Showing 30001 words to 33000 words out of 63876 words

Chapter 11 - JAWAHEER HAUSA NOVELS BY MARYAM OBAM.txt

20 Jan 2025

6923

so ka koya?? Yace komai amma nafi son in fara koyan gaisuwa, nan ta fara koya mai gaisuwa tana fada mai da turanci saita fassara mai, sannan ta koya mai tambayan abu, da wasu yan abubuwa, murmushi yayi tare da kunna wayanshi taji magananta ashe recording yayi, kokarin kwace wayan ta farayi wai zata goge garin haka ta fada jikinshi sukai qasa, wani irin yanayi dukansu suka shiga musamman ma shi, domin kirjinta ne ke kwance akan jikinshi, ganin irin kallon da yake mata yasa ta tashi da sauru tare da fadin kayi hakuri, baice mata komai ba harya tashi sannan yace baki ji ciwo ba? Kai ta daga mishi alaman eh, cikin sanyin murya tace muje gida dare ya farayi, tashi yayi yace muje, mota suka shiga aka sauketa kaman bazai fita ba komai ya tuna oho ya fito har kofan gidan ya kaita sannan yace mata saida safe, bata bashi amsaba ta shige, a falo ta tarar dasu mum harda dad, mum tana ganinta tace jawaheer daka ina kike maiya sami wayanki? Tace mum muna tare da m samir sannan na canza number ne, ido dad ya bita dashi yace saboda me kika canza number kuma baki bamu ba, tace dad m samir ya siya mana dazu nan ta fada musu number din suka saka, dad yace zai tafi hotel din daya sauka mum ta rakashi jawaheer kuma tayi dakin da take kwana ita da mum.










M samir koda ya isa an kira sallah isha'i dan haka saida yayi sallah sannan yayi wanka ya kwanta, amma kuma sai me?? Tunanin jawaheer ne cike a ranshi, musamman dazu data fado mishi jiki ido ya lumshe tare da fadin maike damuna? Kanwata ce da sauri yace no bazan iya ba kanwata ce kawai sabuwan da mukayi ne yasa nake jin wani abu but zanyi dan nesa da ita, duk yanda yaso ya cire tunanin jawaheer ya kasa daka karshe recording din da yayi ya kunna yana jin muryanta yana dariya har bacci ya daukeshi.












Itama ta gefen jawaheer tunanin nashi tai tayi ga wani irin azabban sonshi dake kara shiganta, Allah ya sani tana hakuri da irin son da take mishi amma ya kasa fahimta wani lokacin har tunani take inda zaice ta bashi jikinta zata iya bashi dan dai kawai yasan tana sonshi, duk da wani lokacin tana kokarin cire shi a ranta amma ina abun ya gagara sai dai kullum tayi sallah tana roqan Allah mafi alkhairi.










