Showing 21001 words to 24000 words out of 41148 words

Chapter 8 - KABEER COMPLETE Book Complete Document by Amina Yakubu.txt

28 Dec 2024

4581

megidanta sanan nayi wanka nasa wata fitted gown ta wani material green, dinkin yayi min kyau sosai, simple make up nayi na murza dauri me kyau, sanan nasa sarka da Dan kunne nayi wanka da turare na dauko laptop dina na fara kallon wani film da nayi down loading wa men hubbi maqatal. Sai wajen 8 me gidan ya fito ya zauna a dinning ya kwashi abinci, da zai fita aunty Salma tazo tace naje mu gaisa dama ta bashi lbrina tun dare, har kasa na durkusa na gaisheshi shi ya amsa da fara'arsa kuma yayimin godiya. Yana fita tace nazo muyi break, kunun gyada da plantain kawai na Iya ce, aunty Salma tace Aysha akwai abinda yake damunki, ko vakyason zama damu ne? Sbd dazu dana fito naga hawaye a idonki, nace wallahi ina son zama daku akwai kannena wanda ada nayi zaton uwarmu daya ubanmu daya, junior da basma kusan age mate din su nabil ne mu shaku sosai da yaran ni nake musu komai, duk lkcn dana tunasu sainayi kuka nakejin dadi. Eyya allah sarki kici gaba da hakuri insha Allah wata rana sai lbri, nace hakane kam. To me yasa kuma bakya son cin abinci? Nace ba kin ci nake ba, is my nature, dariya tayi tace aiko gashi nan bakya kiba,nima dariyar nayi daidai nan handsome ya shigo, yau kuma danyen boyel ne ajikinsa cream color gashin nan ya kwanta yayi luf muna hada idon na nemi nutsuwa ta na rasa sabd balain kyaun da yayi, karasowa yayi yace gud morning sis tace morning broz, nace masa INA kwana saida ya Dan lumshe ido ya bude sanan yayi murmushin da yake tafiya da imanin yan mata yace lpy kalau ya kwanan bakunta? Nima murmushin na mayar masa har saida kumatuna ya lotsa nace lpy kalau, duk abinda muke aunty Salma na kula damu, Amma saita yi kamar bamu take kallo ba. Ni nayi serving dinsa ya fara cin abincin saidai duk dagowar da mukayi sai mun hada ido, wani irin kallo yake min Wanda yasa wani mugun sonsa yake yawo acikin jinin jikina, har naji bazan Iya jurewa ba, mikewa nayi na koma daki na kwanta na fara tunani saura 2 month ayi bikinsa wasu zafafan hawaye suka fara zuba a idona, ina sonka kabeer, don Allah ka furta kace kana sona, at least ko baka aureni ba zanji sanyi a raina kuka nake sosai banji shigowarsa ba sai kamshin turaren sa daya daki hancina ya salm Aysha meya faru kuma? Don Allah ki fadamin Aysha, ko zaman gdn nan ne bakya so? Nace aa to fadamin don Allah meye matsalar ya karasa maganar cikin tsananin damuwa. A zuciyata nace ciwon sonka ne matsalata, Amma a fili sai nace ba komai iyayena na tuna bansani ba ko sunada rai ko sun mutu, daugoni yayi ya rungumeni a ajikinsa kiyi hakuri beauty kinji, asan is painful Amma addua zakici gaba dayi indai suna raye Allah yayi gaggawar bayyana su nace amin, hankii ya dauko a aljihunsa ya gogemin hawaye sanan ya kuramin ido da sexy eyes dinsa yayi magana da wata irin voice din da ban taba sanin yanada ita ba yace kayimin alkawari bazaki kara kuka ba, dakyar na Iya cewa na daina, sanan yace zanje mu karasa meeting da muke da Mr President ina ganin sai dare zan dawo idan da wani matsalar kiyimin text kinji? Nace to, kuma don Allah ki ware kuci gaba da hirarku da aunty Salma, kada kai kawai nayi. Harya fara tyfy ya jiyo yace ko Dan smiling bazaki yimin ba? Wani lallausan murmushi nayi masa da har saida kumatuna ya lotsa, sanan yace thank you my sis ya fice ya barni da kewarsa da kuma kamshin turarensa


Maman Aysha
[9/27, 14:55] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“
1⃣4⃣5βƒ£βž–1⃣5⃣0⃣


Shakuwa ce me tsanani ta shiga tsakanina da aunty Salma, wadda har jinta nake kamar blood sister na, na sake da ita sosai har tsokanar juna muke, shima mijinta dake Dan harka ne harshi ake zama ayita hira.


