Showing 33001 words to 36000 words out of 45089 words
Chapter 12 - NIDA PATIENT DINA Book 1 Complete Hausa Novels by Mrs Hisham .txt
ajikinta mikewa tayi ta Isa gaban wardrobe dinta tabude kayan bacci tadauko white color silky riga da wando tasa takoma kan gado tazauna tana tunanin ko ina suhaima taje oho, jawo wayarta tayi takunna data tashiga WhatsApp tana duba messages video call taga zeenat takirata picking tayi tana gyara zamanta, zaune take afalo alamun basu kwanta ba dan tanajin muryoyinsu ganin cute face dinta ya cika screen din wayar cikin daga murya tace " barka matar babban Yaya" cike da tuhuma su fawwaz da areef harda azaad din da yaseer suka juyo suna kallanta Jin abinda taburta, itakuma subul da baka tayi, ganin sun tsareta da ido ne yasa tafuske da " kawata meya hanaki bacci " murguda mata baki fanan tayi kafin tace " aike zaawa wannan tambayar! Yasu Abba da ummi!?" Yar dariya zee tayi " suna lafiya duk sunkwanta ai mune kadai mukayi saura muna kallon wani series ne " takarshe maganar tana kallon azaad dake hakimce akan sofa mezaman mutum biyu yana danna wayarsa fanan nakokarin magana zeenat tacire camera daga face camera tamaidashi back camera taseta azaad, kyawawan fuskanshi ne da cikekken surar jikinshi ya bayyana agaban screen din wayarta wani irin kyau yakara yana sanye da pj mask ajikinshi wani irin kwanciyar hankali taji ya ziyarceta lokaci Daya lumshe idonta tayi batasan dalili ba amma jinta take kamar wacce akawa albishir da wani babban abu, ganin yanayin mood din da fanan tashiga ne yasa zeenat tayi murmushi harseda dimple dinta yalotsa, kamar daga sama taji ance " will you stop that nonsense" dukansu firgita sukayi dagowa tayi taga azaad ne yakafeta da sexy eyes dinshi kamar wani mejin bacci rai abaci cikin dakakkiyar murya yace" bani wayar nan " yafada yana mika mata hannunshi fanan najin haka cikin sauri tayi hanging din kiran, su yaseer dabasu san meyake faruwa ba suka zuba musu ido, cikin inda_inda tace " am sorry ya azaad" tsawa yadaka mata wanda suma dasuke wajan seda suka tsorata " before the count of 5 hand me the phone " ganin hawaye yacika a idonta ne yasa yaseer cewa " we're sorry dude amana afuwa" ko kallon inda yaseer yake beyi ba balle ya saurarare shi so yake yasan wacece zeenat take video call da ita dahar zata juya back camera tana kallonshi dan yasan ba nusaiba bace balle aneesa dan dukkansu basa good time bawani shiri sukeyi ba, kuka tafara hawaye nazuba a idonta tasan inde ya azaad yakarbi wayanta ba lallai yabata ba inma zebata to bayanzu ba cikin sanyi jiki tamika mishi wayar takoma wajan fawwaz ta rungumeshi tana kuka kasa_kasa shafa bayanta yakeyi dan babu yanda suka iya inyayi magana shima yanzu laifin zeshafeshi, Allah sarki fanan baiwar Allah duk setaji badadi she felt guilty akan abinda yafaru danasanin daga wayar tayi dan tasan yanzu kan zeenat abin ze koma tana zaune duk tayi zugum da ita , unlocking wayar yayi dan dukkansu yasan abinda sukasa a password dinsu yashiga WhatsApp wajan calls yashiga ganin number datayi waya dashi last yayi an rubuta πOTHER HALF π₯°, without