Showing 27001 words to 30000 words out of 45089 words

Chapter 10 - NIDA PATIENT DINA Book 1 Complete Hausa Novels by Mrs Hisham .txt

14 Jan 2025

3410

hutu sunzauna ajikinshi Abba kenan ALHAJI MUHAMMAD B MAINASARA bakaramin kama sukeyi da azaad ba ta bangaren zubin halitta , azaad nahango abayanshi suna fitowa tare yanayin jikin su da tsayinsu kusan daya sede azaad yafishi murdewan jiki dakuma tsayi kasancewar shi saurayine...















Nafada mukuma zansake fada yawan comment dinku yawan read more dinku kusha karatu lafiya,se mun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy πŸ‘


via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD


https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe


πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺




Story Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)












Da sunan Allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen πŸ₯°














Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci πŸ₯°πŸ₯°πŸ€Ž














Free book πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


















____________________________________________












Page. 2️⃣3️⃣
















Yana sanye da suit white color se bakin takalminshi ga agogon diamond adaure ahannun shi yasha bakin son glass fuskan nan ahade kamar hadari bakaramin masifar kyau yayi ba azaad kyakyawane nakarshe bugu da kari half-cast ne duk Wanda yakalleshi baya mishi kallon hausa fulani kallon balarabe akemai saboda yadauko umminsa ne kirar jikine yadauko na Abba sekuma farinsu daya hada shisa yakasance fari sosai dan duk yafi mutanen gidan fari tsabar hutu fatar jikinsa Kamar kataba jini yafito, babban abinda yakesa mata suke rushing akansa kenan gashi dogo me murdadden jiki ga manyan idanu farare tass hancinsa kuwa kamar shiya zana abinsa dogon hanci bakin nan dan karami dashi pink yanada dimple Wanda ko magana yakeyi sesun lotsa gashin kanshi yasha gyara atare yake sosai andan sha gefe da gefe seyayi kamar fonk, kunsan irin gashin turawa da na larabawa base nafada muku ba yanada kwantaccen saje baki Wanda shima yasha gyara daga dan gefen wuyanshi akwai zanen tattoo daya fito waje alaman jikinsa akwai tattoo azaad cikekken namijine wanda ko wace mace zatayi mafarkin samu amatsayin miji( nikuwa ISHAM nace aibanga laifin su nusaiba da aneesa ba dasuka nanike masa kamar magnet) Saukowa sukeyi daga matakalan jirgin cikin takun kasaita , hannun azaad narike da jacket din suit dinshi, tunda suka sauko suka tadda yan jarida sun kewaye ko Ina na airport din ga manyan abokanan kasuwancin su tako Ina, ga sojoji kewaye dagurin domin basu tsaro se fadawa dakuma yan uwansu yan masarautar gombe dasuma yanzu suka iso domin tarbansu cika airport din yayi bako matsaka tsinke, tambayoyi Yan jarida suke ta aika musu dakuma faman daukansu hoto ko takansu basubi ba sukaci gaba da tafiya, kirari fadawan nan suka farayi tare da busa sarewa, karasowa fawwaz da areef sukayi atare suka rungume Abba suna mishi sannu da hanya cikin farin ciki da jindadi Abba yake shafa bayansu yana murmushi kafin suka zame jikinsu suka rungume azaad ko wannen su kagani zakaga farin ciki dauke afuskokinsu amma banda azaad da fuskan nan take kamar kullum, bubude musu murfin motar sukayi suka shiga ajere motocin suke, suka jera akan titi suna tafiya slowly, motocin sojoji ne agaba wanda akalla zasu kai motar 10,se motocin gidan sarkin gombe color su fari Suma akalla zasukai guda 8, se motocin gidan MAINASARA family bakake ne su sunkai goma sha hudu 14, daga tsakiya Kuma motocin abokanan kasuwancin su ne wanda kowa da kalan motar sa se karshe motocin polisawa ne wanda suka taho daga government house se jiniya kawai kakeji yana tashi, duk masu ababen hawa sun faka suna jiran wucewarsu , minti 40 ne yakawosu gida Bude musu motar akayi suka fito atsaye a compound din gidan suka samu su ummi, zeenat,anty Amina da itama dazun tazo da yaranta, mommy , Mansoor, anty Zainab ,anty shayida duk suna tsaye suna jiransu, da gudu zeenat tafada jikin Abba tana murna " oyoyo yarinyar abbanta ! Yar autan abbanta " cewan Abba dake rike da zeenat din sakeshi tayi tana kare masa kallo cikin zolaya tace" wow abbana kaga yanda ka Kara kyau da kumatu kuwa Meye sirrin !?" Ta tambayesa tana rike da duka hannayensa biyu dariya jamaan wajan sukayi saboda tabasu da dariya dakuma burgesu yanda suke da mahaifin nasu, lakatan hancinta Abba yayi" uhmmm zee Meye kuwa sirrin daya wuce kwana biyu nahuta da rigimanki Kinga aidole nayi kumatu " nanma kara tuntsirewa akayi da dariya saboda dama Abba ba bayaba wajan barkwanci wucewa ciki azaad yayi dan baze iya da wannan hiran nasu ba Dan yaga bana karewa bane yana mamakin Abba daya tsaya yake biyewa zeenat, da gudu_gudu Faisal babban yaron azaad yabi bayansa yaron sane na amana kusan shekara 10 suna tare Yana mishi hidima black beauty dashi. Part dinsa direct suka wuce Yana shiga dakinsa ya cire necktie dinsa yayi wurgi dashi.