Yauma kamar kullum bayan mun kammala dinner muna zaune anata hira har megdn khairat tayi bacci akan cinyata, nabl kuma INA koya masa h/work saiga adon gari ya shigo, bayan an gaisa yace kwantar da yarinyar nan ki zobomin abinci yunwa nakeji nace to, daki na kaita Sbd tunda nazo gdn tare muke kwana da ita, cusccus akayi wit vegetable soup Dana zuba yace kawomin nan, cin abinci akan carpet yafi dadi nace to yanaci anata hira, nabil yazo ya dameshi sai tsalle yake ajikinsa duk ya hanashi cin abincin ma, yace kai tashi kaje ka kwanta kona Zane ka, banda kiriniya ba abinda ka iya. Dariya aunty Salma tayi tace ai kai ya gado, Sbd ka bani wahala kana yaro, nan ta shiga bamu lbri tace bana mantawa lkcn da muka zauna a London a makotanmu akwai wani yaro, sunanshi selvesta duk ya girmemu, gashi Dan lukuti idan ya kama mutun baya yi masa da wasa Sbd karfinshi super master ake ce masa ga brodana da tsokana kuma idan yayi tsokanar aka dakeshi sai mum tace dole saina fita na rama masa, duk lkcn daka tsokano shi gbn har faduwa yake,Dariya mukasa gabadaya, mijinta yace kai Ashe matsoraciya ce ke, tace wallahi Dan bakaga yaron bane. Adon gari ne yace au ni na manta ma Ashe wayoyina a kashe suke bari na kunna, aikuwa kamar jira suke yana kunnawa calls ya fara shigowa, kuma duk rabi yan matane wasu ya amsa, wasu yayi rejecting kuma don jaraba yana gama amsa wani kiran, wani yake shigowa. Mijin Aunty Salma ne yayi dariya yace ka zama business cenre duk suka kwashe da dariya banda ni da kishi ya cikamin zuciya, wani kiran ne ya kara shigowa da hanzari na dago na kalle shi sainaga yayi wani smiling ya furta zuby can Kasan makogaransa cikin wata sansanyar unique voice dinsa yake mata magana kanajin hirar tasu ta soyayya ce nan take naji kirjina ya cushe, kaina ya fara sarawa tsananin sonsa ya fara yawo acikin jinina, kawai sainaji bazan iya cigaba da zama a wajen ba mikewa nayi nace musu saida safe aunty Salma da tun lkcn da yanayina ya canja tana kula dani tace tun yanzu zaki kwanta? nace eh bacci nake ji to shikenan Allah ya tashemu lpy nace amin


Gani yayi hirar tata bazata kare ba, yace kinga zuby I will call you back later, Ina wani important Abu ne, be jira abinda zatace ba kawai yayi switching off. Dariya babansu khairat yayi yace wato hirar da kuke is not an important issue ko? Anya karbuwar data samu guarantee ce kuwa? Murmushi kawai yayi, aunty Salma tace ai wanan brodan nawa sai a hankali, Amma inaji ajikina akwai yarinyar da zata karya alkadarinka kwanan, kuma you can't denied it. Wata shegiyar dariya yayi yace haba sis kin manta halina, ADON GARI ne fa, aini bana bari son wata ya shiga zuciyata ballatana har ya dameni, nidai zasu soni kuma har zuciyarsu ta nemi bugawa akaina, Amma ni ba wata wadda yarinya data isa na shiga wani hali akanta. Haka kace ko broz? Eh, to shikenan we shall see, mikewa yayi nizan tafi saida safe. Suka amsa da To Allah ya kaimu yace amin


