Showing 30001 words to 33000 words out of 41148 words

Chapter 11 - KABEER COMPLETE Book Complete Document by Amina Yakubu.txt

28 Dec 2024

5113

daukeni, itama tace ba ita bace, zama yayi a cikin motar yana kuka kamar ransa zai fita haba Aysha don Allah meyasa baki gujeni ba sai lkcn da nake tsananin son kasancewa tare dake? Meyasa baki gujeni ba sai lkcn da sonki ya gama yi min illa ajikina? Why Aysha? Meyasa baki kirani nazo an daura mana aure ba kk tafi? Kuka sosai yakeyi daidai nan elbash ya kirashi hlo yallabai munyi waya da mum dinta yanzu tace ta kirata dazu tace mata ta tafi zariya, OK to nagode elbash, ko nazo mutafi zariya tare? A ka bari kawai ba matsala zan tafi ni kadai, duk yadda ake ciki zanyi maka waya, to shikenan Allah ya kaika lpy yace amin. Decoments dinsa daya debo a gd ya cire daga cikin motar ya shiga ya ajiye a dakina, sanan ya dawo ya shiga motar ya dau hanyar zariya.


Gudu yake kamar zai tashi sama zuciyarsa cike da tunani iri iri, driving yake Amma hankalinsa baya kan titin sosai, yaje daidai daka tsalle hannunsa ya kwace, yaje ya daki wata bishiya dagan be kara sanin inda Kansa yake ba, compliment card dinsa aka samu acikin motar sai suka sami no Sulaiman PA suka kirashi suka fada mishi inda abin ya faru, cikin tashin hankali yace gasu nan zuwa, da hanzari ya kira sadiq suka tafi da helicopter cikin kankanin lkc suka isa wajen kafin su karaso sun yiwa Dr marwan friend dinsa waya yace su hadu a orthopedic Hosp din Dr Abdul (asmaul Husna).


Likitoci hudu ne akansa suna bashi emergency care saida suka tabbatar ba matsala sanan suka kyaleshi, saida har yanzu he is unconscious, kuma ya sami fracture a hannunsa na hagu . saida komai ya lafa Sulaiman PA ya kira mum ya fada mata, cikin tashin hankalin da basu taba fuskanta a rayuwarsu ba suka taho asibitin ita da aunty Salma, tunda sukaje suke aikin kuka mum sai fadin maganganu take na nadama, ba yanda su Suleiman ba suyi da ita akan ta tafi gd su su kwana a wajensa ba amma fur mom taki, tace dole ita zata kwana haka suka hakura suka kyaleta.


Yanda sukaga dare haka sukaga safiya, duk bayan mintuna mum take leka kirjinsa taga ko yana numfashi, da safe ma dakyar ta yarda ta koma gd tayi wanka abinci kuwa ko zancen sa baayi kallo daya zakayi musu ita da aunty Salma ka gane suna cikin matsanaicin tashin hankl.


Kaduna
Tun wajen karfe goma na safe gdn mu ya cika da yan Uwa da abokan arziki, masu zuwa yiwa su Abba murnar ganina, kowa ka gani fuskarsa dauke take da faraa duk wanda sukazo sai neehal da Yaya kamal sun fadamin sunansu da kuma dangantakarmu dasu, haka dai akayi ta introducing dina acikin family. Gashi dai acikin farin ciki nake, amma Kasan zuciyata fall yake da tunanin kabeer ko ya yayi da yazo ya samu bana nan? Ko a wane hali yake yanzu? Duk inda yake nasan yana cikin tashin hankli Sbd kabeer yana sona, to yanzu ya zanyi kenan? ki kunna wayar ki ki fada masa kinga parents dinki, yess haka zaayi, da sauri na dauko na fara dialing... Amma sainaji akashe, wasu hawaye ne suka fara zuba a idona masu zafi, daidai nan neehal tazo tace naje ammi tana kirana.


