Showing 39001 words to 42000 words out of 63876 words
Chapter 14 - JAWAHEER HAUSA NOVELS BY MARYAM OBAM.txt
ne yazo a bazata, yace bakomai da fatan anga sako na, dan shuru tayi kafin tace uhm, murmushi yayi sannan yace ina fatan za'a bani dama? Tace Allah ya taimaka ya shige mana gaba, wani irin dadi yaji tare da fadin kenan an bani dama, kai yau ina farin ciki Allah ya dai daita mu, bata ce komai ba sai murmushi da tayi, wani lecturer ne ya shigo tace ina zuwa zamu fara lecture yace ok tare da kashe wayan, sai lecture ake musu amma ita sam bata san mai ake fada ba, domin tayi nisa cikin duniyar tunani ba komai take tunani ba sai na amince ma dr akan yaci gaba da nemanta har Allah yasa su fahimci juna tayi hakan ne da zuciya daya domin tana da burin ta sami miji tayi aure dan ta cire m samir a ranta duk da tun jiya take ta kokarin tusa ma kanta kin shi amma hakan ya faskara, lallai koda banga mum dina ba indai muka fahimci juna dole inyi aure in huta, ji tayi ana mata magana, wata yarinya ce kana ganinta kasan suma suna da arziki, jawaheer firgit tayi taga lecturer din ya fita tace kai ashe har an gama, yarinyar tayi murmushi tare da fadin sunana zarah, yau na fara zuwa lecture saboda nayi ciwo sai nayi differing da yanzu ina 3lv amma yanzu ina 2lv, jawaheer tace Allah sarki Allah ya baki lfya, murmushi zarah tayi tare da fadin baki fadamin sunanki ba, tace jawaheer murmushi zarah tayi tace suna mai dadi zarah ta amshi no din jawaheer tare da fadin in akwai lecture zata dinga fada mata, sannan tace duk abunda jawaheer bata gane ba ita zata dinga nuna mata, nan jawaheer tayi godiya tare da fadin an gama lecture din yanzu? Zarah tace a'a akwai wanda zai zo karfe hudu, jawaheer tace kai bari inje inci wani abu yunwa nake ji, zarah tace muje tare toh, fita sukayi tare suka je wani restaurant a cikin skul din, fried rice jawaheer tace a bata, ita kam zarah snacks ta amsa da drinks suna ci suna fira har suka gama, fita sukayi suka zauna wajan wata bishiya ko wacce na danna wayarta, wayan jawaheer aka fisge daka hannunta da sauri ta dago taga ko waye khalil ta gani dariya tayi tare da fadin bros mai kazo yi? Yace zo muje ki gani, zarah ta dago kai tare da kallon khalil gaidashi tayi jawaheer tace bros dina ne, tace ashe yayanmu ne, dariya yayi sannan yace ma jawaheer ga mota can kije ana jiranki ni bari in zauna a nan muyi fira da zarah, dariya tayi sannan ta nufi motar dan a zaton ta dad ne, tana budewa taga m samir zama tayi a cikin motar tare da rufewa shine a mazaunin driver daka gani shine ya tuka motar, kallonta yayi tare da fadin baki so gani na ba koh? Tace a'a , yace mai yasa kika daure fuska? Tace babu komai, murmushi yayi tare da fadin jawaheer yau baki damu da inda na shiga ba, baki kira niba, tace bani da abunda zance maka ne, yace ok toh bari in tafi, bata bude kofar ba sannan bata motsa ba, ya kuma cewa zan tafi, kallonshi tayi da idonta daya rine kadan kawai take jira tayi kuka, janyota yayi jikinsa yace karki sake kice zaki fito da wannan hawayen, jawaheer na rasa mai yasa ko kadan bana son ganinki cikin damuwa, bana son inyi nesa dake na saba dake cikin lokaci kadan, gobe zan tafi inaso plz koda na tafi kici gaba da riqemin kanki karki bama kowa daman shiga rayuwanki, dagowa tayi ta kalleshi dan bata gane mai yake nufi ba, murmushi yayi tare da fadin nan gaba kadan zaki fahimta abunda nake nufi, but yanzu ina son ki riqemin kanki ban son ko wani namiji ya shigo cikin rayuwanki, naso mu tafi tare sai naga koda munje banda tym nd ban son in barki cikin kadaici, shuru tayi tana tunani toh mai yake nufi kar inbar wani ya shiga rayuwa na? So yake in zauna banyi aure ba..... Katseta yayi da fadin zanyi missing dinki sosai, murmushi tayi tare da fadin nima haka, yace taya zan gane? Murmushi tayi tare da fadin komai kaji na fada a kanka dagaske nake kuma hakan nake ji, a musulunce mace zata iya fadama namiji tana son shi, amma a al'adance abun kunya ne, samir a kasar ku na fada maka ina sonka, amma ka nunamin inyi hakuri naji kuma nayi duk da ban cire raiba, amma a yanz..... Shuru tayi yace yanzu me?? Na hakura dakai ina son nima in sami mai sona inyi aure bada dadewa ba, kallonta yayi yana dan nazari kafin yace zaki iya auran