Showing 54001 words to 57000 words out of 69452 words
Chapter 19 - BAKAR DAULA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Ameera Adam.txt
ka yi bayan bana kusa da kai?" Huzaifa ya ƙare mata kallo yana shirin magana ta ci gaba da cewa, "Sau nawa zan gaya maka ka fita daga rayuwar yarinyar nan, idan ba haka ba wallahi sai na halakata ta hanyar kisa mai muni." Wani uban tsalle ya buga haɗe da girgiza sannan ya rikiɗa zuwa surar matashin saurayin bil'adam, ya kalli matarsa Mugaza tare da sakin wani shu'umin murmushi ya ce, "Wannan yarinyar da kike gani na fansar da raina a gareta idan kin ga ban tsayawa rayuwarta ba sai dai bana numfashi, ita ɗin ta zama jinin jikina ko iyayen da suka haifeta idan suka nemi raba ni da ita sai na tarwatsa rayuwarsu." Jinjina kai Mugaza ta yi haɗe da sakin wata irin shu'umar dariya sannan ta ce, "Wannan shi ne gargaɗi na ƙarshe da na yi maka a kanta, tun da baka ji ba za ka ga ni a gaba kuma idan kwaɓarka ta yi ruwa karka yi kuka da ni. Sai dai zan ci gaba da baka kulawa a matsayina na matarka mai ƙaunarka, amma a kan wannan yarinyar babu wata kalma da za ta sake shiga tsakaninmu. Sai na ladaftar da ruhinta ta yadda za ta yi danasani, sai na azabtar da gangar jikinta domin sai na shayar da ita azaba mai raɗadi" Tana gama maganar ta tashi daga cikin tsibirin ta fice, ko a jikin Huzaifa ya ƙarasa wurin da Raihan take kwance ya sake rikiɗa zuwa siffar marigayya Mama Hasiya haɗe da sauya fasalin wurin, a hankali ya sa hannu ya fara tashinta tare da faɗin sunanta. Ahankali ta buɗe idonta tana kallon wurin da take da Mama Hasiya da take kanta a tsaye.
Bayan fitowar su Intisar a kan idonta Mama Uwani ta sauya Raihan da wata Raihan ɗin, murmushi ta yi don ta fahimci manufarta na yin haka kuma ita ma ta shiga nazartar yadda za ta ɓullo mata. Nan take gida ya ruɗe da maganar macijin da aka gani a ɗakin Raihan, hankulan mutane ba ƙaramin tashi ya yi ba. Lokacin da Mommy ta samu wannan labarin da sauri ta aika aka kira Kabiru (Matashin bafulatani Maigadin gidansu Raihan.) Saboda Kabir bai da tsoro sam, bai fi sati biyu da fara aiki a gidansu Raihan ba. Tsayayyen namiji ne mara tsoro don akwai ranar da aka samun kulɓa a kitchen ɗin Mommy, Kabiru na zuwa ya fitar da shi. Kafin Kabiru ya zo Sulaiman ɗan ƙawar Mommy ya miƙe yana faɗin, "Daga wurin ina yake yanzu na fice da shi, ba wani shege kura ma mun kara da ita mun kaita ƙasa." Babu wanda ya hana shi don jikinsa na rawa ya nufi cikin gidan, saboda yana mutuwar ƙaunar Raihan don haka yake son ya yi wani abin bajinta ko ya samu ya ƙara samun masauki a zuciyar Raihan.
Yana zuwa duk matan da ke zagaye da ɗakin suka dare, ya tura ɗakin da ƙarfinsa. Yana shiga ya samu macijin a tsakiyar ɗakin ya naɗe wuri ɗaya kamar gammo ya fasa kai, bakinsa yana fitar da feshin wuta, a hankali ya waiga yana faɗin: "Wani ya miƙo min katako." Har rige-rigen tafiya mutane suke yi babu jimawa aka ɗauko masa wani ƙaton katako, kansa tsaye ya tunkari macijin cikin dakiya ya ɗaga ya buga masa a tsakiyar ka. Tsalle macijin ya yi, Sulaiman ya gantsare duniyar na juya masa. Sannu a hankali macijin ya rarrafo ya fara nannaɗe shi har sai da ya naɗe masa jiki, nan take Sulaiman ya hau kakari ƙwayar idonsa duka biyun ta faɗo ƙasa, jini ya fara zuba ta hancinsa da bakinsa. Tun Sulaiman yana iya kakari har ƙarfinsa ya ƙare, tsokar jikinsa ta fara burtsowa daga jikin fatarsa nan take hallitar Sulaiman ta sauya tamkar ba bil'adam ba. Mutane na ganin haka suka fita da gudu cikin kururuwar neman taimako.
