Showing 1 words to 3000 words out of 45089 words

Chapter 1 - NIDA PATIENT DINA Book 1 Complete Hausa Novels by Mrs Hisham .txt

14 Jan 2025

3408

🧑‍⚕️🧑‍⚕️NIDA PATIENT DINA🩺🩺
Story written by (MRS 🌹ISHAM🌹)


Da sunan allah me rahama mejinkai🙏 Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy ,yabani iKon gamawa lfy,
Ameen.


Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci🥰🥰




____________________________________________




Page 1️⃣


wata karamar yarinyace dabazata wuce shekara 5yrs ba tashigo gida tana fadin mama,mama, mama, wata kyakyawar mata nagani wacce bazata wuce shekara 40 ba aduniya da sauri mahaifiyarta tafito daga kitchen auta meyafaru irin wannan kira haka, cikin kuka da yarinta tafara magana mama Kinga kin aikeni Khalid yakwace kudin yaki bani. Meya hadaki dashi bana hanaki wasa dashiba bayan kisan yagirmeki ko,mama tagama magana tana kallon autarta Dake kuka. To shikenan Yi shuru bari in kira antynki kuje tare kukarbo kinji auta cikin jindadi auta tace to shikenan mama.


Wucewa direct falo mama tayi tahau kwala kiran FANAN wannan baccin naki ya Isa haka kitashi kizo kisameni awaje, lekawa dakin nayi Dan inga wacece wannan FANAN din. Dakine Dede namasu matsaqaitan karfi masu rufin asiri, ganin wata kyakyawar yarinya nayi wacce aqalla bazata wuce shekara 18 ba tana sanye da wando boom short dariga me karamar hannu gashin kanta kuwa yasauko har gadon bayanta, mikewa tayi tsaye SE anan ne nasamu damar kare mata kallo chocolate color ce,tanada manyan idanu wayanda suka kasance farare, tana da hanci dogo, ga bakinta Dan karar Rami dashi, libs dinta red ne kamar tashafa mishi janbaki, tana da tsawo Dan bazaa sata sawun guntaye ba , kirjinta cike suke da boobs kamar zasu fito waje sannan tanada hips sosai Masha Allah domin yanda take da jiki mekyau da sura bazakayi tunanin shekarunta kenan ba kyakyawace ta ajin farko.


Tafiya tafarayi domin tashiga toilet ta watsa ruwa ko baccin ze saketa, bayan kamar 10mints tafito tana tsane jikinta da wani karamin towel, tunawa datayi mama nakirantane yasa tafara shiryawa da sauri, lotion 🧴 tashafa ajikinta. wata dogon Rigar material tadauka tasaka kafin tadauki man gashi tashafawa kanta ta taje gashinta din tadau ribom dakyar ta iya hade gashin tadaure. Perfumes tafesa ajikinta tadauki hijab Daya wuce gwuiwanta tasa Masha Allah, ta hadu iya haduwa.


Fitowa tayi tasamu mama na gyara shinkafan dazaayi tuwon dare dashi, cikin sanyin murya tace mama gani dago kanta mama tayi cikin zuciyarta tafurta Masha Allah yata allah yakawo miki miji nagari, yauwa dama dazun na aiki auta shine komeya hadata da Khalid yakwace kudi a hannunta Dan Allah jekijimin baasi kikarba kudin kisiyomin kayan Miya dashi karki Dade Kinga yamma tayi ko cikin murmushinta dayake Kara mata kyau tace to mamana bari inji.






Ga wannan kufara dashi se mun hadu gobe🥰🥰🥰🥰






via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD


🧑‍⚕️🧑‍⚕️NIDA PATIENT DINA 🩺🩺Story written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)




Da sunan allah me rahama mejinkai 🙏 Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy Ameen.






Wanann littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci 🥰🥰.






