Showing 12001 words to 15000 words out of 131263 words
Chapter 5 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt
murmushi yayi me sauti har tajiyo shi
Ina amsawa, kije Kici abinci.
Pouting bakinta tayi tace
To Yaushe Xaka zo.
Da sauri ya zaro idanunshi amma yaji dif ta kashe wayar saboda cajinta ya dauke
Shit! Ya furta
Shatuuu ♥️
[6/25, 4:12 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
7
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣shatuuu095@wattpad
Tana tsaye gefen titi hannunta yana dauke da Leda baka da tambarin Sahad stores, Tana Sanye da skirt da riga na atamfa purple da pattern na mint green, yayi mata kyau, kanta ta yane shi da mint green mini veil, hakan ya bawa surar jikinta fita dukkan wani shape seda ya bayyana. Tana nan tsaye wata flashy car ta wuce, se kuma a hankali akayo reverse ya dawo daidai saitin inda Khulthum ke tsaye yayi wining glass dinshi kasa....Huzaifa ne the rich brat shidin yaron wani senator ne a Zamfara Yana level 4 a engineering cikin BUK , kana kallonshi kaga kwallo wanda duniya take damawa dasu. Murmushi yake tayi yace
Abokaina suna kirana lucky Hu saboda I'm always lucky, luck is always by my side. Gashi mun kara haduwa.
Kallonshi tayi batareda ta canja yanayin fuskarta ba tace
Amma kanada naci
Dariya yayi yace
Wanda ya nace shi zai dace ko ba haka hausawa sukace ba ?
Dauke kanta tayi, shi kuma se ta bashi dariya ita a dole Se ta ja aji ,
Ki shigo bai dace rana tana dukan kyakykyawa kamar ki ba.
Bude gaban motar tayi ta shiga yayinda murmushi ya kwace masa, suna tafe Yana mata hira a haka har ta dan fara warewa, bai tambayeta inda zataje ba itama sanyin AC da daddan freshener yasa ta manta, se ganinsu tayi a kofar More and More, dubanshi tayi tace
Banan zan zo ba.
Irin dariyar shakiyanci yayi yace
Ooops nayi tunanin na dakko ki ne we're on a date, amma dukda haka muje ko abu me sanyi ne kisha.
Ledar ta aje cikin motar sannan suka jero, mutuniyata ta saki fuskarta dama Irin rayuwar da take so kenan, rayuwar jin dadi da yawace yawace kamar yadda take ji take kuma gani idan aka dauke ta gidan yan gayu kunshi.
Tunda suka shiga suka samu guri take ta juye juye hakan ya so bawa Hu dariya amma instead se ya musu placing order. Yana zama wayarta ta Fara ringing alamun kira na shigowa, se taji kunyar fito da purse dinta saboda yadda ta kode, dauke kanshi yayi hakan ya bata damar daukowa Sede take yanayinta ya canza saboda Ashir ne me kiran, silent ta maida wayar a haka aka kawo musu Burger da chilled Smoov, itadai tasan tana kallon abubuwan a kofar bakeries haka amma bata taba tasting ba, amma haka ta danne ta dinga ci da kadan kadan har suka gama sannan ya bada bill dinsu suka fita, a motar yake ce mata
A level nawa kike ne?
Dagowa tayi tace
Level 1 nake.
Kallonta yayi kafin ya maida titi yace
Shiyasa Naga Baki gama sakin jiki da mutane ba.
Dan dariya tayi a haka har suka iso wani ice cream joint na cold stone yayi musu ordering suka zauna cikin motar suna sha yake mata bayanin kanshi tunda taji yace babanshi senator ne kuma d only heir of them tasan tayi babban kamu. Gaba daya Khulthum ta manta cewar wai ta fito Kai dinki ne seda Hu yace
Baby da me kika fito yi ne.
Bakinta ta rufe tace
Kasan saboda yadda ka shagalta Danni I totally forgot dinki zan kai.
Dariyar shima yayi yace
Lucky Hu!
