Showing 21001 words to 24000 words out of 45089 words

Chapter 8 - NIDA PATIENT DINA Book 1 Complete Hausa Novels by Mrs Hisham .txt

14 Jan 2025

3418

kiketa kwala kira da safiyan nan!?" Share hawayen Daya zubo mata tayi kafin tace " baba nafi minti 30 Ina tashin fanan abacci haryanzu bata tashi ba" aibasu ma bari tagama fadan sauran maganar ba dukansu suka duhru cikin dakin sun , yanda suhaima tafita tabarta haka suka sameta bakaramin firgita sukayi ba. babane tunda suka shigo dakin yagane abinda yake faruwa cikin kwantar da murya yace " Dan Allah kudena daga hankalinku Ninasan Meye matsalar" da mamaki kwance akan fuskarsu suke binsa da kallo , karewa dakin kallo yayi kafin cikin sanyin murya yace " angaisheki jakadiyar da babu irinta,yar Amana merike Amana , wacce tasan asalin halacci , uwa agun shufai da shufana, jakadiyar da babu kamanta akaff fadin masarautar NASMINAYA , fara me farar aniya , Ubangijin Allah yabiya miki bukatunki na duniya da lahira " cike da mamaki su suhaima da su ya Usman suke kallon baba suna tambayar kansu waye yakewa irin wannan kirarin Banda mama datasan wacece agun . Bakaramin farin ciki dakuma jindadi jakadiya abashiyya tayi ba jin irin kirarin da baba yamata sannan ta fara kokarin bayyana ta............










To muhadu a comment section 😜😜😜😜 semun hade tomorrow in da Rai da lfy Ina godiya sosai Yan comment section Ina alfahari daku sosai da irin comment din ku inasanku sosai🌹🌹πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°.


via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD


πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺






Story Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)














