Showing 27001 words to 30000 words out of 41148 words

Chapter 10 - KABEER COMPLETE Book Complete Document by Amina Yakubu.txt

28 Dec 2024

4578

to Allah ya kawo ka amin, ya lbrn Mutanen gdn? Suna nan kalau, ya neehal ita yaushe ne bikin nata? Ankusa da yanzu tare aka hada ma, mijin da zata aura ne yayi tfy, Amma yanzu ya dawo, Allah sarki shima Dan Kaduna ne mijin? Eh Dr haidar ba, Dan abokin dad dinmu ne alhaji Bashir bakori, shima likita ne yanada asibiti me suna bakori obstetrics $maternity private Hosp, acan neehal take aiki, eyya Allah ya taimaka, Bari na barka haka saida safe to Allah ya kaimu nagode sosai.


Dr marwan friend dinsa ya kira, suna gaisawa yace marwan Kasan Dr haidar Bashir bakori a Kaduna? Sosai ma, he is my friend, don Allah tromin no sa don Allah, me zakayi da ita? Don Allah tromin koma meye zakaji daga baya, OK to zan tromaka yanzu


No tana shigowa ya fara dialing, ana dauka suka gaisa, sanan ya fara masa bayani kamar haka" sunana kabeer M BAGAUDA, mu family friends din gdnsu neehal ne, mahaifiyata tana kokarin hada aurena da neehal, ba tare da saninta ba, kuma nasan kai take so Sbd haka na kira na fada maka kayi saurin yin wani Abu akai, domin kuwa akwai kyakyawar fahimta a tsakanin parents dina da nata, idan har mum dina tayi magana to ba abinda zai hana a auramin ita, Sbd haka Sbd haka kayi kokarin yin wani Abu daga yanzu zuwa next WK, banaso na zama sanadin raba masoya masu tsananin son junansu irinku. Wata sansanyar ajiyar zuciya yayi sanan yace nagode Mr kabeer tabbas neehal ce rayuwata, kuma rabani da ita tamkar rabani da rayuwata ne, insha Allah tun daga yau zan fara daukar mataki, nagode Allah ya saka da alkairi


3days later
Suna zaune da mum dinsa suna hira aka kirata a waya, tana dubawa taga Haj Asiya da sauri ta dauka bayan sun gaisa Haj Asiya tace dama kira nayi na fada miki gobe zaa kawo lefen yarki, kiyi hakuri don Allah na fada miki late, Wallahi abin ne ya taso urgent, muma be fada mana ba sai jiya. Jiki a mace mum tace oh ikon Allah dama kun mata miji ne? Eh anyi mata HAJIYA, ai Dan abokin abbansu ne ma, to Allah ya tabbatar da alkairi tace amin, amma sai kinzo ba HAJIYA tunda abin yazo a kurarren lkci, bikin nan da wata daya zaa saka, so in Allah ya kaimu bikin kyazo, to shikenan Allah ya kaimu.


Kallon shi tayi rai a bace kaji wai lefan neehal zaakai gobe, a zaune yake Amma saida ya mike, neehal din da kike so na aura? Eh wallahi, kai Amma wanan Abu be yimin dadi ba mum, naso na cika miki burinki, naso na auri neehal Sbd na faranta miki mum, Amma Allah yasa haka shi yafi alkairi tace amin son, kaima Allah yayi maka sauyi da mafi alkairi yace amin, bari naje gd amma zandawo da daddare insha Allah, to shikenan saika dawo.


Yana fita ya kira aunty Salma a waya ya fada mata duk abinda ya faru, tayi murna sosai sanan tace zan shigo kano gobe insha Allah, Sbd haka kafin nazo kayi kokari ka sanar da mom maganar Aysha, to shikenan sis nagode.


