Showing 3001 words to 6000 words out of 63876 words
Chapter 2 - JAWAHEER HAUSA NOVELS BY MARYAM OBAM.txt
dad ya kalli mum yace haba bilkisu mai yasa kike irin haka kina ganin yarinya ta shigo cikin wannan halin sai ki dinga sakar mata tsaki ,tace toh mai zance? Indai akan wannan shirmen ne na jawaheer bani da abun cewa sai dai tsakin yarinya kullum bata da aiki sai fadin M samir M samir haba dan Allah ,jawaheer jin haka yasa ta kara fashewa da kuka dad yace yakuri J ki kyale mum dinki sannan M samir zai tashi insha Allah cikin shagwaba tace dad dagaske? Kai ya daga ya kuma cewa insha Allah, hawayen fuskanta ta goge tare da fadin dad dan Allah yaushe zaka hadani dashi? Murmushi yayi tare da fadin Ambassador dinmu na kasar Spain bashi da lafiya yana asibiti munyi magana idan ya warke zai fadamin sai ya hadaku dariya ta saki tare da fadin kai dad ina sonka sosai dad idan ya ganni zaiji yana sona kuwa? Mum tsaki tayi ta tashi tabar wajan dan takaici shiko dad ci gaba yayi da sauraran yar tashi yace sosai kuwa ai nasan idan ya ganki saiya rude sosai dan babu wanda zaiga my daughter yace bata mai kyau ba ,jawaheer cikin jin dadi tace dad kaga idan muka hadu ina gama skul sai ayi bikin mu koh?dariya dad yayi yace duk yanda kika tsara hakan za'ayi tashi dad yayi tare da fadin bari in fita ina da meeting karfe 6 kice ma mum dinki na fita tace ok dad take care yace i will my dear fita yayi ita kuma ta nufi dakin mum din nata ,a zaune taga mum tayi tagumi jawaheer tace mum lfya kuwa? Mum ta sauke ajiyan zuciya tare da fadin yauwa zo nan ki zauna bayan jawaheer ta zauna kusa da mum take cewa dad yace in fada miki ya fita,kai mum ta daga alaman toh, sannan ta kalli yar tata tace jawaheer wai yaushe zaki gane kin girma ne? Yaushe zaki farka daka wannan mahaukacin mafarkin da kikeyi ne? Shifa wannan mutumin da kike hauka a kanshi bai sanki ba yau ki duba shekarunki ishirin a duniya amma baki da saurayi tsayayye duk masu sonki in sunzo sai ki koresu yaushe zaki fahimci cewa shi wanda kike hauka a kansa bazai iya auranki ba..... Kukan jawaheer din ne yasa mum yin shiru tana kallonta cikin kuka tace mum ba mafarki nakeyi ba Mum kema kin san M samir gaskiya ne yana cikin duniyar mu kinga mum shiba mafarki bane mum bana jin zan iya auran ko wani namiji inba M samir ba wlh mum shi nake so inama zan iya nunama duniya zuciya ta taga irin son da nake mishi mum ko kin san idan ban sami M samir ba zaku iya rasani mum wlh ina cikin hayyacina tsantsar sonshi ne yasa nake duk wannan abun mum ki fahimce ni..... Salati mum ta saki tare da fadin nashiga uku wlh jawaheer kin samu tabin kwakwalwa..... Tace mum lafiya na qalau babu abunda ya sami kwakwalwa na ,mum cikin tausayi tace inko babu abunda ya sami kwakwalwanki toh wlh kinyi gamo ne cikin biyun nan dole akwai daya ban taba ganin irin wannan masifan ba dan Allah jawaheer ki cire wannan abun indai kina so in tabbatar da kina cikin hankalinki, kuka jawaheer ta kuma saki tare da fadin mum nayi kokarin inyi hakan amma na kasa mum idan ban auri M samir ba mum bana tunanin iya ci gaba da rayuwa na mari mum ta sakar mata ji kake tas.......
