Showing 33001 words to 36000 words out of 69452 words
Chapter 12 - BAKAR DAULA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Ameera Adam.txt
ƴanmata sha biyar da aka kai wa Yarima dole su baƙunci lahira ko ta tsiya ko ta arziƙi. Kuma samun lafiyar Yarima ba shi zai sanyayar da ni ko ya ba shi damar ɗarewa karagar mulki ba, na yi rantsuwa da tsantar makircina ko da Hasana za ta dawo Daular nan Damina ba zai taɓa aminta da ita ba balle Yarima da nake kallo a tafin hannuna nake iya sarrafa linzamin rayuwarsa yadda nake so." Cike da jin daɗi Boka ya ruƙo ƙugun Usaina ya ce, "Ba don ni nake haɗa miki kayan mallaka ba da sai na ce an ya ba maƙale mata kika yi min ba Usaina? Ba na gajiya da ke da duk wani abu na jikinki, a yanzu da za ki ba ni dama da na huce tulun zafin da ɗauko daga cikin kogona. Amma yanzun ma ba zan ce komai don kin wuce tunanin duk wani mai tunani shalelena, ina fatan dai watarana ba za ki harba min ƙarinki ba dom ba zan iya jurar budulcinki ba." Usaina ta ci gaba da hillatar boka mai zamani tuni suka faɗa duniyar masha'arsu cikin kissa ta furta, "Ka bar min komai a hannuna sauran bayanin za ka ji daga baya. Mai zamani idan na yi maka butulci ai sai na ɗaiɗaice wa nake da shi da zan jingina na ji daɗi. Wancen lusarin mijin nawa kowa?" Boka mai zamani ya taɓe baki ya ce, "Haba Usaina ko kin manta na san kuna ƙulla irin wannan alaƙar da wannan sirrantaccen bawan na ki." Sai da gaban Usaina ya faɗi amma da yake ta ita bariki sai ta wayance ta ce, "Hmm idan wannan bawan ne kar ma ya dame ka domin ina nuna masa kulawa ne domin biyan buƙatar kaina ya ci gaba da yi min biyayya yana kawo min saƙƙonni. " Tana gama maganar ta ci gaba da rikita mai zamani da salo kala-kala.
Lokacin da Sarki Damina ya tashi daga bacci tuni Boka mai zamani ya gama abin da zai yi ya yi gaba, da tarairaiya ta tarbe shi sannan ta furta, "Na yi mamakin yadda ka iya yin bacci a daren yau." Murmushi ya yi yana shirin magana ta ci gaba da cewa, "Farincikin samun lafiyar Yarima ya fi min komai don haka yau ko kaɗan ban runtsa ba. Idan ban manta ba rabona da farinciki irin wannan tun kafin samun ciwon Yarima yau sama da shekara ashirin da wani abu. Kai gaskiya mun gode wa Shakundum ta dubi roƙon da muke yi na tsawon shakaru."Sarki Damina ya faɗaɗa fara'arsa yana faɗin, "Hasana ban da bacci ɓarawo ne babu abin da zai hana ni kwana idanu biyu, kin ga maganar boka mai zamani ta fito fili da ya ce min Yarimana zai warke. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ya ce min yarinyar da zai kusanta ita ce silar samun lafiyarsa kuma har da albarka Ɗa ko Ƴa a tsakaninsu." Ras! Gaban Usaina ya faɗi, a zabure ta furta wannan saduwar da ya yi da su ko kuma wata nan gaba?" Kai tsaye Sarki Damina ya ce, "Wannan dai kin ga ya zaman wajibi na sa a binciki yarinyar don dole Yarima ya aureta tun da na lura alheri ne tattare da ita kuma ƴar baiwa ce." Usaina ta fara sosa kai wani abu na taso mata mai ɗaci a maƙogaro sai kuma ta wayance da cewar, "To mai zai hana ka sa a tara ƴaƴan nawa a bincike su idan aka gagara ganewa ka ga ba sai ka saka a killace su ba, idan aka killace a wani gidan ana kula da su da sannu za a ga wacce take da juna biyu a cikinsu. Idan kuma haka bai yi ba sai ka saka Boka mai zamani ya yi maka bincike a kansu." Cike da jin daɗin shawararta ya rungumeta yana buga bayanta ya ce, "Shi ya sa nake ƙaunarki Hasana, ke wallahi kin ga dai ƴar uwarki Usaina ta mutu ko amma ko ita da kuka kasance ƴan biyu ba za ta nuna miki kaifin basira da tunani ba domin sam hali da tunaninku ba ɗaya ba." Wani abu ne ta ji ya soki ƙirjinta har sai da fushinta ya baiyyana a fili, ganin haka ya sa Sarki Damina ya yi tsammanin ko don ya faɗi wannan maganar game da ƴar uwarta ne ta ji haushi, cikin lallashi ya furta. "Ki yi haƙura ban faɗa don na ɓata miki ba sai dai yabon gwani ya zama dole." Usaina ta wayance tana murmushi ta furta, "Wannan haka ne. Yanzu dai idan an jima zan leƙa na ga sauƙin jikin Yarima, idan ya so sai ka yi yadda na bada shawarar ina ganin zai fi." Sarki Damina ya amsa mata. Daɗi ne ya kamata don ta san duk shawara ɗaya da ta bayar idan aka ɗauketa dole za ta samu mafitar da za ta hallaka su lokaci ɗaya ba tare da wani ya zarge ta ba.
