Showing 27001 words to 30000 words out of 63876 words
Chapter 10 - JAWAHEER HAUSA NOVELS BY MARYAM OBAM.txt
tashi ta amsa tare da ajiyewa kayam fruit ne dasu kaji gassasu, mum taba jawaheer kaza daya ta mika ma mlm da abubakar mlm yace a'a shi tare da matarshi zaici dariya duka sukayi m samir shima yaci kazan yana ta fadin kazan akwai dadi suna tamai dariya yanda yake ta santi, dad yace jawaheer kinji sauki koh? Tace eh dad sai dai bana jin dadin komai amma ganin mum da kakana yasa naji dadi sosai, kowa ya fahimta abunda take nufi wato shiryawan mum dinta da mahaifinta yasa taji dadi sosai, kowa dake dakin saida yaji tausayinta tare dayi mata fatan itama Allah ya hadata da iyayenta, dad yayi murmushi tare da fadin Allah ya kara miki lafiya bari muje mu kwanta dare yayi, duka kowa ya fita amma banda m samir da mum, m samir yana son yi mata magana amma bazai iyaba dan mum na wajan haka ya fita tare da fadin good night, ji tayi kaman ta bishi, koda ya fita ya tarar dasu a waje, abubakar yace ma m samir a gidanshi zai kwana, security dinshi sukace ma abubakar dan Allah yayi hakuri an basu tsaronshi ne idan wani abu ya faru dashi zasu shiga matsala, duk yanda abubakar yaso m samir ya kwana a gidanshi haka ya hakura akan gobe zasu hadu, koda m samir ya koma hotel din daya sauka wanka yayi ya kwanta amma bacci yaki zuwa, sai juyi yake tayi gaba daya tunanin jawaheer yake tayi wanda ya hanashi sakat, ya rasa dalilin da yasa yake tunaninta har yake kokarin hanashi bacci abunda bai tabayi ba kenan ko sonia da yake so baya jinta kaman yanda yake jin jawaheer a yanzu, dan tsaki yayi tare da fadin tausayinta nake ji sai yasa nake tunaninta.....
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 29-30
Haka yaita tunani kala2 yayinda yake ta tursasa ma zuciyarshi akan tausayinta yake kawai, wasa2 har wajan karfe biyu amma babu alaman bacci a idonsa sai tunanin jawaheer gaba daya ma kanshi ya kulle yama rasa mai yake ji a kanta, ganin babu baccin a idonsa ga tunanin yaki barinsa yasa ya tashi ya shiga toilet yayi alwala, sallah yazo yayi tare da roqan Allah akan ya zaba mishi abu mafi alkhairi a rayuwanshi, ya dauki lokaci mai tsawo yana roqan Allah akan ya zaba mishi abu mafi alkhairi, kafin ya tashi ya koma gado yana kwanciya bacci ya daukeshi.
Ta gefen jawaheer ma haka abun yake bata so m samir ya tafi ba, ita inda so samu nema dashi ya kwana da ita amma sai dai hakan bamai yihuwa bane, babu abunda take sai tunaninshi tare dason qara ganinshi, duk da sau da yawa zuciyarta tana kara nuna mata tayi baya dashi dan ba sonta yake ba, amma ta kasa, a yanda takeji inda tana da halin cireshi a ranta data dade da cireshi, itama haka taita tunani har bacci barawo yayi awon gaba da ita.
