Showing 51001 words to 54000 words out of 63876 words

Chapter 18 - JAWAHEER HAUSA NOVELS BY MARYAM OBAM.txt

20 Jan 2025

6931

ita ba kawaye gareta ba dan haka zarah ce taita rabo ta dai bama yan class dinsu, mum ta dauko mai gyara ta fara gyara mata yar tata, kun san farar mace babu wuya abu ya amsheta fatar jawaheer tayi laushi tayi silbi gwanin sha'awa har wani sheki takeyi da walkiya, ga kirjinta ya kara cika domin masu gyaran gaske mum ta dauko mata, anata hidiman biki ita jawaheer abunda yake damunta shine rashin wayan da basayi tunda sukayi a dubai yace mata shima yana spain zai raba kati, basu kara waya ba, gashi wayanshi baya shiga..... Yau za'ayi mothers day wanda mum ta shirya a wani haddan hall wanda saika amsa sunanka zaka iya kamashi manyan mata sun taru sosai masu hannu da shuni amarya saboda bala'in kyau dakyar na ganeta yan class dinsu sunyi mata kara sunzo matan dan event din na mata ne, sannan sunce zasu spain din harda mazan, anyi taron mothers day wanda mawaka daban daban suka baje basirar su, anci ansha kowa yaji dadi ga calender da aka raba wanda zarah ce ta hada musu cikin pics dinsu da jawaheer ta tura mata kwanaki sunyi kyau sosai mutane da dama sunyi mamaki da suka ga mijin nata suna ta fadin sun dace ashe dan kwallo ne kai ta sami mai mugun kudi, bayan sun koma gida saiga kiran samir da sauri ta tashi tayi toilet dan akwai kawayensu na class dinsu a dakinta dauka tayi cikin murya kaman zatai kuka tace hello, yace dear maiya sameki? Tace bakai bane kaki kirana ka kuma kashe waya, yace sorry dear jibi ina nan tafe uwar haka jibi kin zama tawa koh? Dariya tayi tare da fadin insha Allah ina ma auren soyayya mukayi kana so na kaman yanda nake sonka aida abun yayi armashi dariya yayi yace wani irin armashi? Tace mai zaka siyomin? Yace mai wayau kiban amsan tambaya na, dariya tayi danya gano ta tana son canza maganan ne, tace nima ban san amsa ba, yace zaki sani inna dawo bada wasa zan miki ba, dariya tayi tare da kashe wayan...... Jawaheer na gayyatar kowa da kowa daurin aurenta fans😀




























*maryam obam*


*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 51-52














Kiranta ya kuma yi dauka tayi yace naga pics kinyi kyau sosai, tace waya turo maka? Yace zarah nasa ta tura min pics din duk event din da akayi dariya tayi tare da fadin nasan banyi wani kyau ba zolaya na kake, yace uhm idan na dawo zan tabbatar miki da kyan da kikayi dariya ta kara saki tare da fadin sai anjima nabar mutane, yace mutanan sun fini ne? Tace a'a yace gud sai ki tsaya dan ban gama jin muryanki ba, tace uhm janta yayi da fira sosai sannan ya barta sukai sallama fita tayi zarah tace har an gama soyewan dan gulma waya shine a bayi, dariya tayi tare da fadin ehdin ina ruwanki ban san gulma, sauran sukai dariya tare da tashi suka mata sallama ita dama zarah yau tazo sai bayan biki zata koma, tare zasu kwana, raka su sukai har wajan gate akan sai sunzo gobe kamu, ciki suka koma jawaheer tace wai miye tsakaninki da khalil ne? Zarah tace mutunci jawaheer tace uhm in tayi wari maji, dariya zarah tayi suna cikin haka mum ta shigo dakin hannunta dauke da wani cup taba jawaheer tace ta shanye amsa tayi ta shanye sannan mum ta amshi cup din ta fita jim kadan sai ga kayan fruit an kawo musu, zarah ta amsa suka fara sha.












