Showing 15001 words to 18000 words out of 69452 words

Chapter 6 - BAKAR DAULA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Ameera Adam.txt

Advertisement

04 Jan 2025

6134

mutuwa zan yi Kyauta, maza hanzarta ki kare kan ki kada a yi biyu babu." Magungunan saran macijin da ke ɗaure a ƙuguna na kunto ina saka masa amma babu wanda ya yi aiki, ina shirin kun ce wani na ji ya riƙe hannuna yana faɗin, "Wannan ba kamar sauran macizan da kika sani ba ne, ki bar wahalar da kan ki tawa ta zo ƙarshe. Sa'a ta kai miki abar bauta ta baki nasara akan wannan macijin cau cau cau mai gayya mai aiki." Hawaye ne ya zubo min a hankali na furta, "Jarumi uban yaɗiya ya amshi ziyararka, dawa ba daɗi a dajin Bawaya." Ina ji ina gami numfashin Nalami ya ɗauke, gurnanin macijin ne ya sake ankarar da ni don haka na miƙe da sauri na fara lalubar ciyawar da matar nan ta faɗa min, dama na santa a ido sai dai ban san laƙanin da ta sanar da ni ba. Na jima ina abu ɗaya har muka fara wasan ɓuya da macijin yana watso min dafinsa ina kaucewa. Har na fara fidda rai sannan na hangi ciyawar a saman wani shuri, da sauri na dira a kan shurin nan take ya rushe na tsinki ciyawar na murjeta na fara shafe jikina.


Kai tsaye na tunkari macijin ya fara ja da baya ganin yana shirin guduwa ya sa na tafi da gudu na damƙi jikinsa, laushi ya fara yi da sauri na ɗare samansa ya tura kansa a doron ƙasa nan take ya faɗi matacce. Takobin da ke rataye da ni na zaro ba a ɗauki lokaci ba na datse kansa, na sakala takobina ta cikin ƙwayar idonsa na fara jan kan da karfi don nauyin kansa ya kusa girmana a a tsaye. Bakin kogon na ƙarasa sai dai wani abin mamaki na nemi matar sama ko ƙasa na rasa sai jaririnta da ke gefe yana mutsu-mutsu ga wata azurfa a kan cikinsa da wata ƙaramar aska. Daga wurin ƙafafuwansa wani ƙaton ganye ne da aka zuba wasu abubuwa da ban san na meye ba. A hankali na ƙarasa na ɗauki jaririn na rungume tare da kwaso kayan da ta ajiye masa, na fara jan kan macijin a wahale sannan na ɗauki hanyar da za ta sada ni da yankinmu.


Daular Sarki Damina.


Tun da boka mai zamani ya ji muryar babban bawa sarki Damina da sauri ya sanyar jelar dokin hannunsa a cikin sihirtacciyar ƙorama ya yarfawa Usaina ruwan, nan take ta ɓace daga wurin. Shigar Jakadiya ya sa Boka mai zamani ya buga mata tsawa don ya tabbata ta ji duk irin tattaunawar da suke yi, a madadin Jadiya Lami ta razana sai ta rushe da matsanancin kuka tana birgima haɗe da dafa ƙafafuwan boka mai zamani. Mamaki ne ya kama shi matuƙa don haka ya zura mata ido yana shirin magana, sarki Damina ya kutso kai cikin kogon dutsen. Shigar su ke da wuya rijiyar ta sake sakin wata razananniyar tsawa wacce ta sake ba wa boka mai zamani tsananin mamaki, don rabonta da yin haka tun lokacin da yake yaƙinin an sake haihuwar Ƴar sarki Damina ta uku wacce tankasance macce. Sarki Damina ne ya buga wa Jakadiya Lami tsawa yana faɗin, "Me kike yi a wurin nan da tsohon daren nan?" Jakadiya Lami ta sake rarrafawa gaban Sarki Damina ta lashi ƙafafuwansa sannan ta furta, "Wani kyakkyawan mafarki na yi game da yarima don haka na garzayo wurin Boka mai zamani da ya fassara min mafarkina da farar safiya na yi maka albishir da shi, kawai ina sako kaina na ji yana magana da Aljanu yana cewa Mai babbar turaka kwana ya ƙare." Babu alamun tausayi ko mamaki Sarki Damina ya dubi Boka mai zamani ya ce, "Wai haka ne?" Cike da rashin gaskiya Boka mai zamani ya fara gyaɗa kai. Sarki Damina a tsawace ya ce, "Idan haka ne mai ya sa baki same ni da maganar ba? Shin ba zunubi ba ne zuwa kogon boka mai zamani matuƙar ba da izininmu ba?" Tuni jikin Jakadiya ya fara rawa amma sai ta dake ta furta, "Na yi mafarki Yarima ya warke har ya yi aure matarsa ta haifo jariri namiji, wani ƙarin farinciki jaririn da yarima yake haifa har gani na yi ya zama nagartaccen jarumi yana kai maza ƙasa." Nan take sarki Damina ya faɗaɗa fara'arsa sannan ya nuna wa Jakadiya hanya ya ce ta fice, Jakadiya cike da mamaki ta fita don jin kunnenta ta ji muryar Usaina sai dai da shigar ta ba ta ganta ba kuma ta tabbata boka mai zamani ne ya yi wani abin da ta ɓace.