Tun jiya da daddare ammi take Neman layin aminiyarta ta fada mata taga yarta data bata Amma baa dauka ba, sai yanzu ta kara trying kawai saitaji ta dauka da farin ciki mum tace Maman yara tun jiya nake Neman ki na fada miki Allah ya bayyana min nawal, amma shiru baki dauka ba lpy kuwa? Ba lpy Haj Asiya, kabeer ne yayi accident kin ganmu a asibiti har yanzu baisan inda Kansa yake ba, salatin da ammi tayi ne yasa gabadaya muka maida hankalinmu wajenta har Abba, Abba ne ya fara tambayar meya faru? Kabeer ne yayi accident yana asibiti unconsciousness....inajan ambaci kabeer naji zuciyata ta fara bugawa Abba ne ya katse min tunani da cewa ai sai mu shirya mu tafi zama be kama mu ba, amma Ku neehal da Aysha Ku zauna, tunda da baki a gdn idan yaso in zamu kara komawa sai aje daku, da sauri nayi karaf nace don Allah Abba aje damu yau din, yace to shikenan kuyi sauri Ku shirya, ana cikin haka Yaya kamal ma ya shigo yace yanzu wani friend dinsa yayi mishi waya ya fada mishi, bakaken Arabian gown mu kasa nida neehal wato me karatu kamar da muke da neehal tayi matukar baci, komanmu iri daya ne voice dinmu, dariyar mu, tsayinmu everything saidai kawai na Dan fita haske kadan, kuma ni inada dimple ita kuma bata dashi Amma duk da haka ba karamin me curiosity bane zai ganemu, su Kansu Abba da ammi rikide musu muke, a Prado din Abba muka tafi da motoci guda uku na escort dake Abba senator ne.


Bamusha wahalar gane asibitin ba, muna shiga cikin garin kano rayuwata ta baya ta fara dawomin allahu Akbar, Allah me yanda yaso wai yau nice nazo kano acikin gatana, a cikin kwana daya kacal Allah ya canja min rayuwata, yanzu duk rayuwar Dana debe lkc inayi ta zama tarihi dama ance duk me hakuri yana tare da Allah, alhamdulilla allah nagode maka.


Neehal da Yaya kamal ne suka fara shiga dakin da aka kwantar dashi, cikin rashin Sani aunty Salma ta rungume ta tana cewa Aysha INA kika shiga? Ya akayi kk samu lbri? Mum dinsu ce ta katse ta da cewa ke Salma neehal ce fa wanan ina kika sami Aysha kum...bata karasa magna ba muka shigo tare da ammi, gabadaya su kamewa sukayi suna kallon ikon Allah idona yana kaiwa kan kabeer na tafi da gudu na rungume shi INA wani irin kuka me taba zuciya, kabeer don Allah karka tafi kabarni, wallahi idan ka mutu nima mutuwa zanyi...


Maman Aysha
[10/14, 9:53 PM] Chopy: [10/6, 17:51] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“kABEERπŸ“πŸ“


1⃣9⃣0βƒ£βž–1⃣9⃣5⃣


Kuka nake sosai me ban tausayi, Abba ne yazo ya janyeni daga jikin kabeer ya rungumeni ajikinsa, cikin sanyin murya yace min dama kin sanshi ne? Kasa bashi amsa nayi sai aunty Salma ce tace eh Abba itace matar dayake so ya aura, kuma akan hanyar tafy neman ta ya hadu da wanan tsautsayin, mum dinsu kabeer ce tace ikon Allah lalle rashin Sani yafi dare duhu, Ashe aysha yarku ce? Na dauki tsanar duniya na Dora mata, hannunsa ya fara motsawa a hankali sanan ya bude idonsa, a hankali ya fara bin yan dakin da kallo 1 by 1, saidai ya kasa dauke idonsa daga kaina da kuma neehal, idan ya kalleta saiya juyo ya kalleni kuma ya kasa magna. A hankali ya furta ya Allah idan marfarki nake Allah ka farkar dani, karasa wa bakin gadon nayi nace ba mafarki kk kabeer, komai kake gani gaskiya ne Allah ya amsa adduarmu ya nuna min parents dina, wanan twins sis dina ce sunanta neehal a hankali ya furta dama ke blood sister kamal ce? Ya salm Allah me yadda yaso, kokarin mikewa yake Amma Sbd karyar da take hannunsa saiya kasa saida Yaya kamal ya temaka mishi, sanan ya zaunar dashi, Dr marwan da Yaya kamal ne suka taimaka mishi yayi wanka yayi brush sanan aka bashi abinci yaci, sanan mum tace su Abba su karasa gdnta suci abinci ba yanda basuyi dani na bisu ba Amma naki nace zan zauna a wajensa suje su dawo, haka suka dunguma suka nufi gdn mum nida Salma kawai suka bari a dakin, dagowa yayi yace aysha ke bakici abincin ba, nace na koshi kici ko kadan ne kinji, nace to hira muke cikin tsananin farin ciki da son juna