Bai tambayeta inda take Kai dinki ba se kawai taga sun tafi wani tailoring centre a nan wajen new hospital road, yawancin duk budurwar da yayi nan yake kaita a mata dinki, irin designers dinnan Don haka Khulthum tayi shiru Tana tunanin yadda zata iya kai dinki gurin, Amma ta waske suka shiga gurin, yadda suke da mutanen gurin ya tabbatar mata akwai sabo sosae tsakaninsu within 30 minutes an gama komai Harda billing kuma take ya biya through POS hakan ya kara mishi daraja da martaba idanunta. Suna fitowa ana kirayen sallah maghrib hakan yasa yace
Bari muje na kaiki gida, yau munsha yawo.
Murmushi tayi tace
Gaskiya kam.
Suna tafe Yana mata tambayoyi saboda yadda taga yanada kudi kuma tasan ba wani abu bane yasa ta fada mishi Daga inda take, baiyi mamaki ba saboda ya Lura dukkan guraren da sukaje are new to her, ko da wannan ma zai shawo kanta Tunda akwai son abin duniya tun a yau yayi marking.
Seda yayi mata takeaway me kyau kafin ya nufi inda ya Dakkota lokacin sallar maghrib ta wuce ana shirin sallar ishai.
Nuna min Kwanar da zamu shiga.
Kanta ta girgixa ba dadi ranta tace
Mota bata shiga
Se taga bai wani damu ba hasalima wayar ta ya karba Bayan ya gama jujjuya ta sannan ya saka numbers dinshi yayi saving mata kafin ya kirayi kanshi shima yayi saving a tashi. Daga haka sukai sallama ta fito Tana jin tamkar kada ta fito, kamar yadda kullum take tafiya haka ta cigaba da tafiyarta sede tana zuwa tsakiyar layinsu taji an sha gabanta, idanunta ta dago don ganin wanda yake muradin zagi, se kawai taga Ashir tsaye, yana tayi mata wani Irin kallo me Cikeda tuhuma da zargi. Itama kallonshi take tana karantar mood ensa, Baki daya ranshi a bace yake. Ganin haka yasa ta saki murmushi tace
D kayi ta jirana ko? Wallahi.......
Hannu ya daga mata hakan yasa tayi tsit yace
Waye ya fita dake ya kuma dawo dake a mota? Meye Sanye jikinki haka
Ya fada Yana nuna bingilin mayafin da ta yafa a kanta Wanda iya wuya kadai ya tsaya, wareshi tayi tace
Ni? Akace an fita dani? Wa na sani? Yan unguwa nan munafukai ne.
Se kawai yayi murmushi ganin yadda Lokaci daya take raina masa hankali, bai kuma cewa komai ba ya bata hanya Don ta tafi sede ko an inch ta kasa takawa hakan da ya gani yasa yace
Kije gida Seda safe. Yana fadar haka ya buga Lifan dinsa within an eye blink ya bar gurin, itama cigaba tayi da tafiyarta har ta isa gidan tundaga zaure taji Mama tana cewa A'isha
Kin Dakkowa Khulthum Kwanukan ta ko? Se ta dawo baki wanke ba tazo Tana mana diban albarka.
A'isha dake zaune kofar daki Tana yankan farce da fitila tace
Tai ta zuwa mana ina ruwan wani.
Kafin Mama tayi magana se suka tsinkayi sallamar Khulthum, inda Mama kawai take ta kalla tace
Na dawo Mama.
A... A.... Sannu da zuwa.
Imagine! Wanann ne Karo na farko da Khulthum ta fita takai isha'i a waje, ba tareda sunsan tun asali ina taje ba kuma yanzun babu Wanda zaice Daga ina take.... Akwai sakaci sosae na rasa dalilin da yasa iyaye irinsu Ke sakaci da whereabouts din yaransu, talauci ba hauka bane is a trial and test that are never meant to be easy. Saboda Kai talaka ne Seka bar yaranka sakaka kamar tumakai kada ka manta cewar yara Allah ne ya baku amana and you must account for every deeds da kukai a nan duniya.
