Showing 33001 words to 36000 words out of 41148 words
Chapter 12 - KABEER COMPLETE Book Complete Document by Amina Yakubu.txt
kamar taku ce tayi yawa sanan ya kalleni yace kanwarmu nice to met you, dariya nayi nace nice to meet you too, na fita na basu waje.
Da kyar ya samu ta hakura sukaci gaba da hirar su ta soyayya bayan ya tafi ta shigo dakina aikuwa na fara tsokanar ta hydar ya kasa ganeta a tsakanin mu, tace kaddai ki cika baki gb zamu je kanon ai ki bari idan kabeer ya ganeki saiki ji dadin tsokana ta, nace to shikenan Allah ya kaimu gben tace amin, hugging dina tayi tace gud night sis
Maman Aysha
[10/8, 21:33] Amina Yakubu: πππKABEERππ
2β£0β£5β£β2β£1β£0β£
Washe gari muna gama break fast muka fara shirin tafiya kano har dakin Ammi naje nace don Allah ammi ki rokar min Abba ya barni na zauna idan munje na karasa mgnr a kunyace dariya mum tayi tace to Mrs kabeer zan fada mishi Amma kinsan zamuyi missing dinki ko? Saidai muyi hakuri kawai Sbd mu faranta miki, nace thank you mum, you're well come my dota.
Wani hadaddan material muka sa me combination din yellow and red, dinkin Riga da siket ne kayan sun mana kyau sosai red rose silk muka daura, komai iri daya mukasa tunda muka fito falo ammi da Abba suka fara wani irin smiling na farin ciki, Abba ne yace you looks so beautiful my twins Allah ya raya min Ku mukace amin Abba, sanan yace Aysha kince zaki zauna acan ko nace eh yace to shikenan ba matsala muje ko, a tare muka fita a Lexus din Abba muka tafi da motocin escort dinsa guda uku daya a gaba, biyu a baya.
Asibitin muka fara zuwa, muna fitowa daga mota su mum dinshi suna shigowa sai su abba suka tsaya su shiga tare, kuma mukayi gaba, neehal tace ni zan fara shiga, kuma ni zanje a matsayin ki nace to, a zaune yake yayi daidai akan Gado da laptop a gabanshi, sanye yake cikin wata red shirt armless sbd hannunsa, da blue jeans ya kara kyau yayi fresh kamar ba jinya yake ba, shida sulaiman PA ne kawai a dakin, muna shiga neehal ta wuce bakin gadon direct, taja kujera ta zauna a kusa dashi sanan ta gaisheshi ya amsa yana wani Dan iskan smiling, tace honey ya jikin yace da sauki daidai nan ya jiyo muka hada ido nace kanina INA wuni? Yana wata yar iskar dariya yace don't take me as a fool Aysha, kina ganin zaki iya bace min? Tun shigowarku na gane ki, wata sansanyar dariyar farin ciki nayi nace shiyasa nake kara sonka you're very smart, karasawa bakin gadon nayi nace Mrs hydar saiki tashi ki bani kujerar na zauna tunda ya ganeki INA wata yar iskar dariya, tana tru baki ta mike ni kuma sai tsokanar ta nake, na kalli kabeer nace Yaya hydar kasa ganemu yayi, neehal tayi caraf tace ai sabd dare ne shiyasa, nace ba wani nan kareshi kawai kike muka yi dariya gabadaya, Abba ne suka shigo a tare sukace dariyar me kuke tayi ne haka? Na basu lbrn abinda ya faru suma sukayi ta dariya sukace ya kamata kiyiwa hydar abinda zai ringa ganeki da sauri neehal. Bayan sungaida kabeer Abba yace muje gdn naku Aysha nace to, gabadaya muka tafi har mum dinsu kabeer dama tun jiya na fadawa mum zuwanmu.