*comment dinku yana min kadan sannan plz sharhi nake bukata ba thx ba dan yana da matukar amfani*
*maryam obam*
[02/01, 14:23] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
Page 4
Rike wajan tayi tana hawaye mum tace jawaheer ki farka daka wannan mafarkin da bazai taba zama gskya ba, keba yarinya bace ki daina yaudaran kanki kuka mum ta saki itama ta fara magana cikin sanyin murya tare da sigar rarrashi tace jawaheer ke daya ce y'ata mace ina sonki fiye da yanda kike tunani bana son duk wani abu da zai saki cikin damuwa koya taba lafiyanki nafi kowa son inga yau kin sami abunda kike so amma wannan abunda kike so bamai yihuwa bane dan Allah jawaheer ki cire wannan kwallon a ranki da shi dan kwallon da kike so ki nutsu ki fitar da miji cikin manemanki kiyi aure idan kikayi aure hankalinki zai kwanta zaki manta da wani M samir, kai jawaheer ta fara girgizawa tare da fadin kiyi hakuri mum inama zan iya hakan da nayi farin ciki Allah ya sakamin son M samir bana iya ganin zan iya rayuwa da wani namiji inba shiba mum ki fahimce ni ban taba kin duk wani abu da kika fadamin ba wannan yafi karfina ne son M samir a jini na yake wlh mum Allah shine daya koh toh idan ban sami M samir ba zan iya mutuwa tana fadin haka ta tashi tabar dakin mum din nata da gudu tana kuka itama mum din kuka ta saki tare da fadin wlh jawaheer tayi gamo dole insa ayi mata addu'a na shiga uku wannan wani irin bala'i ne ita kuma irin tata jarabawan kenan son bature wanda suke kyamar yan africa suke kiran yan africa animals mum daukan wayanta tayi ta kira maman kabir hjy hauwa, bayan ta dauka suka gaisa hjy hauwa tace bilkisu lfya kuwa naji muryanki kaman kina cikin damuwa? Tace hmmm hauwa kedai bari kawai wlh jawaheer tana son sani cikin damuwa maganan nan bata waya bace kina gida yanzu in shigo? Hjy hauwa tace ina nan ki bari bari ni inzo mum tace toh sai kin shigo ina dakina in kinzo hjy hauwa ta amsa da toh sannan suka kashe wayan.
Basu dade dayin sallama ba hjy hauwa ta shigo gidan, da sallama ta shigo dakin mum, mum ta nuna mata waje tare da fadin bismillah ga waje nan, bayan hjy hauwa ta zauna mum tace hmmm hauwa ina cikin damuwa sosai, hauwa tace mai yake faruwa bilkisu kimin bayani nan mum ta fara bama hjy hauwa labari irin abubuwan da jawaheer takeyi itama hjy hauwa salati tayi tare da fadin ikon Allah wannan wani irin sabon al'amari ne haka? Mum tace wlh kema kya fada yarinya kaman wacce tayi gamo da aljanu, hjy hauwa tace gskya nima ina tunanin haka domin inba aljanu ba babu abunda zaisa ta dinga tunanin haka Allah sarki jawaheer ,mum tace toni yanzu miye mafita? Hjy hauwa tace mafita daya shine mu kaita wajan malami ya mata ruqiya kin san akwai *BAQIN ALJANI* *sunan novel dina* da basa bayyana sai suyi tasa mutum yaita abu kaman hauka ko su hana mutum aure duk yanda akayi jawaheer tana tare dasu inko ba haka ba ai ba zata kamu da son wanda bata taba gani ba bata da tabbacin ma zai aureta ,mum tace oh ni bilkisu na shiga uku ,wlh da walaki dan jawaheer da ba haka take ba tama tsani kwallon kafa amma lokaci daya yarinya ta birkice, yanzu yaushe zamu wajan malamin? Hjy hauwa tace bari in kirashi inji yaushe yake nan, doka mai kira tayi ringing uku ya dauka bayan sun gaisa tace mlm dan Allah yaushe kake nan akwai yarinyar kawata da take da matsalan jinnu inaso mu kawota koh Allah zai sa a dace, ban san mai yace mata ba naji tace toh Allah ya kaimu sannan sukai sallama, kallon mum tayi tace yace gobe da karfe hudu mu sameshi a islamiya sannan tare da jawaheer din zamu ,mum tace Allah ya kaimu, hjy hauwa tace ameen wannan abu sai an hada da addu'a, mum tace kedai bari wlh idan kika shiga dakinta gaba daya hotan dan kwallon kafa dinne duk ta manne shi dashi sai kace abun hauka harta cup din da take amfani dashi na kwallon kafa ne duk an manna hotan yaron a jiki rannan tiles din dakinta naji tana fadin zata sa a saka mata mai hotanshi wai a cire mata na dakinta dakyar na hanata sai carpet tasa ta rufe tiles din carpet dinma mai hotan yaron, hjy hauwa tace ikon Allah jawaheer ita tata jarabawan kenan Allah sarki yarinya mai nutsuwa amma lokaci daya ta canza kiyi hKuri insha Allah gobe idan mukaje wajan mlm komai zai zo da sauki insha Allah, tashi hjy hauwa tayi tare da fadin bari in koma gida dare yayi mum tace toh ngd sai goben fita hjy hauwa tayi
Bata dade da fita ba khalil ya shigo dakin yana fadin mum ina jawaheer naje dakinta inata nocking naji shuru gashi tasa key a dakin kota fita ne? Mum tace hmmm tana ciki babu inda taje ya wuce tana can tana tunanin shirmen banzan ta data saba,khalil yace kai sis rigima dazu muka gamayi da ita wai anji mishi ciwo shine tazo tana kuka wlh mum abun sis ya fara bani tsoro fah ,nasha wasa takeyi amma naga ita dagaske takeyi ashe, anya mum ba zamu kai autarki asibitin kwakwalwa ba, hararanshi mum tayi tare da fadin ai duk kune kuka sata fara kallon wannan shirmen dariya yayi tare da fadin babu ruwana mum tunda bani nace ta kalla ba ita ta kawo kanta harta fara kallo gashi yanzu ta fini zagewa, mum ajiyan zuciya tayi tare da fadin Allah ya kyauta ya amsa da fadin ameen sannan ya tashi yana fadin mum inaso inje dubai cikin week din nan gskya, mum tace mai zaka jeyi? Dariya yayi ya fara tafiya yace indan huta mana na gaji da zama waje daya, mum tace matsalanka ce wannan tunda ga office an baka kaki zuwa kullum kafi son kaita zama gida yau baka can gobe baka can, dariya kawai yayi sannan ya fita.