As expected zata yi magana kan Kwanukan ta amma ta share ta shige daki ta cire kayanta sannan ta fito tayi wanka, tana fitowa mama tace
Khulthum yaronnan Ashiru yazo nemanki Tun rana.
Juyowa tayi tace
Mun hadu dashi, anyi abinci ne?
Ta tambaya Tana duban inda kitchen din yake,
Eh anyi, a zubo miki ne?
Kanta ta girgixa tace
A'a
Daga haka komawa daki tayi inda ta tarar da A'isha tana kife kwanuka, kamar bazata tanka ma taba se kuma ta kasa kasancewar hakan ba halinta bane tace
A'isha waye ya dauki Kwanukan nan?
Banza Aisha tayi mata hakan kuwa ya harzuqa ta Tace
Ke dan ubanki ba dake nake ba
Inkana son zagi nemi yaran ghetto na fada ina kallonsu, juyowa Aisha tayi tace
Kada ki kuma zagin ubana
Ubanki
Ta bata amsa almost immediately,
Na zageshi akwai abinda zaki iya yi ne?
Dariya Aisha tayi tace
Mutumin da bai bar babarshi ba ai ba abin mamaki bane Don kin zagi ubansu, Sede ki sani wanda kike zagi shidinne Gatanki ba gantallalun danginku ba.
Hey! Khulthum case, dama ance Baki yasan me zai fada amma baisan Meye martani ba. Taji Ciwon abin hakan yasa ta durfafe ta suka fara kokawa, Dama Tun suna yara Khulthum ce Marar karfi, yanzu haka ma Bata canza zani ba, kafin Mama tazo Aisha ta jibgi Khulthum gashi Daga ita se zanin wanka wanda tuni ya nemi nashi gurin.
Da sauri ta yar da wayar tare da fitowa parlour a sukanne, yadda ta bude kofar kadai will tell you Abu take so, gaba daya idanu Baba da Mami suka zuba mata hakan yasa se spirit dinta ya ragu, ta tako a sannu ta zauna daidai kafar Baba Tana gaisuwa, shima da dukkan faraa ya amsa mata yana tambayarta karatu da kuma su Junaid and family,
Duk suna lapiya sunce a gaisheku.
Murmushi yayi ya cigaba da kallonshi se Sulaim tace
Mami ina Wayarki?
Dakina
Daga haka ta koma dakin Mamin ta dakko wayar ta zauna gefen gado ta kuma kiran Junaid, Duk tunaninsa Mami ce amma yana jin muryar Sulaim ya gyara zamanshi tare da sake rike wayar a ranshi yace
This girl will be the death of me!
Are you there?
Ta furta mishi,
Am there Sulaimi, ya kikaje?
Alhamdulillah!
Ta bashi amsa se kuma sukai shiru baki daya hakan yasa sukaji tamkar gaba daya globe ya daina rotating round the universe, tamkar Lokaci ya tsaya ne cak! Seda Junaid yace
Have you eaten?
He always ask that, bata son Meye hadinshi da abinci ba, kanta ta gyada tace
I've eaten, abincin Mami kayi missing.
Dariya ya danyi yace
Nima Wifey ta bani me dadi
Dif taji Abu ya tsirga mata Wifey ta maimaita kafin tace
I've to go zanyi bacci.
Kafin yayi magana ta kashe wayar se taji duk yayi spoiling mood dinta wai Wifey! Ta dade da wayar hannunta tana tuhumar kanta dalilin da zatayi fushi Dan ya ambaci matarshi, to idan bai ambaci Subay'a ba Sulaim zaice. Haka tayi ta reminiscing abin cikin ranta a haka Mami ta iske ta, ta dade a tsaye Tana kallon ta ba tareda Sulaim din tasan da shigowarta ba. Taba ta tayi hakan yasa tayi firgigit tace
Mami.......
Kallon da Mamin tayi mata yasa ta kasa karasa Abinda zata fada se sunkuyar da kanta da tayi. Amsar wayar daga hannun ta tayi tace
Kije kiyi shirin bacci I know you must be tired ko?