Acikin gida kuwa tunda zeenat taji abinda Abba yafada tayi narai narai da ido kamar zatayi kuka dariya tabashi yariko hannunta suka fara tafiya Yana ce mata " haba yar autata am just kidding you" ahaka harsuka karasa kusa da su ummi dasuke tsaye wani irin kallon love Abba yakebin ummi dashi bakaramin kyau tayi mishi ba seyagama kayan hausawa yafi karbanta itakuwa se murmushi takeyi tana sunnar dakai dan ita kunya yake bata agaban yayanta , mommy kuwa bakin ciki kamar yakasheta fuskan nan adaure. Kiran areef Abba yayi yamishi magana akunne Sannan yawuce part din ummi su ummi sukabi bayanshi , mommy kuwa fuuuuu tawuce part dinsu rai abace, karasawa areef yayi yacema jamaan wajan " Abba yace in fada muku kujirashi a part dinsa " yawuce ciki.


via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD


πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺






Story & Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)










Da sunan Allah me rahama mejinkai πŸ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen πŸ₯°πŸ₯°




















Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina Allah yabar zumunci πŸ₯°πŸ₯°πŸ€Ž










Free book πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š














&_______________________________________&












Page 2️⃣4️⃣ & 2️⃣5️⃣














Part din Abba bakin suka shiga suka zauna suna jiran fitowarshi babban part ne dan yafi duka part din gidan girma gashi yasha kayan dukiya kam kamar zasuyi magana.
Zaune suke a babban falon kasa sunata hira yaran anty amina aslam da islam se wasan su sukeyi mikewa ummi tayi tahaura upstairs direct dakinta tawuce taje toilet dan tahadawa abba ruwan wanka jin motsi tayi a dakin nata fitowa tayi taga Abba atsaye atsakiyar dakin fuskanshi dauke da murmushin so da kauna yabude mata hannu ahankali taje tayi hugging dinsa dagowa tayi tana kallon fuskansa cike da kaunar mijin nata magana Abba yafara yana fadin" i really miss you my zaujat " " I missed you too" ummi tafadi haka fuskanta yana canzawa ganin kamar ranta adan bace ne yasa Abba tambayarta " meyafaru kuma naga ranki abaci ko bakiyi farin ciki da dawowata bane!?" Jan hannunsa tayi suka zauna abakin gado tana fuskantar shi tace " bahaka bane nafi kowa murna da dawuwarka saboda nayi missing dinka sosai, kawai de abinda kakeyine banajin dadinsa domin baka kyautawa banason ran tashin al'qiyama mijina yatashi da shanyeyen barin jiki dukda nasan iya kokarinka kana kwatanta adalci a tsakanina da mommynsu amma dan Allah kadinga adalci kaga itace uwargidanka uwar manyan yayanka abangarenta yakamata kasauka ba anan ba kokuma kasauka apart dinka nasan yanzu dole zataji badadi kuma tana da gaskiya ko nice zanji badadin hakan mijina kayi hakuri in akwai abinda nafada daya bata maka rai bazan iya zuwa ido inga kana irin haka a tsakaninmu ba " tagama maganarta kanta akasa ( gareku mata masu kishiyoyi karkiyi murna dan wai mijinku yafi fifitaki akan yar uwarki kita farin ciki, zakiga wani namijin Yana fifita daya akan daya Kuma baya iya boyewa wannan rashin Adalci ne zakiga in ranar Kwanan dayan ce zeshiga dakin yar uwarta yaki fitowa dawuri kokuma yaje ya yini agunta , kekuma a maimakon kimishi magana akan hakan badacewa bane sekiyita farin ciki harma yazama kina mata gori tom karkiyi tunanin wai shikadai ne da hakkin rashin Adalci kema harda nake komishon din kema kin bada naki gudunmawan Dan dabaki sakar mishi fuska ba babu yanda haka zefaru kokuma kimishi nasiha akan hakan be kyautu ba zakiga jikinshi yayi sanyi nan gaba dole zeji nauyin sakewa, Amma maimakon hakan se mata suka maidashi ado suna tutiya da miji nasonsu yana banzatar da kishiyarta bazakiyi tunanin namijine fah abinda yawa yar uwata nima inbanyi wasa ba wata rana dole zejuyo kaina saboda zaman aure zamane nahar abada ba kullum bane ake cikin jindadi ba zamane na yar hakuri , tom tunasar da mazajenku akan hakan zesa arage wani rashin Adalcin Allah yakyauta). Tunda ummi tafara magana Abba kebinta da ido wutan sonta nakara ruruwa acikin zuciyarshi tabbas yayi dacen mata aysha macece da har kullum yake alfahari da ita macen kwarai datasan yakamata wani irin tausayinta ne yakamashi aranshi yana fadin "baiwar Allah datasan wacece hafsat dabata tsaya tana cewa bana mata adalci ba datasan irin mugun nufinta akansu da setaji ta tsaneta amma banga laifinki ba dan nasan bakisan ba aure a tsakanina da itaba " ajiyar zuciya yayi yariko hannunta yace " bakomai my wife in sha Allah zangyara karki damu " murmushi tayi tace" yauwwa shukhuran ya Habibi" mikewa yayi yashiga toilet din yasamu yayi wanka ta fito masa da kayan sawansa sannan ta koma kasa. Suna zaune afalon yafito suka je dinning area akayi saving din kowa abinci, kallon Abu tayi tace " ankaiwa bakin dake part din abbansu abinci !? Eh hajiya nakai musu" okay ankaiwa son nashi ne?" girgiza Kai Abu tayi tace " ah ah yanzu aka gama shirya mishi nashi zaakai mai" gyada kai ummi tayi kafin suka faracin abinci shuru sukayi bakajin karan komai se cokula bayan sun kammala ne Abba yamike Yana fadin " bari inleka jamaata " to sukace mai.






