Showing 3001 words to 6000 words out of 131263 words

Chapter 2 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt

Ayshatuu   

20 Dec 2024

5192

waje ta bar su da kamshinta, a kofar gidan Ashir na tsaye gefen Lifan dinshi ya durkufar da kanshi yayinda wani magidanci ke tsaye wanda ya tabbatar min cewar shi ne mahaifinki Khulthum saboda fuzgar kama da suke da Amir, matsowa tayi tace


Baba sannu da zuwa


Juyowa yayi yace


Sannu dai khaltume, kin barshi Yana ta faman jiranki.


Kanta ta sunkuyar ba tareda tace komai ba amma tana takaaicin sunan da Baba ke kiranta dashi Se Kace lokacin jahilliya zai dinga kiranta da khaltume, wucewa Baban yayi nan suka gaisa itada Ashir wanda bakinshi ya kasa rufuwa tamkar gonar auduga shidai Allah ya Dora masa zazzafan son Khulthum yarinyar tayi masa, kallonta yayi yaga Baki daya hankalinta yana kan machine kafin ya kai ga magana tace


Wai se Yaushe ne zaka siya mota? Ni na fara gajiya da ganin ka da Lifan dinnan.


Dan dariya yayi yace


Rai dai Khulthum kuma ma banda abinki nida ba aiki nake ba ina zan samu kudin mota.


Tsaki tayi tace


Maganar kenan kullum, sa'oinka nawa ne suke da mota?


Kanshi ya dafe yace


Khulthum Haba mana, stop comparing me to others, ni daban sauran daban kowa yadda Allah ya tsara mishi daban.


Kara bata rai tayi zatayi magana yayi saurin beating dinta yace


Don't suffocate the environment please, kinga yadda kikayi kyau...... Bana tunanin duk duniya akwai Wanda yayi Saar Irin tawa.


For the first time Tunda ta fito ta saki murmushi wanda yake na gaske daga karkashin zuciyarta tace


Kaima kayi kyau.


Kanshi ya gyada yace


Not as beautiful as you, so gobe zaki fara lecture ko?


Idan ta tuna wannan jinta take burinta yana daf da cika, idan ta tuna makaranta kuma university itadinma BUK tana jin kamar da saa aka haifeta


Abu daya zan rokeki, ki maida hankali Kiyi karatu, kada kina comparing kanki da wasu kowa rayuwarshi daban Allah ya tsara mishi abu na karshe ki kula min da kanki ki rike min alkawari.


Bata ce dashi komai ba Don alkawarin yayi tsauri Bata tunanin zata iya wannan amma karatu confirm zatayi to dole ne ma ai duk kudin da ta kashe wajen registration da komai tayi wasa ai kanta tayiwa.


Ranar ta kasance Monday...... Monday tushen aiki Formula uwar lissafi. Tun asuba Sulaim ta farka, gaba daya kewar Mami take dukda Kwana biu da tayi amma ji take tamkar sunyi shekara basu tare, sallah ta Fara yi sannan tayo wanka ta Fara shiryawa tana yi tana azhkar har ta Kamalla ta Fara kiran Mami sede kafin ta kai ga shiga Mamin ta kirata through her other phone, sun kusa 10 minutes suna waya Tana sake mata nasiha da jin ko akwai wani abu amma tace komai lafiya, a haka sukai sallama kafin ta fito parlour, lokacin shida daidai ta buga, parlon babu kowa amma tana jiyo motsi Daga kitchen hakan yasa ta nufi can, yanmata ne guda biyu suna ta aikin hada breakfast, da sallama ta shiga suma duka suka amsa suka gaisheta fuska a sake, ta ja kujera ta zauna Tana bin movement dinsu da yadda suke aiki Cikeda kwarewa da alamu dai sun samu training a wannan harkar, hira suke Yi suna sako ta a ciki Jefijefi tana basu amsa a haka suka kammalla komai daidai shigowar matar gidan, Tana Sanye da bakin skirt irin boutique dinnan daya Kama Nata jiki se top Fara da matching waist coat a jikinta, kanta bakar hula ce, Tana shigowa gaba daya sukai shiru tamkar ruwa ya cinyesu se gaisheta da suke, kamar kullum babu digon wasa ta amsa se sannan Sulaim tace


Ina Kwana


Juyowa tayi ta dube inda Sulaim ke Zaune, ita bata Lura da ita ba ma kwatakwata, Memakon amsa gaisuwar Tace


Me kike Yi anan? Aren't you going for lecture?