____________________________________________






Page 2️⃣




Tafiya tafarayi cikin nutsuwa tana fito waje kuwa tasauke manyan idanunta akan Khalid Dake wasa a kofar gidansu karasawa tayi kusa dashi tace yaron kirki me yahadaka da auta ka kwace kudi ahannunta. Anty FANAN itace tafara tsokanata shine nafita zan daketa tagudu kudin hannunta yafadi akasa shine nadauka karasa maganar yayi yaname mikawa fanan kudin, sa hannu tayi takarba sanann tace mishi nasan auta da tsokana nan gaba inta Kara kaje gida kafadawa mama kaji ko, to shikenan anty FANAN.
Zuyawa tayi domin taje tayi cafenen da mama tasata bayan takammala siyan abinda yakawota zatabada kudi kawai taji ansa hannu an rufe mata ido dariya tayi tace malama dallah budemin ido angaya miki bazan gane kowaye bane, dariya tabayan nata tayi hhhhh bestie kenan ainadauka bazaki gane bane,zagayowa tayi gabanta tana tambayanta yasu mama, wlh kowa na lfy Amira yau kinje asibiti ne cewar FANAN tana kallon kawarta ta. Amira tace yauwa bestie meya hanaki zuwa yau in charge fah seda yatambayeni ke nace mishi yau kankine yake ciwo shisa bakizoba. Dogon numfashi fanan taja kafin tafara magana kekam yau agajiye nake nasha bacci sosai kawai nace to bari inbari gobe kawai inje, ahh lallai kam kinhuta bestie naga har wani kumatu kikayi dariya dukkansu biyu sukasa.Suna tafiya suna hiransu abin shaawa. FANAN da AMIRA kawayene su tun yarinta kasancewar sunyi makaranta tare Kuma anguwarsu Daya.
Karasowa gida sukayi suka shiga da sallama abakinsu gaida mama Amira tayi ,cikin sakin fuska mama ta amsa tana tambayarta ya mamanki dasu hajiya kowa lfy mama Ina yar auta rigima bangantaba, dariya mama tayi auta rigima kam tana daki wai tana kwalliya dariya Amira tayi tace tom yaukam kwalliyarta fah naga alama semun gudu🤣 . Kai autan maman kike fadawa haka cike da zolaya FANAN tayi maganar, murmushi mama tayi tace dukkanku biyu zakuyi bayani. FANAN karasawa tayi kusa da mama Tamika mata kayan miyan tana mata bayanin abinda yahada Khalid da auta girgiza Kai mama tayi tace allah yashiryamin ke auta amsawa sukayi da Ameen.




Daki suka shiga amira natayiwa FANAN hiran abinda yafaru yau a asibiti zama sukayi akan gado sunata hira can Amira tace nikam yau yabanga yaya Usman ba , wlh nima tunda natashi banganshiba maybe bedawo daga aiki ba sbd wani lokacin tare da baba suke dawowa cewar FANAN, cire hijabin jikinta tayi tarage kayan jikinta domin jinta takeyi kamar zata narke Dan zafi, bestie kinaban mamaki juyowa fanan tayi tana kallonta tace nameye kenan bestie, eh mana kamar wacce kaya yake mintsilinki bakya iyazama da manyan kaya ajikinki kina samun sarari Zaki kwabesu dariyarta medauka hankali fanan tayi tace wlh nikaina abin nadamuna inbada kana nan kayaba kwata kwata bana iyazama da kayan daze dameni uhmmm bestie kekam mijinki zega Abu takarasa maganarta cikeda shakiyanci. Amira allah yashiryeki wasa wasa yarinyar nan kinbaci tana magana tana dariya ahaka mama ta kwalawa mata kira zoki dauka muku abincinku fitowa tayi da zani adaure a kirjinta kare mata kallo mama tayi kafin tace nikam fanan lfynki kuwa ace mutum baya kaunar kaya katuwa Dake kina yawo haka cikin shagwaba tafara magana haba mama duka nawa nake dazakicemin katuwa. Takarasa magana tana buga kafa girgiza Kai kawai mama tayi iKon Allah kekam dakece autana dazamuga tabara wlh wuce kibani wuri daukan abincin tayi tana dariyar mama tashiga daki ta ajiye musu abincin kafin sukayi Bismillah suka fara ci. Suna tsaka dacin abinci auta tashigo musu da pure water dago Kai Amira tayi zatama auta magana, zabura tayi fara innalillahi wainna ilaijiraji unnn ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba aikuwa FANAN asukwane tadago Kai takalli inda Amira take kallo kamar tasa gudu dan yau kwalliyar da auta tacaba kamar wata aljana haka Takoma gashi tabude Baki se dariya take musu dukansu zuba mata ido sukayi kafin FANAN ta iya Bude Baki tace auta Dan Allah kiyi hakuri kidena kwalliyar nan Dan inkikayi fita kikeyi daga jinsin bil adama dahaka ake kwalliya Aida anshiga uku Amira Dake bayanta tafashe da dariya, matsowa kusa dasu tayi tace nayi kyau kuwa kokuma inkara janbaki ? Kode kwalli zankara iye anty aikuwa dariya suka Kara fashewa dashi har suna rike ciki ganin hakane yasa auta tabar dakin tana kuka, tsaqaitawa sukayi da dariya Amira nacewa anty ko janbaki zankara, hararanta FANAN tayi cikin wasa tace kinsan allah badan nasan auta nagidaba dazance aljanace. Kai autan mama kenan. Bayan sungama cin abincine sukaji sallaman baba tare da Yaya Usman a fallo saka hijabinsu sukayi atare suka fito Falon suka tsuguna suna gaida baba cikin zolaya yace yau kam bazan amsa gaisuwarku ba domin kutabo yar shalelena inshigo gida taban lbrn irin dariyar dakuka mata Dan tanuna muku kwalliyar data chaba yakarasa magana Yana Dan dariya Suma dariyar sukeyi kafin Yaya Usman yace baba nifa nayi niyyar guduwa Dan nayau abin ya girgizani cikin dariya baba yace daga gudun ai zaka dawoma bawanda yasani kafin yajuyo Yana amsa gaisuwar su Amira yace mata ya gidan naku cikin girmamawa ta amsa da lfy Lau alhmdllh baba yace ta madallah ya asibitin fatan kunayin abinda yakamata kudingayin abinda yakaiku karku biyewa shashanci amsawa sukayi da in sha Allah baba kafin yace Masha Allah allah yataimaka yabaku nasara akan abinda kukasa agaba dukansu amsawa sukayi da Ameen ya Allah. Mikewa sukayi Amira tamusu Sallama zata wuce gida seda safe sukayi kafin taje tasamu mama a kitchen tana hadawasu baba abinci tamata sallama cikin sakin fuska mama tace to Amira kigaida gida kinji ta masa da to mama suka wuce FANAN tarakata har kofar gida sbd Basu da wani nisa.
Bayan tadawo gida tatsaya dasu Yaya Usman a falo sunata hira cike daso da kauna gwanin burgewa.