Da sunan Allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen.πŸ™πŸŒΉπŸ€Ž














Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci πŸ₯°πŸ€ŽπŸ₯°
























____________________________________________








Page 2️⃣0️⃣












Duk zuba ido sukayi suna karewa dakin kallo kamar daga sama suka farajin busan sarewa hade da kakaki me shegen dadi,wani farin hayaki ne yake ta bulbulowa adakin Yana fitar da kamshi me dadin shaka , ga sanyi me ratsa jiki da zuciya Yana ratsa su , hayakin yanakan cigaba da fitowa tako wace bangare, lungu da sakoh seda yazamana basa kallon komai tsaban yanda hayaki ya maimaye cikin dakin sunfi minti 10 kafin nan yatsaqaita , jakadiya abashiyya nahango tsaye cikin shiga na alfarma dakuma nuna itadin tafito daga masarauta ne , dogon riga take sanye dashi me matukar girma farine tass badigon wani kala ajikinshi se gold,duk jikin rigan anmishi kwalliya da duwatson zinari,
Saman rigan Dede cikinta andaureshi da belt fari da gold stone ajiki hannun rigan nada girma gabadaya rigan an mata kwalliya ne da gold , hannunta Da wuyanta da kunnen ta sunsha kayan ado duk zinarine , fara ce Sosai fari bana wasa ba, Babbar mata ce kyakyawa idonta manyane sosai sannan ba irin namu bane cikin kwayar idon fari ne sal eyeballs dinta yakasance Shiba fari ba shi ba ruwan toka ba se shekin dayakeyi , gashin kanta kuwa tsaban tsawonshi yawuce guiwanta yakusa karasa kafanta Dake sanye da tumsa me matukar kyau kallo Daya zaka mata kagane ita din badaga jinsin bil adama take ba. Suman tsaye su ya al ameen sukayi sunkasa motsa Koda hannunsu ganin aljana agabansu , murmushi me qayatarwane dauke afuskan abashiyya sunkuyar dakai baba da mama sukayi alamar girmamawa sude su suhaima idonsu qyam akanta matsowa tayi daff da inda suke " barka da wannan lokaci yakai Muhammad, uba agun sarauniya wacce takansan shugaba agunmu ,jaruma Kuma sarauniyar nasminaya " tagama fadin hakan tana kallon mama da ita kwata_kwata bataji dadin hada hanya dasu ba tayi bakin cikin hakan matuka aduk sanda suka ambaci fanan amatsayin sarauniyarsu bakaramin Kuna zuciyarta takeyi ba Amma yazatayi kaddara tariga fata haka Allah ya rubuta Kuma shikadai yasan dalilin hakan domin kuwa kowani Dan Adam tun kafin yazo duniya kaddararsa arubuce take da abinda zesameshi , farin ciki ko akasin hakan , wannan ne kadai inta tuna hankalinta yake dan kwanciya tasan komin qaqa yarta bazata taba barinta ba tunda ita ta tsuguna tahaifeta tasha wahalarta . Duk abinda take tunani abashiyya nasane da hakan tausayin mama ne yaka mata domin babu uwar dazataso rabuwa da yarta Koda kuwa babu shakuwa atare dasu Amma babu yanda zasuyi fanan tariga da tazama wani bari na rayuwansu tundaga ranan da takai wata biyar 5 acikin mahaifiyarta. Murmushi tayiwa mama , mayar mata da murmushin mama tayi duk da nata yakasance na yake baba ne yajuya yakalli su ya Usman dasuka daskare guri Daya yace " kukam Baku iya gaisuwa bane !?" Firgit sukayi suna kallon baba da alaman tambaya afuskansu ya al ameen ne yayi karfin halin fadin " wa!waye din zamu gaisar!?" Tsuke fuska baba yayi bakuga munyi bakuwa bane " kallon su suka maiyar kan abashiyya da itama sudin take kallo tana murmushi cikin inda_inda kamar wayanda suka hada Baki wajen fadin " Ina kwanaaaaaaa" fuskanta asake ta amsa musu da "lafiya Lau yarana " sude Basu Kara cewa uffan ba ganin lamarin sukeyi kamar almara wai yau aljanace agidansu sannan baba harcewa yakeyi su gaisheta tabbas akwai abinda ake boye musu. Tafiya takeyi ahankali harta karaso bakin gadon fanan Dan ta tasheta daga baccin datakeyi saboda ta gabatar da sallah, tana kokarin tabatane khairatyyy tabayyana a dakin innalillahi suhaima kam guduwa take kokarinyi ya al Ameen yariketa gam yaki sakinta duk da suma sundan tsorata Amma suka danne yarinyace kyakyawa itama tana sanye da irin kayan da jakadiya abashiyya take sanye Amma nata bekai na abashiyya ado ba itakam khairatyyy gashinta har ja yakeyi da kasa, cikin girmamawa tace " shugaba nayi yanda kika umarceni da inyi sannan yafadamin babu abinda sarauniya tamasa kawai son zuciyane yasashi sha mata jini shine aka yanke mishi hukunci" "Masha Allah khairatyyy Allah yamiki albarka " cikin jindadin anya beta tace "Ameen yake shugaba" maimaita sunan kawai ya Usman yakeyi khairatyyy....? Wow suna me dadi tunda tabayyana yaji ta tafi da imanin shi dukda yadan tsorata , kallonta kawai yakeyi komai nata burgesa yakeyi nan take zuciyarsa takamu da santa ( tofa ana wata ga wata kaikuma Usman meya maka zafi haka daga ganin yar kyakyawar yarinyar aljanu harka folaπŸ€£πŸ˜‚πŸ€£ to nide baruwana nayi nan πŸƒπŸƒ)
Shafa fuskan fanan abashiyya tayi nan take tamike da salati abakinta ita bataga kowa ba se su mama da su baba dasauran Yan gidan kallonsu takeyi da mamaki ganin su kaff adakinsu abinda be taba faruwa ba tunda tasan tayi wayo baba Sau biyu yataba shigowa dakinta nan ma lokacin bata da lafiyane suka shigo shida ya Usman dubata mamace de take shigowa se auta , zura kafafunta kasa tayi tamike tsaye zubewa akasa abashiyya da khairatyyy dakuma sauran dogarawan fanan dabaa ganinsu sukayi akan guiwowinsu kansu akasa . Rike hannun mama fanan tayi tana fadin " mama meyake faruwa na ganku anan wani abun yafaru ne!?" Ya al ameen ne yayi saurin cewa " wai fa suhaima ce tana tashi daga bacci taga kadangare adakin ku shine tafasa ihu mu mundaukama wani Abu ne yafaru Ashe wai kadangare takewa wannan ihun Kai suhaima Allah yashiryeki " kallon cikin idonta yayi ganin ko karyan dayamata yakarbu se gani yayi tajuya tana kallon suhaima tana dariya kasa kasa " wallahi suhaima Allah yashiryeki yanzu kadangare kikewa ihu haka " itade suhaima Jin irin karyan da yayanta ya zambada ne yasata taketa murmushin yake dan haryanzu taki sakin jikinta, " fanan jekiyi sallah kizo kishirya kitafi aikinki Kinga zakiyi letting kinji !? Cewar mama dake ficewa adakin, toilet tashiga zatayi alwala fita suka farayi one by one Amma Banda ya Usman da haryanzu yanata kallon babynshi , ya al ameen magana yake mishi Jin shuru ne yasashi kallon direction din da yake kallo yayi sauka idonshi yayi akan khairatyyy da haryanzu suke zube akan guiwowinsu basu ko dago ba, kama baki Al ameen yayi Yana ganin iKon Allah meyake shirin faruwa meye dalilin da zesa Usman yakafe khairatyyy da ido haka Allah yasa ba abinda yake tunani bane Tabb inde hakane usman yadauko wa kansa dala ba gammo . Jan hannunsa yayi sukabar dakin, suhaima zama tayi abakin gado kasa_kasa take kallonsu dede lokacin da khairatyyy tadago idonta sukayi 4 eyesπŸ‘€ dasauri suhaima takawar da kanta gefe dariya abin yabawa khairat Dan tagane suhaima tsoronta takeji kasancewar ita idonta yafi na jakadiya girma, fitowa fanan tayi daga toilet din tayi wanka tare da alwala hijab tasaka ta tada sallah bayan ta idar ne tana zaune tana azkar ta tuna abinda yafaru adaren jiya Amma setake ganinshi amafarki share lamarin tayi tashi tayi tana cewa " suhaima iyayen tsoro Dan mikomin kaya acikin wardrobe Dina mana " cike da masifa suhaima tace " Nina san kalan kayan dazaki sakane " kumshe dariyan dayazo mata fanan tayi Dan tasan suhaima tashaqa bata Kara bin takan taba taje tabude wardrobe din tadauki abaya Baki me kwalliyar blue πŸ’™...