hesitating yayi dialing din number yafara ringing fuskan nan adaure tamau , tana zaune shuru tana tunanin koya zeenat takare da Mr azaad oho taji wayarta na ringing dasauri taduba ganin friend zeenat ne, hamdala tayi cike da jindadi tadaga , daskarewa tayi ganin face din Mr azaad akan screen din,bin fuskanta da kallo yayi gashin kanta data daure kamar wata karamar yarinya yakalla daga bisani yadan ja tsaki " me kika wani tsareni da wannan idon naki kamar wata mayya !?' yafada yana kallon cikin idonta dasuke farare tass dasu gasu manya masha Allah, gwalo idon waje tayi jin abinda yafada can ciki_ciki yanda bazejitaba tace" aikaima idonka manyane kilama sunfi nawa girma kaima mayene kenan" afusace yace " ke nikike cewa maybe?" Sam batayi tunanin zeji abinda tafada ba cikin muryan firgici tace "Nashiga uku na lalace Mr azaad dan Allah kayi hakuri badakai nakeyi ba wani quda ne yazo wucewa yake kallona ni badakai nakeyi ba" wani irin dariya yaseer da fawwaz suka kwashe dashi Jin abinda fanan tafada wai ita da quda ne ko a ina taga qudan awannan daren,Kara tamke fuska yayi yajuyo yakallesu aikuwa mitt sukayi kamar basune suke dariyaba yanzu , kwafa yayi yamaida kallonsa kanta cikin husky voice yace " meyasa dazun kike kallona " tarin mamakine yakamata taya akayi yasan shi take kallo shida yake danna wayarshi bugo da qarima kujeran dayake zaune bakusada zeenat yakeba,Satan kallonshi tayi dakyau tarasama mezatace mishi ganin yanda yatsareta da ido duk yasa takara birkicewa idea ne yazo mata cikin dabara tace" am dama budurwarka ce tace induba maka lafiyanka shisa nacewa zee ta juyamin inganka domin aiwatar da sakonta and now I can see you're extremely fine byebye good night " ko tsayawa taji mezece batayi ba takatse kiran kirjinta nadukan tara_tara dan tasan haduwansu nan gaba bazeyi kyau ba .
Suman zaune azaad yayi jin irin karyan da fanan tazuba mishi dan takare zeenat aranshi yana fadin" wato kullum tsiwan yarinyar nan Kara karuwa yakeyi " sukansu su fawwaz mamakine yakamasu dama fanan na magana har hakane, lallai yau de tadibo ruwan dafa kanta dan tabari suka hadu da ya azaad hmmm , yaseer kuwa se kumshe dariyan daya taho mishi yakeyi dan karya bito dan yasan bazasu wanye tadadi da azaad ba, one by one suka dinga barin falon zuwa daku nan barcinsu dan karya juyo kansu harsuka watse yarage dagashi se yaseer cigaba yayi da pressing din phone nashi.
Shigowa suhaima tayi da soccer ahannunta cike da snacks ta ajiye musu atsakiyar gadon ganin yanda fanan tayine kamar wanda taga abin tsoro yasa ta tambayeta ko lafiya fada mata abinda yafaru tayi " Tabb lallai fanan sannunki da kokari meya hadaki dama wannan karya mutumin da zan iya rantsuwa baya dariya shine kika tabo ai babban mafita shine koda wasa karki bari kuhadu" ta karashe maganar tanakai snack bakinta , Kara rudewa fanan tayi jin abinda suhaima tafada kuma koda bata fada ba tasan sarai Mr azaad bakyaleta zeyi ba kallon cikin soccer tayi jitayi cikinta akoshe yasa takwanta taja blanket tarufe jikinta tana cewa suhaima " inkin gama kikashe wutan dakin" tayi adduah bacci tarufe idonta .
