi daki amsa call din hajiya!...... Sorry kawata Kinyi missing.... Lokaci daya suka bude idanunsu wanda suka sauke akan junansu Sede lokaci daya kunya ta lullube Sulaim meye haka takeyi? Meye ke damunta? Juyawa tayi zata koma daki tamkar an fisgo Junaid yace
Sulaimi!
Cak ta tsaya tana kokawa da numfashinta sboda yadda Sautin muryarshi ya illata mata oxygen supply dinta Baki daya, a hankali ta juyo ta dubi inda yake bai tashi ba Sede dukkan hankalinshi na kanta, da ido ya mata alaman taje gareshi haka ta tafi cikin nitsuwa ta zauna inda ta Saba zama, idanunta a kasa idanunshi masu huda mata jiki da tarwatsa dukkan kuzarinta suna kanta hakan yasa ta takura matuka shi kuma kallonta yake yana mamakin kanshi, shifa ko Subay'a ya rantse da Rabbul Ka'aba lokacinda yake sonta baiji Rabin Abinda yake ji akan Sulaim ba, yarinyar ta shammace shi da yawa, ta shiga rayuwar shi tayi masa karan tsaye, tayi ma zuciyarshi shigar ba zata....... Abincin da ya Fara ci ya tura Mata yace cikin sassanyar murya
Kici!
Wannan muryar ba wadda xaayiwa musu bace hakan yasa ta dauka ta Fara ci shi kuma ya maida kanshi kan call din Ja'afar da ya shigo masa daidai wannan lokacin. Farin cikin da ta tsinci kanta a wannan Daren ba shida na biyu, Rana ta farko ta Fara tuhumar kanta me take ji game da Junaid? Kada ya kasance zancen su Aimana su Khulthum su khairi ya tabbata, tabbas da zuciyarta ta zalunce ta Tunda babu possibility shidin zai so ta...... Amma fa wannan tunanin Sulaimi ne...... To bangaren Junaid Wannan Daren matarshi