Showing 27001 words to 29601 words out of 29601 words

Chapter 10 - KARA'IN INNA DELU Book Bye Maman Afrah.txt

20 Jan 2025

4304

shi kaɗai ma ya san abin da yake ji saboda maganin fa ya sha shi kaɗai ya san hali da masifar da yake ciki.




"Yau dai na ga avin da ya fi ƙarfina, a ce wai mijin mahaifiyarka yana tsaye a gabanka da gajeran wanda jikinsa na tashi wannan wace irin rayuwa ce" Cewar Abba a zuciyarsa a fili kuma sai ya ce
"Inna dan Allah mu je in taka ku ɓangarenku" Ya faɗa yana kallonsu dan ya ga su ko a jikinsu.


"Ikon Allah na zaune ya faɗi, Sa'adu ni kake kallon tsabar idona kake faɗa mini mu tafi ɓangarena sai kace wanda suka zo da mugun abu in faɗa maka fatalawar ubanka Malam tana can ɓangarena amma ka ce wai mu zo ka raka mu dama ai ba kai ka rako mu nan ɗin ba"


"Allah baki haƙuri Inna"


Banza ta masa idanunta a kan Jauro da ke ta wani harhaɗe ƙafafu dan yanzu maganin nan ya fara tsuma shi.


"Wai kuwa Bebi in fitsari kake ji ai ya kamata ka je ka yi, dan, amma ya za a yi ka rinƙa haɗe ƙafafu kamar ƴan sanda za su sarawa shugabansu"
Jauro kwa ko kaɗan ya kasa furta komai dan gabaɗaya mararsa tsinkonsa take sai wani zate ido yake ya rasa yadda zai yi.


"Bebi a bamu ɗaki a nan mana sai mu yi kwanciyarmu kin san da can da nan duk ɗaya ne"


"Haba ya za a yi mu kwana a nan sai dai a je a kori fatalwar mu koma ɗakinmu ai l
ɗakin mutum sirrinsa"


"Inna bari in je in gani" Cewar Abba yana kama hanya ya buɗe ƙofar ya fita ba tare da ya jira cewarsu ba. Yana zuwa ya shiga ya duba ko ina amma babu kowa dan Abubakar suna fita ya fice dan dama burinsa ya tsorata su, kuma ya san tun da suka fita to ba za su wuce ɓangaren Baba ko Abba ba. Haka Abba ya shigo ɓangaren bai ga kowa ba har ƙuryar ɗakin ya leƙa ya fito ya koma ya kirawo su Innar dakyar suka koma sai da suka tabbatat babu komai suka shiga dan a zatonsu fatalwar ta tafi.


Bayan sun tabbatar babu kowa Abba ya musu sallama ya tafi. Suka shiga ɗaki abinsu.


*WASHE GARI*


Tun kan na shiga ɗakin Inna nake jiyo sautin kukanta sai yi take tana face hanci, ina shigowa na yi tozali da Inna kwance reran magashiyan tana kuka abinta ahi kwa gogan yana gefe ya ɗora kan Inna a kan cinyarsa sai aikin lallashi yake a kan ta yi haƙuri ta daina kuka.




"Haba Jauro yanzu tsakani da Allah baka dubi tsufana ba ka haike mini kamar wata budurwar amarya"


"Haba Delu ki yi haƙuri mana, duka-duka awa takwas ne fa na yi amma gobe tin daga farkon dare har asubahi irin wannan gyara da kika sha aradun Allah ko Kande lokacin amarcin budurci bata kai ki ba"


Wani irin washe baki Inna ta yi jin an yabe ta, amma kuma wani raɗaɗi da ya ziyarce ta sai ya hanata darawa sosai.


A hankali ya kama hannunta ta tashi zaune tana ɗan ciccije baki, kamar an ce ta leƙa ƙasanta aikuwa ta shiga rafka salati tamkar ta ga kwarata turmi da taɓarya.


"Haba Deluna zunzurutun maƙwallaton zuciyata, ai wallahi kin fiye mini mata dubu d...


