Showing 39001 words to 42000 words out of 45089 words

Chapter 14 - NIDA PATIENT DINA Book 1 Complete Hausa Novels by Mrs Hisham .txt

14 Jan 2025

3416

sa hannu akai seyayi dana sani" mugun kallo yakebin yaseer dashi kafin yace" are you telling me to calm down!? After they ruin my reputation and you're telling me to calm down impossible " yafada da karfi cikin dabara doctor ammar yazagaya ta baya yaseta injection din yamishi a hannu ganin alluran ba abinda yamishine yakara musu damuwa yau inde azaad beyi bacci ba basusan yazasuyi dashi ba , lumshewa idonshi yafara slowly_slowly rikoshi yaseer yayi yakwantar dashi akan sofa nan take bacci yatafi dashi , duk shuru sukayi sunma rasa abinda zasuce duk sun shiga cikin alhini, daga waya Abba yayi yakira dpo yabashi umarni akan kar asake sako abinda yadanganci haka a gidan kowani TV sannan amishi binciken suwaye suka aikata hakan yakatse kiran, Abba ne yace " yanzu kowani irin hali gidansu fatima suke ciki se Allah! Wannnan aikin yan adawan azaad ne gashi sun batama yarinyar da babu ruwan suna wannan wani irin bala I ne " haka Abba yadinga fada.




Su baba duk sun dawo gida sunga abinda yafaru a gidan TV gaba daya basa cikin nutsuwarsu mama kam kukan zuci takeyi suhaima ce ma ta iyayin kuka itada Amira ganin suna kukane yasa auta kuka itama baba yana zaune yakasa cewa uffan duk sunyi cirko_cirko abun tausayi babu abinda suke tunani kamar ya fanan zataji intaji wannan mummunar labarin duk suna zaune suna jiran dawowarta daga kasuwa cikin sanyin murya ya al ameen yace " kota dawo kar mu nuna mata wani abu saboda karta fahimmci akwai damuwa " dukkansu sunyarda da shawaranshi domin kuwa su sunfi kowa sanin halin fanan bazata taba aikata abinda zezubar musu da mutunci ba yarinyar da tunda tazo duniya inbanda yan uwanta maza babu wani namijin data taba kulawa Allah isanta, tun karfe 4 suna tajiran dawuwarta amma shuru 5 tayi nanma shuru hankalinsu be kara tashi ba se dasukaji anan Kiran sallah mangrib a masallaci ringing wayar baba yayi yaduba yaga sunan alhaji mainasara ne dagawa yayi suka gaisa suna jajanta abinda yafaru tambayar baba Ina fanan Abba yayi yace tun 3 mamarta ta aiketa amma haryanzu shuru bata dawo ba yanzu haka fita zamuyi mudubota, sallati Abba yake ta nanatawa aranshi sannan yacewa baba bari yasa sojoji da polisawa su duba kaff cikin garin gombe anemota ahaka sukayi sallama fita su baba sukayi kowa yashiga motarshi nemanta sukeyi kamar zasuyi hauka amma ko me kama da ita basu gani ba, acikin daren haka suka shiga cikin kasuwar da babu kowa da torchlight dede wajan yan takalma sukagano jakarta da wayanta aciki dauka ya usman yayi yanunawa ya al ameen cigaba sukayi da nemanta amma shuru, haka suma jami'ar tsaron suketa nemanta har karfe 12 nadare babu fanan babu labarinta zuciyarsu cikeda rauni suka koma gida .
Atsakar gida suka tadda su mama se safa da marwa takeyi harda hajiyarsu amira da Amira ganin su baba sundawo batare da fanan bane yasa zuciyoyinsu karyewa jirine yafara diban mama kamar zata fadi ya usman yayi saurin tarota jikinshi yazaunar da ita , tashin hankali iya tashin hankali yaukam sunganshi yau yakasance bakar rana agaresu har karfe 1 nadare basu runtsaba suna filin gida suna zaune cikeda jimami, haka zalika su ummi suma suna at the same condition babban damuwarsu rashin ganin fanan dabaayi ba azaad har a time din alluran bata sakeshi ba , cike da damuwa ummi tace " yakamata muje gidansu yarinyar nan " ajiyar zuciya Abba yayi yace" inasane Aysha yanzu kinga dare yayi sosai mubari gobe da safe ko " ahaka Suma suke zaune afalo . Sa kafarta kawai takeyi aduk inda tabi domin bata cikin hayyacinta shigowa cikin gidan tayi gaba dayanta tafirgice kamar ba fanan ba , jin motsine yasasu dagowa ganin itace yasa suka mike suna Kiran sunanta atare ko kallonsu batayi ba magana suke mata amma gaba daya bata jinsu falo tashiga direct tawuce dakinsu tana shiga tasaka key tako Ina rufe windows din tayi tasauke labule, dan batasan magana da kowa kuma batasan ganin kowa can karshen gefen gado taje tazauna akasa tahade kai da guiwa kamar wata me bacci , hamdala sukeyi dukda sunga irin yanayin data dawo wannan yatabbatar musu da taji abinda yafaru bubbuga kofar dakin sukeyi dantabude musu kofar amma ina abu kamar wasa har karfe biyar 5 idonsu biyu babu Wanda yaruntsa har time din bata bude kofar ba tunda takifa kanta akan guiwanta bata sake dagowa ba. , Mama kam kamar zatayi hauka haka takeji tarasa inda zatasa kanta daga karshe kuka tasaka musu tana rokonsu dasu fasa kofar kar yarta tamutu kiraye_kirayen sallah asubane yasata dagowa idon nan sunyi luhu_luhu sunyi ja fuskanta yakumbura Sosai, mikewa taje tayi alwala tayi sallah, tunda ta idar da sallah bata tashi akan daddumar ba tana zaune gaba daya jitayi tatsani duniyar ma dakuma kanta, dawowa sukayi daga masallaci baba yabasu umarni dasu fasa kofar dakin nata kawai aikuwa haka akayi suka fara kokarin fasawa jin zasu fasa kofar ne yasa takalli jikin key din da bangon dakin takomar da kanta kan guiwanta har karfe 10 na safe fanan bata bude kofar ba gashi kofa yaki fasuwa babu yanda suka iya haka suka zauna shuru ko breakfast basu samu nutsuwar yiba ahaka su Abba da ummi se yaseer da doctor ammar sukazo gidan suka samesu suma babu yanda basuyi ba amma fanan taki bude kofar....