Washe gari da safe jawaheer ta tashi da wuri, ita ta share tsakar gidan tare da hada kayan wanke wanke ta wanke su tas, adda ta fito tace jawaheer keda baki da lafiya inake ina aiki? Mai makon ta bata amsa saita gaidata da fadin ina kwana adda, murmushi adda tayi tace lfya ya karfin jikin naki? Tace alhmdlh naji sauki, adda tace haka akeso Allah ya kara mana lfya, tace ameen yar tsohuwa, dariya adda tayi tace aina fiki kyan jiki, jawaheer tace wa tab aida ban sami samari ba, adda tace ina samarin tunda kika zo banji anyi sallama ba, niko sanda ina budurwa zo kiga layi, jawaheer dariya take tayi tana fadin ba wani layi kakana kadai ke zuwa inna aureshi nasa ya sallameki dan kin mai tsufa, mum ce ta fito tana dariya tare da fadin ina kwana adda, adda ta amsa cikin fara'a tare da fadin kinga yar nema sauki ya samu zata damemu da surutu, mum dariya tayi dan harga Allah taji dadin yanda jawaheer ta sake yau har take ta fira, wanda rabonta data sake irin haka tunda tasan basu bane iyayenta amma yau gashi tana ta surutu, mum tace adda ina zan sami waina shi nake son ci yau, adda tace shine tun jiya baki magana ba aida anyi yau,kira abubakar ya siyo miki, tace toh daki ta koma ta dauko wayanta ta kira abubakar, sannan ta dawo tsakar gida inna adda da jawaheer keta kulla alale, suna fira, ita hannu tasa ta taya su, har suka gama jawaheer ta daura akan murhu, har alalan yayi suka faraci amma banda mum dan tana jiran waina, sallaman abubakar ne yasa su duka suka daga kai, amsawa sukayi sannan ya shigo ya ajiye cooler din tare da gaida adda, itama mum gaidashi tayi sannan itama jawaheer, bayan ya amsa yake tambayan jawaheer ina m samir bai zo bane? Tace eh bai zo ba uncle, murmushi yayi tare da fadin bari inje in shirya yau yace yawo zamu tare, mum tace yadai kamata shima yaga gari da irin al'adunsu, harya tashi zai fita ya dawi tare da tambayan ina mlm mahaifinsu kenan, adda tace yana bacci, yace mai gari jiya ya ganni yake tambaya na wai dagaske khausar ta dawo gari, nace mishi eh yace shine mlm bai fada mishi ba, nace toh nima ban san dalilin hakan ba nayi tafiya ta, mum tayi dan murmushin takaici tare da fadin naga kasar nan ta kowa ce kuma kowa zai iya zuwa inda yake so, koda can baya rashin sanin yanci nane yasa akamin haka, adda tace Allah dai ya kyauta suka amsa da ameen, sannan abubakar ya fita, jawaheer kam bayan ta tattare kayan da suka ci abinci ta wanke daki ta koma tayi kwanciyanta tare da tunanin m samir, haka taita zama a daki har wajan karfe daya ta fito tayi alwala ta koma tayi sallah, bayan ta idar taji mum na kiranta fita tayi tace mum gani, mum tace kije kici abinci mana, kin shige daki ko dai jikin ne? Tace a'a mum tashi tayi taje ta zuba abinci kadan ta zauna kusa da mum tana ci tana tunanin ina ma mum ce mamanta ta gaskiya da tafi kowa farin ciki, ajiye abincin tayi dan taji yana mata daci, mum tace badai wai har kin koshi ba? Tace eh mum bana jin yunwa sosai, shuru mum tayi dan tasan halin jawaheer ba'a matsa mata akan abu yanzu ta fara kuka, jawaheer damuwa ya mata yawa na rashin ganin m samir haka taita zama har yamma amma shuru bai leqo gidan ba, har mum da dad suka fita koda dad yazo yace ta bisu taki yarda ta bisu tace suje, tana zaune a falo adda ta zauna kusa da ita, duk tana lura da jawaheer tace jawaheer nikam wani irin so kikema wannan yaron haka? Jawaheer tayi dan murmushi tare da fadin adda niwa nake so? Adda tayi dariyan manya tace kaji ja'ira, bayan keda bakinki kin fada munji ko kin manta ne? Jawaheer tace kai ku tsofaffin nan bakwa mantuwa wlh, adda tace jawaheer naga kaman shi bawai yana sonki bane, irin yanda ke kike sonshi, amma zan baki shawara duk da nasan miye so ya kuma akeji dan nima auran so nayi duk da a lokacin ba'ayi, hada ku akeyi sai akaci sa'a muna son juna, ya kamata kibama wani namiji dama dan ya shiga cikin rayuwanki sannan ki nunama samir kema a matsayin dan uwa yake a wajanki yanda shima yake nunawa, ji jaraba wannan abun guda biyu idan kikayi zan kara miki wasu, jawaheer tayi dariya tace zan gwada yar tsohuwa suna zaune kam sai gashi wani yaro yayi sallama, wai ana kiran jawaheer, kallon juna sukayi ita da adda, sannan adda tace kaje kace tana zuwa, yaron ya fita jawaheer tace adda taya zani bayan ban san ko waye bane? Adda tace sai yasa nace kije ki gani, tashi tayi daka ita sai dogon wando da top amma yakai mata giwa sai wani dan shara sharan gyale ta yane kanta dashi, fita tayi taga wata mota kiran matrix tsayawa tayi sai taga an bude motar wannan dr din ta gani wanda ya dubata a asibiti, da murmushi akan fuskanshi yace bismillah ki shigo ciki mana, tace nan ma ya isa ai yace ba mutunci bane mu tsaya a waje...... Hasken mota ne ya hasko su, motocin m samir ne da security dinshi tun daka nesa ya hangosu suna tsaye, bayan motar ta tsaya ya fito zai wuce dr yace m samir tsayawa yayi tare da fadin dr ya aiki? Dr yace lfya tare da miga mai hannu suka gaisa hada ido sukayi da jawaheer wani irin kallo ya mata mai kama da harara, sannan ya shige ciki, dr yace shigo muyi magana, jiki a sanyaye ta shiga ciki,yace nazo inji ya jikin ki? Tace na warke nan ya fara mata surutai wanda gaba daya bama jinsa take ba, shiko m samir yana shiga yaga babu kowa sai adda ya gaidata da hausa tana ta mamaki tare sa fadin sai anjima kallo ta bishi dashi dan mamaki harya fice bata ce komai ba, koda ya fita yaga sun shige mota tsaki yayi tare da kawar da kanshi gefe ya shige mota akaja suka bar wajan.......






