"Haba wace irin Delunka ashe haka ka mini rata-rata, ka kekketa ni, kamar wata takarda" Ta faɗa tana sakin wani marayan kuka


"Haba Bebi amarci ne fa yanzu ma aka fara ai, ni tsakani na da ke babu abin da zan ce sai addu'ar shiga aljanna"


"Yo ba dole ka ce haka ba bayan ja gama dani yanzu Allah na tuba ko tafiya zan taka da ƙafafuna ai na san tatata zan rinƙa yi ni ba wata ƴar shayi ba amma a haɗa ni da tafiya ƙafafu a gwagwgwale" Ta faɗa a ranta a fili kuma ta ce


"Wannan Lanatana an yi shegiyar yarinya kudurarriya, ita ta kai ni gidan mai maganin mata gashi ta janyo mini shan wahala"


"Haba Bebi ni kwa ai na ji daɗin abin da ta yi ai ƴar albarka ce yarinya ai ta gyara aure" Ya faɗa yana washe baki, wata harara Inna ta jefa masa dan yanzu wani haushinsa take ji tana ganin ta yaya za ta zo tana tafiyar tatata a gaban ƴaƴa da jikoki har ma da sirikanta.


"Allah maimaita mana Allah ƙara maimaita mana mummunai" Ya faɗa da sigar waƙa yana wani rausaya kai kamar wani ƙadangaren da ya samu kedar manja.
Banza ta masa ta shiga ƙoƙarin tashi tsaye tana wani ciccije baki.




Ai Inna na duro da ƙafafunta daga kan gadon, ta tashi tsaye sai gata tana sakin wani ihu mai haɗe da kuka a lokaci guda dan ƙafafunta karkarwa suka shiga yi gabaɗaya ta kasa tsayawa da ƙafarta saboda azaba. Da sauri ta koma ta zauna a karkace ta gwale ƙafafu ta ɗauki muhuci ta shiga fifitawa ai wani raɗaɗi da ya ziyarceta saboda yadda iskar ta shiga sai ga Inna na sakin wani hawaye wani na bin wani.


"Sannu Bebi" Ya faɗa yana kanne mata ido. Kanta ta ɗauke duk abin duniya ya isheta.


"Allah raba bawa da wahala wai gwauro a teburin mai shayi, in ba tsautsayin takaba ba auren shiɗaɗɗe ina ni ina wannan aiki fisabilillahi ni ƴasu da wane idon zan kalli Umaru da Sa'adu a ce a daren farkon amarcina an farkeni kamar wata ɗanyar kaza ko ma in ce kamar wani tsohon buhun siminti" Cewar Inna a zuciyarta taa sauke idanunta a kan Jauro.


"Tashi in raka ki bayin " Ya faɗa yana kama hannunta dakyar ta tashi ya shiga kafaɗarta. Taku ɗaya biyu ta yi Jauro bai ankara ba sai ji ya yi ta sakar masa wani uban dundu a bayansa fa sauri ya dakata yana kallonta da mamaki fuskar nn tata sharkaf da hawaye.


"Haba Dulu wai duk amarcin kike yiwa wannan raɓetun da hawaye kamar wata ƴar shekaru sha uku, to aradu a daren farkonmu da Kande cewa take ja mu je direba kar ka tsaya direba amma banda tuƙin ganganci, amma ke ba da waƙa ba lokacin ana aiki sai bayan an gama ki zo ki rinƙa raki har da su duka kamar wanda na saɓi Allah"


Wani haushi da kishi ne suka turnuƙe Inna dan a duniya ta tsani ya yabi Kanden nan bare a ɓangaren aiwatar da sunna dan haka cikin zafin nama ta janye jikinta daga gareshi za ta tafi bayin da kanta aikuwa tana ɗaga ƙafar sai ta zauna a ƙasa ta karkace.


"Wannan dai ragwanta ce aradun Allah Delu"


"Ka manta kakar ragwanta ce, yanzun nan na ji kamar an tsala ni da reza ko adda tsabar raɗaɗi da azaba, amma kana kiran ragwanta mutumin nan jiya ko tausayin tsufana baka yi ba ka rinƙa haƙa rijiya da mugun ƙarfi kamar ka samu shebir, haka na daure sai da ka mini fata-fata, yo ina dalili ina ɗan mafari za a kassara mini mafitar ɗa, wannan ai gamganci ne haihuwa da damina, kana tuƙi baka san hanya ba kawai sai ji nake wani garrrrr, gugurummm, buuuuu, haka kawai ka maidani kamar wata kwalta ina dalili ai ni dai cin amarcin nan bai mini rana ba wallahi yo abin da ka yi ne ya fi ƙarfin hankali da na sani wallahi haka na yi zamana salam-salam babu wani gyara bare matsi, ni ce harda su maida tsohuwa yarinya, ni ce cicciɓi kai babu wani abu da na raga masa na amate dan duk mu damu ƘARAI mai tsayawa a zuciya amma gashi ka maidani kamar wacce aka fiddo daga injin markaɗen kayan miya, ai wallahi ka wuce gona da iri yo ina zan iya tafiya da ƙafata yau ai sai ka kirawo mini Shattu da Lantana dan na san yau dai sai an mini rubdugu"