Shiru na yi lokacin da na ji shela da sanarwar da aka bayar daga wurin Sarki, a tunanina zan iya ɓaddabami na saje da sauran bayin cikin wurin da muka samu a wurin, ina gani wasu daga cikin tsirarun ƴanmatan da aka tafi da mu suka fita wurin mai shelar. Ni da sauran mutum huɗu muka yi shiru kamar ba ma daga cikin waɗanda ake yi wa sanarwar, wani abin mamaki sai ga Dakarun na zaluƙo mu ɗaya bayan ɗaya duk da babu wani abu da za ka kalla wanda ya bambamta mu da waɗancen, idanu ne ya dawo kanmu nan take tsoro da fargaba suka mamaye zuciyata musamman da na tuna irin halin da muka baro yarima a ciki yana wani irin bacci da ban taɓa ganin irin munsharinsa ba. Hawaye ne ya zubo min na fara ayyana irin gashin-ƙumar da za a yi mana domin har lokacin matar da muka samu an farkewa ciki ta gagara ɓace min daga idanuna ba, kuka nake sosai saboda tausayin hukuncin da za mu fuskanta. Ganin haka ya sa ƴan uwana da aka tafi da mu tare suma suka mara min baya kowacce na zubar da ƙwalla, a gaban dubban jama'a aka sake jere mu sarki da muƙarrabansa suna cikin tanti a zaune. Karaf idanuna suka hango min shi a zaune kusa da Mahaifinsa, a wannan karon tsaf na gan shi cikin kyakkayawar shiga duk da ba wata sutura ce a jikinsa face ganye. Amma kana ganinsa za ka bambamce yanayin nutsuwarsa saɓanin jiya da muka same shi a hargitse, a hankali na furta, "Ko kaɗan ba zaci cutarwar da kake min a baya ta kai haka ba, sai ga shi ka raba ni da ƙimata da mutumcina da na jima ina yi wa Goga tanadi..." Maganar da Sarki Damina ya yi ce ta katse min kalamaina, ya miƙe tsaye yana kallon al'ummar da ke wurin yana faɗin, "Ya ku al'ummar cikin wannan Daula, ku yi sani Yarima Ɗana ɗaya jal tilo ya samu lafiya. Ya samu lafiya ne kamar yadda boka ya faɗa min a baya sanadiyar waɗannan ƴanmatan, don haka ya zama wajibi a gare mu; mu killace su domin suna daga cikin masu daraja." Yana rufe baki na ji duka sun ɗauki sowa da tafi cikin farinciki suka shiga raye-raye da bushe-bushe, sai da suka ɗan jima sannan Sarki ya ruƙo hannun Yarima ya fara takowa har gabanmu, tun da na ga haka gabana ya ci gaba da faɗuwa ina tsoron kada ya nuna ya sanni domin na san babu tantama shi ne mutumin da ke fitowa daga cikin tawagar da ke baƙuntar rayuwata. A hankali ya fara nuna masa mu ɗaya bayan ɗaya sannan ya bashi labarin zuwanmu da kai mu wurinsa da aka yi, bai tanka wa mahaifinsa ba illa gyaɗa kai kawai da na ga ya yi sannan suka koma suka zauna. Wurin zama aka nuna mana sannan aka kawo mana kayan ciye-ciye da lashe-lashe. Ina kai loma ɗaya bakina na ji ta min ɗaci sakamakon tuno iyayena da ƴan amanata da na yi, hawaye na goge a fakaice sannan na ci gaba da turawa ba don ina jin daɗinsa ba. An jima ana shagali sannan daga baya aka ɗauke mu daga wurin aka kai mu cikin gidan Sarki Damina, a wani ɗan ƙaramin gida aka sauke mu aka ba mu duk wani kayan buƙata tamkar waɗansu ɓangare daga jinin Sarki Damina.
