Showing 42001 words to 45000 words out of 45089 words
Chapter 15 - NIDA PATIENT DINA Book 1 Complete Hausa Novels by Mrs Hisham .txt
dakin fanan , ganin suntafine yasa wayar akunne yace" me martaba nayi yanda kace " gyara zama me martaba yayi yace asa wayar a handsfree aikuwa haka akayi .
_____gyaran murya yayi kafin yafara magana " assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum " amsawa sukayi yadora dacewa " inason ku saurareni da kunnen basira nasan duk kunajina , naji abinda yafaru kwata kwata bemin dadi ba bani kadai ba hatta duk wani wanda yasan azaadu da wannan baiwar Allah yasan wannan qazafine! Anbata musu suna a idon duniya kowa kallon fasikai yake musu ! To nasamo mafita wanda nasan dukkanku tunanin ku bebaku Shiba babban abinda ze wanke sunan su a idon al'ummar duniya nan da hour 3 zuwa 4 shine su kasance ma aurata!
Nan ne zasu iya fitowa su karyata wannan lamarin da full confidence dinsu Kuma kowa ze yarda dukda zaayi mamakin yaushe babban shahararren Dan kasuwan nan yayi aure batare da sanin duniya ba, zasu iya cewa auran nasu bewuce sati dayaba anajiran dama tayi saukane seta tare wannan shine maganata!?" Kaff dinsu nutsuwa sukayi suna sauraranshi domin maganar shi shine mafita girgiza kai azaad yayi cike da rashin yarda da shawaran yace " no bazeyuba taya wannan zezama solution bazan taba yarda da hakan ba never" kallonshi kawai Abba yakeyi yama rasa mezece mishi duk abinda Mr azaad yake fada akan kunnen me martaba cikin tsawa yace " azaadu ni kake mayarwa magana ina fada kana fada ko ubanka be isa insa doka yaki biba balle kai" afusace azaad yace " shi kace ai taya ze tsallake abinda kafada ai shi ka haifa bani ba sekayi wannan takaman dashi" wani irin tsawa Abba yadaga wa azaad " mahaifin nawa kake maidawa magana saboda gaka ishashen mara kunya ko wannan taurin kan naka azaad kakiyayeni randa zanyi maganinta nazuwa, murmushin takaici me martaba yayi yace " karka damu ai dama masu iya magana sunce kahaifi da baka haifi halinshi ba nikuma zan nunawa azaadu na Isa dakai din ina mahaifin yarinyar!?" Cike da girmamawa baba yace" inajinka me martaba" " kaji abinda nafada bansan kai amatsayinka na mahaifinta ba meka yanke shin kabamu auranta !?" Gaba daya sun daure baba da jijiyoyin jikinshi gashi baze iyacewa me martaba ah ah ba dan dattijo ne me daddaku da Kamala da sanin yakamata mutum ne shi me adalci, inkuma be yarda ba yanaji yana gani sunan yarshi yabaci, awani bangaren kuma ganin reaction din Azaad yatabbatar mishi da bayason fanan shikuma bazeso abinda ze kuntata mata ba he's out of word, tabashi Abba yayi jin bece komai ba jiki asanyaye yace "nabaku me martaba" hamdala sukayi duk da yayyun fanan su ya Usman wani bankwarakwai sukaji lamarin. Tambayar kwatancen gidan me martaba yayi aikuwa dasauri yaseer yaturamai da address azaad de zuba musu ido yayi ganin abinda suke shirin yi wai kamarshi zasuwa auran dole. Motocin masarautar gombe ne tadira akofar gidansu fanan dukda zuwan sirrine mota ukune kawai daga me martaba se matarshi ta biyu Fulani se amintattunshi waziri da galadima se bafade guda daya kiran Abba yayi yasanar mishi dasun iso fitowa abba da baba sukayi suka musu iso farine sol suna matukar kama da abba shigowa falon sukayi suka zauna cikin darajawa da mutuntawa suka gaisa baba ne yace " Al ameen jeka kiramin mamanku " mikewa ya al ameen yayi yakira mama yasanar da ita sunyi baki tafito suka gaisa sannan takawo musu abin sha dasu snacks da fruit mikewa Fulani tayi tabi bayanta suka shiga dakin mama suma suna tattaunawa kan batun duk da basusan abinda ke faruwa afalo ba.
