Showing 15001 words to 18000 words out of 45089 words

Chapter 6 - NIDA PATIENT DINA Book 1 Complete Hausa Novels by Mrs Hisham .txt

14 Jan 2025

3412

kunyane ga surkanki akusa Amma kina irin wannan abun murguda mishi Baki tayi Ina ruwanka ummi de tashi tayi abunta tayi sama anty Amina ma bayanta tabi yarage su zeenat ne afalon kallo takunna musu a TV tashan MBC action suna kallo areef ne yace " zeenat kaimana tashan MBC 2 nasan yanzu suna day breaking" to tace Dan batama San wani film bane shiga tayi aikuwa sukaga anhasko inda wata horror takecin kayan cikin wani ihu suka fasa da ita da FANAN yaseer da fawwaz mezasuyi inbanda dariya harda rike ciki kallon su kawai azaad yayi yadaga musu tsawa "wani irin haukane wannan" shiga cikin rigan nutsuwar su sukayi gashi areef yace baze canza Tasha ba SE rokonsa sukeyi karshema cillawa fawwaz remote din yayi.ganin hakane yasa FANAN da zeenat suka rungume juna da anyi abin tsoro suyi ihu mazan Kuma SE dariya sukeyi Banda azaad da aneesa datayi bacci tana kwance akan kafadar azaad wani wajan dayafi ko Ina tsoro aka nuna wani mutum horrorin suka kwantar suka dauko katon guduma sukayi kaca_kaca da kanshi yatarwatse wani irin ihu suka buga hannu FANAN takai tana ihu tana nuna TV wani irin spark TV yakeyi Yana kawowa Yana daukewa duk Basu luraba still hannun nata nasetin TV duk motsine da zatayi se tv yayi spark tun Basu ankaraba harsuka dawo da hankalinsu wajan itakuwa batama San tanayi ba dungule hannunta tayi da karfi tsabar tsoro tana kokarin rungume zeenat fat!fat!fat! TV yatarwatse yayi condem SE hayaki yakeyi zaro ido sukayi suka kalli TV sesu kalli FANAN ganin suna kallonta ne yasa tace meyafaru ya yaseer nuna mata TV yayi zeyi mata maganan abinda tayi azaad yayi saurin mishi signal da ido akan yayi shuru domin daga gani batasan tayi hakan ba Amma gaba Dayansu sun tsorata da abinda yafaru karasawa tayi kusa da TV tayi tace "subhanallhi meyasameshi yayi haka" bata gama rufe Baki ba jiri yadibeta zata fadi cikin zafin nama azaad ya rungumota kafin ya Ankara harta Suma daukanta chak yayi kamar yar baby ya kwantar da ita akan kujera ana kwantar da ita su ummi suka fito tana fadin " nikam yaran nan lafiya kuke mana ihu " sauka idonta yayi akan FANAN Dake kwance akan sofa dasauri suka karaso meya sameta fawwaz ne yabasu labarin abinda yafaru dukkansu mamaki yacikasu anty Amina ce tace" to me hakan yake nufi shafa kan FANAN takeyi ahankali Kuban ruwa Mika mata ruwa zeenat tayi shafa mata tayi afuska ajiyar zuciya tayi ta tashi tana rike kanta Dake mata azaban ciwo murya narawa tace "wayyo kaina zefita ya Allah,ummi kaina " kwantar da ita ajikinta ummi tayi "sannu kinji bari Kisha magani zedena to aneesa data danyi baccine tafarka tazo gun azaad baby natafi gida okay kawai yace mata kafin ta tafi ......








Tom semun hadu gobe in da Rai da lfy muhadu a comment section ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜ฒ






via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD


๐Ÿง‘โ€โš•๏ธ๐Ÿง‘โ€โš•๏ธ NIDA PATIENT DINA ๐Ÿฉบ๐Ÿฉบ


Story Written by (MRS ๐ŸŒน ISHAM ๐ŸŒน)








Da sunan Allah me rahama mejinkai ๐Ÿ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ














____________________________________________








Page 1๏ธโƒฃ6๏ธโƒฃ










Duka suna zaune cirko cirko sunyi shuru sunrasa abinyi ahaka har aka kira mangrib mazan duka masallaci suka tafi dakyar suka iya tashin FANAN da bacci yadauketa taimaka mata sukayi tamike tana rike da kanta dakin zeenat sukaje adaddafe tayi sallah tadawo tazauna shuru kanta akasa can Kuma kamar wacce aka mintsina ta tuna gida dawo Dede tayi aidasauri tafito dakin duk sundawo daga masallaci suna zaune afalo tafito gudu_gudu mikewa sukayi suma sun dauka wani abun ne yafaru ummi ce tariketa tana fadin" FANAN lafiya" arude tace " wayyo ummi yau nashiga uku Dama mangrib yayi innalillahi wainna ilaijiraji unnn yanzu mezan fada agida anhanani Kai dare awaje "takarasa magana idonta nazubo da hawaye yaseer ne yace "karki damu kizo sena kaiki inwa Yan gidanku bayani" kallonshi tayi tana girgiza Kai "ya yaseer bazaka gane bane daga zarran 5:40 yayi duk inda nake ana San ran dawowana wlh yau nasan mama da baba zasuyi matukar fushi Dani " tafashe da kuka dukkansu tabasu tausayi rungumeta anty Amina tayi tana rarrashinta, azaad da gaba Daya kukanta yadameshi tacika mishi kunne jiyake kamar zeyi hauka saboda ya tsani kukan mace kamar yarufeta da duka haka yakeji ummi tace" azaad daughter (anty Amina kasancewar itace yar farinta bata Kiran sunanta) yaseer Dani da zeenat zamuje gidansu fanan mukaita gida semu bawa iyayenta hakuri duka sunyarda da shawaranta .








Matukar tashin hankali da firgicine yabayyana akan fuskokin mama da baba gaba Dayansu babu Wanda yake cikin hayyacinsa duk sunfito compound din gidan suna jiran dawowar FANAN mama kam takasa jurewa inbanda hawaye ba abinda takeyi damin kuwa sukadai sukasan mezeje yadawo har inde tabiyo Daren nan tafito suhaima ce take rarrashin mama baba ne yace " nasan yata da gangan bazata tabayin abinda ze batamin rai ba da dawowarta awannan dare gwara ta Kwana aduk inda take domin nasan tana hannu nagari fitowarta awannan dare barazana ce ya Allah ka kawo mana sauki " ya al ameen,ya Usman, suhaima duk da hankalinsu atashe Amma kansu adaure yake meyene suke gudun faruwansa domin sun sasu aduhu shuru sukayi suka zubawa sarautar Allah ido.








Bayan sun idar da sallah isha ne suka fito da motoci Dan sukai FANAN gida itakam tsabar tsoron abinda zata tarar agida yahanata magana fitowa sukayi daga falon shiga cikin motar sukayi ummi da azaad da FANAN suna motor Daya SE anty Amina da yaseer SE zeenat motar yaseer ce tafarayin gaba, me gadi yawangale musu gate suna fita na azaad yabi bayanshi guguwane yatashi lokaci Daya Wanda yasa seda suka Dan tsaya domin jiran tsaqaitawansa yafi 10mint kafin yatsaya .














Hhhhhhhhhhhhhhhhhhh TAFITOOOOOO! TAFITOOOOOO SARAUNIYAR tafitoooooo tabayyana burinmu yakusa cika shugabansu ne yake magana Yana kallon madubin Dake gabansa mutum ne zaune akan kujera ta sarauta kansa da kaho๐Ÿ‘น๐Ÿ‘น Daya Baki Daya ja, katone Wanda zaa iya kiransa da basamude halittarsa rabi mutum rabi daba Yana sanye da jan Riga juyawa yayi ga mutanen sa dasuke irinsa sede dukkansu babu Wanda yakaishi girma daga musu hannu yayi kafin yace abinda muke Jira tsawon shekaru 18 yau yagabato garemu ihu suka farayi mara dadinji suna kururuwa shagali sukeyi bana wasa ba.












TANZARZAR nahango Yana zaune akan kujeran mulkinsa tare da Yan kungiyarsa dagaba Dayansu suke sanye da bakaken kaya jikinsu duk gashi๐Ÿ‘บ๐Ÿ˜ˆ Kai bakyaun gani kansu akasa idonsu arufe hannunsu ne dayake dauke da zuku zukun yatsu suka daga sama suna wani irin jujjuyashi suna lankwasashi kamar wasu masuyin rawa gaba Daya wajan yaturnuke da hayaki SE wani irin dariya sukeyi Wanda idan bil adama nawajan baze iya jurewa ba. Cikin wata irin murya me ban tsoro tanzarzar yace" tafito dole mune zamu mallaketa domin tana kunshe da dukan wata irin karfi da jaaazana atare da ita duk wani bayanai Yana dauke da ita tundaga lokacin datake ciki har izuwa yanzu abun da muke Jira yazo garemu hhhhhhhhhhhhhh.
