Kanta ta gyada tace


Na shirya kawai shigowa nayi.


Kafada ta daga Irin damuwarki ce ta dauki abinda zata dauka ta fice itama Sulaim sallama tayiwa su Atika ta nufi dakinta ta shirya cikin simple gown ta lace, ta hada komai cikin karamar backpack dinta ta fito parlour, wannan karan kusan tare suka fito gaba dayansu har yaran.


Yaya ina Kwana?


Ta gaida Junaid wanda ya fito Yana nannade hannun rigarshi, with concern yace


Auta kin tashi Lapiya


Brightest smile ta saki tace


Lapiya lau Alhmdllh.


Basu Kara fadin komai ba suka nufi dining table inda Atika take tsaye Tana jiransu, suna zama Muhammad ya tashi ya dawo cinyar Sulaim, kallonshi Subay'a tayi tace


Koma seat dinka.


Baki ya turo tareda kankame Sulaim, murmushin nan tayi ta shafa kanshi tareda rada masa abu a kunne, take ya fara dariya hakan yasa Ahmad shima tasowa ya dawo gefenta, cikin iyayen basu Kara fadin komai ba haka aka ci abinci wanda kusan Rabi wasa ne tsakanin Sulaim dasu Ahmad. Subay'a ce ta Fara tashi tare da wiping bakinta da saviette ta matso inda Junaid yake ta bashi peck a kumatu tace


Ni na wuce


Murmushi kawai yayi yace


All the best!


Thanks! Ahmad bye.... Muhammad be a good boy.


Daga haka ta zari key din motarta da handbag tayi waje abinta. Junaid ya kalli Sulaim wadda tayi shiru deep in her own thoughts yace


Sakawa Muhammad uniform kuzo mu tafi.


Tohm Yaya .


Basufi 10 minutes ba suka fito shirinsu tsaf waya a kunnenta tana waya, tunda ta fito Junaid Ke binta da ido har Seda ta gama wayar ta kalli gefenshi kafin yayi saurin dauke idonshi, bata damu ba tace


Yaya we're set, ina Ahmad zai zauna.


Se yaji dadi ganin she's concern akan yaranshi yace


Nanny dinsa tana hanya ki barshi gurin cooks din can.


Cikeda gamsuwa ta wuce ta kaishi se kuka yake akan shi binta zaiyi, haka ta taho tana jin wani iri cikin ranta.


Seda yayo baya ya sauke Muhammad a Al'azhar kafin ita dashi suka nufi new site, kasancewar sune most reserve a yaran Mami yasa tafiyar haka akai yita shiru kamar babu mutane. Cikin sa'a wayarta ta Fara ringing, hannunta ta zura ta ciro ta Daga purse tana dubawa taga LUFF, se taji bazata iya picking ba haka wayar ta katse Ja'afar ya sake kira anan ne Junaid ba tareda ya kalleta ba yace


Pick up your call.


Swiping tayi ta Kara kunnenta take Wannan muryar tashi me dadin sauraro ta Fara zagaye mata ko ina na jikinta wanda take ya saka mata wani Irin shauki, ta tabbatar Ja'afar is beyond words ya iya tafiyar da Wannan harkar.


Uhmmm ina Kwana?


Murmushi tayi ta kalla gefen Junaid wanda Baki daya hankalinshi a zahiri yana kan titi ne amma a badini yana gurin Sulaim.


Eh muna hanya........ To zan kiraka Anjima a gaida Mami da Yaya Jawad.


Wannan furucin Nata ya tabbatar masa Ja'afar ne, maida wayar tayi handbag dinta a haka suka isa Faculty of Law, wani Irin dadi taji a zuciyarta this is the beginning of the journey......


Tare suka fito ita dashi, a nutse suke tafiya a haka ya rakata har class Seda ta zauna kafin ya fita dama tun a mota yace Duk Abinda take so ta kirashi saboda shima a Faculty yake.