via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe
π§ββοΈπ§ββοΈ NIDA PATIENT DINA π©Ίπ©Ί
Story & Written by ( MRS πΉ ISHAM πΉ)
Da sunan Allah me rahama mejinkai π Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen π₯°π₯°
Free book ππππ
Alhamdulillah nakusa gama book 1 π₯°π₯°
&________________________________________&
Page 2οΈβ£7οΈβ£
Asuba ta gari ,yau tunda gari yawaye babu Wanda yakoma yaruntsa aiki kawai sukeyi bakama hannun yaro ,anyi yanka duka dade sauransu su anty firdausi ma duk sunzo da junior,karfe 8 suka gama komai wanka fanan tashiga tayi suhaima kam tarigata wanka hartama shirya tana falo , bayan fitowanta ne tashafe jikinta da lotion dinta masu dadin kamshi usual make up dinta tayi powder da kwalli se libs Stick , dogon wando legis baki tasaka aciki tasa bra sannan tadauko abaya tazura ajikinta bude box din datake ajiye kayan dan kunnenta tayi kallonsu takeyi tama rasa wanne zatasa dan batasan abinda ze dameta wani mekama da manne tadauko tasaka hartazo rufewa taga nose pin ita inbama tagani ba mantawa takeyi tana da bulin hanci tadauko fari tayi tasa daga bisani ta tufke gashinta da bakin ribbon, daura gyalen abayan tayi akanta , fesa body spray tayi ajikinta kallon kanta tayi a mirror ganin tayi kyau yasa tasaki tsadadden murmushinta dake kara mata kyau, duk abinda takeyi su jakadiya abashiyya suna kallonta Suma se sakin murmushi sukeyi dan bakaramin farin ciki suke ciki ba yau sarauniyarsu zatayi sauka , waigawa tayi tadan kalli hijab dinta Dake kan gado dan tsaki tayi kadan setaga yayi mata nisa cikin shagwaba tabuga kafa akasa wanda yasa albarkatun jikinta suka motsa afili tace "yanzu dan Allah sena daukoka kaima " jin abinda tafada ne cike da zumudi khairatyyy tadauki hijab din taje kusa da ita tamika mata ita kwata_kwata tamanta da fanan bata ganin su , fanan kuwa sarkin tsoro ganin hijab yabi iska yataso dakanshi yazo yasa tadanja baya tamanne da jikin mirror, tagumi jakadiya abashiyya tayi tana takaici da yarintar khairatyyy ace yarinya shekara 120 amma haryanzu ba hankali girgiza kai kawai tayi tasan sarauniya tagama tsorata , ganin hijab yana tsaye kigam agabanta yasa taketa karanta duk wani adduah dayazo bakinta , khairatyyy kam se murmushi taketa zubawa fanan hankalinta kwance ita aduk duniyar nan sarauniyarsu tana mata kyau matuka bata taba ganin mekyau irinta ba daga ita se gimbiya Afroza , dan itama gimbiya Afroza ba baya ba wajan kyau amma acewar khairatyyy batakai sarauniya ba, shahada fanan tayi tasa hannu takarba tadaga hijab din sama tadinga tofeshi da adduo'i sannan tasa daura nikaf tayi , ba abinda ake gani afuskanta daya wuce wayan nan manyan fararen idonta se faman lumshesu take tasa safa tubarkallahu Masha Allah karkuso kuga irin kyaun da fanan tayi daukan takalminta da handbag tayi tawuce falo duk sun gama shiryawa, haka gifts dinma duk angama packing dinsu tsaff su snacks, nama , cincin,drinks,sesu jotter, mafici ,hanky, tissue bag masu dauke da hotonta ajiki, kwashe kayan ya al ameen yayi zekai su motar Jin fitowanta ne yasa ya tsaya bakaramin kyau tayi ba kamar wata bakar balarabiya, "wow masha Allah yar kanwa irin wannan kyau haka tsaya inmiki pics kafin mufita ko" Al ameen yakai karshen maganar yana zaro wayarsa daga aljihu yafara daukanta hotuna yamata yakai kala 10 kafin yace tom ya isa , wajan mama taje tarungumeta shafa kanta mama takeyi tana murmushi at the same time tana tuna kalubalen dake gabansu dago kanta tayi tace " mama Ina suhaima da auta suka je!?" Shafa kanta mama tayi tace " sunje kai kaya motar suna waje dasu antyn firdausi da babanku dama muma ke mukejira " murmushi tayi meyar sauti tace "to mama muje " fitowa compound din gida sukayi sukaci karo da ya usman yana kokarin shiga falo yakwaso sauran