Muna shiga compound din rayuwar gdn gabadaya ta dawo min, INA gaba suna bina a baya muka shiga har part din mum, INA shiga su junior suka taho da gudu zasu rungumeni, da suka ga neehal kuma sai suka tsaya suna kallonmu, suka rasa wajen wa zasu acikinmu cikin tsananin farin ciki mum ta tare mu saidai itama tsayawa tayi tana kallonmu, ta kasa gane ni aciki ina ganin haka naje na rungumeta kawai saina fashe da kuka, sanan tace su ammi su zauna taje ta kira dad ya fita shigo dasu Abba da Yaya kamal, sanan yaje ya kira mama dasu Yaya zee duk aka hadu, bayan angama gaisawa abbanmu yayi bayani cikin nutsuwa, sanan yayi wa dad godiya sosai kuma yayi mishi addua domin acewarsa bashida abin da zai saka mishi, shima dad ya rokeni gafara yace wallahi besan ya akayi yaji tsanata da rashin tausayi na a zuciyarsa ba, Amma wallahi yayi nadama daga baya, mamace tayi caraf tace nima don Allah ku yafe min, nice silar komai Sbd ni nayi asiri na rabaku Amma wallahi nayi nadama Sbd tun yanzu ga sakamako Nagani da muna gani kamar mu kadai ne gatanki, Ashe babanki babban mutun ne a 9ja, don Allah ki yafemin kinji nace bakomai Allah ya yafe mana gabadaya. A gdn mukaci abinci sanan muka kuma asibiti harsu mum da dad, daganan su Abba sukayi sallama suka dau hanya
Maman Aysha
[10/14, 10:22 PM] Chopy: [10/9, 12:39] Amina Yakubu: πππKABEERππ
2β£1β£0β£β2β£1β£5β£
Su Abba suna tfy mum da dad ma sukace zasu tafi sun bar min su junior dake a gdn zan kwana tace idan na gama zata tro azo a daukemu nace to, suna tfy saiga elbash da murna na tareshi muka shiga ciki ya dubashi ya kara yimin murnar ganin iyayena, sanan yace motata tana nan zai mayar da batir din yakai a wanketa ya kawo min gobe nace to nagode, saida na rakashi har bakin mota sanan na koma. Haka muka zauna da aunty Salma da mum wadda yanzu take nunamin tsananin so, munata hira Sbd yanzu jikin nashi da sauki any time zaa iya sallamar shi ana kiran idar da sallar magrib su mum da aunty Salma sukace zasu tafi, kuma nasan Sbd sunaso subarmu musake ne, amma wani lkcn suna kaiwa 11pm basu tafi ba. Saida na rakasu har bakin mota sanan mukayi sallama na juya na fara tfy kenan kamar daga sama naji muryar Faisal yana kirana, tsayawa nayi har ya karaso ya kalleni yace kin kyauta Aysha, kin samu parents dinki Amma ko ki fadamin, yau kusan 1 WK kenan ba lbrnki yanzu ma Dr marwan ne yake fadamin adon gari yayi accident, kuma yace kema kina nan. Ashe dama soyayya kuke da adon gari? Kunya ce ta kamani gabadaya na kasa bashi amsa, any way ba matsala INA sonki, ban taba son wata ya mace a duniya kmr yadda nake sonki ba Amma inhar zanyi miki adalci, ya zama dole nayi hakuri ki auri abinda zuyarki take so, Allah yasa haka shi yafi alkairi a hankali nace amin nagode Faisal Allah yayi maka sauyi da wacce tafini, wani smiling yayi yace samun irinki da wahala Aysha, na Riga nayi loosing mu karasa ciki na dubashi ko? Nace to a tare muka shiga har cikin dakin muna hada ido dashi yasha kunu, Faisal ne ya karasa har bakin gadon yayi masa sannu ya amsa da fara'arsa har saida suka taba hira ma sanan na rakashi ya tafi. Kabeer yaji haushin rakashi Faisal din da nayi, Amma sai ya basar mukaci gaba da hira ban bar asibitin ba sai wajen 10pm dakyar na tafi sabda banaso nayi missing din shi su junior har sunyi bacci sai daukar su akayi, lkcn da muka karasa gd mum da dad suna zaune suna hira nima na zauna mukaci gaba da hirar sai wajen 11 muka kwanta.