To masu karatu semun hadu gobe, sannan plx kudingamin comment hakan shine zebani karfin gwuiwan cigaba dakawo muku, Amma inna tura Kuna gama karantawa shikenan bazakuce komai haba please Dan Allah mugyara🥰🥰🥰🙏


via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD


🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺


Story written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)
Da sunan allah me rahama mejinkai 🙏 Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy Ameen 🙏🙏🌹






Wanann littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci 🥰🤎






__________________________________________




Page3️⃣






Babane yace to kutashi aje ayi sallah isha mikewa yayi shida ya Usman suka tafi masallaci. Mama itama dakinta ta tafi don gabatar da sallah, ita kam FANAN kasancewar bata sallah seta wuce daki takwanta tajawo wayarta tashiga buga game 🎮. Gajiya tayi ta ajiye wayar tamike tashiga toilet tayi wanka tafito tashafawa jikinta mai da turare kayan bacci tadauko pink color me laushi tasaka sannan tahau gado tunani tashigayi gobe fa zata shiga asibiti inda rai da lfy zatayi kokari tashiga da wuri sannan tayi adduah bacci ta kwanta.




Washe gari


Karfe 7:00am ta tashi daga bacci brush tayi tayi wanka sanan tafito ta saka dogon hijab har kasa tafito taje dakin baba ta gaisheshi daga nan tayi wajan mama suka gaisa tambayar mama tayi Meye zaayi na karyawa , mama tace kiyi Dan wake da tea kawai amsawa tayi to tamike , kitchen tawuce tahada kayan wanke wanke tafito dasu kafin Takoma tana kokarin hada kayan karyawa. Wanke wanke takeyi cikin kwanciyar hankali hartagama taje tajera komai yanda yadace a kitchen sannan tayi shara da mopping komai da komai daga nan Takoma kitchen tacigaba da hada kayan karyawa. Bayan takammala ta juye tea a flask takai falo da food flask ta ajiye direct dakin mama taje tasameta tasanar da ita tagama murmushi mama tayi tace allah yamiki albarka ta amsa da Ameen bari inje inyi wanka to kawai mama tace mata.


