Showing 15001 words to 18000 words out of 63876 words
Chapter 6 - JAWAHEER HAUSA NOVELS BY MARYAM OBAM.txt
ba, ni shege ne? Kuka yaci karfinshi dad duk da wannan abun da kuka aikata saida ka raba mum dina dani? Why? Why? Dad kasan irin ciwon da zata ji kuwa? Kasan wani hali zata tsinta kanta? Shin kasan ya zataji inta tashi bata ganni ba? Duk bakai wannan tunanin ba ka rabata dani, kuka yake sosai lokaci daya kuma ya fita yabar gidan dad din yana kiranshi amma kota kanshi baibi ba ya wuce abunsa cikin tashin hankali koh mota bai shiga ba a kafa yake ta tafiya yayinda mutane suka fara ihu tare da zagaye shi, security dinshi dake binshi dakyar suka fito dashi daka cikin mutane suka sashi a mota, kallon driver din yayi yace ya kaishi gidansa tunda ya fadi haka bai kara cewa komai ba sai kukan da yakeyi har suka karasa gida da sauri ya shiga ya fara dube2 lokaci daya ya furta whr iz she? fita yayi da sauri ya fara tambayan security dinshi ina yarinyar da tazo dazu ina take?......
*maryam obam*
[21/01, 13:45] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 14
Cemai sukayi basu san inda take ba, daura hannu yayi akai cikin wani irin tashin hankali dakyar ya iya shiga cikin gida koda ya shiga shima a falo ya zauna yana kuka sosai wanda na rasa gane na bakin ciki ne kona farin ciki, amma zan iya danganta kukan nashi dana bakin ciki, lumshe ido yayi tare da tunanin yanzu shi shege ne bata hanyar aure aka sameshi ba, innalillahi wa inna'ilaihira jiun, yanzu duk wani kimarsa da darajansa zata ragu a idon al'umma idonshi ne ya kada yayi ja yanzu mahaifiyarshi tana nigeria a garin yola, shida bai taba zuwa nigeria ba taya zai nemeta yasan dad dinshi da wuya ya kaishi, jawaheer ita daya ce zata taimakeshi saboda itama yar nigeria ce, ido ya lumshe tunawa da yayi lokacin daya barta tana kuka akan ya sota, lokaci daya ya kawar da tunanin dan bashi bane yanzu a gabansa burinshi yanzu yaga jawaheer ta taimakeshi domin yaga mum dinshi.
Jawaheer tana kwance akan kujeran falo tana ta rusgan kuka, lokaci daya zazzabi ya kamata mai zafi, wanda yasa duk wani gaba dake jikinta ya mutu, ga kanta dake faman sara mata wanda kukan da tasha ya haddasa mata ciwan kai din da zazzabi, dakyar ta tashi tayi alwala tayi sallah a zaune dan bata ji zata iyayi a tsaye, kuka take tana roqan Allah akan ya zaba mata mafi alkhairi a rayuwanta, harta gama ta kwanta wajan da tayi sallah din, gaba daya taji zaman garin ya isheta burinta ta ganta a nigeria domin kuwa tasan M samir bazai taba sonta ba har abada, dakyar taja jikinta ta dauko wayanta dake ta faman ruri tun dazu, sunan mum ta gani dan haka ta dauka da sauri tare da fadin mum..... Sai kuma ta saki kuka hankali tashe mum take tambayanta maiya faru jawaheer lafiya kuwa? Cikin kuka tace mum magananki gskya ne, tabbas gskyan hausawa ne da suke fadin duk abunda babba ya hango yaro bazai taba hangosa ba, mum cikin damuwa tace jawaheer dan Allah ki fadamin maike faruwa, wani abu aka miki? Tace mum inaso a fara maganan biki na kaman yanda kike so da duk mijin da kuka ga ya muku, mum tace jawaheer dagaske kike? M samir fa? Kina nufin kin hakura dashi? Duk lokaci daya mum ta jero mata tambayoyi wanda yasa jawaheer din wani sabon kuka, cikin kuka taba mum labarin duk abunda ya faru tare da fadin mum jibi zan dawo gida, ki fadama dad yama PA din ambassador magana, mum tace shikenan jawaheer zan fada mishi kiyi hakuri ki cire komai a ranki insha Allah komai zai wuce, tace mum bana tunanin zan cire komai domin son M samir a jini na yake na amince da zanyi aure ne saboda alkawarin da nayi mum inaso ki sani wlh duk wanda na aura gangar jikina ne kawai a tare dashi amma