Ranar Bata wani Saba da kowa ba, taji dadin classes din musamman na English for legal writing, amma logic dinnan ne se a hankali. A haka ranar ta Kare Junaid ya dawo daukarta batareda ta Saba da kowa ba don Tana ganin is too early ta samu kawa.


*I've seen every of your prayers, your comments and wishes. I'll forever remain grateful...... But dont be xpecting post everyday because I've so many things to attend to but will try my every best to see that I didn't keep you waiting......Thanks for understanding*


Shatuuu ♥️
[6/20, 11:56 AM] +234 701 517 3116: *MACE A YAU!*


3


✍️Shatuuu ♥️


Shatuuu095@wattpad


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION




Tunda me napep ya direta a layin da zata shiga gidansu kasancewar machine ne kadai yake iya shiga shida keke cikin kwanciyar hankali amma sauran kam sede addu'a saboda yadda kwata take cike ga kuma tsuku da gurin yayi kowa yasan idan akace Rimin kebe a kano Irin merciless ghetto area dinnan to nan gidansu Khulthum yake, tunda ta sakko mazan dake zaune yan kashe wando suke buga ihun


Talaka me girman kai.......


Se wasu suce


.......Allah zai kona shi.


Sarai tasan da ita suke da Wannan sabon su ne har ta Saba, haka ta ratse ta wuce, gaba daya yau bata wani fahimci karatu ba saboda yadda take kalle kalle tun kafin ta shiga class taga yadda yara kanana suke zuwa cikin manyan dankara dankaran motoci, shiga iri iri ta Kece raini se taji tamkar kowa ita yake kallo a gurin, ga hottest phones da ta dinga gani a hannun mutane ita kuwa tata Nokia torch light ce. A haka ta isa gida amma Tun Daga nesa ta hangi Ashir a tsaye da dukkan alamu ita yake jira , se taji for the first time ta rainashi taji bata tunanin tana ganin Irin wannan mazan a waje zata iya Auran Ashir ta cigaba da zama ghetto gaskiya ina, yadda ta tashi cikin talauci gaskiya ba zata dawamma a cikinshi ba no! And never! Tana zuwa inda yake ta tsaya tana dubanshi shima kallonta yake yana mata murmushi,


Duk gajiyar ce haka ko gaisuwa ban samu ba, bare Ayimin murmushi


Murmushin ta danyi tace


Na gaji Wallahi, ruwa kawai nake son naji a jikina.


Kanshi ya gyada yace


Bari na barki ki shiga gida dama zuwa nayi na ji yadda ramar ki ta kasance, amma anyways gobe ki shirya da wuri zanzo na kaiki....


Ina?


Tayi saurin tambaya, dariya yayi yace


School mana Tunda munada machine inaga zai rage kudin xirga xirgar


Da sauri ta girgixa kanta tace


A'a dan Allah nagode, Dan Allah Kada ka gwada hakan, I'll be OK hakan nan.


Bata jira abinda zai kara fada ba ta shige zaure a ranta tana fadin lallai Ashir Bakada hankali wasu na Zuwa a mota kawai se a ganni kwam kan Lifan Haba dai! Allah ya kiyaye. Shikam baki bude ya tsaya Yana mamakin sanyin Khulthum, hakan nan dai jiki babu kwari ya burga Lifan dinsa ya wuce.


Zaune ta samu Mama da Aisha se Amir suna hira, gidan kalkal yasha Shara gwanin shaawa saboda daga Mama har yaran babu Wanda zakaga element na kazanta a tattare dasu, shikanshi simintin dake malale tsakar gidan an wanke shi tas se kyalli yake, dama bawai tana sallama bane Tunda ba koya maka akai ba kuma baji take a Nayi ba balle tayi picking, haka ta shigo kadaran kadahan kana kallonta kasan rana ta daketa ga gajiya da tayi mata rubdugu, gefen dakin da suke Kwana ta zauna wanda kusan nata ne ma kawai Kwana kawai yaran keyi amma baki daya kayansu da komai yana dakin Mama saboda Khulthum ta kafa ta tsare.


Da kulawa Mama tace


Khulthum an dawo Daga makarantar.


Fuska ta yatsina tace


Mama akwai wahala.