*maryam obam*


*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 33-34














Jawaheer kam bata Jin komai na abunda dr yake fada mata, shima kaman ya lura da hakan yasa yace mata bari ya barta yaga kaman ta gaji, hakan ya mata dadi yace ta bashi number dinta, bashi tayi sannan ya bata ledoji manya guda biyu daya kawo mata, amsa tayi tare dayi mishi godiya sannan ta fita tayi gida, a falo ta tarar da adda tana cin danwake, zama tayi kusa da adda tace adda samir yazo naga bai dade ba ya fita, adda tace hmm aini yau yaban mamaki, kinji hausa gaidani yayi da hausa harda cemin saida safe, jawaheer kam shuru tayi tana tunanin mai yasa ya tafi bai bari ta shigo ba, jin adda tayi ta katse mata tunani da fadin nasan ya ganki keda wani koh? Tace eh adda wannan dr din nanne yazo dubani, kinga yanda ya sakar min harara nan taba adda labarin abunda ya faru, adda tayi murmushi tace jawaheer inaso ki nutsu ki bama wannan dr din lokacinki dan ki nuna ma m samir kema fah akwai masu sonki, jawaheer tace adda shifa dr gaidani yazo yi ba sona yace yakeyi ba, adda tace aida haka zai fada miki, kedai kawai kiyi abunda nace..... Sallaman mum ne ya katse musu firan da sukeyi, jawaheer da fara'a tace mum har kun dawo sannu da zuwa, mum ta amsa tare da fadin dad dinki yace kije yana waje, tashi tayi ta fita ta sami dad a mota, dad yace jawaheer gobe ni zan koma ko akwai abunda kike bukata? Tace a'a dad babu komai sai dai ina son ka canza masu adda gida inda hali, dad yayi murmushi yace naso nayi hakan amma m samir ya rigani dan dazu abubakar yake fadamin fitan da sukayi gida yaje ya siyan musu cikin adamawa, abubakar yace gidan babba ne akwai komai da komai domin gidan wani barawon gwamnati ne wanda ya saci kudi shine gwamnati ta kama gidan ta saida, jawaheer tace kai Allah ya saka mishi da alkhairi, dad ya amsa da ameen, sannan yace an fara biyan kudin aikin haji, zan biya musu sai yasa zan koma ma gobe, sannan ina aiyuka, jawaheer tace Allah ya saka maka da alkhairi dad, murmushi yayi tare da kara son yar tashi ba ita yama abu ba amma tana ta godiya, kudi ya dauko ya bata ta amsa tare da fadin dad nida transfer kamin ma da yafi, dad yace toh riqe wannan din bari in miki transfer din ma, nan ya mata transfer tace kai dad kudin yayi yawa, yace jawaheer kudin da nayi ta sanadinki ne in baki ciba wa zaici, sannan million dari din da mum dinki ta bani lokacin data miqa mana ke, dasu na fara sana'a har nayi mugun arziki inada kalan kudin wajan sau million, na ware miki million dari na ajiye duk sanda naga mahaifiyarki zan bata kudin, wani hawaye ne ya zubo ma jawaheer tare da fadin dad idan na tuna baku kuka haifeni ba ina shiga cikin wani hali, wlh dad zuciya na yana zafi inna tuna hakan dan Allah dad kubar tunamin, ta karasa zancen cikin kuka, ya janyota jikinshi yana bata hakuri tare da fadin jawaheer ke yata ce har gobe, murmushi tayi tare da fadin ngd dad, yace bari inzo in tafi bacci nake ji, tace toh saida safe dad, gida ta koma inda ta sami adda ta fiffito da kayan da dr ya kawo kayan tea ne manyan gwangwani dasu milo sugar kwali dasu biscuit chocolate, mum tace ashe dr yazo dubaki? Tace eh mum, mum tace wannan hidima haka Allah dai ya saka mai, adda ta amsa da ameen, jawaheer kam haushin kayan ma taji tana yi, dan me yasa zai kawo mata suma, tashi tayi ta nufi daki, bata dade da shiga ba mum ta shigo, tace mum ashe samir ya siyama su adda gida? Mum tace eh wlh gobe zamu gidan ma muga in akwai abunda yake bugata duk da abubakar yace basai ansa komai ba, amma gobe zamu mu gani, jawaheer tace Allah ya kaimu, jawaheer ta kasa bacci babu abunda take son ji sai muryan m samir tashi tayi ta fita ta kira number dinshi amma taji ance switch off, tsaki tayi ta koma daki ta kwanta sai juyi take tayi.










