Showing 18001 words to 21000 words out of 69452 words
Chapter 7 - BAKAR DAULA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Ameera Adam.txt
hankali, duk da kasancewarsa tsoho tukuf mai yawan shekaru bai sa ya gagara nuna mata jarumtarsa ta nagartattun ƴan maza ba, ba su suka gama aikata masha'arsu ba sai gabannin asuba. Gudun kada gari ya waye asirinta ya tonu ya sa ta yunƙura za ta tafi, har ta je bakin ƙofa ta koma wurin Boka mai zamani tana faɗin, "Na manta da tukwicin ziyarata, ka ba ni wani abin mana don na faranta ran maigidana." Ɓata fuska Boka ya yi a daƙile ya furta, "Kada ki tunzura ni kishi ya hana ni baki sirrin mallaka, don na tabbata ko Damina bai kai ni kishinki ba." Fari ta yi masa da ido ba tare da ta furta komai ba, ya zura hannu cikin ƙoramar sihiri ya ɗauko jaririn kunkuru, sai da ya sakata ta kwanta ya ɗora kunkurun a cikin gabanta na ƴan sakanni. Sannan ya saka a cikin tashi al'aurar kamar yadda ya yi mata, ya samu dutsen wuta na sihiri aya ajiye jaririn kunkurun ya buga masa nan take ya dagargaje, hannu ya saka ya ɗauke shi ya zuba a cikin wata sihirtacciyar ƙwarya sannan ya tsiyaye mata ruwan a ƙanƙanuwar ƙwarya ya miƙa mata yana faɗin, "Ki tabbatar da kin ba wa Damina ya sha, kuma ki tabbata kin yi tsarki da shi kafin ki yi mu'amala da shi, da idonki za ki gani ba sai na baki labari ba." Cike da farinciki Usaina ta karɓa ta fice daga cikin kogon dutsen a sirrance ta wuce ɓangarenta ba tare da kowa ya ganta ba.
Gari na wayewa Sarki Damina ya saka aka ɗauko gawar Mai babbar turaka a lokacin har ta bushe ta sandare, lokacin da aka je ɗauko gawar Yarima na zaune ya haɗe kai da gwiwa. Ganin mutane ya sa ya tashi a haukace ya yi kansu yana ƙoƙarin yagar naman jikinsu, da ƙyar suka samu aka fita da ita sai dai daga dakarun da suka je ɗauko gawar babu wanda bai raunata ba. Da ƙyar da suɗin goshi suka samu suka maƙala masa sasari a ƙafa da hannu, don yadda suka lura da yanayin ciwon nashi ya fi na kullin tsanani. Saboda yadda ya karya ƙofofi da windunan ɗakin, a lokacin da ya kama ɗan yatsan hannun wani dogarin sai da ya cire shi daga tsintsiyar hannun. Wannan mummunan labarin ba ƙaramin ɗaga hankalin Sarki Damina ya yi ba, haka ya daure ya cije har aka kai masa gawar mai babbar turasa. Kamar yadda yake bisa al'ada duk macen da ta mutu a hannun yarima ko sarkin daular wannan na nuna gawarta za ta albarkaci daular da dodon tsafinsu, kuma ta kan iya zama matsala ga shi yarima ko sarkin da ta mutu a wurinsa. Ana kai wa Sarki gawar ya cire wasu daga cikin gaɓɓan jikinta domin a camfinsu matuƙar ba a yi wannan al'adar ba Yarima ko sarkin da ya yi silar mutuwarta zai yi mummunar mutuwa a hannun mace, wala matarsa ta aure ko macen shaƙatawa. Saboda duk ranar Alhamis sukan ware ta a zuwan ranar shaƙatawa tsakanin maza da mata, mahaifi idan ya yi sha'awar ƴarsa duk ƙarfin sha'awarsa sai dai ya bari sati ya zagayo. Ba abin kunya ba ne a wurinsu don uba ya yi wa ƴarsa ciki kamar yadda suke zube wa a filin da rana tsaka suke mu'amalarsu kowa na ganin ɗan uwansa. Ranar dama suna ware ta ne saboda irin haka shi ya sa suka yi wa ranar laƙabi da ranar nishaɗi. Kaifaffiyar wuƙa mai walƙiya aka ɗauko masa, tsirara aka yi wa gawar mai babar turawa aka kwantar da ita a kan tabarmar kaba, sannan aka ajiyewa Sarki Damina kujera mai ɗauke da siffar mutum a durƙushe alamar ƙasƙantar da kai wuyansa saƙale da kwari da baka. Bayan ya ɗauki wuƙar sai da ya kira sunan Sarauniya Sha kundum sau uku sannan ya sa wuƙar ya fara yankar maman mai babbar turaka, ya zuba su a cikin wani baƙin kasko wanda da alama bai taɓa ganin ruwa da sunan wankewa ba. Yana gama yanka ya buɗe bakinta da kyar ya yanki harshenta, daga haka ya daddatse dungulmin hannu da ƙafarta ya sake zuba wa a kaskon ya miƙawa uwar madafa. Jikinta na rawa ta karɓa ta wuce don gasa wa yarima ya cinye, daga haka aka ɗauki gawar mai babban ɗaki aka kaita ɗakin babban dodo bayan ya tsaface ta aka kaita ramin matattu. Babban rami ne aka tanade shi domin zuba gawarwaki, duk wanda ya mutu a yankin can ake kai su matuƙar ba Sarki ne ya bayar da umarnin a ƙone shi ba.