zuciyata tana tare da m samir mum ki tayani da addu'a kawai Allah ya bani hakuri da dangana amma ina cikin wani hali mum tana fadin haka ta kashe wayan tare da sakin kuka mai karfi, a yanzu jawaheer bata bukatan komai face ta ganta a kasarta nigeria domin ta cire tsammanin m samir zai sota, sai dai koba komai zatai alfahari da ganinshi da tayi tare da kissing dinta da yayi duk da tasan ba abu bane mai kyau tunda ba mijinta bane, sai dai a yanda take jinshi koda jikinta ya nuna yana bukata bata tunanin zata hanashi dan tana mai mahaukacin so, wanda bata ganin kowa sai shi, sai dai kash shi ta gefenshi ba haka bane irin yanda ya nuna baya sonta yasa take ganin kaman zata iya rayuwa da wani wanda ita da kanta tasan karya ne, m samir kadai shine burinta shine namiji daya da zata samu tayi farin ciki a rayuwa koda kuwa zai dinga dukanta ne kullum, lokaci daya ta tashi da sauri duk da bata jin karfi a jikinta tafiya take tana tangal tangal kaman zata fadi kofar gidanta ta nufa ta bude ido ta kurama gidan m samir din wanda hakan ya nuna mata alaman ya dawo yana gida, tunda taga security dinshi, kirjinta taji yana buga mata da karfi, lokaci daya ta fara tafiya domin zuwa gidan har ta kusa shiga ta tsaya, lokaci daya kuma ta juya zuwa gidanta da sauri dan bata jin zata iya zuwa gareshi yanzu, amma koda ta shiga gida kasa sukuni tayi wanda yasa dole ta kara nufa gidan duk da kirjinta na buga mata dan bata san mai zata tarar ba yanzu, amma haka ta daure ta shiga cikin falon gidan a kwance ta ganshi akan kujeran falon kallo daya zakai mishi ka gane yana cikin wani hali dake bukatar taimako, da sauri ta nufeshi tare da fadin m samir, nufanshi tayi tare da fadin baka da lfya ne? Idonshi ya bude daya kada yayi ja ya sauka a kan fuskanta, murmushi ya sakar mata tare da kokarin tashi amma ya kasa, dan haka ta fara kokarin dagashi amma ta kasa, murmushi ya kuma saki tare da fadin na miki nauyi koh? Dan shuru tayi sannan tace baka da lafiya jikinka da zafi u need to see a doctor, ido ya kura mata yace jawaheer kema jikinki zafi kina bukatan ganin dr tashi yayi dakyar tare da janyota jikinshi yace maike damunki? Kirjinta ya fara bugawa da karfi wanda hakan yasa ta kasa magana domin gaba daya tunda ya janyota jikinshi wani irin shock ya kamata tare da shiga cikin wani irin yanayi bakinta sai rawa yake alaman tana son cewa wani abu amma ta kasa, ido ya kura mata yana kallonta lokaci daya ya furta she iz pretty.
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 16
Lokaci daya kuma ya furta nasara akan me? Bata bashi amsa ba dan kuka takeyi sosai ganin bata da niyan bashi amsa yasa ya tashi ya dawo kusa da ita zama yayi kusa da ita tare dasa hannunshi yana share mata hawayen dake zuba a fuskanta, yace jawaheer kibar wannan kukan koma miye insha Allah zaki samu ki dage da addu'a kinji kai ta daga alaman toh, sannan ta tashi tare da fadin sai anjima, bai tankata ba har takai bakin kofa ya kira sunanta tare da fadin inane gidanki? Tace can, dariya yayi tare da fadin can ina? Tace kazo muje saika gani, tashi yayi yana jan kafa dan har yanzu bawai ya warke bane tana gaba yana biye da ita a baya komai nata yana burgeshi kyanta nutsuwanta, maganan ta, tafiyanta kai komai nata ya mishi sai dai baya jin sonta a ranshi amma ya dauketa a matsayin kanwarshi domin so daya ne ya kuma bama sonia wacce bai san inda take ba a halin yanzu dan tunda ta tafi basuyi waya ba duk da yama dad dinshi alkawarin rabuwa da sonia amma baya jin zai rabu da ita dan itace rayuwanshi,.... Maganan jawaheer ne ya katseshi da take fadin shigo mana, sai a sannan ya gane sun zo gidan, shiga yayi da sallama, tace ya zauna a falo, bayan