Daga wurin taron kai tsaye Sarki Damina wurin Boka Mai zamani ya wuce, duk abin da yake faruwa ya zayyane masa da neman taimakonsa. Boka mai zamani yana son yin bincike a gaban Sarki mai zamani amma yana gudun kada wani abu ya faru marar daɗi har Damina ya ga gazawarsa. Don haka ya ƙarfafa masa gwiwa akan hukuncin da ya yanke na killace ƴanmatan a wuri ɗaya kafin cikin da ake tsammani ya bayyana. Cike da murna Sarki Damina ya miƙe har zai je bakin ƙofa Boka ya ce, "Damina ina fatan baka manta al'adar Daular nan ba ko?" A hargitse Sarki Damina ya juya yana faɗin, "Ta me fa?" Cikin rashin damuwa Boka ya ce, "Har ka manta sadaukarwar da ka yi wa Babban dodo abin da ka haifa na fari? Sanin kanka ne duk wani Sarki ko mai jiran gado dole ne abin da za a haifa masa na fari a sallama wa Babban dodo, idan kuma ba haka ba ka san abin da ya wakana ga mahaifinka kafin baƙuntarsa lahira." Dariya ya bushe da ita mai ƙarfi sai da ya yi mai isarsa ya kalli Boka ya ce, "A halin nake ciki ko uwarsa ka ce na sallamawa Babban Dodo zan bayar da ita balle abin da za a haifa masa, na yi alƙawarin a lokacin da yarinyar da ke ɗauke da cikin Yarima ta haihu ko mahaifa ba za ta kai ga faɗowa ba Jaririn zai dangana ga Babban dodo. Buri da fatana dama Yarima ya samu lafiya yadda zan samu magaji kuma ya samu ban damu ba, don haka idan ka cire Yarima da ni zan iya fansar da gangar jiki da ruhin kowa." Yana gama maganar ya fice daga kogon dutsen. Jinjina kai Boka mai zamani ya yi ya ce, "Tabbas kuwa ka yi shuka a idon makwarwa waɗannan kalamai naka tamkar a kunnen Usaina ka yi su."
Zamanmu a cikin gidan Sarki Damina babu yabo babu fallasa domin duk wani abin buƙata babu wanda muke nema mu rasa, sai dai tuni kwanciyar hankali ta yi ƙaura a gare saboda kullin tunani ɗaya a wane hali iyayena da ƴan amanata suke. Ga ƙarin takaici ɗan gidan da aka kai mu a ciki muke rayuwa ko soro ba a bari mu je, sa dai kusan kullin Mahaifiyar Yarima takan kawo mana ziyara, a yadda na lura macece mai mutumci da sakin fuska. Kullin cikin jammu a ciki take tana kawo mana hira masu daɗi da kwantar da hankali, don haka ya sa a duk lokacin da ta shigo wurinmu take tambayarmu matsalolin da ke damummu. Kwananmu goma sha biyu a cikin gidan na fara ciwon kai mai zafi ga yawan kasala da tashin zuciya, sautari a duk lokacin da na ci abinci sai dai na fakaici idanun sauran ƴanmatan da muke tare na tafi banɗaki na kyalaya amaina a can, wannan sauyin da na gani ba ƙaramin ɗaga hankalina ya yi ba domin duk wasu alamin ciki ya bayyana a jikina, ranar da mahaifiyarsa ta shigo wurin mu da yamma haka kawai na ji turaren jikinta na tayar min da zuciya. Na tsugunna ina gaishe na ji na gagara daurewa sakamakon aman da nake jin ya taso min, da gudu na nufi bakin rariya na fara amai kamar zan amayo da ƴaƴan cikina. A wahalce na dawo ina shirin zama mahaifiyar Yarima ta ruƙo hannuna tana duba tafin hannuna, tana gama duba hannuna ta gwala idona tana ƙarewa ƙwayar idona kallo. Sunkuyar da kai ƙasa na yi na ji ta ce, "Tun yaushe kika fara yin aman nan?" A hankali na furta, "Yau kwana uku."