namijin da baya sonki? Tace zan iya indai ni ina sonshi, murmushi yayi tare da fadin mai kike tunanin zai faru bayan auren? Tace zaman hakuri, yace har zuwa wani lokaci zaki ta zaman hakuri dashi, tace bazan iya sani ba, amma idan hakan ya faru zuciyata zata yanke a lokacin, yace ok naji zaki iya aurena bayan kin san bana sonki? Wani irin hawaye ga zubo mata, tace zan iya burina a kullum in kasance dakai a koda yaushe, yace jawaheer shikenan nayi miki alkawarin zan aureki amma inaso ki sani ban taba kallonki a matsayin budurwa taba, sai yar uwata, inaso kiyi tunani akai indai kin amince nanda wata biyu za muyi aure in kuma baki aminceba shikenan kiyi tunani akai, shuru tayi na wani lokaci sannan tace bana tunani akan sonka a kullum tunani na shine in sameka a matsayin miji dan haka na amince, yace ok zan fadama dad yau sai a fara komai duk abunda kike bukata sai ki fadamin, amma ina so ki sani indai kika shigo babu saki kar nan gaba kice baki son zaman, murmushi tayi tare da fadin bana tunanin baki na zai iya fadin haka,yace good zamu koma gida anjima sai mu karasa magana dama ke nazo in gani, tace ok sannan ta fara kokarin bude kofar amma yaki buduwa, kallonshi tayi alaman ya bude mata, yace haka zaki faramin babu wani abu sai kawai ki fita, rufe ido tayi tana dariya sannan ta matsa kusa dashi ta mishi peck a goshi, dariya yayi sannan ya bude mata motar ta fita, da ido ya bita har ta karasa wajan su khalil da suke ta fira shida zarah, tace toh saika tashi ku tafi dariya yayi tare da cema zarah sai munyi waya, tace ok, sannan ya tafi, jawaheer kallon zarah tayi tace badai har an kulla luv ba? Zarah tace haba luv a minti nawa, dariya suka sa dai2 lokacin wannan lecturer din yazo yace ma jawaheer tazo yana son ganinta, bayan ta matsa kusa dashi yace ga no dinshi yana son ta kirashi, bata yayi tasa sannan ta koma wajan zarah tana fada mata abunda yace mata, zarah tace haba nayi mamakin dabai koreki ba, ashe ya kamo fish, dariya sukayi har 4 yayi suka shiga lecture basu fitoba sai 6 gida ta nufa direct a gajiye ta shiga gida babu kowa a falo dan haka tayi dakinta, tana shiga toilet ta nufa tayi wanka wardrobe dinta a kusa da toilet dinta yake kaya tasa sannan ta fito tana fitowa taga mutum a dakin yana kalle kalle, kallonta yayi rai a bace sannan yace jawaheer jiba dakin ki duka pics dina ne harta carpet dinki, indai kina sona mai yasa kike kula wasu mazan?? Ido ta dan zaro alaman wana kula..... Tace ni yaushe kum...... Ya isa ban son jinki dazu waye naga yana baki number kina sawa?? Shuru tayi kaman ba zatayi magana ba, can tace lecturer dinmu ne fah, yace lecturer number din mai yake baki?? Tace yace in kirashi ne zai mun magana, ido ya lumshe ji yake kanshi na mishi wani irin tafarfasa lokaci daya idanshi ya kade yace mai zaki mishi idan kin kira shi? Tace nima ban sani ba, kallonta yayi kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fita fuuuuuuuu, dakinshi ya nufa zama yayi akan gadon dakin shidai yasan bawai son jawaheer yake ba, kawai yana tausaya mata sai yasa yake son ya aureta sannan baya son tana nesa dashi, to mai yasa nake kishi idan wani yana mata magana?? Wata zuciyar tace saboda kana sonta da sauri yace nop, kawai dai dan zan aureta ne dole kuma inyi kishi a kanta,karan wayanshi ne yasa ya dauka yaga dad din su khalil ne dauka yayi dad din yace mishi samir gani na dawo ina falo, yace ok dad ga ninan, tashi yayi ya fita ya nufi falon, samun dad yayi da mum akan dinning dad yace samir ya gida gobe ne tafiyan koh? Yace eh dad, dad yace masha Allah, Allah ya taimaka, yace ameen, yace dad dama inaso inyi maka magana nida jawaheer mun fahimci juna, kuma...... Dan shuru yayi dad yace inaji, yace muna son muyi aure in kun amince, dad cikin murmushi yace alhmdlh alhmdlh abu yayi kyau, mum tace toh yanzu ya za'ayi, amma inaga da an jira an duba iyayenta koh? Dad yace a'a in ba'a gansu ba fah, haka zatai ta zama? Kinga dole kuwa tayi aure, mum tace hakane, m samir yace dad plz ban son bikin ya wuce wata daya, mum harara ta sakar mai tare da fadin toh mara kunya, kai ya sosa tare da tashi yabar wajan suka bishi da dariya, dakinshi ya koma ya kwanta haka kawai yake jinshi cikin farin ciki da annashuwa, haka har bacci ya daukeshi,.
