Showing 69001 words to 69452 words out of 69452 words
Chapter 24 - BAKAR DAULA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Ameera Adam.txt
Sannan wannan Bafulatanin yana ƙoƙarin wargaza shirinmu tabbas za mu ɗau mummunan mataki a kansa, amma fa duk da haka Mahaifiyarki bata sha ba domin za mu ɓullo mata ta sigar da ba za ta taɓa tsammani ba. A yau saura kwana biyar ta fara al'ada don haka zan yi amfani da wannan lokacin, domin alƙawarinta na yi ga ɗakin arziƙi." Raihan ta jinjina kai cikin girmamawa, abar bauta ta nuna wata ƙaramar ƙorama ta ce,: "Ki ɗebi ruwan wanke zunubi ki yi wanka domin kin karya ƙa'idoji da dokar ƙungiya." Raihan na yin wanka kamar yadda Abar bauta ta umarceta ta fice daga kogon dutsen.
Intisar ce ta ɓullo daga ƙarƙashin ƙasa ta yi gaisuwa ga abar bauta, kusan cikin haɗin baki suka furta, "Huzaifa zai aika da Raihan ƙasar India don bincike na musamman akan Raihan." Abar bauta ta yi murmushin takaici ta ce, "Na san da haka shi ya sa na nemo ki yanzu. Zai kaita India ne wurin Kakansa Jibbul-Ƙasi don ya yi mata bincike a kanta, ya ɗora zarge-zarge akanta ciki kuwa har da ke." Intisar ta jinjina kai sannan ta ce, "Tabbas na san za a yi haka domin na san wanenen Huzaifa da bin didiginsa." Abar bauta ta miƙe tsaye sai da ta yi zagaye wurin sau uku sannan ta ce, "Ba zai yi nasara a kanmu ba, domin za mu mallakawa Raihan duk wani ƙarfin iko, idan a da bata san wacece ita ba ya zama dole mu sanar da ita ta hanyar sakata a ɗakin arziƙi." Hankali a tashe Mugaza ta ɗago tana faɗin, "Kina nufin tun yanzu za ta mallaki shuɗaɗɗan ruhi ba sai nan gaba ba ya Abar bauta." Abar bauta ta ci gaba da tafiya tana jinjina kawunan jikinta ta ce, "Alƙawarin ƙungiya baya tashi, matsawar Huzaifa ya kaita wurin kakansa tabbas sai ya gane shirinmu kuma sai Kakansa ya wargatsa ƙungiyar nan. Idan kuwa muka saka mata shuɗaɗɗan ruhi dole zai zama garkuwa a gare ta, za ta gagari Jabbul-Ƙasi da dukkan wani shirinsa.
WASAN YA FARA ƊAUKAN ZAFI🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️ RAIHAN TA KUSA ZAMA SHUGABA LIKAFA TA CI GABA😂😂 MENENE ALAƘAR SHUƊAƊƊAN RUHI DA RAIHAN, SHIN DAMA RAIHAN NA DA WANI A ƘUNGIYAR ASIRI NE DA HAR RUHINSA ZAI MAYE GURBINTA KO YAYA? WACCE ALAƘA CE TSAKANIN SHUƊAƊƊAN RUHI DA KAKAN HUZAIFA JUBBUL-ƘASI? CAKWAKIYAR ƘARA GABA TAKE🥵 MAZA HANZARTA KI BIYA DON JIN YADDA ZA TA KASANCE GARA KI BIYA 300 KI KARANTA AMMA IDAN NA KAMMALASHI SAI KIN SAKA 500 ZA KI SAME SHI🥱🥱🥱 WANNAN SHI NE SHAFIN ƘARSHE WATO SHAFIN ƘAUTA😎 MU JE ZUWA ƳAN GROUP ƊIN *ZAUJATU PAID* A CI GABA DA GASH SUYA SAI RANAR BIKIN NAƊIN 👸🏻 RAIHAN A ƘOGON DUTSEN ƘUNGIYA🤸🏻♀️💃🏼
SHARE HILIS🌚