Tirƙashi! Tabbas yanzu wasan ya fara, kurunkus dai tun da Usaina ta fahimci Kyauta na da ɗan bayani a jikinta🤣🤣🤣 Sai dai akwai ƙura fa wai za a sadaukar da abin da ke cikin Kyauta😰😰😰 Me kuke harsashe shin za su nasara ko yaya? Ina labarin iyayen Kyauta? Shin Kandala ta hallata ta zama matar Sarki Damina kar fa aje allura ta tono garma? Wane ne mai kama da Yarima da yake baƙuntar Kyauta shin wane katon haske Boka ya gani a gefen Sarki Damina? Meye alaƙar Kyauta da Sarauniya Shakundum, kuma me ya sa boka ya gagara gano bincike a kanta? AKWAI TAMBAYOYI DA YAWA DA CI GABAN LABARINE ZAI FAYUACE MUKU💃🏼 Wollah na gaya muku salon labarin nan na daban ne kada ku bari a yi babu.🤭
*KU MATSO KU TAHO*💃🏼
Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananin ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.
Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼
Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰
Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚
*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
[11/5, 3:26 PM] Mai Agogo: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*
© *AMEERA ADAM*
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
FREE PAGE 2
https://chat.whatsapp.com/J0qrgC0rXNQ57u50VzeewR
A hankali Jabun Raihan ta fara bin ɗakin da kallon, miƙewa ta yi ta fara buɗe drowers ɗin kayan Raihan sai kuma ta bi hotunan ɗakin Raihan da ke maƙale a jikin bango tana kallo ɗaya bayan ɗaya, tana jin motsi ta koma wurin kayan abincin ta zauna. Kallon abincin take don sam bai burgeta ba cikin zuciyarta take mamakin irin abincin bil'adam don ita bata ga abin daɗi a ciki ba. Goggo ce ta turo ƙofar tana faɗin, "Rehanu! Ke Rehanu wai ina kika shiga ne tun jiya ban ji wulgawarki ba, yarinya sai iya shege don kin ga na damu da ke." Turus ta yi tana kallon Jabun Raihan da ke cin abinci tana yamutsa fuska, daƙuwa ta yi mata da hannu tana faɗin, "Kin ci ƙaniyarki Rehanu dama kina jina kika yi shiru to kin wulaƙanta uwarki Abu. Meye wannan ɗin kike ci kina yamutsa fuska kamar abinci?" Jabun Raihan a daƙile ta ce, "Gashi kuwa kin gani."
Goggo ta shiga ɗakin ta yi tsaye a kan Raihan tana faɗin, "Oho dai kowa ya raina uwar wani tashi ya raina, wallahi duk maganar da kika gaya min uwarki da Ubanki kika gayawa." A fusace ta ɗago tana duban Goggo da ke tsaye tana zazzaga ruwan masifa, farantan gabanta ta kalla tana motsa baki lokaci ɗaya ta cinye abincin ciki sai kwanukan, tana kallon Goggo kamar wacce ta basu umarni sai farantan suka yi tsalle zuwa gaban Goggo, wuƙar da Mama Uwani ta haɗowa Raihan don ta riƙa yankar farfesun ƙafar sa ce ta yi tsaye a daidai fuskar Goggo saitin idonta tana wani juyi, kamar za ta tsokane mata ido. Jabun Raihan ta kalli Goggo fuska ba walwala tana cewa, "Kika sake zagar mini iyaye sai na tsokane idonki, ke da sake gani har abada. Wannan kwanukan kuwa sai na basu umarni su yi ta ranƙwale miki kai har sai sun illataki." Goggo daskarewa ta yi a wurin, tuni fitsari ya jiƙe mata zani gumi sai yanko mata yake ta ko'ina. Tun Jabun Raihan bata gama magana ba, Goggo ta juya da gudu tana ƙawalawa Mahaifiyar Raihan kira, sai dai yadda ƙafafuwanta suka yi mata nauyi ya sa ta fice da rarrafe zanin jikinta kuwa tuni ya samu mutsuguni a bakin ƙofa.
Tana fita Jabun Raihan ta miƙe tana kaiwa da kawowa don gabaɗaya zaman wurin ya gundureta, abin da ya sa ta bi umarnin Huzaifa don biyan tata buƙatar amma ba don haka ba babu yadda za a yi ta amince da rayuwa cikin siffar bil'adam.
Huzaifa bai tsaya ko'ina ba sai cikin wani ƙasurgumin daji mai ɗauke da jajayen furanni, da jajayen ƙoramu. Komai na wurin ja ne hatta ciyayin da suke wurin, sai waɗansu korayen kifaye da su kaɗai ne suka bambamta da jajayen abubuwan da ke wurin. Kan wani jan dutse ya kaita ya kwantar da ita nan take ya fara gyara mata jikinta, kafin wani lokaci tuni ya gyara mata jikinta ya ɗauko wani ƙaramin jariri da ke kwance cikin wata ƙorama mai ɗauke da siffar kunkuru, sai dai kansa ɗauke