Wani irin gurine Daya kasance komai fari kamshine me dadin gaske ke tashi bana tunanin nan duniyar mutane ne kowa tafiya yakeyi akan iska masu firewa ma sunayi furanni ne tako Ina masu gwanin burgewa Wanda bazakaso ace inde kana wajan nan kabar gunba hango tarin mutane nayi atare Wanda a iya hasashena sunfi karfin dubun nai karasowa nayi sanye suke da fararen kaya komai nasu fari bantaba kallon masu kyau da kyawun halitta irin suba mazansu da matan su , wani irin kujera nagani Wanda yake na zinari yasha ado da gwala gwale wani irin sheki yakeyi wani tsohone yataso me matukar kyau yatsaya agabansu Yana fuskantar gaba Dayansu kafin yafara dacewa " Ni Abdul_shakur Ina me sanar daku yaune ranar da SARAUNIYAR mu ta taka mataki nafarko arayuwarta Wanda ze kusantota damu sannan ze kusantota da wayancan azzaluman makiyanmu nasan yanzu zasu fara kokarin Kaimata farmaki saboda yanzu ne suke da iKon yimata abinda zasuyi dukda ita haryanzu bata gama sannin wacece itaba Kuma menene take dauke dashi ba batasan ma yazata fara amfani da karfinta ba Amma baze dau lokaci ba jaaazana ze bayyana agareta dolene mukareta da iyayinmu " kammala magana yayi fuskanshi dauke da murmushi dakuma damuwa (iKon Allah wannan aisede aljani Taya lokaci Daya Abu biyu zasu bayyana afuskan mutum Tabb nide nayi nan)๐Ÿƒ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ๐Ÿƒ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ๐Ÿƒ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ.










Tafiya suketasha akan titi kwatance gidansu tayiwa azaad har suka iso kofar gidansu fitowa sukayi daga motar yaseer ne yayi knocking gate din FANAN buya tayi abayan ummi ya Usman ne yabude sukayi musabaha "dama Baki kukayi Muna tare da FANAN " cewar yaseer ya Usman yanajin an ambaci FANAN yace "Bismillah kushigo " dasauri yakoma yafada musu sunyi Baki shigowa sukayi da sallama abakinsu falo suka shigo ummi ce tashigo akarshe FANAN Dake bayanta ne tayi sallama ahankali gaggaisawa sukayi ganin yanda FANAN ta takurene yasa mama tamata alama datazo mikewa tayi taje gun mama ta rungumta cikin muryan kuka tace " Dan Allah kuyafemin nasan nayi muku laifi nakarya dokan dakuka gindaya min " shafa bayanta mama takeyi " kedin yace me biyayya munsan bazaki tabayin abinda ze bata mana ba kedin ta musamman ce yata" zuba musu ido mutanen falon sukayi suna jinjina irin soyayyan Dake tsakanin uwa da yarta gyaran murya ummi tayi cike da Kamala tafara Basu labarin abinda yafaru daga spark din da TV yayi harzuwa suman datayi har izuwansu gidan nan bakaramin tashin hankali suka shigaba abinda suke gudu yafaru baba ne yamike yafara safa da marwa Yana nanata Kalmar innalillahi wainna ilaijiraji unnn gumine yawanke mishi fuska kafin yakalli mama yace" mamansu abinda muke gudu yafaru abinda muke tsoron tsawon shekaru 18 yafaru ya Ubangiji Allah katarwatsa mumunar kudirinsu akan wannan baiwar taka dabataji ba bata gani ba ka tsareta da tsarewarka " amsawa sukayi da Ameen ya hayyu ya qayyum duk da yasasu aduhu komawa yayi yazauna fanan ce ta rarrafo gabanshi tarike hannayensa" baba Dan Allah kutaimakamin ku fadamin gaskiyar abinda yake faruwa" shafa fuskanta yayi karki damu lokaci yariga da yazo Amma sekin Jira kadan duka mutanen falon jikinsu yayi sanyi duk da Basu San meyake faruwa ba Amma alamu yanuna wannan ahalin suna cikin hard time.