Yau za'ayi kamu tun karfe biyu aka farama jawaheer makeup ba'a gama ba sai wajan 5 danma tayi alwala kafin a fara saida tayi sallah kafin aka fita zuwa wajan kamu kwalliyan yau tafi ta jiya, a wajan taga adda dariya tayi domin taji dadin zuwanta haka aka sa lalle duk abunda akeyi zarah na daukan ma samir tare da videos anci ansha an kashe naira kaman ba gobe, harda mutanan da ba'a gayyata ba sunzo yau domin kawai ansan dan kwallon kafar da duniya takeyi dashi shine zai auri yar nigeria abun yaba ma mutane da dama mamaki amma duk wanda yaga amaryan sai yace eh gaskiya sun dace domin itama ba'a baya ba wajan kyau koda zarah ta tura ma samir hotuna ganin yanda tayi wani irin bala'in kyau abun ya bashi mamaki uwa uba yaga ta kara girma da cika, ji yake kaman yayi tsuntsu ya dawo gida amma ba hali sai gobe, ranan gani yayi lokaci baya mishi sauri burinshi kawai ya dawo yaga jawaheer dinshi, bayan an gama komai aka koma gida jawaheer dakin da adda ta sauka ta tare tace adda shine sai yau zaki zo? Adda tace ni rabu dani ja'ira sai inji shuru tunda kika tafi sai kawai naji ance wai zakuyi aure shin yaushe kuka fara soyayya ne haka har abun yayi karfi? Dariya tayi tare da fadin to ni ta ina zan fara bada amsa? Adda tace tako ina, labari taba adda yanda abubuwa suka kasance har da amincewan da yayi zai aureta, adda ta nisa tare da fadin hmmm samir kenan ni nasan yana sonki idanshi kawai za'a kalla a ga sonki a ciki, dariya jawaheer tayi tace uhm adda nidai banga komai ba, wai ni kam adda ina dr ne? Adda tace kwanki yazo gida na, nake fada mishi maganan aurenki ai, jawaheer tace eyya kwanaki ya kirani yace min zaizo bai zoba na kirashi lokacin wayanshi a kashe, adda tace kai mutumin nan yana sonki shima sosai Amma zabin Allah koda yaushe muke nema, jawaheer tace haka ne adda tah, adda tace ni karki samin ciwon jiki miko min jakata, tashi tayi ta dauko mata jakar tata, adda ta bude ta ciro wata leda, gora ne guda hudu, taba ma jawaheer gora daya tace gashi maza shanye, tace miye wannan kuma? Adda tace dallah shanye ban son surutu dariya tayi tare da fadin toh mutum zaisha abunda bai sani bane, tsaki adda tayi tace kyaji dashi, bude goran tayi ta kafa kai ta shanye, adda ta kara mata wani, duka gora uku ta shanye, ya rage saura daya adda tace wannan kuma gobe zan baki shi, tace toh yar tsohuwa, nan sukai ta fira tare da bata shawarar yanda zata biyar da mijinta....... Adda tace jawaheer aure ba abun wasa bane, ba abunda za kayi bane yanzu anjima kace bakayi, shi aure anayin shine har abada, dan haka ina mai baki shawara da kiji tsoran Allah ki riqe mijinki da hannu bibbiyu kiyi mishi biyayya yi nayi bari na bari domin aljannarki na karkashin kafarshi yin biyayya ga miji na kara mishi son matarshi, sannan duk inda kike ki zamto mai riqema mijinki mutuncinsa, zaisa mijinki ya yarda dake karki kuskura ki bashi hanyar da zai fara zarginki, domin zargi yana lalata aure, tayi ma jawaheer nasiha mai ratsa jiki inda daka karshe tace mata shi zaman aure hakuri ne gaba dayanshi kin san duk abunda akace bauta sai anyi hakuri, sun dade suna fira kafin ta tafi dakinsu taga zarah nata bacci abunta wayanta taga yana wuta da sauri ta duba taga 11 miscall sa sauri ta bude taga duka na samir ne, kiranshi tayi kashe wa yayi ya kirata da sauri ta dauka tambaya ya jefo mata da fadin ina kika shiga? Tace ina dakin adda, yace tazo ne? Tace eh dazu tazo shine naje muna ta fira, murmushi yayi tare da fadin shine kika manta dani koh dan kinga adda, tace ko daya kana raina koda yaushe kasan ni ce nake sonka kaga kenan bazan manta dakai ba, yaji dadin magananta sannan yace wani irin so kike min? Tace sonda nake maka bazai iya misaltuwa ba, amma ka bari a hankali zaka fahimta, ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin gobe ina nan tafe mai zaki tanadar min? Tace mai kake so? Yace ke kawai nake son gani dariya tayi tare da fadin saurin mai kakeyi? Yace nayi missing dinki sosai uhm kawai tace, murmushi yayi tare da fadin bari in barki sai na dawo goben, tace ok Allah ya kawo min kai lafiya ya amsa da fadin ameen, itama kwanciya tayi tana tunanin samir dinta yanzu gobe shikenan mun zama mata da miji.