Jawaheer tunda ta farka tayi sallah asuba, bata koma bacci ba, har adda tazo da kayan abinci ita da mlm, jawaheer ta gaidasu cikin girmamawa inda suka tambayeta ya jiki ta basu amsa da fadin da sauki, dad dinta ne ya shigo cikin dakin yana fadin mai jiki anji sauki kenan? Murmushi tayi tare da fadin alhmdlh dad, dai dai lokacin dr ya shigo dakin tare da wata nurse, jawaheer na ganin dr ta tashi tare da fadin dr yau zani gida koh? Dariya dr din yayi daya kafeta da ido yace a'a ai kya bari ki dan kara jin sauki koda nanda sati biyu ne, ido ta zare tare da fadin ni kam yau gida zan tafi dan na warke sosai, dr yace shikenan zaki iya tafiya amma ki dinga kiyaye wa ki rage yawan tunani, tace insha Allah, murmushi yayi tare da kallon dad yace alhaji Allah ya kara mata lfya, jiki yayi sauki komai yayi normal, dad yace hakane mun godema Allah komai yayi kyau, dr ya kuma waigawa wajan jawaheer yace zanzo gida inji mai kike tunani haka har ya miki yawa kika fadi lokaci daya, mlm yace likita ni take tunani amm zanyi hakuri in aureta haka, duka suka sa dariya, jawaheer sai tunanin maiya hana m samir zuwa take tayi, haka suka fara shirya kaya har suka fitar da komai aka bama jawaheer magani Suka shiga mota, direct gidan adda suka nufa, koda suka isa jawaheer dakin adda ta shiga ta kwanta dan bata son wata fira a halin yanzu tafi jin dadi ta ganta tayi shuru, tunawa tayi da wayanta dan haka ta fito ta dauki hand bag dinta dake falo, mum tace mata yauwa jawaheer maza kizo kiyi wanka saiki kwanta gaba daya, tace to mum, dan shuru tayi can tace mum kayana basa nan suna hotel din da muka sauka, mum tace bude akwatina ki dauki zani anjima ko gobe kyaje ki kwaso kayan bata kara magana ba ta nufi dakin da kayan mum suke ta dauki zani ta nufi bayi dan tayi wanka, bayan ta fito daka wanka daka ita sai saurin kirji sai kayan data cire a hannu, kasancewan bayin gidan a waje yake, tana saurin ta shige ciki sukaci karo wanda shima a dai2 lokacin ya shigo gidan kuma bayin daka shi sai kofar gidan, tsayawa tayi taga dawa ta buge ganinshi tayi yana mata murmushi itama bata san lokacin data sake murmushin ba, sai taji kaman tayi hugging dinshi, a hankali ya furta mata ya jikin ki? Tace da sauki, yace naje hspt akace min kin dawo gida, ban tashi da wuri ba yau jiya banyi bacci da wuri ba ina ta tunani, tace tunani kuma? Yace eh, shuru tayi tana dan nazari shi kuma idanshi na kanta, katseta yayi da fadin ina mum? Tace tana ciki shiga yayi itama binshi tayi a baya tana shiga tayi daki, mai ta shafa cikin kayan mum ta dauko jallabiya tasa duk da ya mata yawa amma haka tasa, tana zaune tana jiyo firan mum da dan nata, uncle abubakar ya shigo, nan firan ta canza zuwa na ball, mum tace bada ita ba, jawaheer kwanciya tayi amma ba bacci takeyi ba, kawai tana tunani ne, tunda tasan basu mum bane iyayenta take jin wani iri saita tsinta kanta da rashin sakewa kusa dasu, harta dad bata sakewa in yana wajan sabanin da, wani zubin in abun nata ya tashi haka zatai ta shagwabe ma dad dinta wanda a yanzu bata jin zata iyama fira dashi kaman da, wani guntun hawaye ne ya zubo mata, babu komai a ranta sai bakin ciki tare da takaicin mai yasa basu kasance iyayenta na gaskiya ba, mum ce ta shigo dakin hannuta dauke da tray, ganin tana kuka yasa mum tayi saurin karasawa wajanta tana fadin jawaheer mai ya sameki?? Tayi saurin goge hawayen tare da fadin babu komai mum, ido mum ta kura mata tare da fadin jawaheer nasan abunda kike tunani bazai wuce kice bamu bane iyayenki, tun ranan da kika san haka kika rage yin magana damu, kika daina sakewa a gaban mu, jawaheer wlh dai dai da rana daya ban taba cireki a raina ba, har gobe ina miki kallon yar dana haifa a ciki na, mai yasa kema ba zaki daukemu a matsayin iyaye ba jawaheer?? Kuka jawaheer ta kara fashewa dashi tare da rungume mum tana fadin ba haka bane mum har gobe kune iyayena kawai ina takaicin daya kasance baku kuka haifeni ba, amma ban taba canzaku daka matsayin da kuke ba, mum tace toh kiyi shuru ga abinci kici sai kizo muje falo ayi fira dake, bata musa ba ta dauki cup din tea da white rice ns stew ta fara ci, mum tana zaune harta gama ci, duk da ba wani da yawa taci ba, amma tasha tea din da yawa, mum ta dauko mata magani tasha, sannan suka fita falo, tunda ta fito idanshi na kanta harta zauna, akan kujeran dake kallon nashi, gaida uncle abubakar tayi ya amsa tare da tambayanta ya jikin nata? Tace da sauki alhmdlh, murmushi yayi tare da fadin badai ciwon bane yasa kika rame kayan naga ya miki yawa, itama murmushin tayi wanda ya kara fito mata da kyanta, tace a'a kayan mum ne nawa yana hotel din da muka sauka, adda ce ta shigo da kayan jawaheer tana fadin ga wasu da kika canza a asibti na wanke miki su, tace lah adda wanki kuma, keda kanki? Adda tace gasu maza kije kisa sai kuje ki dauko sauran, bata musa ba ta tashi ta nufi daki dan canza kaya, jim kadan sai gata ta fito cikin hijab, ido m samir ya bita dashi dan ba karamin kyau hijab din ya mata