Showing 6001 words to 9000 words out of 41148 words

Chapter 3 - KABEER COMPLETE Book Complete Document by Amina Yakubu.txt

28 Dec 2024

5165

me tsanani don Allah alhaji kayi hakuri da fadar maganar nan, kayimin alkawari ba Wanda zaiji mgnar nan meyasa zaka fada yanzu? Wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata yimin shiru ko ban fada yanzu ba dama wataran dole maganar ta fito, cikin wata dakkyakiyar murya yace Aisha nace na'am inaso yau ki Sani bani na haifeki ba.....innalillahi was inna ilaihir rajuun juyawa nayi na kalli mum nace waye mahaifina? Kamar daga sama naji muryar dad yace itama ba ita ta haifeki ba nan take na fadi sumammiya da gudu aka sami ruwa aka yayyafamin sanan na farfado rungume mum nayi ina kuka me tsuma zuciya nace mum don Allah kice min ba gaskiya bane, don Allah kice ba gaskiya dad yake fada ba, batayi magana ba sai kuka da take me tsanani. Mutsitsika idona na farayi ya Allah kasa mafarki nake....muryar dad ce ta katseni da cewa ba mafarki kike ba dagaske ne bamu muka haifeki ba, wato abinda ya faru shine....


18yrs back
Nakai Jidda asibiti bada shirin haihuwa mukaje ba sbd cikin wata 7 ne, saidai muna zuwa da aka dubata sai akace haihuwa ce, haka na zauna inata addua har Allah ya sauketa lpy, da sauri nurse din tazo tace na kawo kayan baby, sai alokacun na tuna bamu dakko ba, sai nace Amma zanje na kawo yanzu tunda ba nisa sosai. Harna shiga mota zan tayar sai nurse din ta kara fitowa da sauri tacemin iam sorry to say babyn ta koma, saida ka debowa uwar kayanta jiki ba kwari nace to na tafi. Na wuce ta jkin wani gdn gona saina hango cincirindon mutane, sai nima na karasa wajen na tambayi me ya faru sukace wata mata ce ta sato jaririya, ta fada cewa wani Dan siyasa ne yasata ta sato masa yar, Amma bata karasa bayani ba ta mutun, nace INA yar aka miko min ke kinata shan hannu kina kuka, shine na roki yansanda da su barmin ke zan rikeki. Nan take mukaje police station aka bude miki file, suka bani takardu nayi signing aka kafa shedu, sanan na basu cikkaken address dina, na barki a hannun yan sandan na koma asibiti bayan ansallamo Jidda direct police station muka wuce, nayi mata bayanin komai sanan na damka amanarki a wajenta tare da alkawarin ba Wanda zaiji sai ranar auranki.


Wanan shine abinda ya faru kuma nayiwa Excellency bayanin komai yace ya yadda zai aureki a haka, Amma dake baki da mutunci, kuma ke ba gudar jinina bace kika ki bin umarni na, sbd haka inaso ki Sani daga yau bani bake, ki tattara komatsanki kibarmin gdna sbd ko yar Dana Haifa acikina bata isa ta kaucewa umarnina kuma naci gaba da zama da itaba, ballantana ke yar tsintuwa, sbd haka ki manta da kin taba sanin wani me kama dani arayuwarki, mun rabu dake har abada. Mum yace idan ka mata haka bakayi adalci ba, ina kake tunanin zata nufa yanzu? Ta tafi ko inama niba damuwata bace. Tabbas ba damuwarka bace sabda bakai ka haifeta ba, Amma inaso kasani ba ita kadai ka kora ba harni ka kora domin kuwa bazan taba zama agdn nan ba tare da Aysha ba.


