Showing 63001 words to 63876 words out of 63876 words

Chapter 22 - JAWAHEER HAUSA NOVELS BY MARYAM OBAM.txt

Advertisement

20 Jan 2025

7470

jawaheer plz ki tafi ki barni, kuka take sosai tare da kokarin bashi hakuri ganin haka yasa yabar gidan gaba daya cikin bacin rai, zama tayi a kasa tana kuka toh ina zata ma inta tafi sai yanzu tayi nadama akan maganin da take sha, ita a tunaninta tunda mijinta celebrity ne kaman bazai so haiyuwa ba, sannan tana ganin inta haiyu zai canza mata hmmm kunji jawaheer da wani irin tunani, kuka take sosai tashi tayi zata daki jiri ya dibeta ta fadi, tadai farka ta ganta a gadon asibiti ga mum dinta ga samir a kusa da ita, kuka ta saki tare da fadin dan Allah kayi hakuri wlh bada nufin kuntata maka nayi b...... Hannu yasa ya toshe mata baki mamanta ta mata sannu sannan ta fita ta basu waje, kallonta yayi yace jawaheer kina shan maganin planing dan karki haiyu gashi Allah ya kamaki yanzu kina da cikin wata biyu, ido ta lumshe tabbas hakan zai iya faruwa kwanaki tayi missing din kwana daya bata shaba, kuma lokacin bata dade da gama period ba, katseta yayi da fadin idan kikai gigin zubar min da ciki sai nayi shari'a dake, cikin kuka tace kayi hakuri na tuba wlh nayi nadama bada nufi nayi ba wlh saboda sonka nayi haka tace nasha koh ba zaka so haiyuwa yanzu ba sannan ina tsoran in haiyu ka rage sona, hancinta yaja da karfi yace jawaheer karki kara wannan tunanin bana daya daka cikin maza marasa son yara ina matukar kaunan yara,jawaheer karki kara yin wani mummunan tunani a kaina komai zai faru sonki bazai taba raguwa a cikin raina ba, matse hannunshi tayi tana kuka tare da bashi hakuri tace mum ta sani? Yace a'a bata san komai ba ta dai san kina da ciki komai za kiyi min zan jure bana daya daka cikin maza masu yawan kai kara, peck ya mata a goshi tare da fadin mai zaki ci? Tace babu komai bana bukatar cin komai, kwanan jawaheer uku aka sallameta, suka dawo gida samir na nuna mata kulawa sosai daka tace wash zaice mai nene mai yake miki ciwo mai za kici, haka zaiyi ta tambayanta,mum tazo taga jawaheer din ita da dad sati daya sukayi suka koma, mama kullum ita take kawo musu abinci dan tace ta daina girki. An fara world cup samir shi daya ya tafi canada domin da spain za'a fara bugawa, jawaheer kam gidan mama ta koma da zama, kullum tana kan tv tana kallon kwallo, saida yayi wata biyar a can lokacin jawaheer ta kusa haiyuwa an gama world cup kasar spain taci kofi anyi ma yan wasan mugun manyan kyauta musamman ma m samir daya zama zakaran kwallon kafa, tunda sunci world cup kuma duk shi yake zura ball din, m samir ya kara samun mahaukatan kudade sosai, ranan daya dawo gida ba karamin dadi yaji ba na ganin matarshi a gida, tun daka falo ya fara nuna nata soyayya tare da nuna mata yayi kewarta cikin ta yayi girma sosai, tunda ya dawo baya fita yaba mama kudi masu uban yawa a musu siyayyan kayan babys. Wata ranan monday jawaheer ta tashi dana kuda, ama bata bari ya ganeba, tunda yaji ta shuru taki fitowa daka daki ya kira mama, ba'a dade ba mum tazo, dakinta mama ta shiga taganta tana cije baki tare da kuka, da sauri mama ta karasa wajanta tana fadin lafiya jawheer, tace mama ciki na ke ciwo, dauko mata hijab tayi tasa mata dai dai lokacin samir yazo shiya kamata suka fita har mota akai asibiti da ita, ana zuwa akai labour room da ita, samir kasa zama yayi batai doguwar nakuda ba ta haiyu ta haifi yan biyu duka maza lokacin da aka fada musu ba karamin murna yayi shiga dakin yayi yaga yaran kyawawa sak shi, farin ciki yake tayi har baya iya boyewa, mum washe gari suka iso harda zarah kwananta biyu aka sallamesu, gaba daya gidan jawaheer din suka nufa, mum ce ta zauna da ita take mata wanka, samir zama yake ya tasa yaran gaba yaita kallo, wani irin so yake ma yaran tare da mamansu. Ranan suna yaran suka sukaci sunan dad dinshi muhd ali da muhd jibrin sunan dad din jawaheer ana kiran yaran da suhail da suhal, ranan suna an kashe naira dad ya kashe kudi sosai haka dad din samir ma, saida jawaheer tayi arba'in sannan mum ta koma.




















BAYAN SHEKARA BIYAR


Abubuwa da dama sun faru ciki harda kammalawan karatun jawaheer gashi ta kara haifan yan biyu mata, akasa nadia da bilkisu, suna kiransu da ummi da ma-ma, mum din jawaheer ta haifi yarinya mace mai suna fatima, haka zarah ma ta haifi mace mai suna aysha, samir ya kara samun arziki fiye da nada yana bala'in ji da iyalanshi, jawaheer na zaune a daki samir ya shigo yace ina yara? Tace suna bacci, yace bari in kara baki yan biyu, koda yake wannan karan yan uku zan bayar dariya tayi tare da fadin na yaf..... Bata karasa ba ya cafkota tare da kissing dinta, kashe wuta samir yayi alaman in fita daukan rahotan ya isa haka.......... Toh anan zan dakata ALHAMDULILLAH




SAI MUN HADE A SABON NOVEL DINA GODIYA GA MASOYANA MASU BIBIYAR NOVELS DINA MARYAM OBAM NA MATUKAR YINKU SOSAI

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login