Showing 39001 words to 42000 words out of 131263 words

Chapter 14 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt

Ayshatuu   

20 Dec 2024

5195

hannunta ta daidaita zamanta don tuhumar kanta dalilin da yasa take haka, in the first place Meye tsakaninta da Junaid da take jin zuciyarta nayi mata nauyi Duk lokacin da ta ganshi da matarshi, ko dai sonshi take? Se kuma ta Fara fadin No! No it's not possible, it's never gonna happen, to amma Koda tayi denying it obvious abinda takeji game da Junaid so ne, runtse idonta tayi tana girgiza kanta Tana fadin No! Never!! It will never ever and will never happen. Kifar da kanta tayi tana ta tunani wanda ta rasa na Menene Sede babu me bata amsa.




Shatuuu ♥️
[7/17, 5:42 PM] Asma'u Madugu: *MACE A YAU*


16


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


A firgice ta Mike Daga gadon saboda jin har an shiga sallah, da sauri ta shiga toilet tayi Alwala tazo tayi sallah, qurani ta janyo tayi karatu na thirty minutes kafin tayi azhkar se wanka. Tana fitowa ta shirya cikin skirt da riga na atamfa sannan ta zauna gefen gado ta Fara revising book dinta. Nanma she took almost an hour tana abu daya kafin ta aje littafin saboda kiran Mami daya shigo


Mamina


Ta fada lokacinda ta Kara wayar a kunnenta , da murmushi Mami tace


Auta kin tashi lapiya?


Lapiya lau Mami ya gida, Ina Baba?


Ga Babanki


Ta mika mishi,


Baba


Ummu_Sulaim ya shirin exams?


Alhamdulillah Baba.


Allah ya bada sa'a, focus ok


Inshaaa Allah I'll.


Yawwa Allah yayi muku albarka.


Amin Amin ga Mamin.


Mami ma addu'a tayi mata sannan sukai sallama. Tana aje wayar taga message din Ja'afar


Exams are near
Subject are not clear
Question appear
And answers disappear
Oh! My dear
Don't be fear
Bcoz im here 2 wish u,
All clear!
Have a great exam fest all the best!


Itakam Ja'afar ta rasa yadda zatayi dashi, kullum text uku ne morning, afternoon and night. Da karfinahi ya dawo to ita bata san yadda zasui ba. Tsaki tayi ta Mike tayi ta saka hijab sannan ta dauki Jakarta ta fito, kusan duka tare suka fito,
Anty ina Kwana?


Babu yabo babu fallasa tace


Lapiya


Daga haka ta wuce kitchen dan su Atika basu kai ga fito da breakfast ba, Ahmad ne ya nufo inda take Sanye cikin uniform na school tas dashi, dukda bawai Subay'a ke mishi wanki ba amma tanada tsafta dan bazaka taba ganin wani abun kazanta a tattare da ita ba ko yaranta na kullum they appear neat. Cinyar Sulaim ya zauna Yana fadin


Anty morning


Murmushi tayi tana shafa kanshi tareda sake gyara mishi collar Riga tace


How was your night?


Fine


Ya fada Yana grinning ear to ear, kafin ta kuma wata maganar se ga me gayya me aiki Junaid ya fito waya a kunnenshi ya rike da kafadarshi, Dayan kafadar Yana rataye da briefcase dinshi se daya hannunshi Yana saka link jikin Orange long sleeve Shirt dinsa ta kamfanin marks and Spencer, se black trouser na kamfanin tummy Hilfiger, yayi kyau sosae kamar kada ka barshi ya fita. Yana Zuwa tsakiyar parlon, ya aje wayar kafin Sulaim ta gaisheshi Subay'a ta fito bayanta Atika na binta da Jeren warmers, inda yake ta iso tace


Har ka fito?


Kanshi ya gyada yace Yana sake duban wrist watch dinsa baki kirar Penurai, takwas saura kadan shi kanshi yayi mamakin yadda suka makara, ba akai Ahmad school ba, ita bata fita aiki ba sannan exams din Sulaim nine ne


Wucewa Zamuyi mun makara.