Maman Aysha
[9/10, 15:15] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
4⃣5βƒ£βž–5⃣0⃣


Mama ce tayi wata shewa aidama ance sannu sannu bata had a zuwa, nidama nasan komai Daren dadewa asiri zai tonu, an Dade ana nunawa yayyana banbaci agdnan akan ki Ashe ma yar cin arziki ce, Allah ya raka taki gona. Haka na mike na fara Jan kafata da kyar na shiga daki da tattara kayan da nasan zasu min amfani, na janyo katuwar troly na hayen idona ya kafe, Ashe idan mutun yana kuka da hawaye ma rahamane? Falon na dawo na durkusa agaban Abba nace ga mukullin motarka nagode da kulawar da kuka bani, kuma harna mutu bazan taba taba mantawa da abinda kukayimin na alkairi, nagode Allah ya saka muku da alkairi Allah ya biyaku da gdn aljanna. A dakire yace ki rike motar ai taki ce, jiki ba kwari na mike nace mum don Allah ki yafemin, nasan kinyi dawainiya dani irin wadda kowacce Uwa takewa danta,kinyi fama dani tun ina jaririya nagode Allah ya saka miki da mafificin alkairi, kuma insha Allah zanci gaba dayi miki addua irinta da da mahaifi harna koma ga mahallicina, nagode Allah ya kaddara saduwarmu. Jan trolley nayi nafara tfy, da sauri mum ta rike hannuna jirani nazo mu tafi Aysha, ai nima na gama zama a gdnan sbd yau alhaji ya tabbatar min da ya daina sona, tunda ya koreki banga amfanin cigaba da zama dashi ba, alhaji rubutamin takarda ta mu taffadAi idan kinga mun rabu saidai idan mutuwace ta raba, kuma in banda ke da abinki kin manta cewa ni na baki amanar Aisha, kuma yanzu na karba sbd haka yanda na koreta kema dole kiyi hakuri da ita barima ki gani, wayarsa ya dauko ya kira abbanta bayan sun gaisa ya fada masa duk abinda ya faru, shi kuma yace a bata wayar yana bata abbanta yace mijinki ya fadamin abinda yake faruwa, sbd haka kibi umarnin sa idan kika sake kika fita daga gdn bada izninsa ba, ban yafe miki ba kina jina ko? Cikin tsananin kuka tace eh, sanan dad ya kalleni yace you can go. Harna je bakin kofa mum ta kara kirana daki ta koma ta debo wasu kaya ta miko min, wanan sune kayan da suke jikinki lkcn da muka karfeki, wanan kuma zanin goyen ne, wanan kuma sarka tace lkcn dana saya 500k ce Amma yanzu nasan tafi haka ki sayar kiyi amfani da kudin. Inayi miki addua Allah ya takaita miki wahala, yayi gaggawar hadaki da iyayenki cikin dauko, Allah yayi miki albarka kawai ta juya daki da sauri, nima da gudu na bude motata na fita daga gdn.


AmmaTafiya nake Amma bansan inda na nufa ba, saida nayi tafiya me nisa har na Dan wuce BUK new side sanan na tsaya a gefen titi na kifa kaina akan sitayari na fara kuka, ban farga ba naga 10:45pm na kalli wajen da nake ko motsin mutane babu, elbash ne ya fadomin a rai kawai saina kirashi hlo beauty ya akayi? Kazo kan titin gwarzo road gaba da new side kadan ina wajen. Tuki yake kamar zai tashi sama sbd shi a bompai yake, akwai nisa a tsakaninsu Amma sabd gudun da yake sharawa, kuma ba yawan motoci sbd dare ya fara a 30minute yaje wajen acikin mota ya sameni beauty meya faru kika zo bayan gari kika zauna? Cikin kuka nace komai ma ya faru elbash su dad basu suka haifeni ba, bansan iyayena ba, ba wani mutun da zan nuna nace Dan Uwana ne, bansani ba ko iyayena suna dare ko babu dad ya koreni a gdnsa yanzu banida kowa aduniya kuka yaci karfina. Ya salam Aysha zaki Iya driving? nace eh, to shiga mubar wajen nan ki shiga gaba zan ringa binki a baya zoo road zamu kinji nace to.