Zaune take adakinta ta buleshi da hayaki tana Shan shisha kayan jikinta dasu da babu duk dayane hannunta na rike da tiyo din shisan tana zuqa gaba daya abuge take idonta harwani rufewa yakeyi ringing din wayartane yasa tawaro idonta dasukayi jaa picking tayi tasa akunne tana " hello mommy " adaya abangaren aka amsa da " aneesa meyasa duk abinda zangaya miki bakya jine ban hanaki shaye_shayen nan bane ahakan ne kike cewa kinason Azaad inya San kina shaye_shaye zeyarda ya aure kine ansamu Abubuwa sunfara tafiya smoothly and now you're trying to ruin everything right!? rai abaci mommy take magana, wastsakewa aneesa tayi ta kashe choal din katse Kiran mommyn tayi cikin hanzari tamike tanufi toilet dinta tana tafiya tana tangal_tangal kamar zata fadi shower 🚿 tasakarwa kanta tafi 20mint kafin taji tafara dawowa Dede dakin tadawo tana sanye da towel dialing din number mommy tayi bayan tadagane take cewa " am sorry mommy nayi kwana biyu bansha komai bane yau kuma natashi Ina matukar missing dinsu shisa nasha but it won't happen again" ajiyar zuciya mommy tasauke tace " better yanzu abinda nakeso dake duk wani abinda kikeyi kibari kihado kayanki kidawo gidan nan dazama idan Kuma bahaka ba karki yarda kiyi kuka da kowa" cikin rashin fahimta aneesa tace " mommy meyasa zandawo gidan dazama isn't necessary? impact why would I come over to your house and stay gaskiya bazeyuba azaad ze takuramin baze taba barina inyi abinda nakeso ba" cikin tsawa mommy tace " am doing this for your own good aneesa tunda ke bakisan ciwon kanki ba to ki tsaya kallon ruwa kwado yamiki kafa yar alhaji badamasi me ruwa yarsa nusaiba datake mutuwar son azaad yanzu haka flight dinsu yatashi tana hanyar zuwa gombe yanzu shawara yaragewa meshiga rijiya " katse wayarta tayi ranta a matukar bace taurin kan aneesa Yana bata mata Rai.