Kallonshi tayi tace


Kaine ka makara yau bazanje ba saboda open day dinsu Ahmad ne se nine Za'a Fara.


Kanshi ya dan daka yace


It skipped my mind baki daya, Allah ya kiyaye mu zamu tafi , banga Muhammad ba


Ya fada Yana juyawa alamun nema kafin ya maida dubansa ka Sulaim wadda tayi shiru deep in her own thoughts.


Still on bed, Abincin fa?


Kanshi ya girgixa yace


Zubawa Sulaim taci kafin ta shiga hall.


Kanta ta kawar tace


Tazo ta diba da kanta mana.


Kallon Sulaim yayi wadda take ta kallon Subay'a yace


Tashi ki zuba abinci kyaci a hanya.


Kanta ta girgixa Tana zumbura Baki tace


Na koshi


Kallonta yayi ya tamke fuska yace


Bazaki tashi ki dauka ba se ranki ya baci?


Subay'a tayi murmushi Irin haka take son yana ma wannan yarinyar me shegen tsaurin ido, Kallonshi Sulaim tayi yadda taga Fuskarshi yasa ta Mike Don babu wargi Balle tayi musu, kitchen ta shiga ta dakko silver tea flask karami ta tsiyaya plain tea, Dan karamin flask ta zuba Fried yam da egg sauce sannan ta zuba cikin karamin basket tabi bayanshi. Seda yayi warming motar kafin ta shiga suka bar gidan


Nayi lefi ne


Ya fada Yana kallon titi.


Ina Kwana


Don tasan shi ne dalilin tambayar , tabe bakinshi yayi yace


Bazan amsa ba, ni kwata kwata baki damu Dani ba, Mintina nawa Nayi saman kanki amma ko second glance baki bani ba.




Maganar tazo wa Sulaim a bazata hakan yasa ta dago idonta tana kallonshi wani Irin abu taji Yana fuzgar ta like a magnetic attraction, sauke idonta tayi ta kasa fassara abinda yake nufi _bata damu dashi ba ita kuwa ita ta damu dashi_ a hankali taji zuciyrta tana budewa wani Irin unimaginable feeling taji ya baibayeta har ta kasa boye murmushin din da takeyi. Kanshi ya girgixa ya kara fadin


Allah sarki kuma gata na, bazaa bani amsa ba kenan?


Bakinta ta turo kadan tace


Nima bakace ya shirin exams ba.


Dariya yayi yace


OK ramawa kikayi kenan? To we're even yanzun. Have you read well? Ko yanzun akawo paper?


Kanta ta gyada tace


Ready for the battle.


Kallonta yayi a ranshi Yana tunanin har wanne Lokaci ya dauka kafin ya sanar da Sulaimi halin da yake ciki? Karfa wani Daga gefe yazo ya dauke abinda yake ta tattalawa kanshi. A kofar Faculty yayi parking, kallonshi tayi shima kallonta yake cikin ido yana murmushi itama se ta samu kanta da sakar mishi tattausan murmushi kafin ta bude kofar se yace


Sulaim


Juyowa tayi har lokancin bakinta a bude yake ga wushiryar ta a bayyane haka dimples dinta dake both sides sun lotsa, tamkar ana fuzgarshi haka ya daga hannunshi se yayi saurin saukewa don yasan hakan ba girmanshi bane. Kallonshi take ta langwabar da Kai tace


Yaya


Tamkar ruwan sanyi haka kiran da tayi mishi ya isa gareshi, dagowa yayi yace


All the best, idan kin fito Kada ki tafi se five Zamu je gida, kizo office ki huta sannan ki karanta na gobe OK?


Kanta ta gyada daga haka ta rufe mishi kofar cikin nitsuwa ta taka kofar venue din tana jinta tamkar tana shawagi ne cikin gajimare, wani Irin farin ciki taji da nishadi wanda ta dade bata ji makamancin irinsa ba. Shima hakan ce a bangarenashi Don seda yaga ta zauna kafin ya shafa kanshi ya wuce murmushi fal Fuskarshi.