Ina godiya masuyin comment dakumin adduah nagode sosai Ina nan inata ganin wayanda sukemin comment, innaga comment dinki nada yawa zansaki a dayan group din.






Se munhadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy πŸ‘πŸ™




via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD


https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe


πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺




Story & Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)






Da sunan Allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen πŸ₯°πŸ€Ž








Alhamdulillah munzo karshen book 1 πŸ“š se mun hadu a book 2 inda rai da lafiya zamu tafi hutu kamar 1week ko 2weeks,in andawone zaa daura da book 2 inme duka yakaimu da Rai da lfy.






A gaskiya Ina matukar alfahari daku sosai da sosai da yanda kuke bani ruwan comment Lodi lodi dakuma adduah nasara arayuwa Ina me matukar godiya sosai.


Musamman...!






Maman shurem
Sherteen gayu
Eysher raj
Maman junior
Maman yazeed
Umamah Abbas
Snacks craving
Pinky darling
Hauwa'u illiyasu
Oumu Maryam
jiddah
Nana farida
Maarufa Ahmad
Mum basma
Maman widad
Mami
Maman junior
Anty rukkaya
Fatima Hassan umar
Diamond sarah
Maman faruq
Yar mamanta
Ummu amal
Ummu suhaima
Mhizz deejerh
Zainab magarya
Anam
Anty ummi mulki
Maryam said
Khareema
Man munawwara
Etc Dade sauran ku


Yesterday you guys gave me unforgettable hot comments I really appreciate allah yabar kauna inasonku sosaiπŸ₯°πŸ₯°πŸŒΉπŸŽ‰




Wannan last page din sadaukarwa ne garekuπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°.










Free book πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š






꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁


&_______________________________________&


Last page


Page 3️⃣0️⃣






Gaba daya garin gombe da ketare ta amsa da wannan labaran kowa se tofa albarkacin bakinsa yakeyi wasu sun yarda wasu basu yarda ba. TikTok, YouTube, Facebook, Twitter, Instagram, Vidmate, duk wani kafafen sada zumunta ta amsa social media kowa se Allah wadai da halin azaad da fanan yakeyi ko ina kashiga labarin dazakaji yana tashi kenan.