Komawa daki tayi tacire hijab din wanka zata sakeyi sbd ta gaji tahada zufa, bayan 10mints tafito sanye da towel ajikinta Bude wardrobe tayi tafito da uniform nata da handbag da takalminta a tsanake take shiryawa gyara gashinta tayi tahadeshi waje daya tayi donot dashi. Uniform tasa ajikinta wayanda suka kasance white 🤍color tadaura dankwali Amma seda sajen gaban kanta yafito powder Tashafa sannan tasa kwalli a idonta tasa libs stick adan karamin bakinta yayi kamar tasa janbaki.tubarkallah Masha bakaramin kyau tayi ba agogo tadaura a hannunta tasa after dress Baki asaman uniform din hijab dinta Wanda bewuce cikiba tasa feshe jikinta tayi da perfume sannan tadau handbag 👜 dinta tafito falo tasamu harsun kammala breakfast, mama ce tasamata kayan karyawanta zama tayi tayi Bismillah taci badayawaba ta ce mama zantafi allah yabada saa mama tamata sannan tace kije babanku na daki wucewa tayi dakin baba tayi sallama yabata umarnin shigowa mamana harkin shirya eh baba nagama dauko Dari 500 yayi yabata sannan yamata adduah allah yabata saa Ameen babana sena dawo tamishi sallama tafito kenan taci karo da ya Usman yafito da machine dinsa,ya usman ina kwana lfy Lau kintashi lfy ta amsa lfy Lau alhmdllh zokihau in ajiyeki tace to hawa tayi suna tafiya suna hira har suka Isa bakin asibitin SPECIALIST ajiyeta yayi yajuya duba time a wayanta tayi taga 9:30 tafiya takeyi harta karasa addimission ward tana shiga tahango Amira nasawa wata patient drip karasawa tayi gaisawa tayi da Yan wajan cikin sakin fuska da murmushi dauke afuskanta tamusu ya jiki amsawa sukayi dasauki nurse. Karasawa tayi wajan patient's dinta Dake kwance gaisawa sukayi kafin tace mata yajikin naki fatan dasauki washe Baki tayi tace ahh dasauki sosai murmushi kawai FANAN tayi magungunanta taduba taga duk tashasu akan lokaci, nayaune kawai batasha ba dogo Kai FANAN tayi tace kin ci abinci ne amsa mata matar tayi da ah ah banciba Ina mijinki bedawo ba tukun mamakine Yakama fanan tashiga tunanin wannan wani irin mijine matarsa nagadon asibiti bata da lfy sannan ace tunjiya haryanzu bedawo ba balle yasan halin da take ciki allah yakyauta. Kallon matar tayi taga jikinta tayi sanyi cikin tausayawa tace ya sunanki ahankali tafurta sunana balki, murmushi tayi tace anty balki karki damu mijinki yakusa isowa.yanzu Meye yake miki ciwo ah ah nurse yanzu kam jiki alhamdulillah sedan ciwon Kai da rashin karfin jiki ne kawai okay to Allah yakara sauki suna cikin haka mijinta ya karaso wajan Yana wani bata rai yagaida FANAN amsawa tayi tana kallon iKon Allah,cikin Shan kamshi yace ma balki ya jikin tace dasauki daga nan bekara cewa komai ba,FANAN ta lura kamar akwai Dan matsala kallonshi tayi tace inba damuwa inasan magana dakai okay badamuwa fitowa Bakin ward din sukayi . Cike da girmamawa da natsuwa tafara mishi mgn bawan allah ya nunanka sunana Abdul yabata amsa, murmushi tayi cikin tsigan zolaya tace kaikuma malam Abdul haka akeyi , katafi karba masoyiyar taka ita kadai bakowa nata balle naka Yan uwan bataci abinci ba gashi nazo zan bata magani ba abinci Anya ba kishiya kakeson mata ba kuwa takarasa tana Dan dariya shikuwa Abdul wata irin kunya ce takamashi Jin abinda nurse tafada mishi seyaji gaba Daya bekyautaba shuru yayi yarasa bakin magana itakuwa FANAN ganin tayi nasarane jikinshi yayi sanyi tacigaba da mgn malam Abdul kaga bata da lfy kadaure kadinga kula da ita koba komai itadin amanace awajanka aurenta kayi domin kunason juna sannan tace allah yabaku zaman lfy takarasa maganarta tana kallon idonshi, cikin sanyin jiki yace Ameen Ameen nurse nagode sosai da sosai murmushi tayi tawuce ciki tabarshi agun shikuwa daga nan abinci yaje yasiyowa matarshi yakawo mata taci dakanshi yabata maganinta se kallonshi takeyi tana Kara godewa allah dayakawo wannan sauyin dakuma nurse fanan Dan tasan harda taimakonta.