Jawaheer tunda ta shiga daki ta rufe take ta faman aikin kuka a kasa ta kwanta akan hotan M samir tana shafa wajan fuskanshi tana fadin nasan zaka soni kaman yanda nake sonka inaji a jiki na, zanzo gareka very soon inaso ka nuna ma mum lafiya na qalau kawai sonka ne yamin yawa kazo ka aureni ka nuna ma mum baka fi karfina ba ni nasan kaine zaka aureni kazo kaba mum mamaki kaji my luv kuka ta kara saki tare da furta ina sonka sosai nasan yanzu kana cikin wani hali na ciwo amma Allah zai baka lfya inajin zafin jin ciwonka har cikin raina........ Hmmm ku biyoni muga yanda zata kaya da jawaheer a wajan mlm shin zama ta yarda taje kuwa? Dagaske aljanu gareta kaman yanda mum tace duk ku biyoni ...
*maryam obam*
[03/01, 16:47] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 5
KASAR SPAIN
M samir tunda aka fitar dashi daka filin kwallo aka nufi hospital dashi domin ba karamin faduwa yayi ba, koda aka nufi asabiti dashi hannunshi na rike da kafarshi yana cije baki, gocewan kashi yayi an kaishi asibiti kafin ace me har an gyara kafan nan labari ya bazu na ciwon da yaji inda masoyanshi keta jimami koda dad dinshi yazo hspt din cikin tashin hankali amma ganin yaron nashi a zaune yana waya yasa hankalinshi yadan kwanta saida ya gama wayan sannan ya kalli dad din nashi yana dan murmushi tare da fadin dad yakake dad din ya amsa da fadin my son ya kafan naka da fatan dai baka jin zafi sosai kai ya daga alaman eh duk cikin yaren spanish suke maganan, kallonshi dad din yayi sannan yace my son dawa kake waya haka? Ko wacece nasan soyayya kukeyi, dan murmushi yayi sannan yace sunanta sonia yar england ce ba kowa yasan muna soyayya ba sai yasa ba'a baza labarin ba, fuska mahaifinshi ya tamke sannan yace my son ka rabu da ita kasan bana son ka auri wacce ba musulma ba, M samir ya kalli mahaifin nashi sannan yace dad miye dalilinka bayan kasan addini na bai haramta min auran wacce ba musulma ba, baka tunanin jahadi zanyi idan na aureta tayu ta musulunta, kai dad din nashi ya girgiza alaman bazaka gane ba, sannan yace my son kasan kai fitaccene a duniya u r d world biggest celebrity zanso ace ka auri musulma domin duniya tasan kana kishin addininka ka duba ka gani yawanci celebrity musulmai basa auran musulma yawancinsu na rasa miye dalili sannan idan suka auri wacce ba musulma ba tarbiyan yaransu yakan banbanta kai yanzu da kake son auren yar england koh kasan yau idan kuka rabu yaran da kuka haifa sun zama nata? Sannan kasan daka ranan da suka koma gareta addininta za suyi kaga baka da ikon hana su, amma in musulma ce koda yar kasar england dince idan kuka rabu yaranka a wajanka zasu zauna duk da ka'idan kasarsu ce haka mace keda iko da yara amma su musulmai a wajansu ba haka bane tunda ba haka addininmu yace ba ,namiji shine shugaba ba mace ba, m samir murmushi yayi tare da girgiza kai yace dad duk da haka bana tunanin zan iya fasa auren sonia muna son junanmu and tunda tana sona duk wani abu da nace shi za tayi, dad murmushi yayi tare da fadin ba zaka fahimta ba har yanzu kai yaro ne, m samir dariya yayi tare da fadin dad next month zan cika 28 fah shima dad din dariya yayi tare da fadin koda 40 ka kai a matsayin yaro nake kallonka..... Shigowan dr ne yasa firan nasu ya tsaya dr yace ya kafan? Amsawa yayi da fadin ban san mai zance ba inajin zafi sosai ,dr yace kayi hakuri zai rage, kai ya daga alaman yaji, dr yace ga press nan da yawa suna son sanin halinda kake ciki ko zan iya fada musu halin da kake ciki? Yace miko min phone dinka bashi dr din yayi ya shiga wajan recording ya fara magana cikin harshen turanci tunda sako ne yake son bayarwa ga duniya baki daya musamman ma masoyanshi..... Ina lafiya ina kira ga masoya na da suyi hakuri nan bada dadewa ba zasu ganni, amma yanzu ina bukatan addu'a daka garegu ngd yana fadin haka yasa stop tare dayin saving ya mika ma dr din wayanshi tare da fadin kaba yan jarida din, dr din cikin jin dadi ya fita domin wannan maganan da yayi a wayanshi ba karamin kudi zai samu ba dan saida ma yan jarida zaiyi.
