Showing 30001 words to 33000 words out of 69452 words

Chapter 11 - BAKAR DAULA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Ameera Adam.txt

Advertisement

04 Jan 2025

6192

ne bai sanar da ni yana da wani ɗan'uwan ba? Idan haka ne kenan yana da alaƙa da zuwanmu wannan azzalumar Daular, ya aka yi na bar shi a filin can na sake riskarsa a wannan ɗakin har na ji ana ambatonsa da sunan Yarima? Ban gama jerawa zuciyata tambayoyi ba balle na bawa kaina amsa na ji ya yi kukan kura ya fisgi ɗaya daga cikinmu ya fara biyan buƙatarsa da ita, kuka nake mai tsuma zuciyar mai sauraro tausayin kaina ya mamaye zuciyata. Yana gama amfani da ita ya rufe ta da duka kamar ya samu jaka har sai da ta daina motsi. Haka ya bi mu ɗaya bayan ɗaya yana amfani da mu, wanda ni ce mace ta ƙarshe da ya keta wa haddi ya raba ni da martabata ta ƴa mace. Tun yana jikina na ji ya fara wani irin munshari mai ban tsoro wanda haka ne ya tabbatar min da bacci ya ɗauke shi, da ƙarfi na ture shi na koma gefe ina ci gaba da hawaye. Dakarun da suka kai mu ba su suka zo suka kwashe mu ba sai da dare ya tsala sannan aka ɗauke mu aka kai mu wani ɓangare wanda na ji suna kira da, ƴantattun bayi. Wani abu da ya tsaye mini a rai bai wuce yadda komai na Yarima yake min kamanceceniya da Jarumin da ke ziyartata ba, sai dai lokaci ɗaya tsanarsa ta mamaye zuciyata na ji danasanin shigowarsa rayuwata. Gari na waye da shi na yi tozali a tsakiyar kaina ina yunƙurin magana na ji ya furta min, "Kada laifin wani ya shafi wani domin kin san kama da wane bata wane." Bai jira cewata ba ya ɓace min da gani, a hankali na miƙe ina zagaya lungu da saƙon wurin tafiyata keda wuya na ji Dogaran Sarki sun zo da shelar kiran gaggawa da Sarki Damina yake yi ga waɗanda aka kai ɗakin yarima.


Wannan shine shafi na biyun ƙarshe na free pages. Hajiyata kada ki bari a yi wannan tafiyar domin wasan yanzu ya fara ɗaukan zafi💃🏼 Wai ko dai Yarima ya warware ne🥵🤣😂


*KU MATSO KU TAHO*💃🏼


Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananin ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂


Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.


Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼


Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰
Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚


*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
[11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*




©AMEERA ADAM


FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️


Last free page 10


🥳 in ka ji busa tabbata Sarauniya ce ta ƙaraso, ina kuke matan ƙwarai, mata ba muna mata ba, shin kin jaraba kayan *HONEY-DROPS* me kike jira har yanzu?, Manyan mata, mata masu aji na ta dafifi wajen kwasar kayan gyara, me ya sa za ki kashe kanki da ƙuruciyarki, ko tsohuwar ma na zuwa karɓar nata, kina fama da matsalar bushewar gaba, ɗaukewar sha'awa da ni'ima, ƙaiƙayi ko ƙurajen gaba, jin zafi yayin tarawa da maigida, sanyi ya taɓa miki mahaifarki?, Kina ta allura da shan magunguna ba su miki aiki ba, wane kalar infection kike fama da shi?, Staphylococcus, Gonorrhea, Syphilis, UTI, STDs ne?, Share hawayenki kukanki ya ƙare je ki nemi *HONEY-DROPS INFECTION FLUSHER* ke da sanyi sai dai ki ba da labari, kin gama cacar kuɗi, cikin kwana uku zaki fitsarar da duk wani sanyi da dattin da ke tattare a mararki, ki gyara zamanki gidan aurenki don sanyi kashe mace yake har buzunta, duk wani magani da za ki sha muddin da sanyi a jikinki iyakar shi cikinki, ba zai sauka ba. Magani ne ingantacce made of herbs, In kin gama da wannan akwai na gyaran other room, akwai Exclusive Gumba ta manyan mata ke nan, ko matar Gwamna ita take sha, ga Gumbar babbar mace mai tada tsohuwar soyayya, akwai fa tsuumi na matan gaske, akwai *HONEY FLOOD TSUUMI* kan ƙiftawar ido ni'ima ta yi ta kwararo miki, akwai BUJENTA JAGAB, da Tsuumin Ɗafau, daga jin sunan kun san akwai zance na bar muku ku ƙarasa, akwai sauran kaya masu zafi🔥