Mafarkin da Sarki Damina ya yi ya ga Yarima rungume da jariri ga wata matashiyar mace hannunta riƙe da kwari da baka ta saita shi ta sakar masa shi ya faɗi jini na zuba. Ko da Boka ya gama jin jawabin Sarki Damina sai ya ƙarasa bakin rijiyar ya leƙa cikinta. Wani abu da ya ba shi mamaki inuwar jariri ya gani rungume a hannun wata mai saƙale da kwari da baka. Wannan lamarin ya sake susuta tunaninsa a sanyaye ya juyo ya furta, "Ina buƙatar a bar ni na yi nazari zuwa wayewar gari idan lamarin ya gagare ni sai na nemi agajin Abar bauta." Saboda takaici Sarki Damina ko amsa bai ba wa Boka ba ya fice daga kogon dutsen." Sai da ya tabbatar da sun yi nisa da fita sannan ya sake saka jelar dokin ya yarfa a wurin da Usaina take tsaye, nan take ta bayyana tana sakin shu'umin murmushi. Boka mai zamani cikin damuwa ya furta, "Baya ta haihu fa." Usaina ta fara wata irin tafiya tana karkaɗa jiki ta ce, "Da aka yi yaya hatsabibina?"


"Hallaka na sake kusanto ki da ni domin a yanzu haka ƴar uwarki ta sauka kuma da alama jariri namiji ta haifa, ni na sani dama zuri'ar Maharba ba za su taɓa ƙyale mu wataya ba. Sun karya makarin asirinmu akanta kuma alamu sun nuna yaron na tare da zuri'arsu. Ƴaƴan Sarki Damina huɗu kenan maza uku mace ɗaya. Biyu suna cikin masarauta biyu suna tare da zuri'ar Maharba. Matuƙar suka haɗu wuri ɗaya su huɗun daga nan ƙofofin nasarorinmu za su kulle." A hargitse Usaina ta dafe ƙirji tana faɗin, "Ka na nufin Hasana ta haife tayin cikin da ke jikinta? Bayan Yarima ka na nufin akwai wani jinin sarki Damina a Daular nan da ban sani ba?" Boka mai zamani ya bushe da dariya sannan ya furta, "Tabbas haske biyu nake gani a Daular nan wanda yake alamta jinin Damina ne, haske na farko Yarima ne Haske na biyu kuma da alama makusancinki ne kuma ya yi nesa da Damina tun da haka tauraronsu ya nuna min. Sai haske na uku da tun shekaru sha biyar na riske shi a zuri'ar maharba tare da hasken wannan jaririn da a yanzun nan na riske shi tare da su. Sai Hasana da haskenta ya dushe ba na iya ganin komai a kanta ban sani ba za ta kusanto nan ko kuma ajali ya risketa ya yin haihuwa oho? Abu ɗaya bincikena ya nuna min ta haife shi tana rayayya kuma baya tare da ita. To kin ga kenan dabara ta rage wa mai shiga rijiya."