Su abba suna gidansu fanan har karfe 2 na rana dukkansu abin duniya yadamesu har wata har rama sukayi har izuwa wannan lokacin fanan na kunshe adaki bakaramin tausayi tabasu ba ba ruwa ba abinci gaba daya tafita a hayyacinta tawani rame kamar wacce tayi jinyar wata daya fuskan nan yayi fayau kamar ba jini ajikinta tana zaune akan dadduma gashin nan buzu_buzu takafe waje daya da ido.


Yan uwan ummi a dubai sekira sukeyi suna kwantar musu da hankali haka masarautar gombe kakansu azaad yakira abba awaya yake tambayarsa ina azaad yace "yana gida sukuma suna gidansu yarinyar" kafin yakatse kiran.






Jingine yake ajikin makeken gadon dakinshi da alamun sallah ya idar yau yasamu yatashi daga baccin yabiya duka sallolin da akebinshi gaba daya yatashi daga azaad din dana sani yakoma wani daban duk wanda yakalli fuskarshi seya mugun razana da firgita dan yau ne ainihin true color dinshi yabayyana komawa yayi kamar boss, waya yadaga yasa akunne kafin yace " spider inason kafin nan da 1hr kasamonin wayanda sukayi wannan hotunan " yana gama magana kitt yakashe wayarsa mikewa yayi yabude wani locker dake dakin yafito da bindiga piston yasa abayan trouser dinshi fitowa yayi falon kasa fawwaz da areef se zeenat ne afalon suna zaune suna jimami sukaga fitowarshi ganinshi awannan suffar yasa babu wanda yayi kwakwaran motsi haryakai bakin kofar falo zefita wayarshi kirar iPhone 16 tafara ringing dakatawa yayi yaciro wayar yasa akunne spider ne yakirashi yaname sanar dashi ankama daya daga cikin mutanen dasuke dasa hannu, budan bakin Mr azaad yace" beat the hell out of him before na iso " kittt yakashe yafita securities dinsa ne dukansu sukazo suna gaidashi ko kallonsu beyiba faisal ne jiki na rawa yayi saurin karban car keys din awajan driver yabude mishi murfin motar shiga azaad yayi yazauna tada motar faisal yayi gudu_gudu baba me gadi yabude musu gate suka fita duk yan aikin gidan susan abinda yake faruwa bakaramin tausayin me gidan nasu sukeyiba domin su ko aina zasu iyabada shaida akan Mr azaad baze taba aikata haka ba.