Muna da bridal package


Diamond - 100k
Gold - 50k
Silver - 30k


Ga kuma na postpartum (wanda suka haihu don dawo da martabarsu)


Diamond - 50k
Gold - 30k
Silver - 15k


Kuna iya samun mu ta 08167888934, ko 08067770852






Ba ƙaramin ruɗu da tsananin mamaki ya shiga da faruwar lamarin, a saninsa duk rana kamar wannan matuƙar ya miƙa kuka da buƙatarsa ga Sarauniya Shakundum tana share masa hawaye ta hanyar amsar buƙatunsa. Koda ta daina yin magana amma akwai alamun da yake ji na amsar addu'a da roƙon nashi. Miƙe wa ya yi tsam daga wurin da yake ya fara kai kawo a cikon kogon dutsen cikin mamaki, bakin wani baƙin kasko ya tsugunna ya ɗebo garin sihirtacciyar bishiyar kukar da ya taɓa aika wani ɗan autan aljanu ya ɗebo masa a dajin Buzurul-shusu. Barbaɗawa ya yi da zummar ya ga ainihin abin da yake faruwa da Gunkin Sarauniya Shakundum, kasancewar a ƙa'ida idan har Almuru ya yi babu shi babu ziyartar muhallin Gunkinta. A maimakon komai nata ya bayyanar masa sai gani ya yi wutar ta ɗauke, ya gwada haka ya fi a irga daga haka jikinsa ya ba shi tabbas akwai wani sabon al'amari da yake faruwa. Don haka a gaggauce Boka mai zamani ya ɗauko madubih sihirinsa yana karkatar da shi kusurwar kudu ya fara karanta waɗansu irin ɗalasuman tsafi tun bai ƙarasa ba ya ga jini ya ratsa ta jikin mudubin yana ɗiga. Da sauri a jiye saboda sababbun al'amuran da yake gani masu rikita lissafi, ko tunanin me ya yi sai ya sake ɗauko mudubin yana bincike game sauran al'amuran da ke faruwa a cikin Daular. Tamkar an saka masa hoto a majigi haka ya riƙa ganin duk abin da yake faruwa, yana sake karkata mudubin zuwan binciken Sarauniya Shakundum kamar wancen karon haka ya sake ganin jini na ratsowa ta cikin madubi. Yana nan zaune yana ganin abin da yake faruwa sai ganin wata ƙanƙanuwar wuta ya yi harshenta na ratsowa ta tsakiyar madubin, ruwan tsafinsa da ke ƙoƙon baƙin ƙarfe mai ɗauke da waɗansu irin zanen baƙaƙen aljanu ya ɗauko ya watsa. Amma abin da ya sake tsinka hanjin cikinsa yadda ya ga wutar ta taso masa gadan-gadan har sai da ta fara lasar naman jikinsa. A firgice ya riƙa ɗaukan abubuwa yana jefawa don ya samu wutar ta mutu amma kamar ƙara mata makamashi yake yi, babu shiri ya ƙarasa bakin wani gajeren kabari ya ɗebi ƙasar saman kabarin a tafin hannunsa. Nan take ya fara kiran sunayen aljanu, sai da kira sama da goma sannan ya rufe idonsa yana kiran Aljanu Gagare, ya jima yana abu ɗaya sannan Aljani Gagare ya bayyana tare da faɗin, "Me yake tafe da kai a tsohon daren nan ya kai wannan tsoho mai surkulle kala-kala?" Bakin Boka mai zamani na rawa ya furta, "Ka taimaka min Ubangidana Kogon tsafina ya kama da wuta sha'anin Sarauniya yau ya zo da wani irin salo." Yana rufe baki Aljanin ya bushe da dariya mara daɗin saurare sannan ya ce, "Wannan wajibi ne a gare ta domin matuƙar kiɗa ya canja dole rawa ma ta canza. Sarauniyar da ka sani a baya ta bambamta da ta wannan, don haka ka yi takatsantsan wurin tsaurara bincike a kanta idan ba haka ba watarana za ka nemi rayuwarka ka rasata gabaɗaya." Ganin wutar na sake ruruwa ya sa Boka ya ce, "Na ga alama amma ka taimaka min da abin da zan kashe wutar nan ina cikin tashin hankali." Aljanin na jin haka ya ɗiga masa wani yelon ruwa akan ƙasar kabarin tafin hannunsa yana cewa, "Ka murje ta da ƙasar hannunka sosai sannan ka je ka watsa wa wutar, wannan ruwan da ka gani fitsarin ɗan autana ne na lakuta maka shi da ƙasar kabarin can su za su kashe wutar." Da sauri Boka mai zamani ya ƙarasa wurin da wutar take ci, yana watsawa kamar ɗaukewar ruwan sama haka wutar ta ɗauke sai wani irin hayaƙi mai wari da yake tashi a wurin. Daga can gefe Boka mai zama ya zauna yana sauke ajiyar zuciya ya dubi Aljanin yana faɗin, "Lamarin nan ya matuƙar gigita tunanina." Aljanin ya yi dariya mai kama da haniniyar doki sannan ya ce, "Na gaya maka wannan kaɗan ne ka gani matuƙar za ka tsaurara bincike a kan Sarauniya Shakundum." Yana rufe baki ya ɓace daga wurin. Yadda boka mai zamani ya ga rana haka ya ƙarasa ganin darensa idanunsa biyu yana saƙa da warwarar abin da yake daminsa, yau kaɗai ya sake tabbatar da zarginsa na baya. Ajiyar zuciya ya sauke yana gyaɗa kai sannan ya saki wani shu'umin murmushi ya ce, "Tabbas sai yanzu na fahimci kuskurena. Da alama Shakundum ta bayyana a cikin daular nan kamar yadda bincikena na baya ya nuna min tana gabda ƙarasowa Daular nan. Yanzu zamana a cikin kogon tsafin ba shi da wani amfani domin wacce nake zaune domin ita ta bayyana har ta bar cikin kogon nan, amma kuma zan zuba ido na ga abin da zai ci gaba da wakana a cikin Daular. Matuƙar na ga manyan alamomin da nake zargi tabbas kashina da na Usaina ya kusa bushewa. A zabure boka mai zamani ya miƙe kamar wanda aka tsirawa allura a cikin ido, gaban ƙoramar sihiri ya koma ya tsugunna ya hau binkice game da abin da ya shafi Sarki Damina da ƴaƴan cikinsa.