Tana nan Zaune Khulthum ta iso ta zauna gefenta amma saboda yadda Sulaim hankalinta ya tafi akan maganganun Junaid yasa ko daya Bata fahimci zuwan Khulthum ba harseda ta dafa ta kafin ta kalleta, itama Khulthum din kallonta tayi tace


Ke tunanin me kike


Ita kanta bata san ta saki wani Irin murmushi ba seda ta kalla facial expression din Khulthum kafin ta saki murmushi tace


Sannunki, ina Mama?


Tabe bakinta tayi tace


Mama na gida, Ina Yaya?


Wani smile ta saki wanda yake straight deep down from the ventricle tace


Office.


Sosae Khulthum ta ke kallonta kafin tace


Anya Yaya ne kuwa?


Me fa?


Kanta ta girgixa tace


Back to real business muyi revising.


Haka sukai ta brainstorming har invigilators suka shigo aka Fara, tunda aka ce start Sulaim ta dukufa abinta tana ta rubutu se time to time Tana sakin murmushi, can tana last question taji sassanyan kamshin Fierce cologne by Abercrombie and Fitch ko bata dago ba tasan duk duniya mutum daya take jin wannan kamshin a jikinshi kuma shi ne _Junaid_ a hankali tamkar me tsoro ta dago idonta shi ne kuwa yana tsaye kyem a kanta sede Fuskarshi babu walwala he's not the Junaid she left a mota wannan examination officer ne kuma senior lecturer dinta. A hankali ya motsa bakinsa ya furta


Stop staring, kiyi rubutu.


Bakinta ta turo mishi ta maida kanta kasa amma ta kasa cigaba da rubutun saboda yadda taji ya cika gurin gashi bugun zuciyarta is increasing its pace. Ganin haka yasa ya bar gurin kafin daga bisani ya fice a hall din baki daya. Ana cewa pens up ta aje nata akai tattara suka fito baki dayansu, su hudu suka tsaya gefen hall din kowa na fadar albarkacin bakinsa, exams dai babu laifi ta yi dadi sede addu'a. Khairi da Khulthum suka tafi hostel don Khulthum zata shiga toilet yayinda Aimana da Sulaim suka nufi office din Junaid, baya nan se messenger dinsa ne ya bude mata, Kan sofas din suka zauna Aimana tana tabin office din da kallo tace


Office din waye?


Gira ta daga tace


Easy mana, office din Yaya ne


Yaya dai Yaya dai every time, dama nan yake aiki?


Dariya Sulaim tayi wai Yaya dai all the time itafa bata jin wani fadar Junaid da take amma se suce wai common saying dinta kenan.


Eh he's a lecturer here


Kai ta gyada tana admiring gurin kafin kuma ta gyara zama tace


Sulaim


Kallonta Sulaim tayi ta tsaya da danna wayarta tace


Yaya?


Ina wannan brother nawa da ya taba Zuwa daukarmu Yaya Nu'uman?


Ta fada Tana nuna mata hoton Nu'uman a wayarta, karba tayi ta kalleshi, yes she remembers him, wannan shiru shirun shi ne kadai abinda zata fada a kanshi.


Na tuna shi.


Ya min maganar Yana sonki.....


So?!


Sulaim ta fada Tana zaro ido waje, dariya Aimana tayi tace


Keep calm and chill, nace mishi Kinada Yaya.


Da confusion tace


Yaya kuma?


Kafadar ta ta rike tace


Sulaim kenan, wannan Yayan da kike fada is not just an ordinary Yaya akwai wani abu karkashin zuciyarki, tell me kina sonshi ne.


Shiru Sulaim tayi ta kurawa Aimana idanu tamkar amsar tamabayar tana Kan fuskarta ne, baki daya se ta shiga cikin dilemma she's confuse ba kadan ba, ta yaya zaace tana son Yaya Junaid, Yaya fa mijin Subay'a no way he's just an important person cikin Rayuwarta.


Yaya, is an important mutum a rayuwata, Mummy da Daddy suka rikeshi har ya fara aiki, Kinsan ni am an orphan banda uwa banda uba, gidansu ake riko na. Yanzun Yaya shi ne komi nawa kinga dole Nayi maganarshi. Kinyi misunderstanding abin.