ya zauna ne ta nufi kitchen dan ta hada mishi coffee bata dauki wani lokaci ba ta kawo mai amsa yayi ya fara sha, sannan ya dago kai suka hada ido murmushi ya sakar mata yayin da ita kuma tayi saurin kawar da fuska dan taji kunyar kamata da yayi tana kallonshi, jinshi tayi yana fadin ina son idonki yana min kyau, bata iya cewa komai ba sai murmushi kawai da tayi, shima bai kara magana ba harya gama shan coffee din wayanta ne yayi kara dan haka ta tashi ta dauko taga ozil ne , dauka tayi da fadin kabir nayi fushi wlh sai yau? Yace kiyi hakuri m samir nasan nayi laifi tace uhm ni bazan hakura ba gaskiya, ban san mai yace mata ba naga ta saki dariya tare da fadin zan baku mamaki ku dukanku, nan dai sukai ta fira cikin harshen hausa har sukai sallama,
Bayan ta kashe wayan ne ta kalli m samir daya zuba mata ido yana kallonta, saurin kawar da kanta gefe tayi, murmushi yayi tare da fadin wannan wani yare naji kinayi? Tace hausa, kasa fadin hausa yayi dan haka abun ya bata dariya, yace ya akeyi yana son ya iya, tace babu wuya mu a nigeria shine yaran da kowa yakeyi akasarin mutanan kasata koda wata kabila ne zaka sameshi yana jin hausa koda babu yawa domin hausawa sunfi yawa a kasar, yace a nigeria yare daban daban akeyi? Tace eh akwai yare kala kala, akwai fulani, hausa, igbo, yaruba, tibi, igala, idoma, ibra, kurama, gwari, da sauransu, yace kai yare da yawa haka a kasa daya kuma duka yan kasar ne? Tace eh duk yan kasar ne, yace wow inaso inga wa innan yaren, ke miye naki yaren? Tace fulani ce ni, dan shuru yayi sannan yace dayan yaran da naji kinayi ba naki bane kenan? Tace eh, yanda take mishi bayanin abun na sashi cikin nishadi yayin da take ta kara bashi labari akan kasarta shi kuma yana jin dadi, ganin irin kallon da yake mata yasa tayi shuru tare dayin kasa da kanta tana wasa da hannunta, murnushi yayi tare da kiran sunanta yace jawaheer dago kai tayi suka hada ido tayi saurin yin gefe da idonta, domin indai suka hada ido wani irin yanayi take shiga mai wuyan fassaruwa, yace kece mace ta farko da nake son yin fira da ita, idan ina magana dake inajin dadi sosai, i will like you to be my sister, murmushi tayi tare da fadin thanks alot yau ina cikin farin ciki daka daukeni a matsayin kanwarka, insha Allah zakai farin cikin zamana kanwarka tare da alfahari dani, mika mata hannu yayi alaman su gaisa, tashi tayi ta nufeshi tare da bashi hannu yace i luv you sister, shuru tayi domin ta lula wata duniyar inama ace yau wannan kalman daya fada mata a matsayin masoyiyyarshi da bata san wani irin farin ciki zatayi ba, hawaye ne ya fara zuba a idonta, jin hannunshi tayi yana goge mata da sauri ta dago ta kalleshi, shima dai ita din yake kallo, tace yau ina cikin farin ciki ban taba tunanin zan ganka ba a rayuwa na, wannan kukan da nakeyi na farin ciki ne, yau gani ga ka, kafin in ganka an fadamin ganinka tashin hankali ne amma da yake Allah mai tausayin bayinsa ne sai ya hadani dakai ba tare da nasha wahalan da ake fada ba, sai yasa ake cewa kar bawa ya cire rai da ikon Allah, na tabbata addu'ata ce Allah ya amsa sai yasa ya hadamu cikin sauki, yace hakane sister babu abunda Allah bazai iya ba, komai ya faru da bawa ya dauka a matsayin kaddara ne a rayuwanshi...... Shuru yayi lokaci daya kuma yace tabbas dad dina bashi da laifi dan an sameni bata hanyar aureba, lallai haka Allah ya tsara babu wanda ya isa ya canza hakan, laifi daya dad dina yayi daya raba mum dina dani, jawaheer tace shima yana cikin kaddaranka, kallonta yayi ta daga mishi kai alaman eh tace haka Allah ya tsara maka sannan gashi ta sanadin haka mun kara samun kusanci haduwa na dakai shima yana cikin kaddaranka........