_______ kallon ba faden waziri yayi fita yayi yabude motar yadauko sweets da goro aka kawo falon, dan jimantawa baba yace wani hanzari ba gudu ba yakamata kafin ayi wannan auren kusan asalinmu sannan kusan wacece fanan kar ayi aure kuma wata matsala tabiyo baya, hamdala duka sukayi tabbas maganar shi gaskiya ne bakaramin jindadi sukayi ba domin dama kowa burinsa yaji menene taqamemen fanan.
TUSHEN LABARI
Alh umar haifaffen dan gombe ne Kuma dan kasuwane yanada rufin asiri dede gwargwado babu abinda yafi karfinsu shida matarsa rukkaya sunada yara biyu maza, babban dansu shine Muhammad se nabiyu kabiru tunda rukkaya tahaifi kabiru batasake haihuwa ba har suka kammala secondary school dinsu nan ne rukkaya tafara laulayin ciki ana haka suka samu addimission a university jari alh Umar yabasu Suma su tsaya da kafafunsu alhamdulillah sun bude shagunan su a kasuwa na trader suna karatu suna kasuwanci nan ne rukkaya tahaifi ya mace aka samata suna firdausi suna matukar sonta tana ganin gata sosai, har Allah yasa suka kammala karatunsu Muhammad dama shi business yake karanta kabiru Kuma engineering, a time din ne iyayensu suka sasu agaba akan maganar aure Muhammad akwai yar makociyarsu yadade yanasonta amma betaba nuna mata ba da aka matsa musu akan batun aurene yafadawa baba aikuwa sunyi farin ciki domin kuwa sumayya yarinyace kyakyawa me tarbiya da nutsuwa yar shekara 16 haka kabiru ma yafito da budurwansa rahina, acikin watanni kuwa akayi komai da komai aka daura musu aure bayan aure da wata uku kabiru yasamu aikin engineer a bauchi state suntayashi murna sosai haka yadauki matarshi dake da karamin ciki dukkansu basu saniba suka tafi. Laulayin ciki sosai sumayya tafara kamar bazatayi rai ba dan cikin yawahalar da ita sosai bayan wata tara suka haihu arana daya itada rahina suka haifi yara maza dawuwa gida sukayi dan ayi suna atare suna akayi yaron muhammad akasa mishi usman takwaran kakansu marigayi mahaifin alh Umar shikuma dan wajan kabiru yaci sunan alh umar anamai inkiya da Al ameen. Haka suka dinga samun kulawa na musamman agun dangi musamman alh Umar da rukkaya dan bakaramin son jikokin nasu sukeyi ba ana arba'in kabiru yazo yadauki matarsa suka koma bauchi .
Wata rana alh umar da matarsa suka shirya domin zuwa suga inda kabiru yake zaune dan basu taba zuwa ba sun isa bauchi lafiya ,satin su daya suka juyo domin dawowa gombe har tasha kabiru yakaisu sukayi bankwana ahanyarsu ta dawowa suka hadu da hatsari allah yamusu rasuwa firdausi ce kadai tatsira da rai sun matukar girgiza da rasuwan domin mutuwar iyaye babban ciwone haka aka musu Jana'iza aka kaisu gidansu na gaskiya daukan firdausi Muhammad yayi tadawo gidan shi.
Bayan shekara hudu kasuwancin muhammad yana tafiya dede Kuma har lokacin summaya bata kara samun ciki ba itakuma rahina family planning sukayi , daga firdausi har usman suna zuwa makaranta a lokacin firdausi nada shekara 9 usman kuma 4 ahaka suke rayuwarsu duk sanda engineer kabiru yasamu hutu agun aiki suna zuwa hutu da matarsa da al ameen ana haka ciki yabayyana ajikin rahina nanma sunyi farin ciki sosai.
___ sumayya kam shuru_shuru amma se shegen kwadayi dacin kayan kwalam duk babu wanda yakawo ciki gareta saboda har period tanayi wata rana ta tashi da wani irin mugun ciwon ciki nan take sukayi asibiti da ita aka bata gado gwajine farko suka gane tana da ciki harna tsawon wata biyar ajikinta amma ciki plat babu alamunsa wannan lamarin yabawa dangi mamaki tana samun sauki suka koma gida da ita sukaci gaba da kulawa da ita, tundaga wannan ranar suka fara fuskantan wani bakon yanayi akoda yaushe cikin sumayya wani irin daddadar kamshin turarene wanda bazaataba cewa ga kalarta ba akasuwa kokuma awani waje ba kullum gidansu kamshi ne kawai yake tashi Abu na biyu Kuma shine koyaushe sumayya jikinta agajiye takejinshi kamar wacce tayi wani aiki abubuwa de iri_iri.