************
Raihan ta shi ta yi zaune jikinta ba ƙaramin tsami ya yi mata ba, ta dubi Huzaifa da ke cikin siffar Mama Hasiya ta ce, "Mama Hasiya kece? Dama baki mutu ba?" Huzaifa ya gyaɗa wa Raihan kai yana furta, "Ban mutu ba amma na dawo nan wurin da zama za ki zauna da ni?" Raihan ta yi shiru tana nazartar maganarsa jiki a sanyaye ta ɗago tana cewa, "Gaskiya ban yarda ba ina su Mommy?" Huzaifa ya riƙo hannunta lokaci ɗaya ta ji wani yaarrr a cikin jikinta, tana kiciniyar ƙwacewa sai gani ta yi ta fisgo da ƴan yatsu biyu na jikin hannun Huzaifa, a tsorace ta wurgar da su ta fara ja da baya jikinta na karkarwa. Cikin rawar murya ta ce, "Don Allah ki yi haƙuri karki cutar da ni." Ganin haka ya sa Huzaifa ya fara ƙyaƙyacewa da wata irin dariya har sai da ta sa hannuwa biyu ta toshe kunnuwanta, kakin yawu ya yi ya tofar nan take ƙasar wurin ta fara rozayewa ya sa ɗan yatsa ya nuna mata wurin yana faɗin, "Ki bar wahalar da kanki domin ba za ki taɓa guje min ba, ki zo ki shiga wurin nan idan ba haka ba za ki dauwama a wurin nan."
*********
Al'ummar da ke zaman makoki kusan rabi da kwata kowa ya cika wandonsa da isa, don ceton rayuwarsa. Hatta Inno da Goggo cikin ayarin ƴan ceton rai suke ba tare da su mommy sun farga ba. Hankalin Daddy ba ƙaramin tashi ya yi ba da ganin abin da ya faru, a hankali Kabiru ya fara takawa cikin gidan dukda yana ta cin karo da mutane masu guduwa hakan bai hana shi sake kutsawa cikin falon gidan da zai sadaka da ɗakin Raihan ba, a bakin wata ƙofa ya ci karo da Intisar da ke tsaye ƙyam babu alamar tsoro a tattare da ita. Suna haɗa ido ya ji kansa ya sara juwa ta fara ɗibansa, sama-sama ya fara jin wata irin hayaniya har sai da ya dafa kansa da hannuwansa, a hankali ya fara karanto addu'o'in tsari yana karantawa duk wacce ta zo bakinsa. Lokaci ɗaya ya ji komai ya ɗauke masa, ya dawo cikin hankalinsa sai dai tuni jikinsa ya jiƙe da gumi sharkaf. Idanu ya kafe Intisar da su har ya gagara sarrafa kansa, ya fara takawa zuwa gabanta cikin hausar da bata gama zama a bakinsa ba ya ce, "Washeshe kai?" Intisar ta saki murmushi ta ƙarasa gaban Kabiru ta ce, "Kai bafulatanin ƙauye, karka shiga abin da babu ruwanka." Yana shirin sake magana Daddy ya ƙaraso wurin hankali a tashe yana faɗin, "Kabiru mu je ka ga abin da yake faruwa meye abin yi?" Kabiru ya yi gaba yana waiwayen Intisar haɗe da ɗora mata zarge-zarge a kanta.
Da ƙarfin gaske Kabiru ya tura ƙofar ɗakin cikin zuciyarsa yana ci gaba da karanta ayoyin tsari dana kariya, Jabun Raihan ce ta ƙaraso ƙofar ɗakin. Abin da ya ji da farko a lokacin da yake tare da Intisar haka ya ƙara ji a wannan karon a haukace ya juya, ya shaƙi wuyan Raihan cikin wani irin ƙaraji ya furta.