ba, mum tayi murmushi tace jawaheer hijab na miki kyau amma bakya son sawa, murmushi tayi, tana kokarin zama taji muryan m samir na fadin muje mu dawo, dan haka bata karasa zaman ba suka fita, security din na ganinsu suka bude musu baya suka shige, kai tsaye hotel din suka nufa har suka karasa babu mai ma dan uwanshi magana, har suka shiga ciki ta nufi dakin data sauka ta fara hada kayanta tana cikin hadawa ya shigo dakin ya hade hannunshi biyu a kirjinshi ido ta dago suka hada murmushi ya sakan mata tare da nufanta ya zauna kusa da ita, ita dai bata cemai komai ba tana ta hada kayanta, hannunta ya kamo tare da janyota jikinshi kirjinta ya fara bugawa da karfi fuskanta ya dago suna kallon juna ido ta rufe da sauri amma tana jin saukan numfashin shi, jin muryanshi tayi yana fadin kina fushi dani ne? Ido ta bude da sauri ganin har yanzu ita yake kallo yasa ta kara rufe idonta murmushi yayi tare da fadin sunanta jawaheer bata amsa ba haka bata bude ido ba, yace mai yasa kike fushi dani, ido ta bude tare dayin kasa da kanta, ganin haka ya kara janyota jikinshi yace fadamin, tace niba fushi nake dakai ba, yace to mai yasa bakya son yin magana dani yau? Tace ba haka bane , yace toh miye? Dariya ta saki tare da fadin babu komai kawai bana son yin magana ne yau, yace har dani bakya son yin magana? Kai ta daga alaman eh, murmushi yayi tare da sakinta ya tashi tsaye yace ok kiyi hakuri da takura miki da nayi akan saina miki magana, in kin gama ki sameni a mota, da sauri tace to wazai fito min da kayan? Yace keda kanki mana tunda baki son a dameki, murmushi tayi tare da tashi tayi hugging dinshi ta baya tace sorry ba haka nake nufi ba, kana daya daka cikin mutane masu muhimmanci a rayuwa na, koda zan zauna daka ni sai kai bazaka taba gundura na ba, waigowa yayi tare da fadin really? Kai ta daga mai alaman eh, hancinta yaja tare da fadin zo in tayaki hada kayan, zama yayi suna ta hada kayan har suka gama, ya kira masu aikin hotel din suka fara fitar sa kayan zuwa mota, suma fita sukayi ya kalleta yace yau kinyi kyau, tace nagode, bayan sun shiga mota yace ma jawaheer ina ake saida sim? Dariya tayi tace nima ban taba zuwa state din nan ba, amma muje mtn office, tace ma driver suje mtn office yace ok, hannunta ya kamo tare da fadin kema zaki canza naki sim din, da sauri ta dago tana kallonshi tare da fadin saboda me?? Shuru ya mata ba tare daya bata amsa ba, har suka karasa mtn office, fita sukayi suka shiga wani office aka kaisu daka shi sai jawaheer, jim kadan sai ga wani ya shigo yana bama m samir hannu tare da fadin ban taba tunanin zan ganka ba a rayuwa yau gani gaka, m samir yayi murmushi mutumin yace plz zamu iya daukan hoto? M samir yace ok nan mutumin ya fara daukansu, sannan ya tambayi m samir mai yake so yace sim card guda biyu sannan yana son number shigen iri daya, mutumin ya dauko sim biyu ya bashi, special number karshen ne kawai ya ban banta, daya 7 daya 8, nan aka mishi register dayan ma da sunanshi akayi, har aka gama suka fito, nan mutane suka fara ihu tare da daukanshi hoto, dakyar security dinshi suka fitar dashi sukai mota, suna cikin tafiya ya kalli jawaheer yace bani wayanki? Kallonshi tayi ba tare da tace mishi komai ba kota miqa mai, hannu ya miqa mata ganin haka yasa ta bashi wayan, hannu yasa a kunnenta ya ciro dan kunnenta ya ciro abun sim din, ya cire nata yasa mata sabon daya, shima yasa daya a nashi, sai daya gama ya miqa mata wayanta tare da karya sim dinta, da ido ta bishi tana son yi mishi magana amma taga ya daure fuska ganin haka yasa tayi shuru tare da mamakin mai yasa ya mata haka, bai karayi mata magana ba har suka karasa gida, security dinshi suka fara shigar mata da kayan, itama ko kallonshi batai ba tayi cikin gida dan karya mata sim da yayi ba tare da wani dalili ba abun ya bata haushi, yana kallonta ya bita da murmushi dan yasan taji haushi, amma shi daya yasan dalilin da yasa yayi hakan, koda ta shiga a tsakar gida taga adda ita da mlm, bayan ta musu sannu da gida, tace ina mum? Adda tace ta fita ita da babanki basu dade da fita ba, m samir shima ya shigi gidan, tana ganinshi tayi ciki, adda tace toh ni yanzu bajin yaranka nake ba, ta kwada ma jawaheer kira tazo da sauri, adda tace taya zaki shige ciki bayan kin san mu bama jin turanci, fada mishi ya tayaki shigar da kayan, kallonshi tayi wanda shima itama din yake kallo yana mamakin fushin da takeyi dan an karya mata sim, tace ance wai ka tayani shigar da kaya, murmushi yayi tare da daukan akwati itama ta dauki wasu suka shigar dasu haka har suka gama kwashewa mlm ya fita daka gidan dan komawa kasuwa, itama adda ta nufi dakinta, ya rage daka m samir sai jawaheer a falo wanda sukai shuru su dukansu, tashi yayi ya matso kusa da ita, yace mai yasa kike fushi? Mai akayi miki? Tana son ta tambayeshi mai yasa ya karya mata sim amma saita kasa dan ya mata wani irin kwarjini, ganin tayi shuru yace saboda na karya miki sim kike fushi koh? Toh idan na kwace wayan fah????........