Washe gari da wuri na tashi nai break fast nayi wanka, sanan nayiwa kabeer kunun gyada da kosai Sbd yace shi yake so, sai kuma nayi masa paper soup din kifi ragon ruwa soyayyen irish da kuma plaintai, nayiwa mum sallama dad ya bani key din motarsa camry 2015 na tafi da ita asibiti INA zuwa na samu har yayi wanka ya shirya an gyare dakin banda kamshi ba abinda yake akusa dashi na zauna nace gud morning my soul, yace morning beauty ya gajiya? Murmushi kawai nayi nace me zanyi serving dinka? Yace kunu da kosai INA budewa kamshin ya doki hancinsa, ni nake bashi a baki harya koshi sanan na zuba masa kifin ma na bashi saida na tabbata ya koshi sanan na debe kayan na sasu a gefe naje na wanke hannuna sanan na dawo mukaci gaba da hira, daidai nan Dr Abdul da marwan suka shigo Dr Abdul yace ai sallamarka ma zamuyi sai kawai aci gaba da treating dinka a gd yace to shikenan nagode sosai doctor yace a ba wani Abu, Husna tana tambayar ka idan ka warke ya kamata ka kawo mana madan su gaisa yace ba matsala zan kawota insha Allah awaya na kira su mum nace karsu zo an sallame shi zamu taho yanzu. Ni na rikeshi mukaje har mota, bayan ya zauna na zagaya na shiga su Sulaiman suna binmu a baya muka nufi gdn mum dinsu, a part dinsa na gdn zai zauna an tanadar masa duk wani abu na jin dadi daka sani munyi waya dasu Abba na fada musu ansallameshi, Abba yace neehal da hydar zasu zo gobe sauki shirya ki biyosu nace don Allah Abba kayi hakuri ko sati daya nayi, be gama warkewa ba fa dariya Abba yayi yace kai aysha na fuskanci kinfi son kabeer damu, wai ke bakisan munyi missing dinki bane? Dauriya kawai fa muke nanda lkc kadan nasan Kabeer zaice zai turo, so kinga bamu wani zauna dake sosai ba zaayi auren ki, nace to shikenan Abba Allah ya kaimu goben yace amin. Yauma sai dare na koma gd.
Maman Aysha
[10/9, 14:55] Amina Yakubu: πππKABEERππ
2β£1β£5β£β2β£2β£0β£
Yauma da wuri naje gdn, dasu basma mukaje ga yayyan aunty Salma khairat da nabil suka hadu sunata wasa, wajen 12pm su neehal suka karaso ita da hydar muka zauna ake ta chapter a dakin, saika manta ma zaman jinya muke sabd hanun yayi sauki sosai nida aunty Salma muka shiga kitchen muka shirya abinci me rai da motsi kowa yaci ya koshi, sanan mukaje gdn elbash nida neehal matarsa ta haihu mukayi musu barka ta you and your babys dream muka bi nasayi kayan baby na 20k, ita kuma aunty rahama na sai mata turmin Hilton da murna sosai ta tare mu, itama tayi mamakin kamar da muke da neehal mun Dade muna hira ta rokeni gafara nace na yafe mata, elbash ba karamin murna yayi ba, mukayi musu sallama muka koma gdn su kabeer Bayan munyi sallar laasar su neehal sukace zasu tafi nan take gabana ya fadi Sbd Abba yace na bisu, kirnta gefe nayi nace Abba fa yace na biku dariya tayi tace Mr Luv ammi tace a kyaleki, idan sunzo saiku tafi wato son kabeer ya rufe miki ido ko missing dina ma bakya yi ko? Wallahi ba haka bane sis...dadai nan mukazo bakin kofar falon waje, wata pritty girl muka gani tana ta hada su sulaiman da allah akan su barta ta shiga ta duba adon gari amma sunki, neehal ta kalleni tace my sis akwai aiki a gabanki don gaskiya wanan kabeer din naki saikin kara daura belt, kinsan he is more than handsome, dole yan mata su bishi, ammafa bance kije kiyita damun kanki ba sbd yana sonki sosai. Mu muntafi sai munyi waya, nace to Allah ya kiyaye INA daga mata hanu muna dariya har suka bace, sanan na koma ciki.