Ni kuwa tunda na shiga daki nake kuka, wani irin son shine yake addabata wanan wane irin rayuwane? Na kamu da son mutumin da besan inayi ba tabbas ko shakka banyi, ciwon son adon gari shi zai zama ajalina, ita kam zuby Allah ya taimaketa tazo duniya a SAA, Sbd ko be aureta ba, zata iya bada tarihin yayi soyayya da ita, ya Allah ka ciremin son mutumin nan a zuciyata don na fuskanci mayaudari ne, yayi amfani da bewar da Allah yayi mishi ya koyamin sonshi, kuma yayi ignoring dina koda wasa yaki ya nuna yana sona, why me kabeer? Me yasa baka tausayi na, me yasa baka barni da bakin cikin rashin iyayena ba, kake kokarin kara jefa rayuwata acikin matsala, wata zuciyar ce tacemin karki zargi kabeer Aysha ki zargi kanki, Sbd shi besan ma kina sonshi ba, kinyi mistake da kika bari sonshi ya shigeki sabda ba yanda zaayi mutun me kudi, kyakkyawa Dan asali me tulin yan mata buhu buhu ya amince ya aureki, dole yar asali zai aura. Saida nayi kuka me isata, daga baya kuma wani wahalallen bacci ya daukeni.


Maman Aysha
[10/14, 9:53 PM] Chopy: [9/28, 11:59] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“


1⃣5⃣0βƒ£βž–1⃣5⃣5⃣


Gobe ne ranar da kabeer yace zamu koma kano muna zaune muna hira da aunty Salma wajen 5pm, kawai saiga kabir ya shigo, da gudu yara sukayi hugging dinsa dake yana nuna musu so sosai, waje ya samu ya zauna yace kuje a shiryaku mu tafi yawo aunty Salma tace bazakaci abincin ba? Eh yau bana sha'awa, zan sami abinda zanci a rose flower sweet and bakery, nayi karaf nace ka bude a garin nan ne? Aunty Salma tace ai baki Sani ba? Aikuwa ya kamata kije, sabda idan kika shiga na garin nan saiki raina na kano, iya kudin shiga kawai 5000 ne, Ki shirya kuje mana, idan kin dawo zaki bani lbr nace to bari na canja dressing.


Wani hadadden filtex lace nasaka, zanen lemon green da orange color ne ajiki, amma orange din bashi da yawa, rose silk na daura orange nasa sarka da Dan kunne na stones suma orange color, 20k na sayesu, mayafi da shoe&bag ma orange zama nayi nai make up sosai a fuskata sanan na fita, takalmin danasa me tsini ne kos kos din takuna ne ya janyo hankalin su zuwa wajena nan take adon gari yayi mutuwar tsaye, bina yayi da wani irin mayattacen kallo da har naji kafata tana hardewa, da kyar na karasa wajen cikin sanyin murya nace na gama yace OK muje, sis sai mun dawo tace to. Shima saida ya biya kudi muka shiga, haka dokar wajen take, gaskiya kabeer ba karamin me kudi bane, domin kuwa rose flower sweet and bakery dinsa na abuja kadai ya isa ya rikeshi, wato fadar girman wajen ma bata lkc ne, ba abinda babu a wajen, akwai swimming pool, wajen wasan yara ya zuba haddadun motoci irin na wonder land, sai wajen lilo na yara daban, na manya ma daban, akwai wajen game din table tennis, basketball, suluka, volleyball dadai sauran su, akwai lafiyayyen garden da aka kawatashi da hadaddadun shuke shuke irin Wanda ko ranka ne a bace idan kaje wajen saika nemeshi ka rasa, sanan akwai restaurant duk wani kalar abinci ko snacks da abinsha akwai shi awajen, in fact idan kana cikin wajen saika manta a 9ja kake.