Ras! Ya ji gabansa ya yi mummunan faɗuwa bisa abin da idanunsa suka yi masa tozali da su, Sarki Damina ya gani ya bayyana sai waɗansu haske huɗu da ke zagaye da su. Daga bangaren gabas ya hangi wani ƙaton haske wanda ya shafe sauran gabaɗaya, hannu ya saka da niyyar shiga halararsa ya bincika alaƙarsa da Sarki Damina amma sai ya ga duhu ya mamaye wurin, duk iya bakin ƙoƙarinsa ya gagara gane abin da yake son gani. Cike da mamaki ya furta, "Kar dai wannan hasken ma yana daga cikin zuri'ar Damina? Kai an ya kuwa haka ba zai taɓa yiwu ba. Ya zame min wajibi na nemi Usaina mu tattauna domin mu samu mafita."


Kafin Sarki Damina ya ƙarasa gidan shaƙatawarsa tuni aka tuɓe su kandala kowacce sai kare jikinta take yi cikin jin kunya kasancewar haka bata taɓa faruwa da su ba, lokacin da ya ƙarasa yana shiga ya hau ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya yana lashe baki domin ya jima bai haɗu da kyawawan ƴanmata kamar su ba. Kowacc ya je gabanta sai ya saka hannu ya ɗago haɓarta ya ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa sannan ya wuce wurin ta gaba da ita. Nan take ya ji zuciyarsa ta yi matsanciyar kamuwa da ƴanmata biyu daga cikinsu, kamar dabbobi haka ya saka su a gaba yana mu'amala da su, idan ya gama da wannan sai ya koma kan waccen. Ban da kuka da roƙo babu abin da suke yi masa, kallon Kandala ya yi wacce yake kwance share-share a jikinta ya furta, "Ƴan mata kukan me kike yi bayan a yadda na jiki kin saba, ba ni na fara sarrafa linzaminki ba?" Kuka ta fashe da shi a hankali ta furta, "Abar bauta ta shiga lamarinka amma ka taimaka ka ƙyale mu ya shugaba nagari." Duk da ya ji daɗin lafazinta duba da ƙanƙantar shekarunta ya sa ya dube sosai yana cewa, "Ba ma buƙatar jin wani abin bauta bayan Sarauniya Shakundum." Gyaɗa masa kai ta yi cike da gamsu, a yadda ta ji muryaraa ta yi tsammanin zai rabu da su kamar yadda ta roƙa amma sai ta ji ya sake lalubarsu yana ƙoƙarin biyan buƙatarsa. Babu yadda suka iya suna ji suna gani ya yi abin da zai yi da su ya gama sannan ya dube ta ita da Saro ya furta, "Daga yau ke da ita kun zama matan huce zafina." Za a bar ku a nan duk lokacin da na buƙace ku zan zo na same ku, kuma duk wacce ta nemi musamin zan sa a ɗauki mummunan mataki a kanta." Daga haka ya ɗauki wasu manyan ganyaye da yake rufe al'aurarsa ya ɗaura a ƙugunsa ya fice. Dakarun da ke bakin ƙofar turakar ne suka shiga suka fisgi sauran mutum ukun suka fita da su, aka bar daga Kandala sai Saro. Lokaci ɗaya suka rungume juna suna matsanancin kuka, kamar daga sama suka ji shigowar wasu ƴanmata wanda ko ba a faɗa musu ba sun fahimci bayi ne. Sababbin ganye suka kawo musu da abinci mai kyau sannan suka kalli su Kandala suna faɗin, "Tabbas kuna cikin masu daraja tun da a yau haɗuwarku kaɗai da Sarki har ya ƴanta ku. Ku taimaka ku roƙar mini Sarauniya Shakundum ta sassauta min baƙar wahalar da nake sha." Daga Kandala har Saro babu wacce ta tanka mata sai binta suke yi da kallo, don su ko kaɗan wannan ƴantawar bata faranta ransu ba.