With a pity face tace


Ayya sorry for the loss, Allah ya jikansu Amma zancen Yaya ki tuhumu kanki.


Kafin ta bata amsa Sega Yaya ya shigo shida Ridwan. Mikewa tayi ta nufi inda yake yayinda Aimana take mamakin dama Dr Junaid shi ne Yaya? Haba no wonder Sulaim ta falling. Gaisheshi Aimana tayi fuska a sake ya amsa Yana tambayarta exams, itama ta bashi amsa kafin ya maida dukkan hankalinshi kan sarauniyar tashi dake gaisawa da Ridwan


Amarya na tambayarki Bakixo kin ganmu ba.


Dan murmushi tayi tace


Yaya bai kawo ni ba.


Da sauri Junaid ya daga hannunshi sama in surrender yace


Count me out of maganar nan, Ke Yaushe kika ce zakije tsakaninki da Allah?


Turo bakinta tayi tare da jujjuyawa hakan yasa Junaid dafe kanshi tace


Ka manta ranar.


Baki bude Junaid yace


Yaushe kika koyi sharri ke kuwa.


Dariya sosae sukai Harda Aimana dake gefe, Ridwan ya dauki abinda ya shigo dashi ya fice yana ta dariya shi kawai yana ganin Sulaim ma tana son Junaid din, shi kanshi ya rasa dalilin Junaid na kin fadawa yarinyar yana sonta amma zai kara tuntubar shi akan inda aka Kwana.


Kan sofar ya zauna Yana facing dinsu yana ma Aimana tambayoyi kafin ya maida dubansa kan Sulaim wadda ta bata rai kamar ba ita take dariya ba, a hankali ya dubeta yace


Me nayi kuma?


Bakace ya exams ba


A'a sau nawa zan fada ne? Ya exams din to


Cikin nitsuwa tace


Alhamdulillah!


Tashi yayi yace


Kin Faye damuwa Walhi, Bari nayi aikin gabana, Bari kuci abinci ko?


Kanta ta gyada mishi ya koma seat dinshi ya fara aiki Bayan ya bada order. Aimana ta kalli Sulaimi tayi kasa da murya Tace


What a perfect match!


Me?


Keda Yaya mana, Kuna son junanku Amma is like kamar baku fahimta ba.


Dan Allah Kiyi shiru Kada yaji, nace miki he's very important cikin rayuwata!


Waye ya yadda da sulaim?




Shatuuu ♥️


*MACE A YAU*
17 nd 18


✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad


A Kwana a tashi babu wuya gurin ubangiji, ranaku gudu suke suna shudewa tare da kara kusanta mu da kabarinmu, fata daya Allah ya sa mu cika da imani. Exams ana tayi har yaxo saura daya su gama , ranar Friday sun fito Daga Logic and philosophy paper, paper rana ce hakan yasa suna fitowa Junaid Yana jiranta a mota. Ciki ta shiga fuskarta babu annuri ko digo dama kuma yaji a bakin invigilators suna fadin exams din tayi wuya. Tana zama ya fara driving kafin ya kalleta don har lokancin ba tayi mishi magana ba yace


Ya exams din?


Dama abinda take jira kenan ta Fara kuka se yayi shiru Yana Dana sanin yin magana, ta kusan minti biyar tanayi bai hanata ba Sede bawai yana jin dadin sauraran kukan nata bane, seda ta share hawayenta kafin yace


Kiyi hakuri kinji, you will make it.


Kanta ta gyada se taji tsoron ta kusan kashi hamsin ya wuce taji ta samu hope da courage.


Yaya


Na'am


Ya fada ba tareda ya kalleta ba.


Gobe Inshaaa Allah wajen nine zamuje karatu ni da friends dina.


Juyowa yayi ya dubeta idonta har yayi Dan ja saboda kukan da tayi,


A'a


Kai Yaya


Kice musu su zo nan gida kuyi tare hankalina zaifi kwanciya.


Kanta ta gyada tace


Tohm.