Azaad cikin cool voice yafara magana" idan badamuwa zamu iya sanin abinda yake faruwa" girgiza Kai mama tayi tace" bazeyu muyi muku bayani ba domin yin hakan zezama bayyanar FANAN ne cikin sauri da karfi" kamarya bayyanar FANAN bayan gata nan abayyane agabamu Muna kallonta zeenat takarasa maganar tana binsu da kallo duk da basa cikin yanayi me dadi Amma hakan be hanasu murmusawa ba ummi ce tamata signal da ido akan tayi shuru mama ce tamike takira FANAN da suhaima biyota sukayi kitchen drinks tabasu dasu fruit a trays suka kawo falo Bismillah suka musu Dan tabawa sukayi kadan kafin ummi tace" yakamata mu gabatar muka da kanmu sunana Aysha Muhammad azaad mainasara sannan tanuna anty Amina itace first born Dina sannan tanuna azaad Shima danane shine nabiyu Wanda FANAN take kulawa dashi se wannan tanuna zeenat itace auta ta akwai yayyunta maza guda biyu a gida SE wannan Shima Dana ne Dan kawata ne Kuma abokin azaad tun suna yara " Masha Allah, Ubangiji Allah yaraya miki zuriyarki yakara hada kanku babane yake musu adduah duka falon suka amsa da Ameen. Ganin dare nayi ne yasa suka ce zasu tafi sallama sukayi mazan suka rakasu har bakin motar su suka tafi.




Bayan sun dawo ne baba yake ma FANAN Yan tambayoyi "mekikeji ajikinki yanzu karki boyemin" kallonshi tayi cikin nutsuwa tace " banajin komai baba " ajiyar zuciya suka sauke atare shida mama sude sunzuba musu ido kawai tunda sunki fada musu komai, to shikenan kowa yaje yakwanta dare yayi seda safe sukayi suka shige daki FANAN da suhaima hira sukayi kafin suka kwanta tare dayin adduah bacci........


















Meye FANAN take dauke dashi ? Menene jaaazana dasuke son karba daga gareta? Suwaye wayanda suke shirya farmakan FANAN??? Shin wasu irin kungiyoyi ne wannan??? Meye abinda Tanzarzar yake bukata atare da ita?????? Taya akayi fanan takasance sarauniya ๐Ÿ‘ธ????????








Kubiyoni domin kuji amsoshin tambayarku senajiku a comment section ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜






















via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD


๐Ÿง‘โ€โš•๏ธ๐Ÿง‘โ€โš•๏ธ NIDA PATIENT DINA ๐Ÿฉบ๐Ÿฉบ




Story Written by (MRS ๐ŸŒน ISHAM ๐ŸŒน)










Da sunan Allah me rahama mejinkai ๐Ÿ™ Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen ๐Ÿ™๐ŸŒน๐ŸคŽ














Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina Allah yabar zumunci ๐Ÿฅฐ๐ŸคŽ