Washe gari jawaheer nada lecture karfe 8, dan haka da wuri ta shirya duk da ranta a jagule yake, dan tasan m samir yana fushi da ita, gashi yau zai tafi, ji tayi ba zata iya tafiya ba har sai ta ganshi, dakinshi ta nufa taga baya nan, fita tayi ta nufi falo taga mum na gyara kayan abinci akan dinning, tace morning mum, mum tace har kin fito? Tace eh mum gashi har na kusa makara, na tafi sai na dawo, mum tace ok samir yace in fada miki ya tafi, sannan ga sako ya bayar a baki, dam taji kirjinta ya buga wato tafiya yayi shine bai mata sallama ba......
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 41-42
Mum ta dauko wani karamin bag ta bata, amsa tayi ta koma dakinta ta ajiye tare da fashewa da kuka, wato haka za'a fara kenan, kallon jakan tayi ta bude taga kudi masu uban yawa kuma duk dallar, sai wata takarda data gani a ciki, budewa tayi taga anyi rubutu kaman haka...... *ga kudi nan kisai duk abunda kike bukata kin san ban san ya al'adunku suke ba, ki fara siyayyan abunda kike bukata inna dawo sai mu karasa wasu abubuwan, sannan inaso ki sani ni bana daya daka cikin maza marasa kishi dan haka kisan wa zaki aura ina da kishin kaina dan haka dole inyi kishin iyalina, idan kika kara kula wani ban yafe ba sannan idan na sami labari zaki hadu da fishina bye* baki ta sake tana mamaki lokaci daya kuma tayi dan murmushin takaici, tare da tunanin yanda rayuwan aurensu zai kasance ita dashi, bata taba tunanin zata aura mijin da zai bude baki yace baya sonta ba har kuma ta yarda da auran, wani siririn hawaye ne ya silalo mata a fuska jin karan wayanta yasa tayi saurin goge hawayen zarah ta gani, dan haka ta dauka da sauri ban san mai zarah tace mata ba naji tace gani nan zuwa, har takai kofa ta tsaya tare da waigowa komawa tayi ta dauki jakar ta fita, a falo ta kara ganin mum tace yauwa mum gashi kudi ne a ciki yace in fara siyayya kafin ya dawo, murmushi mum tayi tare da fadin ok in kin dawo mayi magana tace ok tare da fita.
Makaranta ta nufa direct bayan tayi parking ta kalli agogon dake manne a hannunta tare da fadin 8:03 Allah yasa bai shiga ba, jakarta ta dauka ta fita ta nufi department dinsu a tare da lecturer din suka shiga, kallonta yayi yace u r lucky 2day, murmushi kawai tayi ta nemi waje ta zauna, inda ya fara koyar dasu harya gama ya musu text, sannan ya kalli jawaheer yace sameni office dina yanzu, yana fadin haka ya fita, kallonshi tayi ta banga mai harara ta baya tare da fadin ko uban me zan mishi oho, zarah tazo kusa da ita tare da fadin sai ki tashi kije, hararan zarah tayi tare da fadin muje ki rakani, zarah tace wa? Ni din? Tab ai in kin ganni a lahira kaini akayi, ke yace kije dan haka babu inda zani, tashi tayi ta fita zarah tayi dariya tare da bin bayanta har kofar office dinshi zarah ta rakata amma taki yarda ta shiga, nocking jawaheer tayi taji shuru karayi tayi sannan akace come in, budewa tayi ta shiga, akan kujera ta sameshi yana duba wasu takardu, ganin ta shigo yasa ya saki murmushi, tare da fadin jawaheer right? Kai ta daga alaman eh, ya nuna mata kujera tare da fadin zauna mana, zama tayi fuskanta tamke, yace jawaheer mai yasa baki kira niba? Tace na manta ne, yace ok so yanzu ni sai ki bani number dinki, ko kuma ki kirani, tace zan kira inna koma gida, yace ok muga wayanki, kaman karta bashi amma babu yanda ta iya ta miqa mai, kiran layinshi yayi sannan ya mika mata wayan tare da fadin baki saving din number dina bama, dan murmushi tayi yace bari in gabatar miki da kaina sunana yusuf, ni dan garin kaduna ne wato dan zaria, ina da mata daya da yara biyu, jawaheer tunda na ganki naji Allah yasa min sonki sannan ni bada wasa nake ba da aure nake