" Sir wannan sune list din kayan da muka fitar awannan shekaran Kuma alhamdulillah duk sun kare komai yatafi smoothly, a motoci kwaya Dari shida na company duka sun kare saura guda gomane suka rage range Rovers , sekuma company shinkafa nanma abuhu million biyar da aka fitar duk sun kare,haka company sauran kayan abincin Suma komai yatafi yanda yakamata kuma ansayar da komai akan farashin daka fada, sekuma azaad unlimited company (inda ake sarrafa kowani irin nau in kayan sawa) nanma duk kayan ciki sun kare anzuba wasu, se manyan super market dinka dakuma manyan shagunanka na furniture Suma haka komai na wannan shekaran yakare anzuba wasu , se gidajen da akeyin renting ( gidan haya) Suma kowa yabada payment dinsa, masu napep masu taxi πŸš• kowa yakawo nashi balance din, se gidan gona Shima anzuba wasu kayan aciki , shopping mall dinkama haka, bayan hakama Muna bukatar sabbin ma aikata akalla guda dari ko sama da hakan wannan shine list din wannan shekaran sir" Faisal yagama magana yana juyawa azaad dake kwance akan lallausan gadonshi laptop din dan yagani , mikewa yayi yace " good job faisal karka damu base kanuna min ba kamanta komai inde abinda yashafi system dinka dana duk sauran ma aikatana ninake juyashi bane, you did a great job, yanzu abu nagaba shine kafadawa marketing manager yakaro sabbin ma aikata sannan kuma kaje kasamu accounter kowani employee dina akara masa salary akalla 50k each employee, sannan kayi arranging din ziyaran daza mukai gidajen marayu in this week" yana magana yana bata fuska kamar wanda akawa dole seyayi maganar, faisal kam ko ajikinshi inda sabo yasaba da halin ogan nashi shekara 10 bawasa ba , cigaba da magana faisal yayi " sir kanada meeting jibi misalin karfe biyu da kautal Jude company, sekuma jiri brothers and son's sunyi request din appointment dakai zaayi accepting dinsu neko Kuma!?" dan daga kai sama yayi kamar wani me tunani can kuma yace "okay I will think about it" okay sir suna cikin haka me aiki takawo musu abincin ta ajiye a dinning area na falonshi kafin tadan daga murya tace" sir your food is ready" tana gama fadin haka ta tafi ko motsawa azaad beyiba ,tashi Faisal yayi yaje dinning din yaga food flask sunkai takwas ajere bude nafarkon yayi yaga fried rice taji nama zuku_zuku plate yadauka yayi serving kanshi yazauna yafaracin abinci yaci yakoshi yasha drinks dinshi tukun yakoma gun azaad yace " sir cikina yadauka nizan wuce se anjuma" yadauki system dinshi dan dama beyi tsammanin amsa ba yatafi.