Daga haka sukai shiru ya cigaba da tukin shi Yana tunanin sakon Mami da safe akan ranar laraba yayiwa Sulaim booking flight ta tafi Kebbi gurin dangin Mami da Anty zahra. Shi a so samunshi ne tayi zamanta Tunda hutun Baifi 2 weeks ba amma Tunda Mami tace haka zaayi bai isa canjawa ba. A wani Pizza joint yayi parking ya shiga ciki ya batta a mota, da Wannan ta kirasu Khulthum ta fada musu yadda Yaya yace Dama Aimana ce suke tunanin ba Za'a barta ba to itama ba'a samu matsala ba. Tana aje wayar daga kiran Khairi call din Ja'afar ya shigo.... Dam! Taji gabanta ya fadi Yaushe rabon taga wannan sunan ya kirata har ta manta, kamar bazata dauka ba se kawai taga bari taji me zaice mata. Tana picking wannan muryar tashi me dadi yace


Susu!


Se ta lumshe idonta saboda yadda sunan ya ratsa ilahirin jikinta, its been a while da aka kirata da hakan, so she missed been addressed as Susu.


Nasan kina jina, nasan kinga messages dina Baki daya, this time around I'm ready Sulaim, bazan Kara miki wasa da zuciyarki ba, I promise you only one more chance


_Baby give me one more chance to be the one to hold your hands, may be we could learn to love again...._


Shiru tayi words suna sinking cikin jikinta tareda sake auna su cikin kwakwalwar kanta, for how many times Ja'afar zaina mata fake promises, kullum maganarshi one more chance. Anya ba wasa take da rayuwar ta ba? Anya Ja'afar is the right person?


Sulaim please


Taji ya katse mata tunaninta, hakan yasa ta bude idonta har lokancin Junaid bai dawo ba tace


Na gaji Yaya Ja'afar bakasan darajar Abinda kake so ba


Sweetm ni ne fa, your Luff ko kin manta?


Dan murmushin takaici tayi wai ta manta, sede ta bude Baki da niyyar magana Junaid ya bude kofar ya shigo hakan yasa ta kasa magana shi kuma Junaid Yana zama yace


Yi hakuri na barki ke daya, I met an old friend.


Kanta ta gyada tace


Uhm.


Dake hijab ne jikinta daya kalleta baiga wayar ba don haka ya cigaba da fadin


Tare mukai NSUKKA dashi Yana da kirki, se yau Allah yayi muka hadu.


Dama hakane kam


Ta fada Tana zare wayar daga kunnenta saboda ba zata iya cigaba da wayar a gabanshi ba. Aikuwa Ja'afar ya dinga kira tana katsewa se taji Junaid yace


Waye ke kiranki?


Kallonshi tayi taga hankalinshi Yana kan titi tace


Yaya Ja'afar!


A bazata maganar tazo mishi hakan yasa yayi wani juyi ya kalleta kanta a kasa taki dago idonta ta kalleshi, se yaji duka ilahirin jikinshi yayi sanyi saboda ya tabbatar Ja'afar baya tareda Sulaim Yaushe suka hade Yana gefe


Yaya!


Sulaim ta kwalla kara saboda motar dake gabansu amma dukda haka Seda ya buga mishi kuma bugun ba sosae bane ba inda Allah ya taimaka, Gaba daya ilahirin jikinta rawa yake tsabar yadda ta tsorata, se ta Fara kuka, bai bi ta kanta ba yayi parking gefen titi ya fito, shima wanda aka bugawar ya fito mutane har Sun taru, ana maida yadda akai.


Fuskarta a rufe da tafukan hannayenta taji an kwankwasa mata kofar side din da take, dago idonta tayi wanda har ya canza kala saboda firgici, da idanun ta bishi da kallo kana kallonshi basai anyi maka bayani ba ya hada jini da larabawa, fari ne sosae tamkar ka taba shi jini ya fito, yana da tsayi sede bayada kiba ya hadu karshe babu karya. Cikin turanci me tsafta babu blonders yace


Ke kyakyawa ce, can I please have your digits.


Yadda ya tsare ta da ido se taji ba zata iya hanashi ba, hakan yasa ta mika mishi hannunta shi kuma ya bata wayarshi ta saka mishi numbers din ta mika mishi tace


Sulaim


Lumshe idonsa yayi yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login