Cikin sauri ya ɗakko riga ya saka mata ya ɗakko tiri kwata wando na jeans ya saka tare da t-shirt ya zo ya gifta ta gabanta zai kirawo mata su Shattu aikuwa giftawar da ya yi duk da halin da Inna ke ciki sai da ta ji ya birgeta kayan da ya saka dan ɗaya daga cikin wanda suka siyo ne. Sauri yake har ya je ya kirawo su, lokacin ma har wajen ƙarfe takwas da rabi, suna tafiya suka haɗu da Abba da Baba suna tsaye suna magana. Da kallo suka bi su Jauro wani takaici na cika musu rai na kayan da Jauron ya saka amma babu yadda suka iya haka suka durƙusa suka gaishe shi, shi kuwa Jauro har da wani saka hannu a aljihu yake wani ƙwambo.


"Baba Shattu lafiya dai na ga kuna sauri" Baba ya tambaya dan bai kawo komai ba.


"Yaro man kaza na yiwa uwaka aika-aika" Jauro ya faɗa a ransa a fili kuma ya ce


"Gyatumarku ce ba lafiya tana nan magashiyan tana neman ɗauki na ce dai bari na samo mata ƴa uwanta mata su suka san yadda kan abin yake"


"Mai ya sameta?"


"Yo ɗan nan kake bincike, amarya ce fa kuma ka san amarya ko ta buzuzu ce sai an...


"Haba Baba Shattu" Lantana ta katse Shattu dake ƙoƙarin sakin layi, dan su Baba basu ma gama gane abin da take nufi ba.


"Ke dai wannan ƴa da shegen sanabe kike yo waye bare a ciki na ga uwarsu ce ita ai damuwarta damuwarsu ce mu je ke in ga halin da take ciki" Ta faɗa tana ɗan faɗansu na tsofaffi ta wuce ba tare da ta jira cewar su Baba ba, Lantana da Jauro suka mara mata baya.


"Allah kyauta" Cewar Abba da Baba da suka haɗa baki wajen faɗa duk da basu fuskanci inda maganar ta dosa ba.




Shattu da Lantana suna shiga suka gant sharaf a tsakar ɗaki dama shi Jauro bai shigo ba a falo ya zauna yana jira su yi abinda za su yi.






"Delu mai zan gani haka?" Shattu ta faɗa da mamaki a fuskarta


"Kai Shattu mi ƴasu wannan al'amari da wuya yake abu ji kake gigigi kaar haɗarin mota wallahi ko darena na farko da Malam ya karɓi budurci ba a yi wannan badaƙalar ba, yo turnuƙun da aka sha ba na wasa bane , Wallahi Lantana ba dan zuciyar musulunci ba a shekara ma ba zan bar kwashe mata sulusin albarka ba, wallahi Shattu da za kinga matantaka ta da kin ga tsiyar da Jauro ya tafka mini, yo ya mini fata-fata kamar ya samu tsohuwar besfa sai da ya mayar da ni kamar an daddatsani da gatari ba ma wuƙa ba" Cewar Inna tana riƙe da haɓarta.


"Haba Delu yo ke garin ya haa ta faru, mu da muna can muna jiran in an ci amarci mu zo mu ci ragowar kazar da safe, sai jin bugun ƙofa muka yi tun da sanyin safiya ina buɗewa sai ga ango afujajan wai mu zo kina buƙatar taimakon gaggawa, na ce masa ka yi aiki ne ya ce ai aika-aika ma ya yi, ke ma ai bakya bari ya miki lugude ba kamar wata gumbar sadaka"


"Haba Shattu dan rashin imani ma haka zaki ce, yo banda dai neman sababi irin naki ya za a yi a haɗa ƙarfin namiji da mace, yo da idan aka maƙureki ko motsin kirki kin isa ki yi, yo ji za ki yi kamar jirgin sama ya danne mota, babu wani kataɓus da za ki iya yi, haba kamar dai baki taɓa auren ba Shattu"


"Yo ko na taɓa aure yanzu mai zan adar abu da ya wuce kamar shuɗewar lokacin bazara, wannan bayani ai sai ke da kika yi ƘARA'I jiya"


"Hummm ni na san abin da na ji jiya ni na san abin da ya ziyarce ni aradu bana ko tantama Jauro ya kwankwaɗi maganin ƙarfi dan ƙarfin nan na jiya ba nashi bane ƙarfi kamar marashin doki, ai da jin ƙarfin ka san ba na tsoho bane"