Maman Aysha
[9/15, 11:22] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
5⃣0βƒ£βž–5⃣5⃣


Tun a hanya ya sanar da Yaya bilal suna zuwa brodan Elbash ne Uwa daya uba daya. suna isa kofar gdn aka bude musu gate suka shiga da motocinsu matar Yaya bilal da faraarta ta karbe mu, sanan aka kaimin kayana guest room, elbash ya kira yayanshi gefe yayi masa bayanin komai sanan ya rokeshi alfarmar na zauna a gdnsa zuwa next WK idan amaryarsa ta tare sai na koma gdnsa. Ni kuwa tunda na shiga guest room din nake kuka Wanan wane irin rayuwa ce? Dad meyasa kayimin haka don Allah? Me yasa bakayi hakuri kaci gaba da zama dani ba why pliss? Kuka nake me tsanani kaina banda ciwo ba abinda yake elbash ne ya shigo dakin Aysha har yanzu baki dena kuka ba? Don Allah kiyi hakuri nasan kina cikin wani hali Amma ki sani akwai Allah, kuma shi yafi kowa sanin abinda yasa kika sami kanki acikin wanan halin, inaso ki mika al amuranki a wajen Allah, kuma kiyi tawwakali insha Allah zai zame miki alkairi, nima nabar aiki a pyramidTV, sbd ke dama na nemi aiki a wajen, so tunda yanzu bakyanan nima dole na tafi. Wato abinda ya faru kafin na fara aiki a pyramid TV ina daya daga cikin masoya kallon program dinki, kuma cikin lkc kadan naji na kamu da sonki kawai saina yiwa dad dina mgn inaso ya Samar min aiki a pyramid da yaki Amma dana matsa masa dole yaje ya sama min, ranar dana fara reporting na roki manaja daya hadani aiki dake sbd na sami saukin samun kanki, saidai Dan banzan kwarjininki ya hana nayi miki mgn, daga baya saina gane kinfi karfina sbd ke zubin matar manya ce irinsu adon gari, tun daga lkcn na canja son da nake miki da irin Wanda Yaya yakewa kawarsa, ina tsananin sonki beauty ina jinki tamkar ciki daya muka fito dake. Sbd haka don Allah ki dena cewa baki da kowa ni zan zame miki Uwa, uba, kuma broda in Allah ya yadda zan rikeki a bisa amana kuma zan temaka miki wajen nemo familynki. Na sami aiki a CBN kuma next WK ne daurin aurena Sbd haka zaki zauna anan gdn zuwa next WK idan amaryata ta tare saiki koma gdn, kuma munyi shawara da Yaya zan yiwa daddynmu mgn ya Samar miki aiki, Sbd kwanan zaa Debi maaikata, kuma dad dinmu ne chairman na civil service commission. Don Allah kiyi hakuri ki cinye jarabawar da Allah ya Dora miki kinji beauty nace to fita yayi ya kawomin yoghurt da pcm nasha sanan na kwanta ya rufemin kofar ya tafi.
[9/15, 15:40] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
5⃣5βƒ£βž–6⃣0⃣


Haka naci gaba da rayuwa a gdn Yaya bilal, matarsa aunty Kulsum tanada kirki saidai na fahimce dana da kishi sosai, shiyasa nake kaffa kaffa saina tabbatar mijinta ya fita office sanan nake fitowa na tayata aiki, sanan yana dawowa nake komawa daki bazan fito ba sai baya gdn. Kullum elbash ya zuwa musha hira dashi yana Iya kokarinsa yaga ya Sani walwala da farin ciki, gabadaya lkcnsa ni yake bawa shi kullum burinsa ya ganni acikin walwala, yauma as usual elbash yazo muna ta hira sai aunty Kulsum tace gaskiya ina tausayin amaryarka elbash, me yasa kikace haka aunty na? Gani nayi kullum anan kake yini, ko irin Dan shirin nan da angwaye suke kai bakayi, dariya yayi yace su sadik abokina sun gama shirya komai, shiyasa na taho wajen yar kanwata ko beauty? Murmushin yake kawai nayi.