Safa da marwa mommy takeyi afalonta fuskanta ahade kamar anmata sako da mutuwa ita kadai se sambatu takeyi " ni Muhammad zeyi kokarin tozartawa wlh be isaba karyanshi yasha karya itakuma aysha senayi maganinta munafukar banza da wofi mtsssw" gaba Daya yaranta tagumi sukayi suka zuba mata ido ganin yanda take maganganu kamar wacce ta zauce anty shayida ce tace " please calm down mommy meyasa kike yawan tayar da hankalinki akan abinda betaka kara yakarya ba wannan aibawani abu bane nide nasan wallahi ummi nasonki tsakani da Allah " wani irin uwar harara mommy ta wurga mata " nide kam banji dadin rayuwata ba Allah yaban yara marasa kishin uwarsu Yan iska marasa zuciya,barinma ke tanuna anty shayida da yatsa nayi dana sanin haihuwarki saboda bazeyu ace nahaifi yarda bata kaunata ba banza laa'nanniya shisa kika kasa samun ci gaba arayuwa keda yara Kuma sede kiga ana haihuwa " ( iyaye yakamata musan irin kalman da zamu dinga furtawa yayanmu domin bakin uwa nada matukar kaifi akan danta walau adduah'ta walau mumunar Baki, Koda yakasance dah namaka laifi duk muninsa karkiwa danki baki domin rayuwarsa ne zetabbare Kuma daga karshe kema kizo kina danasani to miye riban haka, yaro tun Yana dan karami dashi Zaki tankwarashi takan farki mekyau yanda kinsan nan gaba inya girma baza kisha wahala ba, in laifi yayi kimishi fada sosai sannan kijashi ajiki kimai fada yanda nan gaba bazeyi shaawar Kara aikata hakan ba , sannan duka wasu iyayen suna ganin idan yaro yayi laifi akamashi amishi dan bazan duka shine dede to nanma bako wani laifi bane ake bugun yaro, saboda idan jikin yaro yasaba da duka nan gaba koya ganki da bulala wallahi baze gudu ba kokuma kiga alamar tsoro akan fuskanshi ba saboda yariga daya saba da dukan ahakane zakiga yaro yataso marajin magana da rashin ji,.)
Jin irin mugayen kalaman da mommy take binta dasune yasa kukanta da take dannewa yafito Fili, tashi tayi tahaura upstairs dakinsu dasuke ciki time din yanmatancin su ta cigaba da kukanta bin bayanta anty Zainab tayi tana rarrashinta "kiyi hakuri shayida komai lokacine wata rana se lbr yakamata yanzu inda sabo kisaba da halin mommy Kuma kidinga sata a adduah Allah yasa tagane gaskiya " cikin muryan kuka anty shayida tace" anty Zainab irin abinda mommy take mana kamar ba ita tahaifemu ba narasa dalilin dayasa bata kaunar mu tadauki Karan tsana tadaura mana barinma ni tafi tsanata shisa yanzu inbadan Abba da ummi ba wlh se infi watan ni banzo gidan nan ba, anty Zainab ninasan bakin cikine ze kasheni acikin Wanda sukemin gorin haihuwa ace harda uwata wacce yakamata itace zatana rarrashina amma harda baki take
min wai bazan taba haihuwa ba innalillahi wainna ilaijiraji unnn ya Allah kakawomin mafita " tagama magana tana Kara rushewa da marayan kuka rungumeta anty Zainab tayi tana bubbuga bayanta "is okay kinji kokin manta haihuwa na Allah ne shiyake bayarwa alokacin da yagadama in lokacin dazaki samu ciki yayi babu wani mahalukin daze hanaki samu kuma kici gaba da kai kukanki wajan Allah , kidena sawa kanki damuwa kokin manta munada ummi da abba ne ga kannanmu duk suna sonmu ga Amina ma " haka taci gaba da kwantar mata da hankali hartasamu tayi shuru.