Hankali a tashe mazanmu da mata suka shiga kiciniyar kare kan su sai dai tuni suke yi yunƙura cin mu da yaƙi, ganin haka ya sa Mahaifiyata ta miƙo min jaririn hannunta tare ta damƙa min hannun Kandala a cikin nawa ta furta, "Ki kula da su kamar yadda kika ɗauki alƙawari domin ina da yaƙini waɗannan sun fito daga cikin Baƙar Daula ne domin su farmake mu su bautar da mu, ba na son rayuwarki ta gurɓata a can ku bi yamma da gari domin ku tseratar da rayuwarku. Duk garin da kuka samu a gaba kada ku yi sanya ku yi ƙoƙarin ɗaukar al'adarsu matuƙar ba al'adar da abar bauta za ta yi fushi da ku ba ce." Hawaye na zuba na furta, "Kina ganin zan iya tafiya na bar kuna cikin wannan halin? Ba na son na rasa ku domin tafiyata tamkar rasa ahalina na maharba ne..." Ba rufe baki ba mahaifiyata ta hankaɗa ni cikin ƙaraji tana faɗin, "Tarayyarki da mu tamkar kasancewarki a baƙar daula ne, baƙar daular da gara kura da yi fata-fata da naman jikinka a kan kasancewar bawa a cikinta. Jikina yana ba ni maganar abar bauta ce za ta tabbata lokacin tarwatsewar yankin nan ya zo." Ina ji ina gani na riƙe hannun Kandala ɗayan hannuna rungume da jariri muka nufi wata siririyar hanya da take da mahaɗa da tsibirin abar bauta. Lokacin da muka shiga siririyar hanyar kukan ƙananan yara da na masu matsakaicin shekaru suka ratsa dodon kunnena, ihun mahaifiyata da na ji ne ya sa ni gagara haƙuri har na leƙa kaina don ganin abin da yake faruwa, muna haɗa ido da ita na ga ta girgiza min kai alamar na tafi a daidai lokacin wasu manyan dakaru suka fara ɗaure hannuwan mutanen yankinmu a jikin wani murtukeken ita ce. Ana ɗaure su ana tafka musu manyan bulali a jiki, wanda saukar bulala ɗaya ba sa ɗagota sai da fatar gangar jikin mutum, gawargwakin ƙananan yara da manyan da aka karkashe a wurin ba za su irgu ba, ana cikin haka jaririna ya fata motsi da alama kuka zai yi. Duk yadda na kai ga aikata wani abu daga cikin al'amuran tsafi da siddabaru abin ya gagara, ganin yana son tona wurin da muke laɓe ya sa na saka ɗan yatsana na rufe masa baki. Inuwata da wani Badakare ya hango n a ji yana nuna wa wani ɗan'uwansa hanyar wurin da muke laɓe da bashi umarnin ya kamo mu, jikina na rawa na kama hannun Kandala muka fara gudu hankali a tashe. Ba zato ko tsammami na ji na bugu da wani abu, ɗago kaina ya sabbaba min hautsinewar ciki. Hautsinewar da ta sa gumi ya fara karyo min nan take, domin haɗuwar karonbattar da na yi bata da maraba da mun yi gudun gara mun faɗa gidan zago.
😂 Wollah akwai ƙura fa.Ni kaina na ji faɗuwar gaba yasin 😰 wannan baƙar daula ko kaɗan bata yi ba.
*KU MATSO KU TAHO*💃🏼
Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananin ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.
Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼
Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰
Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚
[11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️
Free page 7
🥳 in ka ji busa tabbata Sarauniya ce ta ƙaraso, ina kuke matan ƙwarai, mata ba muna mata ba, shin kin jaraba kayan *HONEY-DROPS* me kike jira har yanzu?, Manyan mata, mata masu aji na ta dafifi wajen kwasar kayan gyara, me ya sa za ki kashe kanki da ƙuruciyarki, ko tsohuwar ma na zuwa karɓar nata, kina fama da matsalar bushewar gaba, ɗaukewar sha'awa da ni'ima, ƙaiƙayi ko ƙurajen gaba, jin zafi yayin tarawa da maigida, sanyi ya taɓa miki mahaifarki?, Kina ta allura da shan magunguna ba su miki aiki ba, wane kalar infection kike fama da shi?, Staphylococcus, Gonorrhea, Syphilis, UTI, STDs ne?, Share hawayenki kukanki ya ƙare je ki nemi *HONEY-DROPS INFECTION FLUSHER* ke da sanyi sai dai ki ba da labari, kin gama cacar kuɗi, cikin kwana uku zaki fitsarar da duk wani sanyi da dattin da ke tattare a mararki, ki gyara zamanki gidan aurenki don sanyi kashe mace yake har buzunta, duk wani magani da za ki sha muddin da sanyi a jikinki iyakar shi cikinki, ba zai sauka ba. Magani ne ingantacce made of herbs, In kin gama da wannan akwai na gyaran other room, akwai Exclusive Gumba ta manyan mata ke nan, ko matar Gwamna ita take sha, ga Gumbar babbar mace mai tada tsohuwar soyayya, akwai fa tsuumi na matan gaske, akwai *HONEY FLOOD TSUUMI* kan ƙiftawar ido ni'ima ta yi ta kwararo miki, akwai BUJENTA JAGAB, da Tsuumin Ɗafau, daga jin sunan kun san akwai zance na bar muku ku ƙarasa, akwai sauran kaya masu zafi🔥
Muna da bridal package
Diamond - 100k
Gold - 50k
Silver - 30k
Ga kuma na postpartum (wanda suka haihu don dawo da martabarsu)
Diamond - 50k
Gold - 30k
Silver - 15k
Kuna iya samun mu ta 08167888934, ko 08067770852
Girma da siffar Badakaren ne suka sake hargitse lissafin rayuwata, a hankali na sake ja da baya ya yin da yake sake tunkaro mu gadan-gadan hannunsa ɗauke da wani mummunan ƙarfe wanda aka naɗe jikinsa da manyan ƙusoshi, a zafafe ya ɗaga da niyyar buga min a tsakar ka cikin shammata mahaifina ya kai masa duka a wuyansa. Take suka fara kokawa ganin haka ya sa mahaifina ya yi mini alama da mugudu ni da Kandala, gudu muke kamar ranmu zai fita don na gama tsorota da yanayin azzaluman mutanen da suka fito daga baƙar daula. A yadda na bar mahaifina da Badakaren ina jimamin halin da mahaifina yake ciki don na tabbata zai yi wuya idan bai yi wa mahaifina taron dangi sun hallaka shi ba, sai da muka yi tafiya mai nisan gaske sannan muka raɓa cikin wata bishiyar ɗorawa mai duhu muka zauna muna hutawa, waige-waige nake yi don ganin hanyar da zan samu ruwan da zan ɗebo mana musha saboda zafin ranar da ya busar da maƙogaronmu. A wahalce Kandala ta kalle ni idonta na zubda ƙwallah tana faɗin, "Kyauta ƙishirwa za ta kashe ni maƙoshina ya bushe." Jijjiga jaririn nake saboda kukan da yake ta tsalawa wanda na tabbata kukan wahala ne sannan na furta mata, "Riƙe min shi ki kula da kyau zan duba mana ko da ƙorama a kusa idan muka sha sai na duba ko zan samu wani naman dawan na gasa mana." Karɓarsa Kandala ta yi na miƙa cikin dajin ina duba hagu da dama ko zan samu ƙaramar ƙoramar da zan ɗebo mana ruwan, ko kaɗan ban yi tunanin wurin da zan ɗebi ruwan ba babban burina bai wuce mu samu ruwa kowanne iri ba ne. Daga can nesa na hango wani bafulatani yana tafe da shanunsa wanda hakan ne ya tabbatar min da kiwo yake, gudu-gudu sauri-sauri haka na rinƙa tafiya don na ƙarasa na cimma masa koda zai sa ya taimaka min, yana ganina ya fara bina da kallon tuhuma don ko bai faɗa ba na san