Washe gari tunda jawaheer tayi sallah asuba take ta kallon wayanta tana tunanin kota kira m samir ne, amma tana tunanin kaman bai dace ta kirashi yanzu ba, dan safiya ne, haka ta zauna akan dadduma harta fara bacci, bata farka ba sai wajan 9 ta ganta akan gado, murmushi tayi dan tasan mum ce ta kawota gadon, fita tayi ta nufi toilet, tana fitowa taga adda tace ga ruwan wanka nan dama yanzu zan kiraki, jawaheer tace toh yar tsohuwa, ansan ruwan tayi ta shiga toilet din, wanka tayi sannan ta fito ta shirya cikin atamfa riga da skirt ya mata bala'in kyau kaman ba itaba, adda tace kai jawaheer atamfan nan ta miki kyau amma na lura dake kaman ke bakya son irin wannan kayan kin fison kiyi ta shiga kaman ba musulma ba, dariya jawaheer tayi tace lah nice ba musulma ba? To a kunnen mai gidan, dai2 lokacin mlm ya fito yace kyaleta amarya ta kishi takeyi dariya adda tayi tace ni na yafe mata kai, jawaheer tace kaji kishin koh kaman dagaske take, dariya duka sukayi mlm yace yaushe zaku gidan? Mum tace anjima kadan abubakar muke jir..... Bata rufe baki ba saiga sallaman abubakar da m samir sun shigo, gaban jawaheer ne ya fadi kallo daya ya mata ya kawar da kanshi, gaida su mum yayi, itama jawaheer ta gaida uncle dinta, ya amsa sannan ta gaida m samir wanda ya amsa a dakile ba tare daya ko kalleta ba, mum tace ma m samir yaci abinci kuwa? Yace a'a tace ai naga alama murmushi yayi mum ta kalli jawaheer tace kema kije kici abinci kafin mu tafi, sannan ki dauko m samir kayan tea tace to, kitchen din adda ta nufa ta hada mishi kayan tea tare da soya mai akwai, falo takai mai shi daya ne a falon su mum na waje suna fira, ajiye mai tayi tare da fara kokarin hada mishi yace no leave it zanyi da kaina, sororo tayi tare da ajiye spoon din jiki a sanyaye, tana son yin magana taji yana fadin gobe zamu tafi abuja, da sauri ta dago tana kallonshi amma shi ba ita yake kallo ba, tace da wuri haka, bana tunanin zan biku gaskiya wani irin kallo ya mata da yasa tayi saurin yin qasa da kai, adda ce ta shigo tace jawaheer kuyi sauri mana, fada mishi dan Allah tunda baji nama yake ba, cikin sanyin murya tace ance kayi sauri muje, kai ya daga alaman yaji, tashi tayi itama ta fita waje da ido ya bita harta bace mai sannan ya lumshe ido, tana tafiya yaji abincin ya isheshi dan haka tashi yayi ya fita shima, uncle abubakar yace zaije kasuwa bada shi zasu ba, mum da adda suka shiga mota daya jawaheer da m samir kuma mota daya, sai security din dake mara musu baya, sai sharara gudu mota takeyi amma babu mai cewa komai, wayan jawaheer ne ya fara kara dan haka ta duba taga number ne, mamaki tayi toh wa yasan number dinta ita dai tasan bata kira kowa ba, har kiran ya tsinke wani kiran ya kara shigowa ta kalli m samir taga ba ita yake kallo ba dan haka ta dauka, tana dauka taji anyi mata sallama ta amsa yace nasan baki ganeni ba koh? Tace eh, yace dr ne, harga Allah ta manta ta bashi number dinta, tace eyya yaka koma gida? Yace lafiya qalau sai dai na tafi da tunaninki, tayi dan murmushi wanda a dai2 lokacin m samir ya waigo suka hada ido, wani irin kallo ya mata wanda yasa tayi saurin juyar sa kanta gefe, ci gaba tayi da wayan taji an fisge, da sauri ta waigo taga yana watsa mata wani irin kallo, yace dawa kike waya? Tace friend dina, yace ok daka yanzu in zakiyi waya a gabana karki karayin wani yare sai english, bata ce mai komai ba ya jefa mata wayan tare dayin tsaki kadan, bai kara ko kallonta ba balle ya mata magana wayanta ne ya fara kara, ganin number din dr yasa ta kashe wayan gaba daya, tafiya suke har suka karasa wani dangareren gida sukai horn mai gadi ya bude, suka shiga ciki bayan an faka suka fito, m samir yana fita baiko bi takan jawaheer ba ya nufi wajan su mum, jawaheer kam canjin da yake nuna mata ya fara damunta domin taga yana nuna halin ko in kula da ita tun jiya, amma koma dai miye yau sai taji miye dalili, shiga gidan sukayi wani dangareren falo suka shiga wanda yaji kayan more rayuwa, adda salati ta fara tana fadin ina zamu kai wannan gida? Dariya su mum suke ta mata suna fadin adda an zama yan gayu, gidan yayi bala'in haduwa gashi gidan sama, falo biyu ne a 'kasa sai daki daya a kasan, sama kuma falo daya ne sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login