7:30pm
Ya shiga gdn mum cikin sa sanye da farar jallabiya saida ya durkusa ya gaisheta sanan ya zauna, sun Dade a zaune ba wanda yayi magna, sanan daga bisani ya daure yace mum wata magana nake so muyi dake, go ahead son INA jinka, dama game da zancen aurena ne, tunda Allah beyi da neehal ba, na samu wata yarinyar da nake so, alhamdulilla mum tace, Abu yayi dadi wacece ita? Yar gdn waye? Kuma a wane gari take? Mum ban taba yi miki karya ba, kuma yanzu ma bazan miki ba Amma don Allah mum inaso ki taimaki rayuwata ki amince min da auranta sabd ban taba son mace a duniya kamar yanda nake sonta ba. Sunanta Aysha, a gdn alhaji Ahamad TURAKI ta rayu tun tana jaririya, shi ya bata tarbiya ya bata ilimi daga karshe ya koreta Sbd son zuciya, ataikaice dai a yanzu batasan kowa nata ba, Amma idan kin amince min ni zan aureta haka, tanada tsananin kirki, tanada tarbiya, tanada kyawawan dabiu da kallo daya zakiyi mata kiji kina sonta.........wata mahaukaciyar tsawa ta daka mishi da har saida yayyan hanjinsa suka kada, sanan tace duk abinda take dashi ya tashi a banza tunda bata da asali, idan har kaga auran nan ya yuyu saidai akan Abu biyu, ko bana Raye, ko kuma bada yawuna ba, Amma indai ina Raye ban amince ka auri yarinyar da bata da asali ba da kakkausar murya ta karasa maganar mikewa tayi zata shiga daki yayi sauri ya rike kafarta yana wani irin kuka me ban tausayi don Allah mum ki taimaka min, wallahi Aysha ce rayuwata, idan har ban aureta ba zan iya rasa rayuwata, wallahi mum idan ban aureta ba mutuwa zanyi plissssss! Aikuwa saidai ka mutu, daidai ka auromin Marat asali a yanda matsayin ka yake a Nigeria, gara ka mutu ta zare kafarta ta shigewarta daki. Ya Dade yana kuka a wajen, daga baya ya dauki key motarsa ya fice daga gdn


Maman Aysha
[10/3, 17:44] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“


A kwance nake abin duniya yayi min zafi, na rasa inda zansa kaina tunanin kabeer da sonsa ne fall zuciyata yau kwanansa uku kenan rabonsa da gidan nan, sanan idan na kirashi a waya baya dauka nayi duk tunanin da zanyi ko zan gano lefin da nayi mishi Amma ban gano komai ba, kullum acikin zuba ido nake ko zaizo amma shiru gashi yace na daina fita office. Baba mero tayimin rarrashin duniya amma na kasa hakuri.


Ina idar da sallar isha'i naji wani irin zazzabi ya rufe ni, kawai saina tafi daki na shiga bargo na kwanta banda rawar Dari ba abinda nake, ga wani irin missing din kabeer da nake, daidai lkcn ya shigo gdn a sukwane, ko gaishe da baba mero beyi ba yace ina Aysha? Tana daki, kawai sai yayi hanyar dakin a bakin gadon ya zauna kamshin turarensa sa ne ya tabbatar min shine da sauri na mike na zauna Aysha me yasameki kk kuka? Cikin shagwaba nace bakai bane yau kwana uku baka zo gdn nan ba, kuma na kiraka a waya kaki yin picking, nayi maka text ba reply. To Amma meya dameki da rashin zuwana? Ba Faisal yana zuwa ba? Kafe shi da ido nayi INA kallon kwayar idonsa, at d same time kuma hawaye yana ambaliya a idona, nayi miki tambaya kinyi shiru? Meyasa kika damu da rashin zuwana? Sbd INA sonka, ko kanaso ka fadamin har yanzu baka gane INA sonka ba? Meyasa baka tausayi na? Meyasa.......shitttt hannunsa ya Dora a saman pink lips dina Aysha nima INA sonki kuma INA tausayinki, ban taba sanin meye so ba sai akanki, Aysha you're my first Luv, my heart, my soul, my everything idan har ban aureki ba zan iya rasa rayuwata, kuma mum bazata taba bari na aureki ba dole sai an gano family ki, inaso ki kara tambayar su mum dinki ba wani leaked da zai baki Wanda zai taimaka wajen gano su? A iya bayanin da sukayi min gaskiya babu, Amma zan kirata ta Kara tambayar min shi, is alright ni zan tafi saida safe, hannuna ya rike inaso ki Sani INA sonki kuma duk duniya ba Wanda ya isa ya rabani dake gud nyt