5pm yahuza suya
Yan mata da samari ne zaune anata shakatawa kowa yana harkar gabansa, a gefe grp din yanmata ne masu ji da Kansu da yawan su zai kai su goma suna shan ice cream suna hira kawai saiga wata kyakyawar yarinya tazo wajen tace hii friends sukace hlo ralma ya gari tace gari ba dadi, kamar ya ba dadi? Baku da labrn ADON GARIN yan mata da samari yayi accident a tare sukace what! Yaushe kenan? Cikin damuwa tace yau kwana hudu har an sallameshi ya koma gd, tab aini banji lbrnsa ba kwana biyu I tot yayi tafiya ne, ya salam ya zama dole naje Dubiya koda bazai amsamin ba, kinsan ganin fuskar guy din nan kadai farin ciki yake sani koda kuwa hararata yayi, ramla tace aikuwa dakyar idan zaa bari ki ganshi, domin kuwa PA da body guards dinsa ne a gdn sai sunga dama ake shiga nima yanzu daga can nake da renin hankali littafi da Biro suka bani sukace na rubuta sunana. Zuby dake gefe tana sauraransu tun lkcn da akace yayi accident tayi mutuwar zaune a zuciyatta tace yanzu adon gari yayi accident har ya kwanta a asibiti Amma ban sani ba, cikin tashin hankali tacewa body guards dinta kuzo mutafi, tana tafiya suna take mata baya suka nufi gdn mum.
Su neehal suna tfy na bude motar da nazo da ita na dauko wata rigata aciki, na shiga dakin aunty Salma na gdn nayi wanka na dauki rigar ta Dana dauko a mota English gown orange me spagetti hand ta Dan tsuke daga sama rigar tayimin kyau sosai na yane kaina da karamin orange gyale sanan na fesa turare a falo na sami mum da aunty Salma suna hira nayi musu sannu na wuce dakinsa, a zaune yake da friends dinsa harda Dr Abdul sunata hira, INA shiga na juyu da baya da sauri mikewa yayi ya biyo bayana, a corridor muka hadu yace ya kk koma? Kafin nayi mgn yace inason shan fruit salad nace to, saida na fadawa mum a kunyace sanan na nufi kitchen na fara hada mishi in few minutes na gama lkcn Dana kaimasa shida sadik ne kawai a dakin, INA shiga sadik ya fita a kusa dashi na zauna na fara bashi kamar wani karamin yaro yana sha muna hirar mu ta soyayya
Kamar an jefota daga sama ta shigo dakin suna hada ido ta fashe da kuka haba kabeer don Allah, wacce irin kiyayya kake nunamin? Ina matsayin matar da zaka aura, Amma kayi accident harka kwanta a asibiti ban sani ba. Kiyi hakuri zuby, wallahi hnklna ne baya jikina, komawa tayi ta daya gefenshi ta zauna sanan cikin kissa tace ya jikin? Yace da sauki dauke fruit salad bowl din tayi tace bari nima na samu ladan kawai ta fisge spoon din hannuna ta fara bashi abin mamaki sainaga ya bude baki yana karba, na kafeshi da ido amma ko ajikinsa nan take naji zuciyata ta fara zugi mikewa nayi zan fice daga dakin sainaji ya ruko hannuna yace INA zaki? Murmushin karfin hali nayi nace zan Dan Baku waje ne Ku Diskanta kaida madan dinka na zare hannuna na fice daga dakin
Maman Aysha
[10/14, 18:45] Amina Yakubu: πππKABEERππ
2β£2β£0β£β2β£2β£5β£