Su Abba basu dawo ba zai after 4, suna zuwa befi da 15 mint ba sukace mu tafi, nan take hnklina ya tashi na marairaice nace don Allah Abba Ku barni na zauna anan, idan an sallame shi saina koma gd wata dariya Abba yayi wadda na tabbata ta yake ce, kafin yayi magana mum dinsu kabeer ta rungume ni tace Aysha kiyi hakuri ki bisu Ku tafi kinji, suna tsananin bukatar kasancewa tare dake, ko kin mata sun dauki shekaru masu yawa suna kishiruwar rashin ki, sai jiya Allah ya bayyana ki baki wani zauna tare dasu sosai ba kuma kice zaki zauna anan? Ki kwantar da hankalin ki time to time saiki ringa zuwa kina dubashi kinji nace to. Fita sukayi gabadaya suka barni dagani sai shi a dakin, na karasa jikin gadon nace zan tafi Allah ya kara sauki yace amin harna fara tafiya ya riko hannuna na juyo a hankali muna hada ido ya sakarmin murmushin sa me tsada sanan yace iam going to miss you Aysha, I wish you safe journey, I Luv you a hankali na furta I Luv you too INA kuka saida na tsaya na goge hawayen daya zubomin, sanan naje na sami su Abba a waje muka tafi


Maman Aysha
[10/6, 20:58] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
1⃣9⃣5βƒ£βž–2⃣0⃣0⃣


Sai jikin magrif muka shiga kd muna zuwa gd kowa ya shiga yayi wanka mukayi salla, sanan muka taho dining mukaci abinci, bayan mun gama Abba yace na basu lbrn rayuwata na zauna na fara basu tunda ga farko har karshe ba Wanda beyi kuka ba acikin su, sun tausayamin sosai sanan Abba yace haka Allah yake jaraftar bawansa, in banda jarabawa ya zaayi ace kamar yata tana yawon Neman inda zata zauna, Allah yasa haka shine mafi alkairi a rayuwarki nace amin. Sanan na kalli su Abba nace Abba kuma kunji lbrn wacce ta sace ni, kuma me yasa ta saceni? Yace kwarai kuwa, me aikinmu ce ta sace ki wato abinda ya faru shine