Tunda muka shiga wajen muke cin karo da hadaddun yan mata da samari, kai har matan aure baa barsu ba duk Wanda ya kallemu saiyaji mun burgeshi Sbd kyau da kuma dacewar da mukayi, direct wajen wasan yara muka je aka sasu mota suna ta murna mota tana zagayawa dasu, wasu kujeru muka samu muka zauna, kawai saiga wasu yan mata guda biyu sunsha kyau sukayi mana sallama, sanan daya daga cikinsu ta dubi adon gari tace don Allah ka temakeni ka bani koda 1 minut ne na ganka, basarwa yayi kamar beji me tace ba, Mr kabeer don Allah ka taimaka min, cikin fushi yace wai bakiga tare nake da wife dina bane, ban yarda ba, ba matarka bace ai daurin auren babban mutun Wanda yayi suna har a kasar waje irinka bazai boyu ba, da yanzu duniya ta Sani Kai musulmi ne kuma da Allah na hadaka, don Allah ka taimaka ka saurareni. Mikewa yayi suka koma gefe sanan ta fara masa bayani ni sunana juwaira Yusuf, dad dina ne minister of education, ranar da akayi bikin bude wajen nan na fara ganinka, kuma tun ranar na kamu da sonka saidai na rasa yanda zan hadu dakai sai yau. Kneel down tayi don Allah Mr kabeer ka taimaka ka aureni koda ata biyu ne Sbd wallahi INA tsananin sonka, naji Amma ki tashi, Sbd gbdaya idon mutane akanki yake ban damu ba kallona da mutane suke ba shine matsalata ba, ka amince da soyayya ta shine matsala ta, to naji tashi muyi magana, mikewa tayi ta zuba masa ido, kiyi hakuri don Allah idan nace zan aureki nayi miki karya, ban taba sha'awar mata biyu ba kuma insha Allah har abda bazanyi ba, kuma na Riga nayi dating matar da zan aura so INA yimiki fatan alkairi Allah ya baki Wanda ya fini, Tahowa yayi ya barta a wajen tana kuka yana zuwa yacemin taso mu tafi garden nace yaran fa? Daya daga cikin staff dinsa na wajen ya kira yace ya kula dasu khairat idan sun gaji ya rakosu guarding yace to


Wajen sabd shakatwarsa kadai ya tanade shi, sai yazo ake budewa ya gyara wajen sosai muna zuwa ya kwanta akan grass carpet ya lumshe ido, ya Dade a haka sanan ya ya bude a hankali ya kira sunana cikin damuwa yace Aysha me yasa yan mata suke bina? me yasa suke cewa suna sona? Akwai kyawawan samari masu kudi, masu class, wasu dunfini kudi ma Amma me yasa yan mata basa binsu Sani? Why me? Banaso nayi hurting din mutun, amma yan matan da suke sona sunsa dole inayi, what am I going to do? Aysha fadamin meye solution? Me zanyi su dena bina ba tare da na wulakantasu ba? Wallahi dani mace ne, da nikaf zan ringa sawa, cikin wata cool voice yayi magana Aysha fadamin me yakamata nayi? Nace kayi aure, idan sukaga kayi aure zasu Dan rege binka. To wa zan aura? Zuciyata har yanzu batasan zuby, na kasa son zuby Aysha, akwai mutumin daya da zuciyata takeso, saidai abune me wahala aurena da ita ya yuyu. Me yasa? Is a secret, tashi yayi ya zauna ya rike hannuna sanan ya kafeni da wani irin kallon daya saukar min da kasala yace ki tayani da addua Allah ya warware min matsala ta acikin ruwan sanyi, will you? Kai na daga masa Sbd gabadaya jikina ya mutu. Wani lallausan smiling yayi yace mrs Faisal, kuna waya kuwa? Nace eh ai na fada masa ma gobe zamu tafi, kai sorry wallahi na manta na fada miki an fasa tafyar gobe, Sbd me? Kinsan dad dinsu khairat yayi tfy ko? Eh, shine tace na taimaka na bar mata ke zuwa next WK saiki tafi, kai gobe zaka tafi kenan? Nan take naji gabana ya fadi, duk da nasaba da aunty Salma, Sbd shi nake jin dadin zaman garin, Ciwon sonsa zai wahalar dani kenan,,,,,,,,Tunanin Faisal kike ko? Kiyi hakuri ai kuna waya, sati dayan kamar yaune a wajen Allah, muje mu tafi naga magarba ta kawo kai