Wani irin gagarumin fadane yabarke tsakanin jinsin fararen aljanu dakuma mugayen kungiyoyin asiri, har cikin masarautar nasminaya suka shiga suka cimmusu da yaki bakaramin dauki badadi akayi ba awannan daren inda aka kashe rayuka bila adadi, yakine da akayisa akan hular sarauta dake kan sarki abdud daar shine sarkin dake mulkan duka wani farin aljani sarkine da yafita lamba daya domin kuwa adaline yanason jamaar sa haka Suma suke kaunar sarkinsu fiyeda rayuwarsu zasu iyayin komai akansa da matarshi sarauniya ajeebah da yayansu guda uku maza biyu mace daya da yarima Aadhil se yarima Aahil se yar karamarsu gimbiya Afroza, farmakansu da kungiyar SATANIC dakuma kungiyar BAPHOMET shuuman kungiyoyine masu kashe rayukan al'umma domin su samu biyan bukatarsu matsafane sosai Kuma tushensu daga turai ne sundade suna son kwace kambun sarautar sarki abdud daar domin insuka sameshi bakaramin karfin iko da tsafi zasu samu ba so suke su mulki duniya da mugun nufinsu. Duk farautar sarki abdud daar dasukeyi yana sane dasu bedaga hankalinshi ba domin ya yarda da Allah shine merayawa Kuma me kashewa jakadiya abashiyya taso sarki abdud daar yadau mataki amma yakijin ta. Acikin yakin da akayine aka kashe matar sarki abdud daar ajeebah dakuma danshi yarima Aadhil wasu suka mutu wasu suka raunata dakyar sarki abdud daar yasamu yadinga buya awasu sassan duniya ganin duk inda yayi sesun cinmarne yasa kawai yafado duniyar bil adama neman inda ze boye kambun sarautar yakeyi amma yarasa harya fara tunanin barin jinsin bil adama fara firewa yayi ahankali domin gaba daya sunji mishi rauni ,dakatawa yayi lokaci daya sanadiyar jin kamshin turaren sauban dayayi mamakine karara yabayyana akan fuskanshi dama aduniyar bil adama ma ana samun yaya yan baiwa masu sauban ajikinsu tabbas nan ne yakamata yaje ya boye kambunshi domin yanada yakini kambun zetsira daga wayan can azzaluman bin direction din dayake jiyo kamshi yadingayi harya iso dakin mama dake kwance suna bacci hankali kwance duk dayasan abinda ze aikata zunubine amma babu yanda ya iya dolenshi yayi hakan inkuma ba haka suka samu kambun sarautar da akawa lakabi da ( JAAAZANA) tabbas zasuyi zalunci yanke shawara yayi yashiga cikin mama ganin ya macece yasashi tunanin anya zata iya tsira daga sharrinsu kuwa tunawa dayayi itadin yar baiwace zata iya tunkararsu tayakesu hartaci galaba akansu domin takasance me karfi biyu daga jaaazana yayi sama yayi wasu sambatu nan take yanarke yakoma kamar ruwa jijiyoyin jinin jikinta yabi yadinga zuba mata su harseda suka gauraya da jininta tsaff sauran daya rage kuma yasa mata acikin cikin mama tayanda shine zezama ruwan shanta yana gamawa yafito daga cikin, dolenshi yamusu bayani domin kuwa yarsu yanzu tarigada tazama shugabarsu dole duk daren dadewa zata tafi tabarsu dan karamin guguwa yatayar saboda yasamu sutashi aikuwa da sauri baba da mama suka tashi wato(sumayya da Muhammad) ganin farin balarabe atsaye akansu yana sanye da fararen kaya sukwal kayan anmai ado da lu'u_lu'u jikinshi se zubar da jini yakeyi adan tsorace suka mike tsaye suna adduah dan sunsan de wannan ba mutum bane suna tsayawa kuwa sarki abdud daar yazube akan guiwowinshi ya sunkuyar dakai alamar girmamawa wa shugabarsu datake cikin ciki cikeda mamaki baba yace " bawan Allah daga ina meyakawo wajanmu Allah yasa bada mugun nufi kazo mana ba " mikewa sarki abdud daar yayi yafara basu labarin shi wanene shi daga karshe yabasu labarin abinda yasa yazo wajansu