"Washeshe kai? Me kake yi a wurin nan?"
DA ALAMA KABIRU YA YANKI TIKITIN BARIN AIKIN GADIN DA YAKE YI A GIDANSU RAIHAN😂 TO WAI SHI MA KO YANA DA ALAƘA DA SU NE😂 SHIN DADDY ZAI ZURA IDO YA GA AN MAƘURE GUDAN JININSA? SHIN SU DADDY ZA SU FARGA DA MAMA UWANI BA MUTUM BACE SHI NE AINIHIN ALJANIN DA KE RAYUWA DA ƳAR'SU? KO KUMA HUZAIFA ZAI ƘYALE KABIRU HAR YA TONA MUSU ASIRI🤭🤭🤭
TAFIYAR FA HAR YANZU BA A FARA BA DOMIN LABARIN TAFE YAKE DA SARƘAƘIYA🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️ KARKU MANTA HAR YANZU RAIHAN BATA SAN MAMA UWANI CE TA KAWO WANNAN TSIBIRIN BA, ITA DAI TA BUƊI IDO DA MARIGAYYA MAMA HASIYA. WAI INA LABARIN INNO DA GOGGO NE INA SUKA BAZAMA WAYE ZAI TARO SU? 😂😂
Share Fisabillah🌚
[11/5, 3:26 PM] Mai Agogo: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*
© *AMEERA ADAM*
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
FREE PAGE 7
Daddy yana tafe Raihan na riƙe a hannunsa har suka shiga cikin gidan ayyane-ayyane yake yi, yana mamakin wane irin macijine da nan take zai naɗe mutum ya kashe shi, kuma a ce ya fito daga ɗakin Raihan ɗin sa. Kwafa ya yi yana tunanin irin matakan tsaron da zai ƙara akan na da, har suka shiga ciki. Mommy jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba don tun lokacin da abin ya faru ta fahimci macijin ɗakin Raihan ba ainihin dabba ba ne. Sai dai a wannan karon ta ci alwashin faɗawa Daddy gaskiya duk irin ɓacin ran da zai yi, don haka suna zuwa ta nemi ganawa da shi a sabon ɗakinsa dama gidan ya gina shi ne da sunan bayan wasu watanni su tare, amma kasancewar ba a gama masa ƙaƙale-ƙaƙale ba ya sa suka dakata da komawar, amma dole ta sa suka tashi a rana tsaka suka koma. A gaggauce Daddy ya dubi mommy ya ce, "Faɗi ina jin ki, kin san yanzu aka yi mini waya wai ankai su Inno da Goggo Hisba dole sai na zo, wani tashin hankali wai an tsinci su Inno a cikin masallacin Malam Isa na ƙarshen layi." Sai a lokacin Mommy ta zaro ido don bata san abin da yake faruwa ba, ganin ta shiga tashin hankali ya sa ya dube ta fuska ba walwala ya ce, "Ba fa wani abu ne na ɗaga hankali ba, komai ya zo da sauƙi yanzu dai ina zuwa." Yana gama maganar ko jiran cewarta bai yi ba ya fice daga ɗakin, jigum Mommy ta yi abu goma da ashirin ya haɗe mata.