sonki, shuru tayi tana kallonshi, tare da takaicin kalaman da yake fada mata, amma ya dan burgeta dan da farko tayi zaton kalan lecturer din nanne masu bata yan mata, amma sai taji sabanin haka, sannan yusuf ba laifi yana da kyau sannan mijin nu nawa ne a ko ina, amma ita bata ganin kowa sai samir dinta kawai.... Katseta yayi da fadin jawaheer ya naji kinyi shuru, magana za tayi ta kasa ganin haka yasa yace kije zan kiraki zan baki lokaci kiyi tunani akai, da sauri ta tashi ta fita, wajan zarah ta nufa, zarah na ganinta ta tashi tare da fadin ya akayi? Tace hmmm muje kiji, suna tafiya tana bama zarah labarin abunda ya faru, zarah tace kai amma ni kam jawaheer mai zai hana ki yarda dan naga....... Tace dakata taya zan yarda bayan nanda wata biyu biki na, ido zarah ta bude tare da fadin ke dawa? Jawaheer tace m samir, shuru zarah tayi tana nanata sunan tare da fadin ni kam ina jin sunan, yauwa na tuna wani dan kwallon kafa ne mai irin sunan, jawaheer tace to ni dan kwallon zan aura, zarah kwashewa tayi da dariya tare da nuna jawaheer da hannu tace wannan wasan naki daban dariya yake, jawaheer tace kece kike da ban dariya amma banda lokacin miki bayani in lokaci yayi zaki gani, zarah dai dariya take tayi alama jawaheer wasa take mata, ganin tana kokarin mai data mahaukaciya ko kuma makaryaciya yasa jawaheer tace ni kinga tafiya ta, tayi gaba abunda zarah saboda dariya ma kasa binta tayi, ita kam jawaheer tayi gaba abunta.
Jawaheer koda taje gida a wajan bukka taga mum dinta da dad suna fira ga kayan abinci nan a wajan kala kala, nufansu tayi cikin fara'a tare da fadin dad mum sannunku da hutawa, amsawa sukayi su duka da fadin yauwa, zama tayi tare da fadin mum ina khalil ne wai? Tace ya fita shida ozil, tace lah ya dawo ne? Mum tace eh ya dawo dazu, dad yace jawaheer kinci abinci kuwa? Tace a'a yace haba bakinki ya nuna hakan, mum ta fara zuba mata tare da fadin babu yanda banyi da itaba amma taki ci da safe, mutum yaita zama da yunwa in kika jajibo ma kanki ulcer aike kika sani, ita dai jawaheer shuru tayi tare da amsan abincin ta fara ci, taci sosai sannan ta ajiye, bayan ta kammala mum tace jawaheer nasa an canzo kudin da samir ya baki duka kudin million 200 ne, zamu tafi dubai muyi siyayya a can na kayan akwati kafin ya dawo muji yanda yake son a tsara dan kin san mutum celebrity bazai rasa yanda yake son bikinshi ya kasance ba, cikin jin kunya tace toh mum, dad yace amma kudi ai yayi yawa, mum tace baiyi wani yawa ba,yar tawa ai mai tsada ce, dariya dad yayi yace nima haka dan nawa, ita dai jawaheer tashi tayi dan wani irin kunyan mum taji tanayi yanzu, suna ganin ta tashi suka sa dariya.
Dakinta ta shiga tare da ajiye jakarta, ta fada toilet tayi wanka, wani irin nishadi take ji sosai, duk da tana cikin damuwa na sauyin da samir yake nuna mata kafin ya tafi, gashi yau abunda ya mata ya bata mamaki tafiya babu sallama, wayarta dake kan gado taji tana ringing nufan wayar tayi tare da dauka taga zarah ce, dauka tayi taji zarah na fadin wlh jawaheer kin bani dariya dazu, tsaki jawaheer tayi tare da kashe wayan tace banda lokacin wannan tsokanan naki yanzu wlh zarah, kiran zarah dinne ya kuma shigowa dauka tayi tare da fadin miye kuma? Zarah tace miye na kashe wayan kuma? Tace naga kina son mai dani kaman mahaukaciya ne, zarah tace ko daya abun da kika fada ne kawai yake sani dariya, amma wai wasa kike koda gaske? Jawaheer tace akan mai zan miki wasa bari in turo miki saqo ta whtsapp yanzu, kashe wayan tayi ta tura mata pics dinsu da m samir kala kala, aiko tana gani ta doko ma jawaheer kira amma taki dauka daka karshe ma da taga ta dameta saita kashe wayan, tana fadin bari