A sanyaye ta Mike batace komai ba ta fita a dakin yayinda Mami ta shiga call log dinta Eldest ta gani wanda ya tabbatar mata Junaid Sulaim ta kira. Call duration ta duba wajen 7 minutes hakan yasa taji abu ya darsu a zuciyarta amma koma dai Menene she will keep eyes on both of them.
Shatuuu ♥️
[6/27, 3:29 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
8
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Daidai bugawar agogon dake Makale jikin bangon dakin daidai fitowar Subay'a daga parlonta, tana sanye da Abaya beige color tayi rolling da milk din mayafin da sukaxo tareda abayar. Junaid na zaune kan two seater gabanshi system dinshi ce akan center table se kafafunsa da ya daura akai. Aiki yake sosae Don Tun Azahar yake Abu daya sallah ce kawai ke tashinshi. Tun kafin ya san da zuwanta turaren da take using me dadin kamshi ya bayyana kanshi, lumshe idonsa yayi a hankali kafin ya bude su ya zube a kanta, ko bata fada ba yasan fita zatai saboda kayan dake jikinta,
Papa aikin ne har yanxu?
Ta tambaya Bayan tayiwa kanta masauki a gefenshi, kanshi ya gyada tareda dagowa ya furzar da iska me huci yace
Wallahi kua Mimi dake haka yaran Ke ce mata.
Shagwabe fuska tayi wadda tasan baya taba resisting ta saka hannunta a kan sumar shi wadda babu gashin ma saboda yadda ake saisaye ta akai akai. Tace
Sulma ta haihu an hour ago.
Dagowa yayi Sulma sister Subay'a ce tare akayi musu aure shekara takwas kenan amma bata taba haihuwa ba se yau shi baisan tana da ciki ba ma. Murmushi ya saki yace
Mashaa Allah Alhamdulillah! Me ta samu?
Baby girl!
Addu'a yayi sannan ya cigiba da aikinsa duk da yasan abinda ta ke nufi amma se ya share ta. Ta kusan 5 minutes ganin idan ta zauna haka Itace a cuce hakan yasa tace
Papa ina son Zuwa ne.
Bai kalleta ba yace
Se da safe is already late yanxun.
Baki ta turo tace
Haba mana Honim har na fadawa Yaya Suhaila tazo mu wuce tare.
Pen din hannunshi ya aje tare da rufe system din ya dago ya zube idonshi cikin nata, kasa jurar kallon tayi hakan yasa tayi kasa da kanta, babu alamar wasa yace
Subay'a kullum kin fison ki nuna min abinda kike so shi zaayi? Abinda zuciyarki ta Raya miki se kin yishi. Banda kin raina ni ma se da kika shirya kika hada connections dinki sannan zaki zo ki fada min? Nace ba zaki je ba idan kuma ban isa ba ga hanya nan.
Yana Kai aya ya Mike ya fara tattara kayanshi ranshi a bace saboda ganinshi raini ne kawai dan ta samu yana tolerating dinta shi ne zata dinga duk Abinda ta ga Dama, shi ba irin sauran mazajen yan uwanta bane da zasu dinga biye wa matansu.
Tashi tayi ganin ya nufi daki ta bishi, ranta a bace amma Tunda ita take neman abu dole ta yi kasa da kanta. A bedroom ta sameshi Yana jona system dinshi, a hankali ta bude Baki zatayi magana yayi saurin daga mata hannu yace
I've said enough kiyi yadda kike so, idan Kinje ya rage naki..
Bata jira komae ba ta fice daidai shigowar Suhaila parlon, dama ita daya ce shi mijin na waje dan haka tana shigowa ta Fara fadin
Subay'a fito mu tafi ko ma dawo da wuri.
Yadda taga Subayan yasa tace
Kada kice ya hanaki Zuwa?
Kanta ta langwabar Cikeda bacin rai tace
Wai se gobe.