Wani irin farin ciki ne ya kamani, nan take na nemi zazzabin da nake na rasa duk da akwai a lot of challenges a gbna Amma Kalmar so daya furta yana min tasa na manta da komai. Baba mero ce ta shigo dakin hankali a tashe me yace miki Aisha? Baba mero ki tayani murna, kabeer ya furta yana sona, ya amince da soyayya ta yau, dariyar farin ciki tayi tace alhamdulilla Allah ya tabbatar da alkairi nace amin, yanda naga dare haka naga rana Sbd farin ciki, a Daren na kira mum na tambayeta tace bata Sani ba, kuma tana tsoron yiwa dad magana sabda ya hanata tayi mishi mgn akan abinda ya shafe ni, sai nace ta a wacce police station ne? Tace ta tarauni ce, anan mukayi sallama tanata kuka tana yimin addua.


Washe gari
11am a kano tayiwa aunty Salma, tana zuwa gdn mum ta wuce ta sameta tayi kuka idonta duk sun kumbura nunawa tayi kamar batasan abinda yake faruwa ba tace mum baki da lpy ne? Ai gara rashin lpy da abinda yake damuna, subahanalla me yake damunki? Dan uwanki ne yake son jefani acikin wani hali wai ya rasa wacece zai aura duk yan matan duniya sai marar asali. wanan ce damuwarki? Kwarai kuwa, to ki kwantar da hankalin ki wanan ai ba abin damuwa bane mum, bakisan me Allah ya rubuta akan abin ba, ni a ganina indai yarinyar mutuniyar kirki ce kawai ki barshi ya aureta mum.......rufe min baki daga ke har shi Baku da hankali, dama nasan bayan shi zaki bi,,,,,,,basu San shigowarsa ba muryar sa kawai sukaji yana cewa don Allah mum ki temaka min na aureta, sister don Allah kisa baki mum kar sai bayan na mutu kizo kina Dana Sani, Sbd wallahi idan baki bari na aureta ba mutuwa zanyi, ya karasa mgnr yana kuka, itama aunty Salma kukan take. Ka mutu mana wanan wacce irin tsinanniyar yarinya ce da take Neman wargazamin family na? Wanan ai ta zama annoba wai a INA ma kasanta? Ya zama dole tabar garin nan a yau, ko kuma nasa akasheta, bari na kira Dan lami akarada ya samomin address dinta, yanajin haka ya mike ya fice daga gdn


Direct gdn da nake ya nufu a hargitse yace ki sauri ki shirya duk wani Abunki me amfani, zanzo na daukeki mutafi BAGAUDA a daura mana aure, kuma ana daurwa zamu bar kasar Sbd haka ki sauri ki shirya Kai kawai na gyada masa ya fice daga gdn, yana fita na hada kayana na bawa baba mero 30k nace ta koma gd, sanan nasa hijabi da nekaf, na dauki key din mota baba mero tana kuka nima inayi na fice daga gdn.


Direct police station na tarauni naje nayi musu bayanin abinda ya kawoni, suka binciko file din sukace tabbas anan ne, saidai Wanda yayi handling case din a waccan lkcn yayi ritaya, nace to su taimaka min da address din gdnsa naje, sukace to, 10k na basu su raba nayi godiya na tafi.