Tirƙashi shin wane haske ne bayan jaririn hannun Kyauta tun da boka ya ce haske biyu ne a hannun maharba? Shin ina Hasanar Usaina ta nufa da ta bawa Kyauta jaririnta? Za su iya aiwatar da maganin kafin rundunar mayaƙan nan ta riske su ko kuma za su riske su? Ka da ku manta matashin nan fa ya sanar da su duk abin da yake faruwa a garin su Kyauta kun ga ba lallai su yi sanya ba? Tabbas labarin yanzu aka fara domin salonsa daban yake bayyana harsashenku ta sigar Commenta don mu ji me kike tsammanin.💃🏼




*Ummu Aslam Bint Adam*🌚
[11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*




©AMEERA ADAM


FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️


Free page 6


🥳 in ka ji busa tabbata Sarauniya ce ta ƙaraso, ina kuke matan ƙwarai, mata ba muna mata ba, shin kin jaraba kayan *HONEY-DROPS* me kike jira har yanzu?, Manyan mata, mata masu aji na ta dafifi wajen kwasar kayan gyara, me ya sa za ki kashe kanki da ƙuruciyarki, ko tsohuwar ma na zuwa karɓar nata, kina fama da matsalar bushewar gaba, ɗaukewar sha'awa da ni'ima, ƙaiƙayi ko ƙurajen gaba, jin zafi yayin tarawa da maigida, sanyi ya taɓa miki mahaifarki?, Kina ta allura da shan magunguna ba su miki aiki ba, wane kalar infection kike fama da shi?, Staphylococcus, Gonorrhea, Syphilis, UTI, STDs ne?, Share hawayenki kukanki ya ƙare je ki nemi *HONEY-DROPS INFECTION FLUSHER* ke da sanyi sai dai ki ba da labari, kin gama cacar kuɗi, cikin kwana uku zaki fitsarar da duk wani sanyi da dattin da ke tattare a mararki, ki gyara zamanki gidan aurenki don sanyi kashe mace yake har buzunta, duk wani magani da za ki sha muddin da sanyi a jikinki iyakar shi cikinki, ba zai sauka ba. Magani ne ingantacce made of herbs, In kin gama da wannan akwai na gyaran other room, akwai Exclusive Gumba ta manyan mata ke nan, ko matar Gwamna ita take sha, ga Gumbar babbar mace mai tada tsohuwar soyayya, akwai fa tsuumi na matan gaske, akwai *HONEY FLOOD TSUUMI* kan ƙiftawar ido ni'ima ta yi ta kwararo miki, akwai BUJENTA JAGAB, da Tsuumin Ɗafau, daga jin sunan kun san akwai zance na bar muku ku ƙarasa, akwai sauran kaya masu zafi🔥


Muna da bridal package


Diamond - 100k
Gold - 50k
Silver - 30k


Ga kuma na postpartum (wanda suka haihu don dawo da martabarsu)