Murmushi Mama tayi tace


Se hakuri, Aisha tashi zubowa Yayarki abinci.


Turo Baki A'ishan tayi tace


Mama ita taje ta zuba da kanta mana, Kinsan ko an zuba mata zatace ba zata ci bane.


Mama tanada wani abu matsawar ta saka Abu ka Kiyi to tabbas zata tashi tayi da kanta, Sede abinda ka koyawa yaro shi zai tashi dashi don kuwa ance Tun ranar gini Tun ranar zane, idan baka aje ba Kada Kace zaka dauka. A wannan zamanin kayiwa yaranka tarbiyya ma ya aka Kare balle Bakai ba, tashi tayi da kanta taje kitchen ta zubo mata abinci ita kuwa tana zaune ta harde kafarta se cika take tana batsewa, saboda yadda Khulthum bata fara'a ko tayi kwatakwata Bata mata kyau, mutum ce da bata fara'a a cewarta gwara ka tsare gida saboda gudun raini, gata da girman kai kuma haduwar ku ta farko kallon kaskanci Xata fara Yi maka not knowing dukkan kaskanci a kanta ya kare, haka babu wata muamala me kyau tsakaninta da yan uwanta, idan tayi musu magana to tabbas aike ne ko rashin mutunci.


Mama na kawo abincin Khulthum ta yamutsa fuska tace


Mama wannan ne abincin?.....Innalillahi!


Ta dafe kanta, kallonta duka sukeyi babu wani mamaki a ciki don wannan shi ne least abinda Khulthum zata iya yi Balle yau Baba bai bada kudin cefane ba haka ya fice Don yace shi ko sisi bai Kwana da ita a jikinshi dama gurinta yake karba idan Irin haka ta faru to Tun safe ta tafi makaranta hakan yasa ya fice abinshi itakuwa Mama ta sirfa gero ta hada da wake ta dafa matsayin kundin kaza. Kafin Mama ta fadi wani abu tuni Khulthum ta shige daki, se gata da kwano ta fito hakan ya tabbatar musu abinci zata siyo,


Wallahi Mama duk laifin kine abinda Khulthum takeyi, kawai saboda Bakuda kudi mu talakawa ne shi ne take Wannan rashin mutuncin, kina kallo ta fita Siyan abinci amma kin kasa magana, Haba Mama!


Amir ya fada bayan fitar Khulthum, Aisha ce tace


Wallahi kua talauci ba hauka bane kawai don Bakuda kudi se ya zamana shi kenan se ta dinga juya Ku? Kun kasa yin komai kun zuba mata ido.


Nanma har Aisha da Amir suka gama 'yan mitocinsu Mama batace uffan ba. Babu dadewa Khulthum ta dawo da abincinta me rai da lafiya.


Safiya ce ta asabar, gabaki daya gidan yayi shiru kasancewar kowa hutawa yake, a hankali aka turo kofar dakin na Sulaim inda take kwance saman gado tayi daidai, a hankali Atika ta Dan taba ta, dake baccin bayan asuba ne ba wani Nisa yayi ba hakan yasa ta bude idonta, se kuma ta rufe idon saboda yadda hasken yayi mata yawa, a hankali ta sake budewa lokacinku ta gama adjusting to rays din.


Ina Kwana Anty Sulaim.


Bata fuska tayi tace


Atika lapiya dai ko?


Kanta ta gyada tana kuma murmushi tace


Lapiya lau, an gama breakfast.


Hannunta ta daura a kai tace


Amma Atika se a barki, ina bacci......


Se kuma tayi shiru kawai kafin tace


Ina fitowa.


Daga haka Atika ta fice Sulaim ta sauka tayi brush sannan ta wanke fuskarta ta zura hijabi ta fito, Ahmad da Muhammad na parlour sunyi wanka an saka musu kaya me kyau Wanda zai baka clue din fita zasui, suna jin sallamar ta suka nufe ta inda ta tsaya tana jin maganganun su Tana dariya, a haka Junaid da Subay'a suka fito, hannunsu ta rike baki bude tace


Yaya good morning, Ina Kwana Anty.


Seda ya kare mata kallo wanda idan bawai kana kallonsa bane ba zaka fahimta ba kafin yace


Morning Sulaim


Subay'a ya kalla wadda Baki daya hankalinta yana kan Ahmad yace


Suby answer her.