Alhamdulilla na sami gdn mutumin a naibawa yake, kuma na sameshi yayi min bayani cewa matar tace a wani asibiti ta satoni me suna Dr Eze clinic $maternity a Zaria, unguwar chikaji, godiya nayi masa sosai na bashi 10k, sanan na dauki hanyar zariya


Maman Aysha
[10/14, 9:53 PM] Chopy: [10/4, 12:09] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
1⃣8⃣0βƒ£βž–1⃣8⃣5⃣


Tafiyar 2 hours ne ya kaita zariya, da tambaya ta sami unguwar, tana shiga cikin unguwar ta tambayi asibitin aka nuna mata, saidai abinda ya firgitar da ita shine asibitin ya tsufa sosai daga gani an Dade baa bude shi ba, na Dade a bakin wajen a tsaye daga baya na hango wani dattijo da shekarunsa zaikai 55 yana zaune a kofar gdnsa, karasa wa wajensa nayi na durkusa na gaisheshi shi, sanan nace don Allah baba tambaya nake yace inajinki yan nan, ni yar jarida ce, nazo ne nayi tambayoyi akan asibitin can, kuma na ganshi a rufe, wai ai asibitin nan yakai shekara 19 da rufe wa, meyasa aka rufe shi baba? Sbd an sace wata jaririya a asibitin, to yanzu a INA zan samu me asibitin baba? Yarinya me asibitin nan tunda yayi ritaya ya koma jaharsu dama Dan anambara state ne. To don Allah zaka iya tuna iyayen yarinyar da aka sace? Kuma don Allah suna raye ko sun mutu? Yana nan a Raye, uban dakina ne sati uku daya wuce ma naje wajensa yatemakamin da kudin gado 1 million ya bani, mutun ne me tsananin kirki da temako, amma yafi shekara goma da komawa Kaduna, kuma akwai matakan tsaro sosai a gdn, domin kuwa be zama dole abarki ki shiga ba nima don securities din gdn sun sanni ne, sbd ni tsohon driver sa ne. cikin farin ciki nace baba nice jaririyar da aka sace don Allah ka taimaka min ka kaini gdnsa a Kaduna yanzu, nayi maka alkawari zan baka 500k nima, aa yarinya ya zaayi ban sanki ba na yarda dake, yanda rayuwa nan ta koma, gaskiya bazan je ba, zan dai yi miki kwatance kije durkusa wa nayi nace don Allah baba ka taimaka min kaifa da bakinka kace akwai tsaro a gdn, idan naje ni kadai ba zaa barni na shiga ba wallahi ni ba macuciya bace, to shikenan idan dai har da gaske kk ke yarsa ce to tabbas yau kakata ta yanke saka domin kuwa a wancan zamanin ma million daya yasa duk Wanda ya samoki, Amma ba a sameki ba, to Amma kinada abinda zaki nuna musu da zasu yarda cewa ke yarsu ce? Eh inada shi, to shikenan Allah ya kaimu lpy nace amin.


Cikin nutsuwa nake tuki na matsu mu karasa kd naga iyayena farin ciki ne fall zuciyata ji nake kamar a mafarki, wai yau nice naji wani Abu game da iyayena, wata zuciyar tace wani Abu kawai? Ai yau ranace da bazaki taba mantawa da ita a rayuwa ba, ni kadai nake dariya Sbd tsabar farin ciki