Wani irin zafi Kabiru ya fara ji a jikinsa kamar wanda yake gaban wuta, hajijiya ya ji ta fara ɗaukansa ga wata irin matsa da macijin yake yi masa, tun yana daga tsaye har ya durƙushe a wurin yana son furta ayar Allah, amma macijin ya matse masa maƙogaronsa. Kakari ya fara yi kamar wanda ransa zai fita, a zuciyarsa yana son biya ko da ayatulkursiyyu ce amma wani abu mai nauyi ya ji ya tokare masa ƙirji kamar dutse. Yana cikin wannan halin ya ga ɗaya daga cikin macizan ya miƙe tsaye cak ya fasa kai, a hankali fatar jikin macijin ta fara saɓewa tana fita daga jikinsa sai kuma ya fara rikiɗa daga siffar maciji zuwa siffar bil'adam. A hankali wata matashiyar mace ta bayyana ilahirin jikinta gashi ne tun daga kanta har zuwa ƙugunta, ya yin da ƙugunta yake a nannaɗe cikin surar maciji. Harshe ta fara zaro masa nan take wani jaririn maciji ya faɗo, ta damƙe shi a hannunta ta kalli Kabiru da yake cikin mummunan hali ta fara magana, "Kai matashin bafulatani, wa yace maka takun saƙa da ni sauƙi gare shi? Ka san wa ka illata kuwa? Ka san wa ka kashe min kuwa? Ko kana tsammanin ka ci bulus ne?" Kabiru ya ɗago yana sauke numfashi da ƙyar idanunsa jawur ga gumi na ci gaba da tsiyaya daga jikinsa. Baki yake son buɗewa amma ya kasa, ganin haka ya sa ta sake bushewa da wata mahaukaciyar dariya sai da ta yi mai isarta sannan ta fashe da matsanancin kuka, ta jima tana yi sai ta tsagaita da kuka ta sake kallonsa ta ce, "Ba kai kana taƙama da addu'a ba ka yi ta mu gani, har za ka kashe min miji kana tunanin za ka zauna lafiya?" Macijiyar na gama maganar ta fara rarrafowa zuwa gaban Kabiru, ganin ta nufoshi gadan-gadan ya sa Kabiru ya ƙara yunƙura yana ja da baya, ya fara bude baki yana ƙoƙarin karanta addu'a haɗe da motsa baki sai dai ko kaɗan muryarsa bata fitowa, tana tunkararsa hushin numfashinsa ya doki gangar jikinta ba shiri ta ja da baya saboda wani irin zafi da ta ji yana fita daga bakinsa. Kallon-kallon suka fara yi a tsakaninsu, bata daddara ba ta sake yunƙurowa a kashi na biyu da niyyar hallakashi. Duk yadda Kabiru ya kai ga buɗe muryarsa ya yi addu'a abin ya gagara. Dabara ce ta faɗo masa ya fara biya ayatulkursiyyu a zuciyarsa, tana tunkaro shi ya fara tofa masa. Ganin tana niyyar hallaka ya sa ta sake yin baya, nan take macizan da ke gewaye da shi suka ɓace. Ƙaton da ya naɗe shi tuni jikinsa ya saki da ƙyar ya rarrafa ya bi ta jikin bangon ɗakin ya ɓace. Ɗakin Kabiru ya rage daga Macijiyar sai Kabiru, ya yin da ta sake kafe shi da ido tana ƙare masa kallo don ta fahimci makasar da za ta samu a jikinsa ta yi masa illa. A wahalce Kabiru ya faɗi can gefe yana mayar da numfashi, jikinsa gabaɗaya ya yi ja saboda irin tsananin matsar da macijin ya yi masa. A hankali jikinsa ya fara raɗaɗi, yana kai idanunsa kan fatarsa ya lura da yadda ta fara sauya launi zuwa fatar maciji. Macijiyar kallon Kabiru ta yi ta fara ƙyaƙyacewa da wata irin shu'umar dariyar ƙeta, hankalin Kabiru ba ƙaramin tashi ya yi da ganin abin da yake faruwa da fatar jikinsa ba. Yana tsaka da tunani ya riski muryar macijiyar tana faɗin, "Ka kashe min mijina ba tare da wani dalili ba, Huzaifa ya nemi tallafin mijina akan ya zo taimakonsa ka kashe shi, zafin mutuwarsa ta sa na ji tamkar na kashe ka amma ba zan kashe ka yanzu ba sai na gama wahalar da ruhina da gangar jikinka sannan na hallaka da hannuna. Ka je ko da wannan hallitar fatar macijin na barka ƙuncin rayuwar duniya ya ishe ka." Tana gama maganar ta sake naɗewa ta koma murtukekiyar macijiya, juyi ta fara yi daga wurin da take nan take ta baje a ƙasa ta fara nutsawa cikin ƙasa har ta ɓace ɓat. Ilahirin jikin Kabiru ban da rawa babu abin da yake yi, babban tashin hankalinsa yadda ya ga fatar jikinsa ta koma ta maciji illa iya fuskarsa, hannu da ƙafarsa ne kaɗai basu rikiɗa ba da yake macijin bai taɓa masa nan ba.