Maman Aysha
[9/29, 17:37] Amina Yakubu: πŸ“πŸ“πŸ“KABEERπŸ“πŸ“


1⃣5⃣5βƒ£βž–1⃣6⃣0⃣


Ana kiran sallar magrib muka shiga gd KB yayi alwala ya tafi masallaci nima daki na shiga nayi alwala bayan mun idar da sallah muka fito falo aka debo take away din da mukayi a rose flower sweet and bakery muka baje gabadayanmu mukaci, sanan aka fara hira, sai wajen 10pm Mr kabeer ya mike yayi mana sallama har yakai bakin kofa ya juyo yace lovely sis ba rakiya? Murmushi nayi nace muje na rakaka har bakin mota na rakashi saida yace bude motar ya shiga sanan yace ina fata sati dayan da aunty Salma ta kara miki be bata miki rai ba? Wata yar sansanyar dariya nayi ace ba damuwa 1 WK din kamar yau ne ai. To ya zakiyi da Faisal? Zaki iya coping da rashin ganin sa harna 2 wks? A zuciyata nace wanan mutumin Dan renin hankali ne, kodai ya gane na kamu da sonshi, shiyasa yake min haka? Amma a fili sai nace face dinsa kawai nayi missing, Amma ruhin mu yanan manne da juna, da har nake jin kamar muna tare. Yanayin sa ne ya canja, cikin shan mur yace min gud nyt.


Yanayin yanda ya shiga damuwar nima sainaji banji dadi ba, jiki ba kwari na shiga gdn aunty Salma tace ya tafi nace eh, to zauna muyi wata magna dake nace to da gaske ne kin dauke ni a matsayin blood sister ki? Nace eh, zanyi miki tambaya Amma don Allah Aysha karki boye min komai ki fadamin gaskyr abinda yake cikin zuciyrki nace to, a zaman da nayi daku na sati daya nan, na fahimci akwai soyayya me zafi tsakanin ki da broda saidai kunki Ku gaskanta hakan a junanku, Sbd haka inaso ki fadamin kina sonsa? Kuka na fara eh ina sonsa Amma kuma nasan yafi karfina, nayi kokarin hana zuciyata ta kamu da sonshi, but I fell, ina tsananin sonshi Amma ba yanda zaayi kabeer ya auri marar asali Irina,,,,,sauri tayi ta rufemin baki karki damu shima yana sonki, naga zallar sonki a kwayar idonsa, nafi kowa sanin halinsa Aysha, kuma inaso ki Sani a sanina bayan ni, kece mace ta farko da kabeer yake zama yayi hira da ita cikin sakin fuska, kice mace ta farko da kabeer ya fita outing da ita, sanan kece mace ta farko da Ya nunawa caring, wanan shi ya tabbatar min da cewa he is in Luv wit you, kuma kema kinyi deserving a so ki, kinada wasu qualities da sai an Tara mata dubu baa sami guda goma irinki ba, matsalar ki guda daya rashin sanin iyayenki, wanan kuma bazai hada aure ba indai yana sonki, mun barwa Allah, yafi mu sanin dalilin da yasa yayi haka. Idan ba zaki damu ba inaso ki ringa amsa wayar Faisal a gabn broda kinji? Nace to, zaki iya tafiya saida safe nace Allah ya kaimu


Washe gari


Sai wajen 9am na tashi na shirya break fast, yau kunun gyda da kosai nayi Sbd aunty Salma tanaso sanan na soya Irish da plantain na dafa ruwan tea komawa daki nayi nai wanka, nasa wata English gown peech color nayi fakin din gashina ya kwanta luf a gadon bayana, idan ka ganni saika ce swara ce, Sbd muna kama sosai, saidai ni dimple dina ya fito sosai.


Sai wajen 9:30 ya shigo gdn a dinning ya samemu muna cin abinci, shima yazo yayi joining dinmu ba karamin murna yayi ba daya samu kunu da kosai Sbd yanaso sosai kallona yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login