1 WK later
Yaune aka fara gudanar da bikin elbash, run da aka fara bikin ko waya elbash baya samun damar kira, aunty Kulsum ta bukaci da muje wajen bikin Amma naki sabd nasan staff din pyramid TV zasu, koma duk jama'a sun San abinda ya sameni, so banaso na hadu dasu, ba kunya tace min ni kuma banaso na tafi na barki da mijina a gd, Sbd gaskiya kinada fitinennan kyau idan na barku komai zai Iya faruwa shiyasa nake tsananin tausayawa amaryar elbash Sbd zata kunshi bakin ciki. Yanzu kiyi tunanin inda zaki ki zauna kafin na dawo, wasu zafafan hawaye ne suka zubomin nace bari naje gdn siyama kawata, idan kin dawo saikimin waya, to shikenan, ni na fara fita daga gdn sanan ta tafi gdn surunkanta inda ake gudanar da bikin


1wk later
Anyi biki angama lpy amarya ta tare a gdnsa dake ring road dad dinsa ne ya Gina masa gdn kyauta ya bashi. Ina daki a kwance ina aikin kuka naji muryarsa aunty Kulsum tana tsokanarsa ango kasha kamshi sai yau aka sami damar fitowa, haka dai suka gaisa ya shigo dakina ya salam beauty har yanzu baki dena kuka ba dauki mayafiki mu tafi shi ya dauki trolley din muka fito nayiwa aunty kulsum godiya muka tafi. boys qtrs din gdnsa ya bani ciki da falo da toilet ne gdn nasa yayi kayau sosai sabd zaikai 15 million shi kanshi ginin BQ din yayi kyau, kuma elbash ya gyara min duk wani Abu najin dadin rayuwa ya sakamin Sbd TV plasma me kyau ya saka. Bayan mun ajiye kayan yace akwai abinda kk bukata ko abinda be miki ba? Nace komai yayi nagode allah ya saka maka da gdn aljanna yayi murmushi yace amin, sanan yace mu shiga ciki yayi introducing dina awajen amarya tunda muka shiga naji gabana yana faduwa kujera ya nunamin yace na zauna ya kira ta nace to. Sun dade kafin su fito, harna fitar darai dasu sai gasu ta makale ajikinsa kaina yana sunkuye har suka karaso suka zauna ina dago kai muna hada ido naga ta mike cikin bscin rai tace Aysha Ahamad TURAKI itace yarinyar dakake fada cafdi ai wallahi bazai yiyyu ba gaskiya ban yadda ba idan sonta kake kawai ka aureta Amma ya zaayi na zauna da wanan kyakyawar yarinyar agida daya bayan ba muharramarka bace shut up Rahama ban kawo Aisha gdn nan ba saida kika amince, me yasa yanzu zakimin haka? Da zan aureta da ban aureki ba sabd na riga saninta kafin ke, na dauki Aysha ne tamkar blood sister na kuma bazan miki dole ba, idan har kince bazaki zauna da ita ba bazan takura miki ba ke matata ce kuma ina sonki so kinga Dole na baki hakkinki, Amma inaso kisani zuciyata bazata taba yafe miki ba domin kuwa kin hanani na aikata aiki na alkairi. Cikin kissa tace ba komai angona magna ta wuce na hakura Allah yasa haka shi yafi alkairi cikin farin ciki yace amin nagode, sanan yace don Allah inaso ki riketa a bisa amana kinga kin girme mata shekararki 22, ita kuma 18 so kinga a matsayin kanwa take a wajen ki Sbd haka don Allah ki rike amana saida tayi wani fari da ido sanan tace ba matsala sanan ya kalleni yace Aysha ki dauki rahama a matsayin yayarki kinji nace to zama tayi akan cinyarsa swit heart na hada maka zobon fa na dauko maka? Ina ganin haka na mike nace zan koma daki saida safe elbash yace tsaya kisha zobo mana nace na gode, na fita na koma daki saida nayi kuka me isata sanan nayi bacci. Washe gari bayan elbash ya fita wajen aiki aunty rahama tazo ta kirani nayi mata aiki haka na wuni ina aiki har girki ni nayi mata tana kwance. Haka rayuwata taci gaba agdn kullum wuni nake ina aiki saita dadaici ya kusa dawowa sanan tace na koma part dina aunty Kulsum matar Yaya bilal ta kara zugata tsana take nunamin a fili kwata kwata banajin dadin gdn, gashi elbash idan ya fita tun 7am sai 6pm yake dawowa. Gashi ta hana shi zuwa part dina, sbd tace idan ya kara shiga saita fadawa iyayensa ya kawo mata karuwa ya ajiye a gd, shiyasa yake lallaba ta yanzu mostly saidai muyi mgn dashi a waya, Amma duk da haka yana Iya kokarinsa yaga ya kyautata min.