Driving faisal yakeyi amma besan inazasuje ba gashi yana tsoron tambayar ogan nashi, ganin shuru baze kaisu ko inaba yasa murya nadan rawa yace " sir inazamuje" ciki_ciki azaad yace " my jungle" okay faisal yace dan yasan wajan nan ne azaad yakeda bosawan yaranshi sannan anan ne duk wanda yamishi laifi yakesa adauko shi yamishi mugun hukunci daga bisani yamikashi hannun yan sanda. dajine daya amsa sunanshi daji bazaka taba tunanin akwai bil adama aciki ba wani tankamemen gidane nahango daga nesa ga wasu Yan daba se buge buge sukeyi kamar wani abu suke hadawa ga wasu agefe se gasa rago sukeyi dukkansu duk wanda kika kalla kinsan ainihin cikekken dan dabane agun kirar jikinsu ma kadai zebaka labari , tunkafin motar takaraso sukayi cincirindo suna jira isowar boss dinsu motar na tsayawa wani daga cikinsu yabude mishi kofa wani yazo da lema yana rike mishi dashi dan kar rana yatabashi wani ne yazo kamar wani basamude yazo yatsaya agaban azaad kansa akasa yace " boss can I help you with the shirt" gyada mishi kai yayi nan take yasa hannu yaballe mishi botiran riganshi yakoma gefe yatsaya cire rigan azaad yayi gaba daya nan take wannan kirar nasa yabayyana ga tattoo dake jikinshi tafiya yakeyi cike da izza yashiga ciki, sekwasan gaisuwa sukeyi wani bangare yanufa daga nesa babu abinda nakeji daya wuce ihu da kururuwa shiga wajan yayi wani matashine wanda akalla zekai shekara 27 zaune akan kujeran karfe anmishi daurin goro sunmishi mugun duka jikinshi se fitar da jini yakeyi ihu yakeyi kamar wanda ake zarewa rai juyawa azaad yayi yakalli spider nan take yakawo mishi kujera asetin matashin zama azaad yayi yasa hannu yadago fuskanshi agalabaice yake kallonshi dakyar ya iya furta "dan Allah ranka yadade kamin rai kayi hakuri" wani miskilin murmushi azaad yayi kafin yace" waya saka wannan aikin" shuru yayi bece komai ba alamar baze fada ba , dungule hannun azaad yayi nan take jijiyoyin hannunsa suka fito yakai mishi naushi afuska seda hakwaranshi guda shida suka zube hanci da baki suka fashe se jini suke zubarwa juyawa yayi ga spider yace " ban wuka" dasauri spider yaciro wuka a kugunshi yabashi yana karba beyi wata_ wata ba ya caka mishi acinya razanenne ihu yasa seda gidan ya amsa,daga wukan yayi zesake caka masa yayi saurin fadin" kamin rai wayyo zan fada ! Zan fada maka wayanda suka sani " shafa kanshi azaad yayi yace " good boy maza fada inajinka" yana hakin wahala yace " Alh Ibrahim tijjani ne yasani ! Nafada maka dan Allah kabarni intafi " tunda ya ambaci sunan alh Ibrahim tijjani azaad yaketa girgiza kai dan yasan babu wanda zasu mishi haka sesu amma yafison ya tabbatar tukun nan, lallai alh Ibrahim yatabo ruwan dafa kansa amma yanzu yasan kafin gaskiya tafito seyadau lokaci yana cikin wannan tunanin wayarshi tayi ringing dubawa yayi yaga abba ne ke kiransa kamar baze daga ba can kuma yadaga yasa akunne yace " hello" ajiyar zuciya abba yayi jin yadawo normal dan dama faisal ne yace mishi yafarka, cikeda bada umarni abba yace mishi " duk abinda kakeyi kabari kazo gidansu fatima" tofa tunani yafarayi wacece kuma fatima kamar baze tambayi abba ba can Kuma murya ashake kamar wanda akawa dole yace " wacece kuma fatima" rike baki abba yayi kamar wanda yake gabanshi daga karshe yanisa yace " to nurse dinka yanzu base anjuma ba kazo gidansu" seyanzu yatuna da ita tare aka musu qazafi tausayinta yaji ganin ita macece sun bata mata suna gwarashi namijine amma itafa sun cuci rayuwarta tabbas bazetaba barinsu susha iska medadi ba sesunyi danasani aikata hakan mikewa yayi su spider suka bishi abaya.