A fusace Hatsabibiya ta ɗago da ta sake kallon Intisar ta ce, "Idan ba mu kashe shi ba kina da hanyar da za mu ɓullo masa? Ko kuma kina da shawara akan yadda za mu kawar da tunaninsa akan Raihan?" Intisar ta yi shiru tana nazari don ita kanta ta san wanene Huzaifa da tsananin bincike irin nasa, ta san tun da ya kafa mata ƙahon zuƙa dole zai bi diddigin wacece ita da asalinta. Ta san muddin ya gano ta ba ƙaramar ƙura ce za ta tashi a tsakaninsu ba, a baƙar zuciya irin tashi yana iya hallakata. Don ma tana amfani da sirrin tsafi da sihiri ko a yanzu yadda ya ɗora ransa akan Raihan da tuni ya gama da ita. Tana cikin tunani ta sake riskar muryar Hataabibiya ta ci gaba da cewa, "Idan har baki da wata dabarar ga tawa shawarar." Intisar ta dubi Hatsabibiya tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ina jin ki Uwargidana maganin kukana, da ke da Abar bauta ku kaɗai na dogara da ku duniya da lahira (Wa'iyazubillah) ke kika saba ɗauke min duk wata damuwata a yanzu ma ina biye da ke don jin mafitar da za ki kawo mana kafin abar bauta ta bayyana."
Hatsabibiya kanta ya sake girma, ta miƙe daga wurin da take ta ɗauki wani dogon ƙaho mai faɗi da tsawo ta kafa shi a bakinta sannan ta durƙushe a gurin. Ta kafa tsinin ƙahon a doron ƙasa sannan ta busa shi da ƙarfinta, lokaci ɗaya tsibirin ya ɗauka tsananin ƙararsa kamar zai tsaga dajin gida biyu. Tun bata rufe baki ba aljanu masu ɗauke da munanan hallitu suka fara fitowa wasu daga ƙarƙashin ƙasa wasu daga cikin duwatsu ya yin da wasu suka fara fitowa daga ɗakin tsafi. Kafin wani lokaci tuni sun taru suna masu sujjada a gabanta, tare da yi mata kirari kamar yadda suka saba sannan suka ƙame wuri ɗaya suna jiran umarninta.
Wani irin kuka haɗe da dariya ne ya fara tashi, lokaci ɗaya tsibirin ya fara girgiza suna nan tsaye wannan mummunar hallitar mai ɗauke da kawuna (Abar bauta.) Ta ziro kawunanta zuwa harabar wurin da take. Suna yin tozali da ita suka kwanta a wurin har hatsabibiya suna masu yi mata sujjada, haɗe da kirari. Kafin ƙiftawar ido Wani baƙin aljani ya dira a gabanta cikin girmamawa yana tambayarta.
"Ya ke uwargijiyata shin jariri kike buƙata, uwar jariri tsoho ko tsohuwa kike buƙata." Ɗago da kawunanta ta yi, sai ta saki kuka kamar na bujimin sa. Jin kukan San ya sa aljanin sake rissunawa yana faɗin, "Kin samu kin gama." Yana gama maganar ya ɓace daga wurin.
Kallonsu ta yi ɗaya bayan ɗaya sannan ta fara magana da murya mara daɗin sauraro, "Duk abin da kuka tattauna mun saurara don haka babu amfanin maimaitawa sai zartar da hukunci." Jikin Intisar tuni ya fara tsuma nan take gumi ya rufe ta, don bata san irin hukuncin da Abar bauta za ta yanke a kan Huzaifa ba. Tana tsaka da nazari ta riski muryarta tana ci gaba da cewa, "Ba za mu kashe Huzaifa ba sai dai dole a sauyawa taku salo, sanin kanku ne a da ɗanyan kifi yana haukatata. Sakamakon ɗan da ta haifawa Huzaifa yana da haɗin jinsi da hallitar kifi. A yanzu za mu sake haukatata fiye da lokacin baya, a cikinku waye zai iya aiwatar da abin da muke buƙata?" Wata aljana da ta miƙe tsaye tana faɗin, "Abar bauta zan riƙa haukatata da surar mahaifiyarta..." Tun bata rife baki ba Abar bauta ta katse ta cikin tsawa tana cewa, "Kina tunanin wannan mafita ce? Idan kika yi haka dole za su nema mata