Duk nurses din wajan sunata kula da patient dinsu wani babban mutum ne yashigo wajan yanda ake ta gaisheshi ze tabbatar maka da shine in charge na asibitin. Hango Amira yayi yakirata ta karaso bayan sungaisa ya tmby ta Ina fanan ko yauma batazo ba ah ah tazo bari inkirata Yana tsaye agun Amira suka jero tare da FANAN Yana ganinta yawashe Baki Yana kare mata kallo kamar wani maye ciki ciki FANAN tace mishi Ina kwana amsawa yayi yata washe baki kamar gonar auduga, tafiya yafarayi yajuyo yacewa FANAN kibiyoni office Dina. Tsaki FANAN taja saboda yanzu inda Wanda tatsana bewuce in charge nasu ba sbd yanda yasata agaba da maganar banza. FANAN kije kiji Meye damuwarshi Kuma yau hmmm kawai fanan tace tawuce office nashi.......




To zamuji yanda FANAN zata kare itada in charge nasu




Please kudingayin comment 😍😍😍🙏


via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD


🧑‍⚕️🧑‍⚕️NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story written by ( MRS 🌹 ISHAM 🌹)
Da sunan allah me rahama mejinkai 🙏 Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy Ameen 🙏🌹






Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci 🥰🥰🥰






____________________________________________




Page 4️⃣




Cikin bata fuska ta Murda handle din office din tashigo da sallama abakinta,atsaye tasameshi Yana faman jiranta cikin daddadar muryanta tace doctor gani wani irin malalacin murmushi yayi sannan yafara kare mata kallo daga sama harkasa idonshi kurr akan kirjinta yakafesu da ido lura da hakan datayine rai abaci tace zan iya tfy, karasowa yayi kusa da ita Yana kokarin rungumeta taja baya,ya rungumi iska , uhmm haba mekyau bekamata kinamin haka ba bakisan irin yanda nake mugun shaawarki da kaunarki ba burina kullum nakasance kusa Dake dazaki bani dama dakinga irin gata da kulawan dazanbaki sekinfi ko wace ya mace karasa maganar yayi Yana kashe mata ido Daya cikin salo irin na cikkakun Yan bariki, wani irin takaicine da bakin ciki Yakama fanan jitake tamkar tashaqeshi kozata huta, tsaki taja tare da wurga mishi mugun harara kafin tafara fadin.. kaikam wlh bakaji dadin rayuwa ba nasan idan baka da yar data kaini kakai ka haifeni Amma katsaya kana fadamin maganganun banza to bari kaji infada maka in sha Allah, allah bazetaba baka saa akaina ba. Kuma inawa kowace yarinyar fatan allah yakiyayesu daga sharrinka na neman aikata zina dasu allah yafika , bakaken magana take gaya mishi Amma shi wani irin Kara burgesa takeyi se kallon Dan karamin bakinta yakeyi kamar yaje yayi kissing nata juyawa tayi tafita a office tana Dana sanin fara aiki anan. Shikuwa gogan naku Yana tsaye Ayanda ta tafi tabarshi wani irin wutan shaawarta ne yake Kara wuruwa mishi afili yafara magana Yana fadin FANAN in sha Allah sena aureki domin in kawar da abinda nakeji akanki idankuma kinki kota halin Yaya sena sami abinda nakeso.


Fitowa tayi tana tunani kala kala aranta nayanda yanzu manyan mutane suka zubar da girmansu kowa yazama Dan Iska azuciyarta tace to Allah yashiga tsakanin nagari da mugu nikuma dake bayanta na amsa da ameen 😜. Komawa tayi ward din sukaci gaba da aikinsu lura da mood dinta da Amira tayine tace mata bestie na meyafaru ne naganki wani iri ajiyar zuciya tayi tafara bawa Amira lbrn yanda sukayi da doctor Ib girgiza Kai kawai Amira tayi tace wannan mutumin baze taba canjawa ba allah yakyauta suka amsa da Ameen.



6:00pm Dede suka fito tare suna rike da hannun juna har suka tsallaka titi suka tare adedeta sahu amira ce takemishi kwatancen anguwar tasu me napep Dubai quarters zaka ajiyemu shiga sukayi suna yar hira harsuka iso suka sallameshi sallama sukayi kowa hanyan gida tanufa. Cike da gajiya FANAN tayi sallama dagudu auta tazo tana mata oyoyo, oyoyo autar mama anty sannu da dawowa yauwa auta Ina mama tana falo ok kawai tace tawuce falon anan tasamu mama tagaisheta amsawa tayi zama FANAN tayi akan cusion tana cewa wlh mama yau nagaji sosai murmushi mama tayi tace to sakaliya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login