Baki Suhaila ta tabe tace
Ke kuma se goben kenan? Kowa ya tafi se ke daya zaki zauna se Kace tsoronshi kike ji, ni Wallahi na rasa me ke damun Junaid dinnan.
Ba Abinda yake damuna, magana ce na gama amma idan Ke kike auranta you can go with her.
Haka suka tsinkayi muryarshi Yana fada Ashe Tun shigowar Suhailan ya fito dan daukar Flash dinshi. Itama Suhaila Bata da mutunci tace
Oh haka kace to Wallahi se taje, Sede kayi duk abinda zakai.
Kunsan hali ya banbanta hakan yasa bai ko daga kai ya kalleta ba ya wuce bedroom dinsa, Suhaila ta dubi Subay'a wadda jikinta yayi sanyi tace
Zo mu tafi?
Ina? Na fasa kinga ranshi ya baci kawai nazo da safen
Ta fada Tana me jin takaicin Junaid, su takwas suke gurin hajiyar su amma baki daya Junaid shi ne me matsala bai taba yadda an juyashi ba kamar yadda ake juya sauran sirikan kuma lokacinda ta aureshi tunani suke sun auri wawa Ashe ba anan abun yake ba. Cikeda bacin rai Suhaila tace
Karki cemin threat din Wannan hopeless element din zai sa ki fasa zumunci? Idan akwai me Zuwa gurin Sulma ai a bayanki ne.
Itama tana jin hakan amma Tunda take da Junaid Bata taba ganin ya Daga murya haka ba, it's unlike him Wannan yasa taji tsoron fitar take.
Nidai kawai kije Yaya Suhaila kinga kar na bullowa kaina wani aikin.
Wata harara ta watsa mata Tace
Kinsan Allah kafata kafarki wawuya kawai.
Haka Suhaila taja Subay'a suka tafi, Junaid dake jin komai ya saki murmushi ya fito lokacin har sun bar gidan. A cikin mota kasa sakewa tayi, suna gaisawa da Ishaq ta bame bakinta, tana jin yadda suke hira amma ita kam babu Wannan damar a haka suka iso Standard hospital dake tarauni lokacin goma Harda yan Mintina amma dakin da take kamar rana, Tun a parking space suka hadu da mijin Safina, Surayya da ita Sulma din. A waje ya tsaya suka shiga ciki a cikin su takwas Samina ce kawai bata nan itama sun je Mexico ne itada yaranta, Tun dazu da taji labari take jin tamkar tayi tsuntsuwa ta taho amman babu Hali. Suna shiga suka samu hajiya tana zaune kan wata kujera dake dakin su kuma sauran suna kasa an shimfida carpet se hira suke yayinda Sulmar idanunta ke a runtse tun dazu take son ta runtsa Tunda an sha artabu amma by mere kallo abin bazai samu ba. Suna zama aka Fara sabuwar gaisuwa se hira ta kuma ballewa, Sulma ma haka ta shiga anayi da ita. Mukhtar mijin Suhaila ya shigo Yaga baby sannan yayi musu barka ya koma waje hakan yasa hajiya tace
Subay'a ke ina naki dan ka gadama ko bai gadamar ba.
Kafin ta bada ansa Suhaila tayi caraf tace
Kinsan hajiya me yayi mana...... Nan ta kwashe komai ta fada musu, wani mugun zagi Salima ta saki tace
Shiyasa kika shigo jiki a sanyaye, Ke wacce Irin Shashasha Allah ya hada mu da ita? Ke me miji ko to Samina ma da bata kasar jibi zata iso.
Ba haka bane.....
Rufe min baki
Hajiya ta fada
Sau nawa ina ja miki kunne akan mijinki, yaro daya kusan shekara takwas kin zauna Yana juya ki Kece koma baya cikin yan uwanki, to ki sani har ayi suna babu Wanda na daukewa zuwa yaga Sulma don gobe gidana zan tafi da ita.
Da sauri Sulma tace
Gidanki hajiya? A'a munyi dashi gida zan zauna.
Suhaila ce