Ina fita daga dakin yace ta daina bashi fruit salad din haka ya ishe shi, bayan ta ajiye bowl din tace honey dama inason mgn dakai, ba tare daya kalleta ba yace inajin ki, yauwa Kasan a yadda muka yanke date din bikin mu nida kai, yau saura sati uku kenan bikin, kuma Kasan har yanzu a family Ku ba Wanda yaje gdnmu akayi mgn, ni kuma gsky banaso na rasaka, shine nace me zai hana tunda baka da lpy idan time din yayi a daura auran idan yaso daga baya sai a daura auranku da Aysha kuma a hada bikin lkc daya ayi, murmushi yayi sanan yace duk yanda kk ce haka zaayi Allah ya kaimu lkcn cikin kissa da farin cikin samun nasara tace amin
Ni kuwa INA fita daga dakin wasu hawaye suka cika min ido, saida na tsaya a corridor na goge sanan na fita falon, aunty Salma da mom suna zaune na musu sannu na wuce daki, aunty Salma ce ta biyoni tace aysha me yake faruwa naga kmr ranki a bace yace? Kakaro murmushi nayi nace kaina ne yake ciwo shine nake so na Dan kwanta tace OK bari na baki pcm kisha Allah ya sauwake nace amin
Tana fita na shiga tunani wato kabeer har yanzu yana son zuby? Anya da gaske yana sona kuwa? Wata zuciyar tace INA ganin tausayin ki kawai yake, amma gaskiya yafi son zuby. Wani kishi naji ya addabi zuciyata kawai saina dauki phone dina na fara kiran neehal, bugu daya ta dauka INA kuka na bata lbrn abinda ya faru, nace kuma da yacemin baya sonta fa, kuma Itama Dan jaraba har yanzu taki hakura dashi, neehal tace ke waye zai samu opportunity din data samu kuma yayi wasa, ai samun miji kmr kabeer sai me tsananin SAA da kuma rabo, Sbd kabir allura cikin ruwan kogine, kinga kuwa sai me tsananin rabo ne zai sameshi kema kinyi shirme da kikayi fushi kika fito daga dakin, Aida saiki tsaya Ku buga da ita, my sis inaso ki sani kabeer yanada wata baiwa da ba kowanne namiji bane yake da ita, Sbd haka ki tashi ki koma dakin ki bashi duk wani caring daya kamata, kinji ko nace to dariya tayi tace Mrs kabeer saina kara jinki nace ok thank you my sis kicewa ammi I miss her so much. Ina kashe wayar na mike na kara gyara fuskata, sanan na fice zuwa dakin, INA shiga ya Bini da wani irin kallo ko zama banyi ba nace me kake sha'awa ci a dinner? Yace yimin cuscus da vegetable soup to kawai nace na fita daga dakin, cikin 30mint nagama komai, har zobo me hade da kankana nayi masa, INA kaimishi na koma daki nayi sallar magrib shima ya fita yayi salla zuby kuwa Dan gadara a dakin tayi salla. Ban koma dakin ba saida nayi sallar isha'i INA shiga naga zuby tana serving dinshi abincin wani irin bakin ciki naji ya cika min zuciya juyowa tayi tai wata dariya sanan tace sannu da kokari, cewa nayi bari nayi assisting dinki tunda ke kinyi girki kin gaji, murmushin yake nayi nace karki damu duk daya ne ai, zama tayi a kusa dashi tana bashi lbri shi kuma yana cin abincin yana dariya, yama manta da INA wajen danaga haka kawai saina hau online na fara charting da yan grp dinmu na maman aysha grp muka fara hira sainaji zuciyata tayimin dadi. Time to time yake dagowa ya kalleni, ni kuwa na manta dasu. Bayan ya gama yace Aysha abincin yayi dadi thanks allah yasaka da alkairi, ba tare da na dago ba nace amin. Shiru dakin yayi na yan mintuna sanan zuby ta mike tace honey zan tafi saina dawo gobe, yace to Allah ya kaimu.
Tana fita ya dawo kusa dani ya zauna Aysha naga kmr kina fushi