"Yo kema baki zauna hakan ba ai ɗure- ɗurenki da kika yi kaɗai ya isa ki zautar da ɗan tahalikin nan"
."To dan na yi ɗure-ɗure sai aka ce ya mini fyaɗe yo meye marabar dambe da faɗa ai wallahi mai maganin matan nn da ta dafa mini cicciɓi na cicciɓe mata albarka kanta ya fi cikin kwando dan idan da sauran albarka ma a kanta to bai fi cikin cokali ba dan wallahi ta cuceni ni kaina ban san iyakar cutar da ta mini ba, in ba rashin imani da tausayi ba ta yaya za ta bai wa tsohuwa abinda zai zama ajalinta, kawai ta saka in ke tafiyar tata ta ni ba ƴar kaciya ba cinyoyin nan nawa kamar an karairaya mini ƙasusuwan saboda tsabar suke sagewa yo ina dalili wannan amarci ko wahala ai daga yau mi da Jauro haihata-haihata mun yi hannun riga, da rana dai ma yi waricinmu ido na ganin ido amma waricin na hira ba wani abu ba dare kwa na yi zai kwana a falo ni in ɗaka yo aradu sai dai mu raba jaha...


"Haba Delu ke da kije da kishiya ko kin manta da Kande ne, maimakon ki ɗaura ɗamarar ƙwace mijinki ta hanyar rattaba sunna sak ba gajiyawa amma daga yi rana ɗaya ki sare kina maganganu masu sakin layi kina nuna gajiyawarki zai raina ki bayan kin san da bakinsa ya ce awa bakwai yake kwashewa yana sunna da Kande" Shattu ta katse mata maganar.


"Ke dallah rufe mini baki kar ki yi saɓo ma yo wace kishiya kuma, ƙyaleni da maganar sunnar nan yo shegiya ce ni zan yi kishi da aikata sunna, sai kace wacce uwata ta ce jeki kya gani, zan zauna ake rugurguzata kamar wata ƙanzon tuwo, to indai kin ganni a lahira kaini aka yi amma ba da ƙafata na je ba"


"Da Allah kar ki bani kunya ya kike neman bada mata Delu, kina ga dai yau ɗaya yadda ya susuce sai rawar ƙafa yake a kan ki, ba saboda komai bane kuwa sai dan canjin da ya ji amma kina neman ɓata rawarki da tsalle"


"Allah wadaran naka ya lalace yo ina ruwana da rawar ƙafarsa ai ko rawar ɗuwawu zai yi babu abin da ya shafi Delu, babu abin da zai shalle ni kuwa, da kike maganar zan bauar da mata to wallahi na bayar da mata kyauta kuwa indai a kan wannan doguwar sunnar ne da ake gabatarwa babu ƙaƙƙautawa kamar kamar sallar tarawihi'


"Ikon Allah na kwance ya faɗu ke kwa Delu ina soyayar da kike ikirari kina yiwa wannan bawan Allahn tun ta budurta?"


"Na bi soyayya da gudu dan gwafar ubanta, yo ina dalili indai a kan wannan abin ne na jiya na yafe wannan ai wahala ce ba soyayya ba, ina laifin ma a yi abu saisa-saisa Shattu amma abu yake tahowa ruuuuuu kamar tasowar guguwa babu tsayawa sai kace za a yi tashin duniya, kamar ana yaƙin duniya na uku, yadda tsohon nan ya mini rata-rata wannan ko likitocin da suke ɗinke mata idan sun ƙaru a haihuwa wallahi sun yi kaɗan su ɗinke ni kin dai ga yadda suke ɗinke su kamar wasu ƙwarake, ni yanzu yadda na yi wayam ɗin nan a ɓarɓarke sai ko a samo allurar makaffi da zaren buhu a ɗinke ni, in ban ɗinku ba sai dai a ɗora ni a kan keken ɗinki a ɗinke ni yadda ake ɗinke zanen atamfa, in ban ɗinku ba aradu Shattu sai ko a barni a haka in tafi har kabari a ɓarke, kai wannan ƘARA'I bai mini rana ba Shattu" Ta faɗa tana sakin kuka hannayenta bibbiyu a kumatun ta, ta yi tagumi kamar wacce aka faɗawa saƙon mutuwa.
A NAN FREE PAGE YA KARE
Mai son ji har karshen labari ya biya 500 ta faiza Abubakar 9030283375 opay a tuntubeni ta 09013181851

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login