Abangaren aneesa kuwa bakaramin tashin hankali tashiga ba Jin datayi wai nusaiba nahanya batayi wata_wata ba ta mike trolley dinta tadauko duk abinda tasan zatayi amfani dashi tasaka aciki , wando jeans fari tasa da Tshirt orange color tasa Sannan tadauki wata karamar gyale fari tadan Yana akanta number masu aikin gidan takira shigowa dakin wani security yayi nuna mishi trolley dinta tayi yafitar dashi waje yasa mata a boot sannan tafito afalo tasamu hajiya Zainab ( mahaifiyarta) ko kallonta batayi ba tawuce abunta girgiza Kai hajiya tayi tace "Ubangiji Allah yashiryamin ke yasa kigane hanya"


Horn sukayi wangale musu gate din akayi driver yashigo yaje yayi packing fitowa nusaiba tayi tana bin gidan da kallo setaga komai yacanza ko dan tadan dade batazo bane shiga ciki tayi driver nabinta abaya da akwatin kayanta,suna shiga falo tahango ummi dagudu tafada jikinta tarungumeta " wayyo ummina nayi missing dinki wallahi " shafa kanta ummi tayi "nima haka nusyy ya mutanen gidan " kowa klau ummi kallon zeenat tayi wacce tayi kicin_kicin da rai kamar batasan da zuwanta ba tabe baki nusaiba tayi ummi ce tace " tom tashi kije kiyi wanka kizo kici abinci Koh!?" Tom ummi haurawa upstairs tayi tashiga dakin datake sauka Dan kwata_kwata basa shiri da zeenat jininsu bezo dayaba balle suzauna daki Daya.


Fitowa fanan tayi cikin shirinta tsaf na tafiya afalo tasamesu suna kokarin fara karyawa "baba nizan wuce"


Jiya danayi posting kukata magana short page ne bashida yawa Gsky page din yayi guntu , to abinda yasa banasamun comment yanda nakeso ne kamar jiya mutane kalilan ne sukayi comment , nibazance bazanyi posting ba Amma kam zakuta ganin guntun page inde bazaku dingayi comment ba . Ballema in bakuyi comment ba wlh ba lallai inyi posting gobe ba🀷










SE mun hadu gobe ko jibi inda Rai da lfy


















via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe


https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe


πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺






Story Written by ( MRS 🌹 ISHAM 🌹)