abubuwan dasuka rage ganin irin kyaun da kanwarshi tayi ne yasa yayi murmushi nan ne naga tsantsan kama dasukeyi da fanan sede shi fari ne sol shida auta dasu mama da baba harda su suhaima kaff gidan fanan ce black beauty me chocolate color skin , wajansa taje tarungumeshi bubbuga bayanta yayi yace " Masha Allah feeena you look so gorgeous" sa hannu tayi tarufe fuska tana kyalkyalewa da dariya jan hancinta yayi yariko hannunta sukayi waje motoci ne akofar gidan guda uku dana baba sena mijin anty firdausi dana ya al ameen, wai waigawa tayi tana neman baba anty firdausi tace" mekike nema ne haka!?" Maida kallon nata kan anty firdausi tayi kafin tace" Banga baba da suhaima ba " " suna motar shi ai" bata sake cewa komai ba taje tabude murfin motar tashiga gaida baba tayi cike da farin ciki yace" tubarkallah yata Allah yamuku albarka " amsawa sukayi da ameen, kallonta suhaima tayi " sweet sis kinganki kuwa kamar inhadiyeki" dariya dukansu sukayi fanan zatayi magana auta tarigata da fadin " ai nima ranan saukana haka zanyi kyau ko baba" tafada tana turo fuskanta wajan fuskan baba ita adole tana jiran amsa " kwaraima yar baba " Horn ya al ameen yamusu tada motar baba yayi yaja motar sukayi gaba, 30mint ne yakawosu makarantan Dharul_huda, sunayin packing suka fito shiga cikin babban hall din makarantan su mama direct inda iyaye da yan uwa suke zama sukaje bangaren mata su baba ma sukaje bangaren maza suhaima ce tarike hannun fanan suna tafiya cikin nutsuwa harkan dandamalin da amaren sauka suke amira ta taso tazo tarungumeta " oyoyo besty na " rike hannunta fanan tayi tace " bestie harkun iso kenan " "iyi muma bamufi 10mint dazuwa ba " gaisawa suhaima da amira sukayi daga bisani suhaima takoma wajan zamanta, karasawa wajan zamansu sukayi fanan duk tamika musu hannu sukayi musabaha,dukansu hijab dinsu white color da nikaf afuskokinsu se ID card nasu ,shigowa manya manyan malaman gombe irinsu sheikh kabiru gombe , Dr isah Ali pantami, sheikh adamu Muhammad dokoro , sheikh hamza Muhammad Adam, malam sani Muhammad sani, dana makobtan gari irinsu, sheikh dahiru bauchi, sheikh sani yahaya jingir, Dr auwal isah yalwa dade sauransu.da manyan malaman makaranta suka zauna a idan aka tanadar musu sunata musabaha da junansu , motocin su Abba ne suka shigo makarantan kusan motar 8 , securities ne suka bude musu marfin motar suka fito duk sunsha manyan kaya kaff dinsu sunzo amma banda mommy da Mansoor ,su anty shayida kuma duk sunkoma gidajensu, cikin hall din suka shiga hangosu mama tayi cikin sakin fuska tamike tanufesu gaggaisawa sukayi kafin su fawwaz da areef sukaje indasu ya usman suke zaune suka zauna suna gaisawa hannu Abba yamikawa baba sukayi musabaha, dukansu zama sukayi suna sauraran qira'an da aka Kunna a loud speaker na sheikh sudais, zaune yake acikin motar yajinginar da kanshi ajikin seat din sanye yake da dakakkiyar shadda daya amsa sunanshi ko makahone yataba yasan me matukar tsadane brown color half jumfa dinkinma kansa abin kallone,hannunshi nadaure da agogon diamond se walkiya yakeyi kafarshi nasanye da takalmi baki me shegen kyau yatsun kafan nan Zara_zara dasu farare tas , yasawa fuskanshi facemask gashinan yasha gyara beyi niyyar zuwa ba amma haka Abba da ummi suka sashi agaba taya zaayi nurse dinshi zatayi sauka yace bazezo babu yanda ya iya haka yataho zuro kafarshi daya waje yayi kafin yafito wow handsome tafiyan shinan dayake tafiya da hankalin duk wani me kallonsa yakeyi securities 5 suke take mishi baya duk suna rike da bindigu, shiga cikin hall din yayi nan take kallo yadawo kanshi duk da yasa facemask amma yawancin mutane sunganeshi danshi din na dabanne , zama a Daya daga kujerun dake kusa danasu abba Yana danna wayarsa bekara dagowa ba balle yasan me ake ciki .