Some yrs back
Ni Dan asalin garin makarfi ne, mahaifina shine sarkin garin, kuma tsohon attajiri ne, bayan na gama karatun sec sai maihaifina ya turani Cairo nayi university, kuma anan na hadu da mahaifiyarku ita balarabiyar misra ce so familyn mum dinki gabadaya suna misra kanwarta jalila ce kawai anan 9ja ita Hutu tazo suka hadu da mijin. Bayan na auri amminku har an haifi kamal saina fada harkar siyasa na tsaya takarar chairman din garinmu, da temakon Allah da temakon ubangidana alhaji Mohd BAGAUDA na samu nayi nasara, Sbd kirki da kuma kyautatawa jamaa da muke, bayan munciye shekarunmu sai yan garin suka kara tsaidani, a lkcn kuma akwai abokin takarata alhaji tasi'u hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, lkcn da ake rungutsumin siyasa zaayi zabe, daidai lkcn aka haifeku bazan iya fadin irin farin cikin da nayi ba a wanan ranar domin kuwa nurse din data yimin albishir din haihuwarku ma kyautar mota na bata. Alhaji tasi'u shine yasa a saceki Sbd bokansa ya fada masa cewa duk duniya ba abinda nakeso kamar Ku, kuma dole sai anyi sacrificing daya daga cikin Ku asirin zai yuyu, wanan dalilin ne yasa ya hada baki da Uwani me aikin mu ya bata 1million ta saci daya daga cikin ku. A gdn gonarsa na kura sukayi da ita zasu hadu, Dake Allah ba azzalimin bawansa bane akan hanyarsa ta zuwa kura daga zariya yayi accident, kuma yasa aka nemoni yayi min bayani da bakinsa ya nemi gafarata, washe gari Allah yayi mishi rasuwa. Tun daga lkcn muke Neman Uwani amma ba lbrnta har se yanzu da kikazo mana da lbrn ta rasu. Mun shiga tashin hankali marar misaltuwa a game da batan ki, kullum acikin addua muke Allah ya bayyana mana ke indai kina Raye, Sbd haka ba abinda zamu cewa Allah sai godiya. Jibi insha Allah zamu koma duba kabeer, idan munje zaki rakamu gdn mutumin daya rekeki muyi misu gdy nace to Allah ya kaimu yace amin, naga dare ya fara ya kamata muje mu kwanta ko? Mukace to, kowa ya mike Yaya kamal ma yayi sallama ya tafi gdnsa.


Dake angyaramin dakina INA zuwa na haye gado na kwanta saidai fur bacci yaki dauka na so da tausayi n adon gari ne a zuciyata, phone dina na dauko na fara dialing no Amma akashe, wani irin xugi da zafi zuciyata ta fara in har banji voice dinsa to confirm bazan iya bacci ba, to wa zankira ya hadani dashi? Aunty Salma zuciyata taban amsa, da sauri na fara dialing no ta bayan mun gaisa nace mata ya me jiki tace da sauki, Amma ni na dawo gd Dr marwan ne zai kwana a wajensa nace ayya to Allah ya sauwake saida safe. Yanzu ya zanyi kenan? Neehal ce ta shigo dakin da sauri tace my sis ga hydar zaku gaisa INA karba yace kanwarmu ya kk? Nace lpya kalau, haka dai yayi tamin surutu, daga karshe mukayi sallama na bata wayar yanayin yanda suke ta soyayyarsu a wayar sainaji hnkl ya kara tashi, kawai saina fashe da kuka da sauri neehal tayi sallama da haidar tazo ta rungume ni meya same ki kk kuka sis? Na rasa yanda zanyi nayi mgn da kabeer, kuma gashi bani da no Dr marwan, hydar yanada ita bari nasa ya tro mana, ba mata lkc ya tru ai kuwa da sauri na fara dialing yana dauka nace ya hadamu, cikin unique voice dinsa yace aysha bakiyi bacci ba? Ta Yaya kake tunanin zan iya bacci bayan phone dinka akashe take? Tunanin ka ya hanani bacci kabeer, tausayin halin da kake ciki ya hanani sakat, ji nake kamar na cire ciwon ya dawo jikina, inasonka kabeer, INA maka son da ko kuda banaso ya tabaka, kuma gashi na jawo maka ciwo kana zamanka, duk ni na saka a halin da kake ciki yanzu don Allah kayi hakuri kuka ya kwacemin, da wata irin cool voice yake magna stop crying Aysha, don't blame your self bake kika jamin ba haka Allah ya rubuta, kinga iam not feeling fine, kuma kukan ki yana kara tayar min da hankali so don Allah kiyi shiru, yanzu lkcn farin ciki ne, kinga yanzu ba abinda zai hana muyi aure ko? Nace eh, so dariya da godewa Allah ya kamata kiyi ba kuka ba kinji? Nace to, nayi missing dinki sosai yaushe zaki dawo ki ganni? Abba yace jibi zamu zo, Amma idan nazo bazan tafi ba, ni zanci gaba da kula dakai har saika warke, wata sansanyar dariya yayi yace are you sure? Nace yes, still dariyar yake da gaske zaki iya rikeni, ki feeding dina, kimin every thing da nake bukata, nima dariya nayi nace emana, yace to shikenan we shall see, I love you Aysha, nace I Luv you too, gud night OK night


Maman Aysha




[10/14, 10:22 PM] Chopy: [10/8, 18:50] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
2⃣0⃣0βƒ£βž–2⃣0⃣5⃣


Washe gari a makarfi muka wuni aka zaga dani gidajen yan Uwa alhaji kakanmu kamar ya cinye ni sabd murna kowa sai Jana yake ajiki a hanya nake cewa dad dama haka muke da dangi? Yace su yanzu yan Uwana kawai kk gani, zamu sa rana muje misra kiga familyn amminku nace to Allah kaimu yace amin.