dakuma ajiyar dayayi ajikin yarsu datake ciki dakuma mugayen kungiyoyin dasuke son kasheshi dakuma yaqarsu da yar cikinsu zatayi yahada dabasu hakuri sannan yamusu waazi da kaddararta ne tazo ahaka , inbanda innalillahi wainna ilaijiraji unnn babu abinda suke nanatawa kuka mama tafashe dashi cikin kuka tace " baka kyauta mana ba baka kyautawa rayuwarmu ba yar jaririyar dabataji ba bata gani ba wacce batama zo duniya ba zakasa rayuwarta atasgaro meyasa bakaje wajan wasu ba kazo gunmu wallahi kacuceni kuma allah seya sakamin nida nake mahaifiyarta kake kokarin rabani da yata zakasamin ita acikin rigamarku " ta karashe maganar tana kuka me tsuma zuciya riketa baba yayi yana rarrashinta, sosai sarki abdud daar yaji tausayinsu amma bashida zabi jaaazana yarsu ta zaba dole itace zata mulki masarautar nasminaya daga kai yayi yakalli sama nan take jakadiya abashiyya tabayyana itama jikinta duk rauni da manya_manyan masu mukamai a nasminaya kusan su 10 suka bayyana suna kallon mama suka zube akan guiwowinsu cikin girmamawa bayani sarki abdud daar yamusu yace ga" amanata kuma sarauniyarku tagaba ku kula da ita kubata dukkan kariya da rayukanku karku yarda kubar wani abu yasameta koda kuwa kuzaku rasa naku rayuwar" juyawa yayi ga abdud Shakur babban nahannun damanshi yace " kaida jakadiya abashiyya amanarta na hannunku ku kareta daga sharrinsu tanzarzar karda kusake waninku yayi gigin fada mata ko ita wacece harse lokacin karfin iko zefara bayyana ajikinta itada kanta zata gano ko ita wacece kuma tabar duniyar bil adama takoma masarauta domin baku kariya " yagama jawabinsa yaname juyawa gasu baba " yace iname nemar afuwarku daku yafemin dan banasan inmutu da hakkinku akaina dan Allah kuyafemin yarku tana cikin kariya babu abinda zesameta sekun tabka wani babban kuskure dazesa sufara farmakanta! Nan ne itakuma zata fara taka matakin rabuwa daku" cikin tsoro baba yace" menene wannan kuskuren dazamu kiyaye " domin su gaba daya sun gama tsorata dasu " budan bakin sarki abdud daar yace " ko wani irin hali zaa shiga karku yarda sarauniya takai dare awaje inkuma hakan yafaru to sukuma zasu fara farmakanta da dukkan karfinsu " jiki asanyaye baba yace zamu kiyaye in sha Allah kallon fuskanta mama sukayi wacce har alokacin kuka takeyi jakadiya abashiyya tace " sumayya kuyi hakuri ku gafarta mana dole zamu kasance daku har tsawon sanda sarauniya zata koma gunmu zamuta bata kariya da rayuwarmu " watsa mata harara kawai mama takeyi itakuwa abashiyya se murmushi takeyi mata ganin lokaci nakurewane yasa sarki abdud daar yace" bakuce kunyafemin ba dan nasan mutuwa zanyi ba lallai musake haduwa ba" hada baki sukayi wajen cewa munyafe maka duniya da lahira murmushi gaba dayansu sukayi, lokaci daya dukansu suka bace batt komawa masarautar sukayi suka samu anmusu taasa sosai shahada sukayi sukaci gaba da yaki cikin rashin saa tanzarzar yayi nasaran kashe sarki abdud daar har lahira, zagaye masarautar sukayi kaff basu samu jaaazana ba hakan yasa afusace sukabar nasminaya.
Bakaramin takaici sukayi ba da mutuwar sarki da matarsa da danshi ba sunji badadi sosai babu abinda yake kona musu rai kaman isukaga kujeran mulkinsa babu kowa akai tunsuna boye musu gaskiya har suka gaji jakadiya abashiyya da abdud Shakur ne suka fito suka musu bayanin kan cewa sarauniyarsu na nan zuwa garesu nan bada jimawa ba sunyi farin ciki dajin wannan maganar haka suka dibi dakaru fiye da dubu zuwa ga gidansu sarauniya domin bata kariya.