___fara Kiran dalibai yan sauka akeyi suna zuwa suna karatu har aka iso kan amira daga ita se fanan dan sune karshe tasowa Amira tayi tazauna gyaran murya ya mu'alim dinsu yayi yayi Bismillah yajawo mata ayah acikin suratul yunus cikin muryanta me dadi tafara karatun harta kammala anata attakhabir ,komawa mazauninta tayi , Kiran sunanta akayi Fatima muhammad Umar gabanta ne yafadi ganin dubun nan jamaa kowa yazuba ido yanason kallon wacece Fatima da aka kira , cikin tafiyanta irin na mahauniya tafara tafiya gaba daya idon jamaa nakanta ahaka tadake tasamu guri tazauna tana gyara mic din asetin bakinta , Daya daga cikin manyan malaman ne yayi Bismillah yajawo maya ayah a tsakiyar suratul yaseen , Jin tafi minti 3 batace komai ba har anfara kokwanton ko akwai abinda yake damuntane jikinsu baba ne yayi sanyi ganin fanan takasa magana daya daga cikin malamansu mata ne tamike zatazo taga abinda ke faruwa kawai sukaji tayi Bismillah kafin tafara rero karatu cikin qira'a me dadi wanda duk wani musulmi inyaji se jikinshi yayi tsuma dakuma yin sanyi bama iya musulmai ba duk wani me sauraro , Jin zazzakar murya nakaratu ne yasashi dagowa bashiri kallo daya yamata yaganeta dukda akwai nikaf afuskanta wani irin nutsuwa ne yaji yana ratsashi bashi kadaiba duk wani wanda yake wajen abinda yakeji kenan bakaramin ratsasu karatunta yakeyi ba, inbada jinjina kai babu abinda malaman sukeyi domin sundade basuji irin wannan qira'ar ba tabbas wannan yarinyar yar baiwace Allah ya azurtata da murya dakuma sani. Kallonta yakeyi yama kasa kauda idonshi akanta jiyayi duk wani laifi data mishi yahakura baseya hukuntata ba , Yan gidansu kuwa se murmushi sukeyi bakaramin proud sukeyi da itaba, karatu takeyi kanta akasa har tadasa ayah, cikin sauri sheikh kabiru gombe yadauki mic yajawo mata wata ayar a suratul Ar_Ra'ad badan komai yasa yayi hakaba sedon basu gaji dajin zazzakar muryanta ba intana karatu jisukeyi kamar karta dena, karatun takeyi zuciyarta fess babu wani guntun damuwa kokuma bacin rai gaba dayansu kwanciyar hankali ne ya bakuncesu, dasa ayah tayi tana sadaqallahul_azeem , duk jaman dake wajan suka amsa da Allahu akhabar, lumshe ido azaad yayi yana sake tsadadden murmushinsa medaukan hankali. Babu abinda kakeji awajan nan inbada ansakuwan Allahu akhabar da akeyi kowa seyabonta akeyi domin bakaramin burge kowa tayi ba kowa babban burinsa shine yaga fuskar wannan baiwar Allah , komawa tayi wajan zamanta tazauna, malaman ne sukayi waazi dakuma jawabi da jinjinawa yan sauka dayi musu adduah Allah yabasu ikonyin aiki dashi, Dr isah Ali pantami ne yakarba mic yafara kwarara musu adduo'i kafin yakoma kan fanan yana samata albarka da yabonta domin tayi abinda kowa yake matukar alfahari da ita daga karshe yabata kyautan naira dubu dari biyar amsawa waje yayi da Allahu akhabar, haka sheikh dahiru bauchi Shima yamata adduah dakuma kyautan gida , sheikh kabiru gombe ma yakyautan mota da gida yamata , haka Abba ma yamata kyautan 1million ummi Kuma sarkan gold da dankunnen su masu kyau da tsada , haka kowa yadinga mata kyauta naban mamaki. Mama se hawayen farin ciki takeyi bakaramin alfahari sukeyi da itaba domin ta kara kankaro musu kima a idon dubun nan jamaa. Mikewa azaad yayi yaje kan dandamalin akamika mishi loud speaker cikin harshen larabci yafara magana yamusu adduah sannan kowani dan sauka yabashi kyautan dubu dari dari fanan Kuma kyautan 1.5million yabata da babban shagon saloon dinshi dake cikin anguwar dawaki me suna beauty saloon waje ne me matukar girma wanda se macen datakai tukun take zuwa yana gama jawabinsa yafita a hall din, mamakine yakama fanan ganinshi agun dan batayi tsammanin zezo ba.
___________ ya mu'alim dinsu ne yakirata tafito yabukaci data dan dage nikaf dinta dan kowa agun burinsa kawai suganta sunce nikaf dintayi kyakyawan cute face dinta yabayyana kowa seyaba kyaunta yake anata daukarta hotuna kam ba adadi karban mic tayi cikin harshen larabci tadinga musu godiya sannan tamika musu tafita