NIGERIA ABUJA
washe gari bayan jawaheer ta tashi bata fito daka daki ba ganin har 11 yayi bata fito ba yasa dad dinta ya nufi dakinta amma a rufe saida ya kira sunanta sannan ta tashi tazo ta bude mai kofar, rungumeshi tayi tana kuka tare da fadin dad dazu naji a news M samir ya sami gocewan kashi dad dan Allah ka kaini spain in ganshi ko zanji dan sauki, dad cikin tausayin y'ar tashi ya dagota daka jikinshi yana share mata hawayen fuskanta yace kiyi hakuri jawaheer ki daina wannan kukan nayi miki alkawarin hadaki dashi indai Ambassador kasar spain na nigeria ya warke, cikin kuka tace dad koba ta hanyar ambassador ba zaka iya hadamu plz dad do something ni daya nasan mai nake ji a cikin raina dad yace shikenan my dear zansa a mana visa na kasar spain zamu tafi cikin week din nan cikin jin dadi tace i luv u dad, dariya yayi tare da fadin muje kici abinci toh ,binshi tayi suka nufi dinning zama sukayi dad da kanshi ya zuba mata abinci ta fara ci mum ta fito tagansu ta tabe baki tare da fadin Allah ya baki lfya jawaheer dad yace bata jin dadi ne? Mum tace a'a ina nufin lafiyan wannan sabon haukan da yake son kamata, tamke fuska dad yayi tare da fadin kinga bilkisu ki dinga sanin abunda zaki dinga fada akan jawaheer bana son irin abubuwan da kike mata kina nunawa kaman baki damu da ita ba,mum tace Allah ya baku hakuri nayi shuru dad yace hakan shine alkhairi jawaheer na zaune tana jinsu lokaci daya kuma ta fada duniyar tunani gata a kasar spain sun hadu da M samir ya ganta ya rude harya furta mata kalman so ido ta lumshe cikin jin dadi a hankali ta furta i luv you too wanda bata san maganan ta fito ba jin mum dinta tayi tana fadin kaga abunda nake fadama koh wlh jawaheer tayi gamo da aljanu, ya kamata ka yarda da abunda nake fadama, dad baice komai ba illa kallon jawaheer din da yake tayi cikin tausayi duk cikin yaranshi yafi son jawaheer sai yasa komai ta kawo yake dauka harya biye mata amma a gskya wannan karan shima ya fara tunanin abubuwa da dama duk da dai baya son ya nuna mata ta gane, ganin irin kallon da dad dinta yake mata irin kallo na tuhuma yasa tabar wajan da sauri, mum hannu ta tafa tana fadin oh ni bilki naga takai na, yarinya sai tayi abu kaman mai aljanu anjima kuma tayi kaman mai tabin hankali, dad yace wlh bilkisu abunda kike ma jawaheer inda badan ke kika haifeta ba da sai ince kin tsaneta ne, akan me zaki dinga danganta ta da me aljanu ko tabin hankali duk wannan maganganun da kikeyi sam bai kamaceki ba ki daina ma y'ata irin wannan munanan alkaba'in bana so, shuru mum tayi bata kara cewa komai ba dad tashi yayi tare da fadin ni na tafi villa ina da meeting da shugaban kasa, mum tace Allah ya taimaka amma dan Allah kayi hakuri bana so ka fita kana fushi dani kaji my handsome, dariya dad yayi tare da fadin kin iya zolaya bilkisu ki ganni tsoho dani kice min wani handsome cikin dariya itama tace ai a haka kullum nake ganinka, fita yayi yana fadin bari in tafi 12 dai2 zamu fara tattaunawa, har yayi nisa mum tace anjima zamu fita nida jawaheer cikin jin dadi yace ko kefa ai yana dakyau ki dinga janta a jiki sosai