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 31-32
Kallonshi tayi ya sakar mata murmushi tare da daga mata gira, yace jawaheer banso ana damunki sai yasa na canza miki sim nd kuma ban san any abu da zai daga miki hankali kin san abubuwan da suka faru na sanin basu mum bane iyayenki kin san tunda maganan nan ta fito kowa zaiji, nd kuma nasa wasu za suyi ta kiranki dan suji maike faruwa, banso wani koh wata su daga miki hankali har zuwa sanda zamu gano inda iyayenki suke, hannunta biyu ya kamo ya matse tare da fadin sai yasa na karya layin, murmushi tayi tare da fadin banyi fushi ba, kawai na dan damune akan mai yasa ka karya sim din ba tare da kamin bayani ba, amma yanzu da naji komai sai naji hankalina ya kwanta komai kuma ya wuce, yace dat my sister, yaushe zamu tafi abuja? Tace ba kace sai anyi kwana biyu ba,yace yes inaso in saba da kakanninmu gashi kuma bana jin yaranku, tace bari in fara koya maka, yace yauwa amma ba'a nan ba, kizo mu tafi waje, tace ok bari in canza kaya, yace ok ki sameni mota, daki ta shiga tasa wata jallabiya tare da yafa gyalen jallabiyan, ta nufi dakin adda taga tana bacci dan haka ta fita kawai tana shiga mota taga anja bata cemai komai ba har suka isa wani hadaddan restaurant babu kowa sai su kadai daka gani yasa an kama mai wajan ne duka, shiga sukayi suka zauna, kallonshi tayi tace mai za muyi a nan? Yace abinci zanci kin san ba komai na iya ciba, nd ke kuma baki damu damai naci ba, tayi narai narai da ido tace nifa kasan bani da lafiya ba yau na dawo gida bama, murmushi yayi yace hakane, my baby da sauri ta dago ta kalleshi hada ido sukayi ita tana mamakin sunan daya kirata dashi, shiko yana mamakin mai yasa kullum jawaheer take kara kyau, idan yaga ta mishi kyau yanzu anjima kuma sai tafi kyau,hura mata fuska yayi tayi firgit tasa hannunta ta rufe fuska tana dariya, dai dai lokacin masu saida abincin wajan suka zo suna tambaya mai za'a kawo musu, fada musu yayi ita tace tuwon semo miyan kuka, suka tafi, basu dade ba suka kawo abincin, sannan suka roqeshi akan su dauki hoto dashi, bai musa ba haka ya tashi suka dauka, suna ta murna, zama yayi yana kallon abunda jawaheer zata ci, lokaci daya kuma yayi dariya yace jawaheer miye haka? Tace mene? Yace wannan abun da zaki ci miye? Tace tuwo, kasa fadan sunan yayi, tace ka gwada ci akwai dadi sosai, kai ya girgiza alaman a'a, murmushi tayi ta fara ci, mai yakon yaci nashi saiya tsaya kallonta yanda take ci sai yaji abun ya burgeshi, dan haka shima yasa spoon cikin tuwan yaci ido ta kura mishi, taga ya cinye ya kara ci wasa wasa sai gashi ya cinye tuwan duka, saida ya gama yace ashe akwai dadi sosai dariya tayi tace abincin mu yana da dadi, murmushi yayi sannan ya fara cin farfesun kazan da aka hado mata dashi bai wani ci da yawa ba ya ajiye tare da kallonta yace ban taba cin abinci mai yawa irin haka ba, dariya tayi tace dan wannan abincin shine mai yawa? Yace eh mana, yace toh a fara koyamin hausa, tace mai kake