Sai wajen 6pm muka shiga kd, muna zuwa muka watsa ruwa mukayi sallar magrib, sanan nabi lfyr gado na kwanta bansan lkcn da bacci ya dauke ni ba, sai can naji neehal tana cemin na tashi muje muci abinci, nace nifa ba kullum nake cin dinner ba kuje kuci kawai ni zansha cooker Oates da snacks, wato bakya son cin abinci ko? Zan hadaki da ammi ai, da gudu ta fita dining tana zuwa ta tarar su kadai ake jira, ammi tace INA Ayshan kuma? Wai bazataci ba, cooker Oates zata sha Abba yace kirata, a waya ta kirani nazo Abba yace dole sainaci abinci nace Allah Abba nakoshi, Abba yace to je ki hada Oates din kisha nace to.


Ina daki INA duba abu acikin laptop dina saiga neehal ta shigo cikin shirin ta tace my sis hydar ne yazo, Amma ke zaki fara fita a matsayin nice, so nake na gwadashi na gani ko zai ganeki, amma fa sai kin cire kunyar nan taki, nasan zaki iya tashi ki shirya nace to, pyjamas ne ajikina Riga da wando kawai saina Dora bakar after dress akai ta bani turenta nasa, sanan tace swit man nake ce masa, kuma INA Dan durkusa wa idan zan gaisheshi nace to. Wit confidence na tafi INA zuwa bakin kofar naji gabana ya fadi, Amma kawai saina basar na shiga nayi mishi sallama ya amsa sanan na durkusa na gaisheshi na samu waje na zauna juyowa yayi ya kalleni yace nayi missing dinki sosai my baby, tunda sis dinmu ta dawo kin manta dani cikin shagwaba nace to ba muna waya ba, eh munayi, amma ba kamar eye contact ba, to ai yanzu gashi ka ganni ko? Murmushi yayi yace eh, kinsan INA sonki da yawa shiyasa, nafiso kullum na saki a gabana INA kallon ki, neehal ce ta shigo da tray ta durkusa ta gaisheshi nan take ya zama comfuse, zuba mana ido yayi yana so ya gane wani Abu kawai saina katse shi da cewa to ga kanwar tamu nan saidai ka manta baka tambayeta me jiki ba, Kasan fiancΓ©e dinta mukaje dubawa a kn jiya, may b zakasanshi ma Mr kabeer M BAGAUDA, yes nasan shi very nice guy, bansan shine patient din ba ai da naje na dubashi, wallahi baby guy din yanada kirki sosai wani farin ciki naji ya kamani, shaf na manta plan din da muka hada nace saika zauna dashi ma zakaji ya kara burgeka, shiyasa nake kara sonshi wallahi....... Cikin kidima da tashin hankali hydar yace kaddai maganar daya kirani kwanakin baya ya fadamin ta tabbata? Neehal a gabana kk cewa kina son wani?mikewa nayi nace relax Mr hydar, iam aysha tunda ka kasa ganemu ga neehal din can, sis iam sorry kinsan indai zaayi maganar kabeer dole sainayi magana, amma wacce magna kabeer ya fada maka hydar? Da mum dinshi taso hada auran shi da neehal, shine ya kirani ya fadamin Sbd na dauki mataki, juyawa yayi ya kalli neehal yace baby abinda yasa nace zan kawo lefe urgent kenan, turo baki tayi tace ni nayi fushi dakai tunda ka kasa gane ni, ta juya ta fara tafiya mikewa yayi da sauri yayi hugging dinta yace iam sorry my dear

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login