Almost an hour ne yakawosu gidan shigowa yayi compound din gidan qin shiga yayi dukda yanajin muryoyinsu ganin tsayuwar yayi yawa yasa faisal yin sallama fitowa ya Usman yayi yagansu mikawa azaad hannu yayi sukayi musabaha da yamikawa faisal Bismillah yamusu akan sushigo , shiga sukayi zama yayi akujera mezaman mutum daya kasa_kasa yabude baki yagaidasu amsawa duk sukayi suna jajanta abinda yafaru shide kala bece musu ba amma sunbashi tausayi sabodashi ne rayuwar yarsu yake kokarin tarwatsewa . Idonshi akasa yafara bin mutanen dakin daya bayan daya yana kallonsu ganin beganta afalon bane yayi tunanin ko tana daki.
____kallonsa Abba yayi yace " azaad fatima tunjiya data samu labarin abinda yafaru takulle kanta adaki haryanzu bata bude ba tunda tashiga baakarajin motsinta ba dan Allah kozakayi naka kokarin kozata bude kofar!?"Abba yagama mgn yana nuna mishi kofar dakin, Duk tsareshi da ido sukayi suna sonjin mezece, harkusan 10mint bece komai ba harsun cire rai akan zebasu amsa,mikewa yayi yaje bakin kofar yatsaya yamarasa mezece cikin sexy voice yace " Fatima kibude zamuyi magana" shuru sukaji can kamar 2mint yasake cewa " Fatima kibude zamuyi magana " kamar amafarki takejin muryansa yana mata gizo_gizo akunne kara kasa kunne tayi kozata sakeji can tasakejin yayi magana dasauri ta dago kanta tana kallon jikin kofar dakyar ta iya mikewa kamar zata fadi tangal_tangal tayi kamar zata fadi tasamu tatsaya dukda dishi_dishi take kallon komai nadakin tsaban yanda tagalabaita tun dogon rigan jiyane ajikinta haryanzu gaba daya baa ganin fuskanta saboda yanda gashin nata yabazu sannu ahankali take taka kafarta hartakai bakin kofan without touching the door shi dakanshi yabude kansa , jin Karar kofa ne yasashi dagowa su baba duk tasowa sukayi suka tsaya agefen azaad suna kallonta takawa yayi kusa da ita yasa hannu yatattare gashinta yamaidasu baya, seda yaji dam akirjinshi bashi kadaiba hartasu Abba gaba dayansu sun firgita daganin yanayin fanan gaba daya lokaci daya tazafge kamar wacce tayi jinya fuskan nan yakumbura idonta yakara girma gaba daya tafita a hayyacinta, mama kwalla fal a idonta tace " innalillahi wainna ilaijiraji unnn ji yanda sukasa yata tashiga wani hali wallahi Allah seya saka mata " matsowa tayi daff da azaad dayake tsaye agabanta kallon jikin idon juna sukeyi babu ko kyaftawa hannunta tasa tacakumi kwalar rigarshi cikin muryan daya galabaita tace " Mr azaad inason kafadamin mena musu meye natsare musu meye hadina dasu dazasumin haka" cikin kara zare ido tacigaba da fadin" kasan mesu kace akaina cewa sukayi wai ni karuwa ce mazinaciya nasha zubar da ciki, wai ni dadironka ce kana kwaciya dani meye na aikata aduniya dana cancanci wannan qazafin meye na aikata musu da zafi haka" takarasa maganar da karfi tana jijjigashi, bakaramin dauriya sukayi ba mazan kamar su zubar da kwalla sukeji ummi kam gaba daya tausayin fanan yakamata tarasa ma yazatayi mama se share hawaye takeyi , ba abinda kakeji afalon se sheshekan kukansu Amira, suhaima da auta.
__ sa hannunshi yayi duka biyu yatallafo kumatunta cikin husky voice yace " kifadi duk wani abinda ke ranki domin bakiyi magana da kowa ba kiyi kuka son ranki zakifi jin raguwar radadin dake kunshe azuciyarki " kallonshi takeyi ido cikin ido kamar me neman wani abu gyada mata kai yayi kafin yakara maimaita" kina bukatar kuka ! Kiyi kuka " nan take hawaye yafara gangarowa daga idonta kamar wanda aka kunna famfo rike hannunshi tayi kam kafin tasaki wani irin marayan kukan dake cinta tun jiya amma takasayi durkusawa kasa tayi tana kuka bana wasa ba,babu wanda yayi kokarin hanata dan dama abinda take bukata kenan tayi wannan kukan komai zataji yazo mata dasauki kukanta tasha ma ishe kafin ummi tazo tadagata tarungumeta suka zauna akan kujera sambatu tafarayi acikin kukan wanda baama jin metake fada tsaban yanda kukan yayi yawa, kusan 1hr tana kukan kafin tasamu relief tayi shuru tana bin kowa da ido abincin da suhaima tadafane takawo mata da ruwa Abba ne dakanshi yace " Fatima kice abinci kinji" gyada mishi kai kawai tayi kafin tasa hannu tadauki spoon din tafaraci jallof din macaroni ne da kifin ruwa kadan kadan takeci dukda bakinta ba apatite haka taci abincin tura abincin gefe tayi ta kwantar da kanta akafadar ummi , dukansu tattaunawa sukeyi tayanda zaasamo mafitan wanke sunan azaad da fanan doctor ammar ne yace" inada shawara " duka kallonshi sukayi suna jiran suji mezece " meze hana azaad din da fanan sufito suwa yan jaridar bayani kancewa sharri aka musu " girgiza kai yaseer yayi yace " wannan bazeyi aiki ba waye kake ganin ze yarda da wannan maganar dakayi ko sunfito social media sunfada bazasu taba yarda ba" jinjina kai sukayi tabbas abinda yaseer yafada gaskiya ne babu wanda ze yarda baba ne yabude baki zeyi magana kira yashigo wayar Abba me martaba sarkin gombe ne yake kiransa dagawa Abba yayi kafin yace " umarni zanbaka dakai da azaad din kuma abinda zanfada shine babban mafita daze wanke musu suna yanzu kaida suwaye a inda kake !?" Kallon yan falon Abba yayi kafin yace" nida iyayen Fatima ne da yan uwanta sekuma mu " me martaba ne yace " kacewa matan subamu waje zamuyi magana " batare daya katse Kiran ba abba yace " dan Allah inba damuwa kudan bamu mintuna kadan zamuyi magana, tashi sukayi ummi narikeda fanan dake binsu da ido mama ta mata Bismillah suka shiga dakinta sukuma su amira suka shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login