suturar jikina yake kallo wacce ta bambamta da irin ta shi, kallon kaina na yi daga ni sai guntuwar fatar da ta rufe min ƙirjina da wacce na suturta al'aurata, sannan na ɗago na kalle shi yana sanye da farar rigar saƙi ta kala-kalan zarurruka, sandar hannunsa ya ɗaga na ji yana yin yaren da nake tsammanin fullaci ne sannan ya yo kaina da sauri zai sauke min ita. A razane na ja da baya cikin hakki ina faɗin, "Abar bauta bata wanzar da zalinci a doron ƙasa ba don haka kada ka cutar da ni." Sauke sandar ya yi ƙasa sannan ya furta, "Hai meye abar bauta kuma? Ke kam aljani ne ko mutum?" Dafe kaina na yi saboda matsanancin ciwon da yake min sannan na furta, "Ni mutum ce tare nake da ƙanwata ka taimaka mana ka ba mu ruwa mu sha." Kallon da yake min ne na tabbatar min da har lokacin bai gama aminta da ni ba, don haka na ga ya runtse ido yana ci gaba da fulatanci sannan ya kara sandar hannunsa a saitin kaina. Ya ɗan jima a haka sannan ya buɗe idonsa ya ce, "Zan taimaka maka ina ƙanwar taka?" Hanyar da na baro su Kandala na nuna masa, ya ƙurawa wurin idanu sannan ya ciro kurtunsa ya miƙo min. Har na ɗaga kai zan sha na tuna halin da na baro su Kandala, da sauri na sauke shi na ce masa. "Ka taimaka ka cika ladanka ka bar ni na kaiwa ƙannena su sha. Idan ka yi haka abar bauta za ta albarka ci kiwonka." Ɓata fuska na ga ya yi don haka gabana ya faɗi, ina shirin roƙonsa na riski muryarsa yana faɗin, "Kada ki sake danganta ni da abin bautarku domin Yesi Almasihu zai yi fushi da ni saboda na haɗa bautarsa da waninsa." Shiru na yi ina mamakin maganarsa domin a iya sanina bayan abar bauta babu wani abu da ake bauta wa a faɗin duniya. Da yake ina cike da son biyan buƙatar kaina sai na gyaɗa masa kai cike da godiya, har na juya zan nufi hanyar na ji yana faɗin, "Ki bar hanyar ɓata ki dawo kan shiriya ko za ki samu gidan daɗi wato aljanna domin mu mabiya Yesu Almasihu mun kasance masu karamci da taimakawa saboda Allah." Ko kaɗan ban gane abin da yake nufi ba don haka ban amsa masa ba, sai na kawar da maganar cikin amsar da na bashi da cewar, "Zan gaggauta kai wa ƴan uwana akwai jariri ina tsoron kada ya mutu." A hargitse ya fura, "Jariri kuma?" Na gyaɗa masa kai, jin haka ya sa ya kaɗo shannunsa ya rufa min baya muka tunkari wurin da su Kandala suke. A galabaice muka same su don haka cikin hanzari na karɓi jaririn na fara bashi a lokacin tuni ya gaji da kuka ya sake yin bacci, sai da ya sha ya ƙoshi sannan na miƙa wa Kandala ita ma ta sha ta rage mini. Tausayin Jaririn ne ya kama shi ya dube ni yana faɗin, "Idan ba za ki damu ba ko na tatso masa nonon Naggen can ya sha." Ban san lokacin da murmushi ya suɓuce min ba na furta masa, "Na gode sosai da taimakonka." Nonon saniyar ya tatsa da ɗuminsa ya miƙo mini na ɗan riƙa bashi kaɗan-kaɗan yana sha. Sai da na lura ya ƙoshi sannan na miƙa wa Kandala ta shanye sauran, miƙe wa na yi na yi na yi masa godiya muna shirin tafiya ya furta min, "Yanzu ina za ku tafi ke da kika ce baki da kowa?" Idanuna ne suka ciko da ƙwalla na furta masa, "A da ni ƴar gata ce gaba da baya, sai dai a yanzu ba ni da kowa ban san inda za mu tafi ba." Tambaya ya sake jefo min nan take ya bashi labarin abin da ya baro mu daga yankinmu, ya tausaya mana sosai don haka ya yi alƙawarin kai mu rugarsu domin ya taimaka mana, duk da ya gargaɗe ni a kan na ɓoye addinina idan kuwa na bayyana shi a rugarsu za su iya korata daga garin. A yadda ya ba ni labari tun tasowarsu iyaye da kakanni babu wani addini da suka sani face Kiristanci, a kan shi suka kafu Yesu Almasihu suke bautawa don haka ba su yadda akai musu kowanne irin addini saɓanin nasu ba. Ba ni da zaɓi don a lokacin burina bai wuce mu samu