Asubar fari a sirrance Boka mai zamani ya rikiɗa zuwa siffar Tsuntsun kai tsaye ya tashi ya nufi cikin gidan Sarki Damina, daga kan katangar ɗakin Usaina ya tsaya yana wani irin kuka da ba kowa zai fahimci inda kukan ya dosa ba. Cikin bacci Usaina ta yi mafarki da Boka mai zamani yana tsala matsanancin gudu ga wata baƙar guguwa na biye da shi, tana daga nesa har suka tunkarota gadan-gadan. Duk yadda ta kai ga yin gudu abin ya gagara ko ƙafarta ta gagara motsawa, don haka ta fara karara ihun neman ceton sai dai bata yi aune ba baƙar guguwar ta turnuƙe su gabaɗaya. A zabure ta tashi zaune jikinta na rawa, sai da ta buɗe idanunta ta riski kukan tsuntsun kamar yadda ya saba zuwar mata a duk lokacin da yake da wata muhimmiyar magana da ita. A hankali ta miƙe ta fice ta bar Sarki Damina buɗe da baki yana sakin munshari. Tana fita ta buɗe wani ɗan ƙanƙanin ɗaki da je can nesa da ɗakinsa tsuntsun na ganin haka ya rufa mata baya. Sai da ya yi girgiza ya dawo suffarsa ta ainihi Usaina ta dube shi ta ce, "Mai zamani akwai matsala." Boka ya dube cikin damuwa ya ce, "Ita ce take tafe da ni. Ni na ga masifa yau ganin idona." Nan take ya bata labarin duk abin da ya faru a kogon Tsafinsa, tana gama jin jawabinsa ita ma ta zayyana masa abin da ta gani a mafarkinta sannan ta ɗora da cewar, "Sirrantaccen bawana ya sanar da ni abin da ya hana ni bacci, wannan baccin ma da ya ɗauke ni ɓarawo ne kuma rabon zan ga wannan mafarkin ne. Ya sanar da ni an kawai Yarima yanmata shabiyar kuma tun da ya gama mu'amala da su yake wani irin bacci da bai taɓa yin irinsa ba. Yana farfaɗowa ya fara wani irin tarkacen amai, kasan aman me aka ce min ya yi?" Boka ya girgiza mata. Usaina cike da damuwa ta ci gaba cewa, "Ina laƙaninnikan da ka ba ni na bashi yana yaro?" Boka ya gyaɗa kai.Ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Su ya amayar an ce har da baƙar allura da kan maciji. Kai ba za su lisaafu ba kuma wai yana dawowa hayyacinsa ya fara cewa me yake yi a wannan gidan. Mai zamani in taƙaice maka labari alamu sun nuna Yarima ya dawo hayyacinsa don har ni da Damina mun je mun gano halin da yake ciki." Boka mai zamani ya yi taku biyu jiki a sanyaye ya ce, "Ta faru ta ƙare... Amma duk da haka ba za mu tozarta ba zan kira Manyan baƙaƙen aljanun ƙarƙashin ƙasa na nemi agajinsu. Abu ɗaya nake so da ke." Usaina ta zuba masa ido tana jiran jin ta bakinsa, boka mai zamani ya ci gaba da cewa. "Ko da wasa kada ki yadda Damina ya lura da halin da kike ciki. Ki sani har yanzu yana kallonki da sunan Hasana, ki nuna masa kin fi kowa farinciki da samun lafiyar Yarima haka zai sa mu sake samun yadda za mu murƙushe rayuwarsa." Usaina ta saki dariyar ƙeta tana faɗin, "Kada ka manta ni ce fa Usaina. Bari ka ji ko ni ina tsoron shu'umancina ba don komai ba sai don sanin makircina. Waɗannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login