Wata bakwai ciff_ciff mama tafara nakuda aikuwa adaren ranan jakadiya ce ta karbi haihuwar ganin fuskan sarauniyarsu dakuma bayanta nadauke da zanen tambarin masarautar su (tattoo dake bayan fanan) yasata shiga cikin farin ciki mara misaltuwa daduk masarautar nasminaya, duk data kasance bakwai ni amma tafi wani dan wata taranma girma dakuma kuzari jakadiya ce tabukaci da abawa sarauniya nata dakin daban saboda suji dadin kula da ita dukda basaso haka suka ware mata dakinta daban ranan suna yarinya taci suna Fatima suka mata lakabi da fanan, ahaka tadinga girma dawasu abubuwan mamaki atare da ita Kuma koda wasa basa yarda tayi nisa da gida dazesa takai mangrib kansu daya da suhaima yar gidan kabiru.
___ tunda takai shekara 10 kuma wayan nan abubuwan al'ajabin suka dena bibiyarta kawarta daya dal itace amira, fanan nada shekara she uku aduniya mama tasake haihuwar ya mace suka samata ilham (auta) time din kuma su usman suka gama makaranta , haka fanan da Amira suka girma harsuka gama secondary school dinsu tare akasamo musu addimission a garkuwa school of health lokacin suna aji hudu a islamiyya, dake 2yrs program ne suka gama dawuri sukayi graduate batare da bata lokaci ba baban Amira yasamo musu aiki a asibitin specialist suka fara aiki, akaxo akayi auren anty firdausi, babban abinda su baba suka fara lura dangane da fanan shine babu wani namijin dayataba tunkararta da sunan yana sonta abun yadaure musu kai Sosai amma haka sukayi shuru.
Wannan shine takaitaccen tarihinmu cewar baba ba karamin girgiza sukayi ba dajin haka abin yabasu mamaki fiyeda yanda baa tunani gyaran murya me martaba yayi yace " tabbas fanan baiwar Allah ce wacce batasan komai ba ta cancanci girmamawa da farantawa kafin tabar duniyarmu domin ni inada labarin nan domin kafin sarki abdud daar yabar duniya Abdud Shakur yasameni yafadamin abinda yafaru dukda bansan waye sarkin nasu ba amma na tausaya musu matuka gashi bamuda hanyar taimaka musu sede nasa akata musu adduo'i! Nasan abdud Shakur ne alokacin da natafi aikin hajji nida iyalaina muka hadu dashi muka fara abokantaka be boyemin komai ba yafadamin shi jinni ne hakan bedameni ba mukaci gaba da zumunci duk sanda yasamu lokaci yakan kawomin ziyara ,ranar wata jummaa ne cikin tsohon dare yazomin amafarki naganshi acikin mawuyacin hali nan ne yake sanar dani abinda suke fuskanta yakuma bayyanamin kancewa sunyi sabuwar sarauniya ashe fatima ce Allahu akhabar " azaad de jinsu kawai yakeyi shidama tunda yaga fanan yagane bawai wani abu bane ajikinta itadince dakanta duk da bawai yayi believing da wayan nan abubuwan bane adduah yadingayi Allah yasa su shashantar da maganar auren. Haka suka cigaba da tattaunawarsu, Abba yace " ai dah nakowane Allah Ubangiji yakareta dakuma al'umman musulman duniya daga sharrinsu" amsawa sukayi da Ameen fara raba goro akayi ganin da gaske sukene yasa azaad cewa " Abba amma kasan dacewa akwai alkawarin aure tsakanina da aneesa " Abba zeyi magana me martaba yarigashi da fadin" karka damu aikana da daman dazakayi hudu" dariyar shakiyanci yaseer yasa. Shuru yamusu yana sake_saken aranshi, haka aka daura auren azaad muhammad mainasara da Fatima muhammad Umar akan naira dubu dari biyu lakadan ba ajalan ba nan take suka fara gaggaisawa da juna suna taya juna murna bakin ciki kamar zekashe azaad afusace yamike yafita a falon bin bayanshi doctor ammar da yaseer sukayi. Su ya Usman kuwa tunda sukaji wacece kanwarsu din gaba daya walwalarsu taragu barinma insuka tuna zata tafi tabarsu wata rana.
Bada umarni me martaba yayi akira mishi matan gidan kiransu ya al ameen yaje yayi suka fito danduk wainar da ake soyawa basu saniba zama sukayi suna gaida me martaba kallon fanan da har time din take kwance akan kafadar ummi yayi gyaran murya yayi yabude taro da sallama " Fatima