2wks later
Elbash ya shigo da farin ciki yace albishirnki nace goro yace an daukeki aiki zaki ringa koyarwa a wata secondary sch a yankaba da murna na karbi offer nace nagd Allah ya saka da alkairi yace amin munde zakiyi reporting nace to.


Monday 8am
Na fito cikin shiri na shiga nayiwa aunty rahama sallama yauma as usual ta farfadi bakaken maganganunta Wanda idan da sabo na saba. Naje nayi reporting principal ya bani js3 da ss1 na ringa daukar su English, naji dadin kasancewa da yaran sosai, daga fara zuwana har mun saba dasu. Tunda na fara zuwa aiki na rage shiga damuwa sabd ko rahama ta bata min rai INA haduwa da students dina sainaji na manta.


3 months later
Na goge sosai da teaching malamai da students din sch din kowa sona yake na saba sosai da sch din. Yauma as usual yara sun fita break mu kuma muna staffroom muna ta hira dasu malama halima principal ya aiki a kirani ina zuwa naga fuskarshi a cikin damuwa saida yayimin nasiha sanan ya mikomin takarda a envelope yace daga ministry of education ne aka aiko ya bani sun sallame ni daga aiki sabd sunyi bincike sun gano ni ba yar asalin jahar Kano bace, saidai idan zanyi casual


Maman Aysha
[9/15, 18:48] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
6⃣0βƒ£βž–6⃣5⃣


Innalillahi wa inna ilaihir rajuun kawai na Iya fada sana na karba dama da bag dina a hannuna sbd haka INA fitowa daga office din PC mota ta kawai na shiga na tafi gd, direct part dina nashiga na fara kuka kamar raina zai fita waye yayi min wanan abin? Waye yasan niba yar asalin Kano bace, kuma me natare mishi? Haka na wuni a kwance band aikin kuka ba abinda nake matar gdn ma batasan na dawo ba. Sai wajen 6:30 lkcn na tabbatar elbash ya dawo yaci abinci sanan na kirashi a waya ya najin muryata cikin kuka ya mike a zabure rahama ta Dora kanta a ciyarsa besam lkcn daya dauke ya tashi ba tana tambayarsa me ya faru ko takanta be bi ba ya nufi part dina yana zuwa yace meya faru naji kina kukan da kika Dade kinayi takardar na dauko na mika masa ya karfa ya karnta, shima salati ya saki, sanan yace bari ya kira dad dinsa yaji ko yasan Wanda ya fadamusu . aikuwa dad dinsa yace duputy governor ne ya dasu su rubuta sabd ba asan asalina ba, sai yace to dad ka dauke ta contract mana, bazaiyiyu ba elbash sabd ya kafa matakai akanta, ka bawa abokin naka hakuri, to shikenan dad nagode. Matsowa yayi ya kama hannuna kiyi hakuri beauty don Allah karki daga halinki akan wanan abin, nayi miki alkawari zan nema miki aiki a company, idan company ni ne bashida damar da zaisa a koreki kinji nace to, zanyi tafiya zuwa abj gobe kwana uku zanyi, idan na dawo zansan ya zaayi nace to nagd ban karasa maganar ba kuka yaci karfina kamani yayi ya Dora kaina a kafadarsa yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login