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 17
*ina yinku masoya novel din jawaheer kaman yanda kuke son novel din jawaheer nasha kira da message kuyi hakuri na jina shuru insha Allah zan dinga muku posting kullum koda ba yawa😆*
Yace kaddarana?? Kai ta daga mishi alaman eh, tare da fadin gashi ta sanadi na zaka kasata nigeria, murmushi yayi tare da fadin hakane harna kosa inje koh Allah zaisa inga mum dina, inko hakan ta faru ban san wani irin farin ciki zanyi ba, jawaheer tace insha Allah zaka gan..... Bata karasa ba tayi shuru tana kallonsa shima din ita yake kallo cikin sanyin murya tace kana da pic dinta?? Shuru yayi can yace a'a bani dashi, tace sunan anguwansu a yola din fah? Shima yace bai sani ba, jawaheer tace toh taya zamu nemota?? Wannan ba abu bane mai yuhuwa dole muna bukatar sunan anguwansu ko kuma hotan ta, wani irin zufa ne ya keto ma m samir wanda gaba daya shi baiyi tunanin haka ba dan yana ganin yana zuwa nigeria zaiga mum dinshi toh taya ma zai ganta shida bai santa ba, bai taba ganin hotanta ba, hannunsa ya buga a dayan hannunshi tare da tashi ya kalli jawaheer yace zanje wajan dad dina ya fadamin sunan anguwan su, coz i only know her name, fita yayi da sauri, duk da dingishi yakeyi, koda ya fita security dinshi na nan tsaye suna jiranshi, yace ku dauko mota muje gidan dad, daya ne ya tafi sai gasu da mota har biyu ya bude ta farkon ya shiga, kai tsaye gidan dad dinshi ya kara nufa, a falo yaga dad din nashi a zaune idanshi yayi ja, yana ganin dan nashi ya tashi da sauri ya rungumeshi yana kuka, jikin m samir yayi sanyi tare da tausayin dad din nashi, cikin kuka dad din ya fara magana samir yanzu zaka gujeni koh? Zaka koma wajan mum dinka gaba daya, bazan bar hakan ya faru ba, dad din mum dinka yaki bani ita bai lura da irin son da nake mata ba, dan kawai ni farin fata ne bai lura da cewa duk musulmai daya bane, samir har yanzu ina son mum dinka sai yasa nake masifar sonka ban san damuwa a tare dakai in wani abu ya sameka inaji kaman mum dinka ya sama, plz dnt leave me, m samir ya danja jikinshi daka na dad din nashi ya fara magana kaman haka dad bazan taba gudanka ba kaine mahaifina nasan irin son da kake min amma dad plz ka barni inje inga mum dina koda once ne in my lyf, tasan danta bai mutu ba sannan tasan danta baya mugun hannu, na tabbata har yanzu bata cikin nutsuwa tunda danta ya barta, dad din kai ya girgiza yace ina tsoran kaje kaki dawowa son, m samir yace dad indai ka fadamin inda take one week zanyi kawai in ganta in dawo kasan inada wasa nan da sati biyu, dad din shuru yayi can ya nisa yace sunan anguwansu guyuk idan kaje kace a nuna maka gidan liman, murmushi m samir yayi najin dadi yace ashe kakana liman ne a anguwansu, dad din yace eh, sannan yace toh taya zaka kaida baka san kasar ba? Yace dad akwai wata yar nigeria tare zamu, dad yace wacece a ina ka santa? Murmushi yayi tare da fadin haba dad nifa duk wanda nace maka na sani ba abun mamaki bane, dad yace hakane amma ya akai tazo wajanka harta ganka kuka hadu kuka saba, dariya m samir yayi yace hadin Allah ne, dad din murmushi yayi tare da fadin ina son ganinta, m samir yace gobe zan kawo ta bari in sanar da minister zan tafi nigeria jibi suyi arranging dad din yace ok m samir tashi yayi tare dayi ma dad din sallama.
Tunda m samir ya fita jawaheer taji wani iri amma taji dadin sabawansu lokaci daya ido ta lumshe tana jin nishadi, burinta har yanzu bai wuce ace yau ya yarda zai aureta ba ita koda zai aureta baya sonta zata so haka, amma tunda yace a matsayin kanwa ya dauketa hakan ma abun alfahari ne a wajanta wasu ma signing dinshi suke nema su samu amma abun yaci tura ita kam gata gashi har kissing dinta ya taba yi wani murmushi ta saki cikin jin dadi haka har bacci ya dauketa.
Washe gari da safe tunda jawaheer tayi sallah asuba tayi wanka, ta koma bacci bata farka ba sai wajan karfe goma tana tashi ta kara komawa tayi wanka, tasa wata doguwar riga tare da daura karamin gyalen rigan, kitchen ta nufa ta hada tea dan gidan babu masu aiki tunda su mum suka tafi suma suka wuce, tana cikin shan tea din taji nocking tashi tayi ta nufi kofar tare da tunanin ko waye, tana bude kofar taga mutum a tsaye cikin riga da wando yayi mugun kyau ya hade hannunshi biyu yana kallonta tare da sakar mata murmushi ganin irin kallon da take mai yasa yazo kusa da ita tare da mata peck a goshi yace morning sis, firgit tayi ta fara kame kamen mai zata ce, ganin haka yasa ya kamo hannunta tare da shiga cikin gidan yace nazo ki rakani wajan dad dina yana son ganinki, ido ta zaro tare da nuna kanta alaman ni zai gani, kai ya daga mata tare