Diamond - 50k
Gold - 30k
Silver - 15k


Kuna iya samun mu ta 08167888934, ko 08067770852


Ban tabbatar mun yi tafiya mai nisa ba sai da na ɗauki hanya don nufi cikin garinmu, sai dai tsawon tafiyar da galabaitar da na yi ne ya sa na yanke shawarar hutawa ga jaririn hannuna sai mutsu-mutsu yake wanda nake zargin yunwa yake ji. A bakin wata ƙorama na tsugunna na saka hannuna na rinƙa ɗebo ruwan ina bashi, bai sha da yawa ba hasali ma bacci na ga ya ci gaba da yi kamar ba shi yake mutsu-mutsu ba. Bakin wata bishiyar tsamiya wacce take maƙotaka da bishiyar kuka na koma na zauna don na huta, na rungume jaririn tare da kan baƙin macijin da nauyinsa yake wahaltar da gangar jiki da ruhina. Jingina kaina ke da wuya sama-sama na fara jin takun tafiya da haniniyar dawakai, ajiyar zuciya na sauke cike da fargaba don ina tsoron kada mummunan yanayin da nake fuskata ya raunatar da ruhina har na kasa kare rayuwar jaririn da na yi alƙawarin tsayawa kai da fata don kula da shi. A ɓangare guda ga mahaɗin maganin da zai ceto yankina wato macijin da ke tare da ni wanda rasa shi tamkar rushe yankinmu da bautar da mu a baƙar daular da zalincinta ya kewaye duniya. Ido na ƙurawa jaririn da ke bacci na sake matsa shi gam a jikina kamar wani zai ƙwace shi har sai da na ji yana motsi alamar matsewar da na yi masa ya takura. Harshen wutar itacen ce zame min fitila don haka na ɗago shi da hannuna ina haska wurin da nake tsammanin daga nan wurin motsin yake, ƙura ce ta garwaye wurin lokaci ɗaya dakarun suka zagaye ni kamar yadda suka saba a duk lokacin da suka ziyarce ni, ziyarar da take sabbaba mini karayar gangar jiki da ruhi har na kasa bambamce a wace duniyar na ke. A hankali ya fara takowa haye a kan dokinsa fuskarsa kamar kullin ɗauke da murmushi yana sake kusanto ni, sauka ya yi daga kan dokin ya ƙaraso wurina ya tsugunna. Idonsa ya kai kan jaririn hannuna take hantar cikina ta kaɗa duk da na san ba ni da ragonta a ɓangaren jarumta, amma ba zan yaudari kaina ba tun da na san sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi. Kafin ya yi wani yunƙuri na furta masa, "Wane ne kai? Kuma me ya sa kake ziyartata a lokacin da nake cike da ƙwarin gwiwa da cin alwashi? Me ya sa duk faɗin yankinmu ni kaɗai haka take faruwa da ni?" Sai da ya saki yalwataccan murmushi sannan ya furta, "Saboda ke ba irinsu ba ce. Ke zara ce a cikin taurari, kina rayuwa da jinin yanki biyu mafi alheri ga daula guda. Ki ba wa jaririn nan kulawar da ta da ce domin shi jininki ne, zuri'arki ne kuma danginki ne..." Tun bai ƙarasa ba na katse shi da furta, "Na kasance ɗaya daga cikin jinin maharba, mahaifiyarsa da bakinta ta ce min ita ba ta daga cikin ahalinmu ta yaya zai kasance dangina, ahalina kuma zuri'ata. A cikin dokar daji na haɗu da mahaifiyarsa yanzu haka ina fargabar yadda zan sanar da dangina wane ne shi da yadda na same shi ba tare da wata shaida ba, ka dubi girma da tsafin abar bauta kada ka sake hargitsa lissafin rayuwata ko ka nemi cutar da ni kamar yadda ka saba a..." Miƙewarsa ce ta katse ragowar maganata, sai da ya yi taku uku sannan ya juyo ya furta, "Na fi mahaifiyarsa sanin ainihin abin da ya faru a ɗaruruwan shekarun da suka gabata, ki yarda da ni ni mai ƙaunarki ne ba zan cutar da ke ba. Abu ɗaya na sani akwai wani mummunan lamari da zai faɗo rayuwarku nan ba da jimawa ba, dalilin haka zai sababba rikicewar al'amura da dama. Amma ina mai shawartarki a duk in da za ki tsinci kan ki; ki kasance mai juriya da jajircewa, da sannu za ki fahimci saƙona gare ki." Yana zuwa nan a zancensa kamar ɗauke war walƙiya haka suka ɓace min sama ko ƙasa. Maganganunsa ne suka ci gaba da yi mini yawo a kwanyata, a hankali na yunƙura na fara jan kan macijin da ke gefena na rungume jaririna na ci gaba da tafiya. Sai da na yi tafiya mai nisa daga nesa na fara hango bukkokin garinmu, a wahalce na sauke ajiyar zuciya saboda sanyin farincikin da na ji. A lokacin da na ƙarasa wasu daga cikin dangina sun fara dawowa saboda tuni asuba ta yi haske ya fara ratsowa, mahaifiyata ce ta fara hango ni cike da murna ta tarbe ni nan take aka shiga iface-iface da samun nasarar da na yi. Lura da jaririn hannuna ya sa suka fara bi na da kallon zargi da tuhuma, a daidai lokacin mahaifina da zugarsa suka dawo sai dai a yadda na lura mun myi rashin maza da yawa. Ganin haka ya sa matan da suka ga babu mazajensu suka fara koke-koke da alhinin rashinsu. Mahaifina da sauran tawagar ne suka ɗauki kan macijin zuwa tsibirin abar bauta, ya yin da mahaifiyata ta ja hannuna har zuwa ɗaki ta fara jero mini jerin gwanon tambayoyi. Iya abin da na sani shi na sanar da ita, jiki a sanyaye ta yi wa jaririn wanka ta tatso nonon akuya ta bashi nan take ya hau sha. Tana gama shayar da shi muka tunkari tsibirin abar bauta sakamakon kiran gaggawar da ta aiko ana yi min, ta cikin mutane na riƙa kutsawa har na isa gare ta; ya yin da idanun mutane suka dawo kaina.