Rana dai bata karya sai dai uwar diya taji kunya inji masu iya magana, yau take friday ranan daurin auren jawaheer da samir da misalin karfe daya da rabi aka daura auren akan sadaki naira dubu dari wanda dubbanun mutane suka shaida cikin daurin auren harda shugaban kasar spain da manyan yan kwallon kafa da abokan arzikin samir duk sunzo tare da masoyanshi shugaban kasar nigeria shine wakilin jawaheer, an daura aure mutane sun watse ana ta san barka, tunda aka daura auren aka fadama jawaheer wani irin faduwa taji gabanta nayi ga jikinta yayi mata wani irin nauyi ta rasa gane wani irin yanayi take ciki farin ciki take ko akasin hakan, tana zaune a dakin adda ta kwanta adda ta shigo tana fadin kinzo kin kwanta a nan ga mutane can anata tambayanki har samir dinma ya dawo ashe kina nan, bata motsa ba balle tayi magana, jin muryanshi tayi ya shigo dakin lumshe ido tayi yau itace rana ta farko da take jin kunyan hada ido dashi, kiran sunanta yayi da jawaheer tashi kiga kyautar da nace zan baki ranan daurin auren mu, kamar karta tashi amma ta tashi taga wata mata amma tasa nikaf da wani namiji kallo daya zaka masa kasan balarabe ne, namijin ya fara fadin Allahu akbar wlh wannan yarki ce nadia ga kaman ku nan sak, jawaheer kam ta shiga rudani, matar ta cire nikaf jawaheer bata san lokacin data saki ihu ba tare da nuna matar da hannu dan tabbas itace a wannan hotan na passport lokaci daya kuma tasa kuka tare da fadin dama kina raye shine baki taba nema naba? Matar ta matso kusa da ita tana kuka dai dai lokacin mum da dad suka shigo dad yace tabbas itace ta bamu jawaheer, matar tace jawaheer shekaru ishirin da biyu yanzu ina fama da ciwo wanda ba komai yaja min ba sai tunanin kina wani hali, a ina zan ganki na bata tsawon wannan lokacin da tunanin inda zan ganki iyayena sunce in cireki a raina dan sun san hala kin mutu amma naki yarda da hakan, sai gashi a yau tunani na ya zama gaskiya ta nuna m samir tace lallai jawaheer kinyi dacen miji shine ya sadani dake Allah yayi ma aurenku albarka, jawaheer cikin kuka tace mai yasa kika bayar dani mai yasa kika gujeni tun ina yar karama ta? Matar ta nisa sannan ta sauke ajiyan zuciya tace yanzu zan fada miki.....










TUNA BAYA.....


sunana nadia ahmad yar kasar saudiya iyayena mu biyu suka haifa nida yayana muhd, mun taso cikin gata da kulawa kasancewan mahaifina mai kudi ne shi sosai, ummi na tana ji dadi fiye da komai nata tun ina yar karamata ake fadamin inada kyau, tun banyi wayau ba nake da burin zama doctor sau tari in ummi ko abba na tambaya na mai zan zama sai ince doctor haka na taso da son zama dr har na gama secondary skul dina na fara jami'a inda na sami course din da nake so wato dr, zan karanci fannin zuciya hawan jini da suger, a lokacin maza da dama suna rubibina amma bana basu dama, domin karatu nasa a gaba, gashi iyayena duk abunda nace shi sukemin har yayana yayi aure amma ni ban taba tunanin yin aure ba harna kammala karatu na fita da first class gwamnatin saudiya ta bani aiki duk da dad dina yaso ya gina min asibiti na kaina nace a'a kasata zanma aiki, ana cikin haka wani dan uwan abba na yazo yace yana sona naki yarda abba na har yayi fushi tare da fadin ya kamata ace nayi aure, nace mishi zanyi amma ba yanzu ba, ana cikin haka shugaban kasar nigeria a lokacin yazo da mahaifinshi asibitin da nake aiki wanda a lokacin ciwon zuciya yake nice dr din da zan dubashi, cikin ikon Allah na fara dubashi yana samun lafiya, ashe president muktar kabir sona yake lokacin kasancewan mahaifin nashi ya dade a asibtin yasa muka saba dasu, harya samu sauki aka sallameshi bayan sun koma muna waya akai akai harya fito ya fadamin abunda ke ranshi a lokacin nima banyi musu ba na amince mukai ta soyayya har magana taje wajan iyayena inda suka nuna su sam bazan auri dan nigeria ba sai dai in auri dan kasata, haka naki yarda na bijire musu har abinci na daina ci na daina sha na rame sosai, ganin haka yasa sukace sun amince amma duk abunda ya biyo baya babu ruwansu, hakan yamin dadi ba tare da tunanin komai ba nace na amince, haka akayi bikin mu aka tawo dani nigeria muka sauka a villa, inda matarshi take mai suna hauwa, matarshi ta amsheni hannu bibbiyu hakan yamin dadi, saida mukai sati biyu muna amarci kafin ya koma kan kujeransa wanda yaba mataimakinsa na wucen gadi, mutane da dama suna ta bani kyauta dan inyi musj hanya wajan mijina, daka baya ya hana dan baya son kowa ya sanni, haka na daina fita amma ita uwar gidanshi kowa ya santa, haka muke zama dashi bai taba haiyuwa ba, ina zuwa kam na sami ciki, tun daka lokacin na fara ganin sauyi wajan kishiyata yayin da mijinmu ke murna, a lokacin ta fito da kishinta karara harda kanin mijinmu yake biye mata ita tana tsoran in haiyu in mijin mu ya mutu in fita gado tunda ita ance ba zata taba haiyuwa ba, shiko kanin mijinmu yna tsoron in haiyu a hanasu gado, hka suka tsangwameni, wata rana president yayi tafiya suai hatsari a jirgi babu wanda ya rayu, gashi a ranan na haiyu, a gida aiko inata wajan window din daki na naji hauwa da kanin mijinmu suna fdin suje su kashe abunda na haifa, babu shiri naje dakina na dauko kudade nasa da password dina nayi sauri nayi rubutu, na fita daka gidan ashe sun ganni suna ta bina shine na hadu da wa innan bayin Allah na basu ke da nufin koda sun kama ni, ni daya zasu kashe, amma Allah bai basu sa'a ba na tsere, dakyar na samu akamin password da wuri nabar kasar na koma saudiya wajan dangina, koda na fada musu abunda ya faru, abba ya fadama gwamnatin saudiya ta kwatar min yancina yanzu hauwa da kanin mahaifinki suna bursuna za suyi shekara hamsin da aiki mai tsanani tunda sunyi niyan kisan kai Allah bai basu dama ba, har yanzu ba'a raba gadon mahaifinki ba saboda baki dawo ba kuma hauwa na prison, nasha zuwa nigeria ko zan ganki amma babu wani labari sai shekaran jiya wannan bawan Allah yazo min da maganarki da farko ban yarda ba saida muka ga pics dinki ya kuma fadamin shine zai aureki, naji ddi sosai domin shiba karamin mutum bane sananne ne, kuma naji dabi'unsa masu kyau ne ta nuna mutumin da suka zo tare tace ga yayana , rungumeta jawaheer tayi tana kukan murna tare da kara godema Allah da aka haifeta ta hanyar aure nadia taita ma su dad godiya bayan an kimtsa dad ya dauko kudi yaba nadia yace ga kudin da kika bamu lokacin, kai ta girgiza tare da fadin dawainiyar da kukayi da jwheer banda abunda zan biyaku wannan kudin naku ne halak malak, dad yana ta mata godiya, samir kam sai kallon jawaheer yake yana bukatar su kebe amma taki tashi kuma ta lura da hakan.......
