Da sunan allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen πŸ™πŸ₯°πŸ₯°














Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci πŸ₯°πŸ€ŽπŸ₯°














Free book πŸ“šπŸ“šπŸ“š












____________________________________________














Page 2️⃣1️⃣












Mika mata kudin transport dinta baba yayi tare da adduah adawo lfy "Ameen baba" , tana tsaye abakin titi tafi tsawon minti 15 babu abun hawa kasancewar yau jummaa baa fiya samun ababen Hawa ba harta fara tunanin komawa gida tama ya Usman ko ya al ameen magana wani yakaita Sega napep hamdala tayi kafin ta tsayar dashi tashiga tafada mishi inda ze kaita, sallamarshi tayi, ta kwankwasa gate din baba me gadi yabude ganin itace yabata hanya " ah ah fanan kece sannu dazuwa" cewar baba Yana Maida gate din yarufe murmushi fanan tayi cikin faraa tace " Ina kwana baba antashi lfy " "lfy Lau alhmdllh ya gidan naku!?" " Kowa lfy " wucewa cikin gidan tayi tana tafiya cikin nutsuwa kamar wacce take tausayin kasan Dede tasa Kai zata shiga falon sukayi karo da juna, bige kanta tayi da faffadar kirjinshi baya tayi zata fadi yayi saurin riko kugunta yadawo da ita jikinshi dago Kanta tayi tasaukeshi akan fuskarshi da ke nan kamar kullum ba annuri Dan ja dabaya tayi cikin calm voice tace " Ina kwana Mr azaad!?" Jin shuru be amsa mata ba yasa tafara satan kallonshi kasa kasa sanye yake da wando transuit se singlet wanda yabawa murdadden jikinshi daman fitowa waje komai kana kallo barinma 6packs din cikinshi da dantsen hannunshi kafarshi sanye da sau ciki alamu yanuna daga gym yake shagala tayi da kallonshi tsarin jikinsa ba karamin burgeta yayi ba setaji kamar takai hannu ta taba, shikuma ganin ta kafeshi da idone yasa yagane inda hankalinta yake murmushin gefen baki yayi yamatso daff da ita bata ankara ba taganshi akusa da ita sosai baya takara jaa hararanshi tayi kafin tace " wannan wani irin iskancine " kara matsota yayi cikin sexy voice yace " ni kike cewa Dan iska ko!? "Ah ah nibance maka dan iska ba kawai banasan abinda kakeyine" lumshe idonshi yayi yamatso da fuskanshi dede kunnenta yafara mata magana me kama da rada" da bakyaso din meyasa kike kallemin jiki!? Naga alama ma sokike kitaba ko!? Zare ido tayi cikin inda_inda tafara fadin " ni yaushe nakalleka me!mema zangani ajikinka din " tagama magana tana murguda mishi Bakinta dayasha libs gloss se sheki yakeyi , cije libs dinshi yayi da dan karfi yatsareta da ido azuciyarshi Yana aiyana yanda zemata hukunci tunda batada kunya dole in koyawa yarinyar nan hankali tunda tacemin Dan Iska zataga iskanci " bata hanya yayi tawuce tana Harare_harare ita kadai murmushi yayi inya tuna irin hukunci daze mata nan gaba bazata kara cewa wani dan Iska ba balle shi. Shige falo tayi ganin basa falon kasa yasa tahaura sama aikuwa anan tasamesu Amma Banda ummi da anty Amina data koma gidanta, zeenat ce tafara ganinta tsalle tayi tafada jikinta suka rungume juna " wayyo kawata gaskiya nayi missing dinki sosai yau nake cewa zanje gidanku" hararanta fanan tayi " uhmmm sekace dagaske aida kinyi niyya Dana ganki kafin inzo ninayi fushi malama ban hanya in wuce " areef da fawwaz se dariya suke musu jin draman su areef ne yace " tabb gaskiya fanan karki yarda datayi niyya aida tazo " " to sannu dan hana ruwa gudu wato zaka hada bom ko!?" Cewar fawwaz dariya sukayi Jin dogon tsakin da nusaiba tajane yasasu juyawa suna kallonta, fanan ganin bakuwar fuskane yasa tace "mata sannunki" ba yabo ba fallasa ta amsa da "yawwa" jan hannun fanan zeenat tayi zuwa falon ummi samunta sukayi tana rike da Qur'anic tana Karatu zama sukayi suna sauraron kira'anta medadin sauraro sunfi tsawon 20mint kafin ta dasa ayah, kallonsu tayi murmushi dauke afuskanta tafara magana" fanan dama kina tafe kenan" cike da kunya tace"iyi ummi! Ina kwana " lfy Lau ya mutanen gidan" kowa na lfy " Masha Allah kin dubashi din ne!? Gyara zama fanan tayi kafin tace " ah ah nazo zanshigo muka hadu dashi kamar akwai inda zashi" okay, hiransu sukaci gaba dayi.




Mommy da aneesa nahango zaune akan kujera mommy nata kimtsawa aneesa makirci da yanda zatayi danta dinga jan hankalin azaad yadawo kanta " yanzu abinda nakeso dake kitashi kitafi part dinsu kije wajenshi kiyi duk abinda nafada miki saura kiyi falling dina " Mikewa aneesa tayi tadauki wayarta tabar part din, tadoshi part dinsu ummi tsayawa tayi daga bakin kofan falo tana kallon nusaiba da ita kadai tarage a falon tana chatting shigowa tayi taje ta zauna a kujera dake facing din nusaiban , tun tsayuwarta abakin kofa nusaiba taganta ko dago Kai batayi ba tacigaba da chat dinta , ganin datayi nusaiba taki kulata ne yasa tace" ke uban me kikazoyi a gidan nan " kallon renin hankali nusaiba tawatsa mata kafin tace " kedin uban meye yakawoki gidan nan din? " gyara zama aneesa tayi tafara magana"aini inada right din da zanzo gidan nan aduk lokacin danake so Kuma intafi aduk sanda nakeso tunda very soon am going to be their daughter in_law Kinga gidan nan yanzu nafara zuwa " wani irin kululun bakin ciki ne yatokare wuyan nusaiba " hmmmm kikace Zaki zama surkansu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login