Kamar yadda badakaren ya rarraba su ɓangare daban-daban haka shi ma ya saɗaɗa ta wani lungu don yunƙurinsu na yi wa yankin ƙawanya, sai da suka zagayen yankin da sihirtaccan yashin baƙar daula mai karya kowanne irin tsafi da sihiri sannan suka bi ta hanyoyi daban-daban, kusan lokaci guda suka bayyana a lungu da saƙon garin kowannensu ɗauke da miyagun makamai wasunsu ɗauke manyan bulalai, ya yin fa wasunsu suke riƙe da manyan itatuwan da ake ɗaure bayi a jiki, dubannin jama'ar da suka hango a kan tsibirin ne ya tabbatar musu da sun dira a yankin da bawan nan yake yi musu leƙen asiri. Don haka suka yi kukan kura suka nufi wurin da niyyar su afka musu farad ɗaya, jin ihunsu ya fargar da su Kyauta nan take hankulansu ya tashi don kowannensu ya ajiye makamansa balle su yinƙurin kare kansu. Sai dai duk yadda suka kaiga yin amfani da layar ɓata ko shashatau haƙansu ya gagara cimma ruwa, don haka suka zage aka fara musayar ƙwanji.


Daular Sarki Damina.


Ajiyar zuciya Usaina ta sauke cike da damuwa da ƙuncin ta furta, "Tabbas akwai gagarumar matsala domin a kowanne lokacin kwaɓata na iya yin ruwa tsululu, zan fara binciken hasken da ke cikin Daular nan bayan Yarima idan har na gano shi tabbas sai na hallaka shi a ruwan sanyi, ba na ta Yarima dama tuni na rufe babin rayuwarsa tun da; da shi da matacce duk ɗaya suke a wurina. Sai wancan hasken da ya ɓulla cikin zuri'ar maharba shi ma dole na daƙile shi ya koma duhu, ka yi sani ya kai boka mai zamani koda zan rasa raina na yi rantsuwa da albarkar Sha kundum jinin Damina ba zai ƙara hawa kan karagar mulkin nan ba." Boka mai zamani ya janyota jikinsa yana ƙoƙarin biyan buƙatarsa sannan ya furta, "Mutum irinki na matuƙar burge ni, ƙwarin gwiwarki da dakiyar zuciyarki abin a yaba miki ne. Sai dai ki sani ko shi Damina bai taɓa sanin yana da wani ɗan bayan Yarima ba, shi wannan hasken ya fito daga jikin wata baiwarsa ne hatta ita kanta baiwar ba ta san ɗan da ta haifa jinin Damina ba ne. Lamarin akwai ɗaure kai amma zan taimaka miki domin cimma burinki tamkar cika nawa ne, yanzu dai mu bar wannan maganar ki zo ki ramawa kura aniyarta." Usaina bata musa masa ba don haka ta ci gaba da karye-karye cikin salo mai jan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login