A kofar wani dankareren gd yace na faka motar, nace masa nan acce unguwa ce baba? Yace unguwar rimi kenan, nace kai Amma unguwar tanada kyau fita yayi yayiwa masu gadi magana batare da mata lkc ba muka shiga gdn. Gate uku muka tsallake kafin mu hango kofar falon shiga gdn, fadar haduwar gdn baa magana, a kofar falo muka tsaya ya kirashi a waya ya fada masa cewa yana tafe ne da wani abin alajabi da mamaki, abin mamaki na me kuma mallam musa? Yallabai kayi mana izini mu shigo zaka ga komeye, OK shigo, bude mana kofar akayi muka shiga muka zauna a falo few minutes sai gasu shida kyakyawar matarsa waje suka samu suka zauna, sanan yace inajinka mallam musa, wanan yarinyar ce ta sameni tayi min bayani cewa itace yarku da aka sace shekaru 19 daya wuce, a tare suka mike sanan matar tasa tace cire dikaf din fuskarkarki, ba musu na cire daidai nan neehal take sakkowa daga kan step muna hada ido tayi mutuwar tsaye cikin tashin hankali matar gdn tace tabbas ko shakka banyi ke yata ce, sabd dama Ku identical twins ne keda neehal, saida me zaki kara nuna min na tabbatar da hakan? Hand bag dina na bude na dauko zanin goyo, pink din overall da kuma yar karamar azurfar da mum ta bani na mika mata, a lkc guda suka zube sukayi sujjada a kasa, sanan suka furta alhamdulilla a tare, da gudu matar tazo ta rungumeni tabbas ke yata ce nawal, dama kina da rai, Allah mungode maka daka nuna min wanan rana, zuwa yayi ya janyeni daga jikinta ya zaunar dani akan cinyarsa ya rungume ni tsam ajikinsa da har inajin bugun zuciyarsa neehal ma da gudu tazo ta rungumeni kuka muke sosai ba Wanda yake bawa wani hakuri, mallam musa yana gefe yana kallon ikon Allah, saida mukayi me isarmu sanan kowa yayi shiru, sai alokacin ammi ta tuna ta kira Yaya kamal ta fada masa cikin murna da farin ciki yace yanzu zai biyo flight ya taho. Godiya sosai Abba yayi wa mallam musa sanan ya bashi kyautar 5 million murna wajen mallam musa baa magana daga karshe yayi mana sallama ya tafi


8pm
Zaune muke akan dining muna cin abinci cikin farin ciki da nishadi har Yaya kamal da amaryarsa sun karaso, neehal ce ta kalli ammi tace dama mu yan biyu ne Amma Baku taba fada mana ba? Yaya kamal yace ni na Sani, kece dai baki Sani ba, tace Allah sarki Ashe inada yar Uwa ban Sani ba shiyasa INA yawan kama ammi a daki da kayan jarirai a hannu tana kuka, idan na tambayeta saitace min ba komai, ni kuma nayi zaton ko son haihuwa take, gabadaya akada dariya har Abba sanan ta kalli ammi tace wacece babba a tsakaninmu? Ammi ta cewa neehal kece babba neehal, ke kika fara shan iskar duniya sanan sai ita Abba ne ya rike kafadata yace hankalin mu ba karamin tashi yayi ba lkcn da aka sace ki, kuma ina ne tabbatar miki da cewa tun lkcn muka shiga kuncin rayuwa tun ranar da akace an haifa min Ku ban kara shiga farin cikin da yakai nayau ba, nasan agajiye kike kuje dakin yar uwarki Ku kwanta idan Allah ya kaimu gobe sai ki bamu lbrn abinda ya faru tun lkcn da aka sace ki zuwa yau nace to Abba, nayi musu sallama muka tafi. Tare muka shiga da neehal tanata tsokanata wai dole nace mata Yaya neehal Sbd ta rigani shan iskar duniya. Tunda nake bacci ban taba yin me dadi irin na yau ba


Maman Aysha grp INA fata munyi celebrating din farin cikina daku? πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ hhhhhhhh


Maman Aysha
[10/4, 17:32] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
1⃣8⃣5βƒ£βž–1⃣9⃣0⃣


A bangaran kabeer kuwa, yana fita daga gdn da nake gdnsa ya koma yayi wanka ya hada duk important decuments dinsa, ya shiga mota ya taho gdn a. Hmm me karatu zokaga adon gari mutumin da yake yawo da motoci sama da goma yau tashin hankali yasa yana yawo da guda daya, guda dayar ma shi yake driving da Kansa.


Yana zuwa gdn yaga ba kowa sai megadi daya tambayeshi yace bamufi 30mint da fita daga gdn ba, phone dinsa ya dauko ya fara dialing no ta Amma ya jita switch off, saiya kira baba mero itama tace nace mata ta koma gd ni na tafi Neman iyayena, Amma ban fada mata inda na tafi ba, yana kashe wayar ya kira Faisal ko yasan inda na tafi? Shima yace tun dazo yake kiran layina be samu ba, elbash ya fado masa arai, yana kiransa shima yace rabonsa dani tun jiya da mukayi waya, ya kira aunty Salma ma ya tambaya ko mum tasa a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login