____________________________________________












Page 1๏ธโƒฃ7๏ธโƒฃ












5:20am suka farka daga bacci sallah sukayi bayan sun gama azkar ne FANAN ta tashi ta haye gado taci gaba da bacci saboda bacci takeji sosai suhaima ce tafito tayi aikin gidan gaba Daya tamusu breakfast harsun fara karyawa mama tace "suhaima Ina fanan din take " Takoma bacci cewar suhaima Jin hakan yasa Basu Kara magana ba sukaci gaba da karyawa , har karfe 11 tagota bata tashi ba time din su baba duk sun fita yarage daga mama SE suhaima da fanan Dake bacci. Tashi tayi daga bacci tana salati da Mika zuro kafanta kasa tayi gashin kanta duk ya babbaje toilet tanufa bayan 7mint tafito daure da towel gaban mirror tazo ta shafa man gashi tasa cum ta tajeshi ta hadasu guri Daya ta daure Mai Tashafa ajikinta sannan tadauko kaya wando ne falazo me manyan fulawa SE riga body hook ja tasa hula Baki bakaramin kyau tayi ba wayarta tadauka takunna ganin time din tayi "wai gaskiya yau nayi bacci sosai" falo tafito tasamu mama da suhaima gaishe da mama tayi kafin tazauna sallaman Amira sukaji tashigo gidan afalo tasamesu tagaida mama, besty ykk suhaima ya gajiya zama tayi suna hira dasu tana rike da yar karamar bakar jaka ahannunta kallon mama tayi tace " mama dama nazo in tambayeki ne FANAN zata rakani gidan anty fati hajiya ce ta aikeni " mama har cikin zuciyarta bataso FANAN tafita Amma kawai tace "to shikenan Amma karku Dade kunji " to sukace suhaima ganin zasu tafi subartane yasa tace nima zani bari in dauko hijab dina" sallama sukawa mama suka fito su uku suna tafiya suna hira Amira ce tace " bakusan meyafaru jiya ba hajiya ta aikeni cafene nayarda kudin duka dakyar na iya dawowa gida Dan banma San yazanyi ba" suhaima tace"wai garin Yaya haka katuwa Dake kika zubar da kudi " lallai kam to ai tsautsayi bata yanda bata kamawa Kuma Allah yayi ba rabo bane " cewar FANAN "ato fada mata de sukaci gaba da tafiya suna hira , wata corner suka sha aikuwa turus suka tsaya sakamakon abinda suka gani karnuka ne guda 3 suna kwance abinsu , tsoro ne yarufe su "wayyo Allah kare yazamuyi mu wuce nan Dan Allah gashi hanyar dayane "amira tagama magana tana rike hannun FANAN Da karfi FANAN cire takalmanta tayi tarike ahannun tafara fadin " karkuja abinda zesa karnukan nan subimu muwuce kawai karma ma mu nuna mungansu kundeji Ina" takarasa maganarta tana kallonsu to shikenan tafiya sukeyi sanda sanda kamar wasu marasa gaskiya harsun kusa wucesu suhaima ta dantabo Amira, ke Amira kindauka karene aikuwa ihu tafasa tasa gudu karnukan๐Ÿฆฎ na ganin haka suka fara haushi kan kace me sun bisu gudu sukeyi kamar kafarsu ze fita fanan kam da take rike da takalmanta ko juyawa batayi ba balle ta kallesu gaba Dayansu rabuwa sukayi kowa hanyanta daban tabi Ashe karnukan ma sundade da Dena binsu Basu sani ba Amira ce tajuya taga basa binta tsayawa tayi tana Maida numfashi hango bishiya tayi taje tazauna agun tana tunanin inasu FANAN sukayi, ke suhaima dataga gudun baze kaita ba kawai tafada wani gida suna ganin tashigo da gudu Suma sukashige daku nansu a tamanin๐Ÿ˜‚ can wata tace baiwar Allah meyake faruwa ne awajan cikin Maida numfashi tace "wlh karnuka ne suka bimu "sake Baki sukayi suna kallonta yanzu akan kare kike irin wannan gudun lallai kam sannunki fitowa tsakar gida sukayi Daya daga cikin matan gidan taleka waje tace" sunkoma bakowa awajen sallama tamusu tafito tana ta leke_leke tafiya tafarayi yanzu yazanyi innemo su Amira gashi nabar wayata agida yanke shawara tayi gwara in koma gida seyafi min takama hanyar gida , gudu takeyi kamar Wanda Zaki yake bi harta hau kan titi bata sani dukda titin shuru ba motoci, tafiya yakeyi a motor kamar walkiya tagilma wul๐Ÿƒ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ ta gabanshi taci gaba da gudunta birki yataka Yana mamakin wacece haka take wannan uban gudun duk yanda akayi wasu ne suka biyota, bin bayanta yayi da mota harya iso kusa da ita da sauri yafito gashi taki tsayawa taku uku mekyau yayi yariko hijabinta yajawota baya aikuwa kamar wacce take Jira Takoma bayansa ta kankameshi tana fadin " kataimakeni zasu kamani " sa hannu yayi yajawota yadawo da ita gabanshi zaro ido yayi ganin itace " ke Meye kikeyi akan titi kamar wata mahaukaciya kalan motar yabigeki ko " Jin daddadar muryanshi ne yasa tadago ido cikin muryan tsoro tace " Mr azaad wlh karnukane suka bimu zasu cije mu Dan Allah kataimakeni " zuba mata ido kawai yayi tsaban takaici yarasama bakin magana yarinyar nan da kanwarshi ce irin dukan dazemata seta koma hankalinta yanzu dama duk uban gudun nan datakeyi WA karene ba abinda yakeyi Banda jefa mata harara gashi a ido de kamar wata me hankali Jan hannunta yayi yaje yabude motar yajefata ciki kafin yashigo yaja be tsaya Ako inaba SE akofar gidansu. Ahankali yace "saukamin a motar tunkafin in karkaryaki " dasauri tasauko tana nagode Mr azaad kaceci rayuwata tana magana tana haki shiga gida tayi abunta , shide lamarin yarinyar nan mamaki yake bashi daga gani an sakalta tane tsaki yaja kafin yaja motar shi yayi gaba.




Tundaga tsakar gida takejin muryan Amira da suhaima suna bawa mama labarin abinda yafaru shigowa falon tayi tana galla musu harara " kufa kwata kwata bakwajin magana seda nace mutafi ahankali Amma seda kukasa suka bimu" zama tayi taci gaba da Maida numfashi"nikam garin Yaya muka rabune kowa yadawo daban daban " inji suhaima aikuwa dariya suka fashe dashi ba qaqqautawa seyanzu ma suke tuna irin gudun dasukayi dariya sukeyi kamar cikinsu zeyi ciwo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login