Abangaren gidan su fanan kuwa yanzu shirye_shiryen saukan fanan akeyi haka gidansu amira ma Dan makaranta daya sukayi DHARUL_HUDA.
Dukansu suna zaune afalo harsu baba yau basu fita kasuwa ba saboda shirye_shiryen saukan gobe dazaayi, fanan nazaune itada suhaima atsakiyar falon hannunta dauke da jotter da pen tana rubuta list din mutanen dazasuzo tana sanye da wando falazo black me manyan fulawi fari tanason falazo sosai dan tafi sakewa acikinshi, se farar riga kanta da hula ita kuma suhaima list din abubuwan da ake bukata take rubutawa,
Dago Kai fanan tayi tace "mama nagama rubutawa bansan ko akwai wayanda suka rage ba " suhaima ce tace " kin saka gidansu ummi a list kuwa " " ah ah bansa ba basuma san zanyi saukan ba shisa bansa ba" cewar fanan dake kokarin rubuta sunan nasu a jotter ta, mama ce tace " aikuwa de yakamata asa inyaso tunda basu saniba anjuma al ameen seya kaiku gidan kubasu kati " to shikenan, mikawa ya usman list suhaima tayi dan tagama rubutawa karba yayi yana dubawa can kuma yace " iyakacin abinda ake bukata kenan !? Naga kamar list din yayi guntu" Yana magana yana kallon list din Jin abinda yafada ne yasa mama tace " inga ni" tashi yayi yaje yabata yadawo yazauna , duddubawa takeyi pen tadauko ta kara rubuta abubuwan dabata gani aciki ba bayan tagamane tamikawa baba yakarba yace" shikenan ko " eh sukace, mikewa baba yayi yadauki car key dinshi yace " Usman tashi ka tada mashin dinka ka kaini indauko motar muje kasuwa kaikuma Al ameen seku shirya kuje ka kaisu " dukansu Mikewa sukayi mazan su ya al ameen sukayi waje sukabi baba , ya usman yatada mashin baba yahau suka fita daukan motar saboda gidan baze dau motar biyu ba shisa baba yake baro nashi a inda ake gadin motoci yacewa ya al ameen yadinga packing din nashin kawai, fitowa fanan sukayi harda auta itama zatabisu dogon hijab duka sukasa , suka sameshi a motar shiga sukayi yatada motar suka kama hanyar gidansu azaad, fanan kwatance tadinga yimishi harsuka iso fitowa baba me gadi yayi ganin bakuwar mota yasa yazo dubawa dan leko kai fanan tayi tagaisheshi washe fuska yayi ganin itace yakoma yawangale musu gate shiga cikin gidan yayi , bayan yayi packing suka fito, hango zeenat da fawwaz fanan tayi alamun fita zasuyi karasowa wajan su sukayi mikawa ya al ameen hannu fawwaz yayi sukayi musabaha idon fawwaz ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login