Dago kanta tayi ta kalli Sulaim wadda itama kallanta take, ciki ciki tace


Lapiya.


Tana rufe bakinta Atika ta iso ta fada musu an gama komai, tare suka jera zuwa dining, Atika ta bubbbude warmers da plates din, babu inda Subay'a ta sauke idonta se akan danwaken dake gefe,


What nonsense is this Atika?


Ta fada Tana daga murya hakan yasa gaba daya kowa hankalinshi ya koma kansu,


Dan wake? Wayace kiyi.


Sulaim ce ta dubi Subay'a tace


Ni na saka Ayimin Inaso zanci.


Wani kallo ta watsa mata yayinda Atika jikinta ke rawa don halin Subay'a bbu wasa, Dama seda ta fadawa Sulaim strictly ake bin timetable din ba'a canjawa se da izinina Subay'a amma tace itadai ayi mata


Wayace miki ana canja mana tsarin timetable dinmu? Wa ya Baki izinin ki bawa cook dita order? This is.......


Meye haka Subay'a? Bana son irin haka, Bana so kowa Yana da right ya zabi abinda zaici, ba dole Se wanda kika gindaya ba.


Junaid ya katse ta, iya kulewa takai , take ta aje spoon din hannunta ta koma daki, bai kara fadin komai ba, itama Sulaim din se taji komai ya fita mata a kanta hakan yasa ta Mike da nufin komawa dakinta Amma tana aje wannnn spoon din taji wannan sharp eyes din da duk duniya bata tunanin akwai Wanda kallonsa yake affecting dinta kamar Junaid ba, kallonshi is skin piercing se ya tsaga dukkan fatar mutum ya shiga jiyoyinsa, kallon yasa ta duburburce ta Fara fadin


Yaya bari nayi wanka......


Kici abinci tukun


Ya fada a nitse amma muryar kawai zatace maka order aka bayar, haka nan babu yadda zatayi ta zauna taci abinci, dake wasu abubuwan Sulaim exactly Irin na Junaid take hakan yasa seda Subay'a ta fito basu gama breakfast ba, gefenshi ta tsaya tace


Zamu wuce.


Ba tareda ya kalleta ba yace


Allah ya kiyaye.


Itama been the Subay'a yasa Bata bi takanshi ba taja yaranta wanda tuni suka gama shiryawa don al'ada ce duk wata Saturday din duniya zata tafi gidansu wanda ke Magajin Rumfa a cikin kano. Amma daga aurenta zata iya irga sau nawa taje Kaduna gidansu Junaid, bai taba mata maganar hakan ba Sede ya kwashi yaran Yaje dasu. Shi ya fara gamawa yace


By 2pm zan fita idan zaki bini to?


Agogon dake jikin bango ta kalla, karfe Tara da yan Mintina hakan yasa tace


Allah ya kaimu.


Daga haka suka koma dakunansu, wanka ta Fara yi ta Nemo kayanta ta aje, gado ta fada ta janyo system ta Fara kallon Indian film na We're Family tana kalla tana cin popcorn, a haka har tazo karshen film din, yadda Kajol take bankwana da yaran yadda duk yadda take son yaran, take protecting yaran, take basu dukkan wata kulawa da soyayya ya tsinka zuciyar Sulaim gashi ta mutu ta barsu, haka kowacce uwa Ke son danta? ai kawai se ta tuna Mummy da Daddy dinta, kawai se ta kifa kanta ta Fara kuka tamkar yau aka dakko ta Daga makaranta akace sun rasu haka abin ya dawo mata sabo dal, ta dinga kuka Tana Shesheka I missed you Daddy and I missed you Mummy.... Allah ya haskaka kabarinku. Tafi Mintina talatin tana Abu daya kafin ta tashi ta nufi bayi ta wanke fuskarta sannan tayi sallah ta daga hannunta sama cikin kaskantar da Kai tace


Allah ni baiwar kace me tarin kurakurai, Allah ka gafarta min ka haskaka kabarin Mummy da Daddy........


Se kuka ya kara kubce mata, ita kanta tasan ba karamin kokari tayi a rayuwarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login