*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 53-54














Mum din jawaheer ta kalli samir tace wani shirye shirye za kuyi kuma yanzu? Yace dinner ne amma a spain za ayi da yau kuma so mu wuce can ma dan dinner din gobe ne, nadia tace eh toh sai a shirya koh tunda kun tsara hakan, hakan ko akayi aka fara hadama jawaheer abubuwan bukatanta harda kawayenta aka akai airport cikin masu tafiyan harda adda😀 jawaheer ita da m samir suna mota daya driver na jansu, hannunta ya riqe tare da matsewa yace kin kara kyau da girma miye sirrin? Fisge hannunta tayi dariya yayi yace nayi laifi kenan? Kai ta girgiza alaman a'a, tace ban san da wani baki zan maka godiya ba, amma zan dan gwada nagode daka sadani da mum dina yau ya kasance min ranan farin ciki ranan da aka daura min aure kuma ranan daka kara min wani farin cikin nima Allah ya bani ikon faranta ma.... Toshe mata baki yayi da hannunshi sannan ya matsa kusa da ita yace yau nima zaki bani abunda nake so, tureshi tayi ya fara dariya ita kam ta rufe fuska har suka isa airport suka shiga jirgi, jirgi biyu ne aka basu dan mutanan sunyi ma jirgi daya kadan dan naga harda yan jawaheer fans group a tafiyan da yan hausa novels da yan maryam obam novels da sauransu...... Kowa ya shiga jirgi aka daga zuwa kasar spain duk yawan mutanan nan a hotel aka saukesu sannan ance suci komai kyauta duk abunda sukeso ga kudi da aka basu gaskiya sudai shar yan biki, ita kam jawaheer da mum, dinta da dad dasu adda gidansu na kasar suka sauka, jawaheer da mama take kiran mum dinta, jawaheer na makale da mamanta shiko samir gidanshi ya nufa yana shiga yaga sonia abun ya bashi mamaki hugging dinshi tayi tare da fadin congratulations na tayaka murna, abun ya bashi mamaki musamman da bata nuna komai ba akai, dakinshi ya nufa ya fada toilet dan yayi wanka bai dade ba ya fito yasa wasu kananan kaya sunyi mishi kyau sosai, ji yayi yana son jin muryan jawaheer dan haka ya dauki wayanshi ya doka mata kira, amma a kashe dan tsaki yayi tare da fadin bata sa sim

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login