Showing 21001 words to 24000 words out of 29601 words
ta gabaɗaya zai gudu da ita ya mata fyaɗe, dan sosai ta tsorata da lamarin abin da saurayin nan ya mata, sannan bata zaci Jauro zai iya ɗaukanta ba. Tana ɗan ɗago fuska ta sauketa a kan fuskar angon nata da ta sha manja abinta sharkaf, kamar daron da ake siyar da manjan wani tausayin kansu ne ya kama Inna Delu ganin halin da suka tsinci kansu a ciki a yau da ta kasance ranar farinciki.
"Bebi in ce dai ka sumar da shi da ƙarfen nan?" Cewar Inna tana kallonsa. Ai maganar nan da Inna ta faɗa Jauro ji ya yi wani kishi ya ƙara taso masa gashi ba ya so ya faɗa mata gaskiya ta ga ragwantarsa dan haka sai ya ce
"Ai na masa illa, ma dakyar mutane suka ƙwace shi, yana can lange-lange aka tafi da shi asibiti" Ya faɗa yana kallon gefe dan kar ta gano ƙaryar da ya sheƙa mata. Wani daɗi ne ya baibaye Inna jin an ɗau mata fansa hakan ya sanya ta ƙara jin ƙaunar Jauro a ranta.
"Lallai na auri miji na nunawa sa'a" Ta faɗa a zuciyarta tana jinjina jaruntarsa.
Tun da ya ɗakko Inna Delu mutane suke ra binsu da kallo samari da ƴan mata kuwa sai ihu suke ganin ango ya yiwa amarya ɗaukan jarirai, hakan ya sa wurin ya ƙara kacamewa da ife-ife shi kuwa bai bi ta kan koa b duk da nauyi yake ji da ya ɗauki Inna kamar wanda ya ɗauki buhun gero, dan dakyar yake ɗaga ƙafafunsa ƙarfin hali ne kawai yake. Ɗakin da aka ajiye musu kayan da za su canja da magriba saboda ƙayatarwa to yanzu kuma tun da komai ya kwaɓe musu dole yanzu su canja kaya tun da kayan sun ɓaci da manja.
Suna shiga ɗakin Jauro ya nufi wata kujera mai zaman mutum ɗaya da ke ajiye yana zuwa jaɓar ya saki Inna a kan kujerar ashe kujerar tsohuwar kujera ce dan haka Inna ji kawai ta yi ta ɓurma ciki, kafin raɗaɗin faɗawar ya gama ratsa t sai ji ta yi mazaunanta sun yi karo da wata ƙusa wani uban ihu ta saki wanda ya saka Jauro da ke sunkuye ya ɗago dan tun da y jaɓar da ita a kan kujerar ya sunkuya saboda ƙagewa da bayansa ya yi na gudun da ya tiƙa da kuma ɗaukan da ya yiwa Inna.
"Wayyo ni Delu yau dai ina ganin sauyawar kalolin rayuwa kamar wacce iyaye suka jeki ka gani, in banda jafa'i da neman rarrabuwar sassan jikin mutane ya za ayi a ajiye wannan ƙazamar kujerar mai jiki duk ƙusoshi " Ta faɗa tana ƙoƙarin kai hannu wajen mazaunan nata tare da sakin wani kuka.
"Haba Delu wai me yasa kike haka ke ba damar a yi abu sai ki ɓare baki ki fara kuka kamar matar marigayi, saboda ke ga mai arahar hawaye"
"Au haka ma zaka ce Jauro, bayan ka jefa ni kan ruɓaɓɓiyar kujerar nan na faɗa a kan ƙosa"
"Wato Jauro gatse-gatse ko sakayawa babu, ko kan ƙaya tsidau na jefa ki ai kya gode mini domin kuwa na yi namijin ƙoƙari da na ɗakko ki a hannu na, tun daga filin can har nan, hannu na da kafaɗata kamar an sara mini da gatari saboda tsabar ƙagewa da suka yi"
"Na faɗa Jauro, kamar wani wanda na yi saɓon Allah dan na faɗi sunanka shin da soyayya ma tana bari masoyi ya ji nauyin masoyi, baka ga yadda turawa ke ɗaukan matansu ba"
"Ashsha Allah baki haƙuri Bebi" Ya faɗa dan kawo ƙarshen maganar.
Banza ta masa tare da taɓe baki, tashi ta yi dakyar daga kan kujerar ta shiga bayi ta wanke fuskar tas ta fito ta cire kayan ta sanya wanda Lantana ta kawo musu, shi ma ya shiga bayin ya gyara jikinsa tare da canja kayan nasa sai gasu sun fito a amarya da angon su. Hannunta ya kama suka fito suna sakarwa juna murmushi gabaɗaya wuri ya ruɗe da fitowarsu haka suka ƙarasa wajen teburinsu.
"Yanzu amarya da ango za su yanka cake" MC ya faɗa.
Cikin washe baki suka tashi Jauro sai washe baki yake jin zaa yanka cake dan gabaɗaya yawun bakinsa ya tsinke. Haka suka kama hannu a tare suka yanka cake ɗin.
"Ango zai fara bawa amarya a baki sai ita ma ta bashi" Cewar MC.
Jauro hannu ya kai ya ɗakko cake ɗin da ya gutsuro da wuƙa, ya nufi bakin Inna da take wani ɗan sunkuyar da kai alamar kunya irin ta amare, dakyar da ta buɗe bakin aikuwa ya saka mata, a take aka ɗauki ihu da tafi.
Inna tunda cake ɗin ya isa bakinta ta ji wani irin ɗaci da tsami a lokaci guda haɗe d warin kananzir, amma haka ta daure ta ɗan runtse ido yadda mutane ba zasu lura ba ta haɗiye ba tare da ko taunawa ta yi ba ita kaɗai ta san bala'in da ke cikin cake ɗin wanda ya ziyarceta amma kuma bata ya aka yi haka ta faru ba.
"Amarya sai gareki ke ma za ki bawa angon naki cikin shauƙi na soyayya" Inna da ta yi nisa wajen tunanin ya aka yi haka ta kasance ta tsinkayi muryar MC yana magana.
Inna cikin rashin kuzari ta yanko cake ɗin ta ɗauka a hannunta, tunda ta fara yankowa yawun Jauro ya cigaba da tsinkewa sai haɗiyewa yake wani yawun na ƙara taruwa, bare da ya ga ta ɗakko a hannunta ai har wani dillo harshe gake, sai dai yadda Inna ta birgeshi ƙato ta yanko ya san dai duk faɗin bakinsa dole wanda ta yanko ya cika masa baki. Inna kuwa tunaninta ɗaya kar fa ta saka masa a baki ya kunyata ta, dan ta san dai akwai gwarama matsawar Jauro ya ji ɗanɗanon cake ɗin gashi tana so ta masa bayanin kar ya kunyata ta amma kuma idanun jama'a a kansu, sannan tana so ta masa raɗa a kunne sai dai ta ga gabaɗaya hankalinsa a kan cake ɗin yake sai wani raba ido yake yana washe baki.
"Haba Delu ƙur'ani kika yi jinkirin saka mini cake ɗin nan a bakina sai dai jama'a su ga yawu yana dalalowa daga bakina saboda gabaɗaya yawuna ya tsinke ƙiris yake jira ya zubo" Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma sai ya shiga ɗan kannewa Inna ido ɗaya yana mata alamar ta sama.
Hannu ta ɗaga a hankali tana so ta saka masa a bakin nasa har dai ya yi ƙarfin halin cewa
"Wannan ɗaukan alhaki da yawa yake Delu mai magana (MC) A dodon magana (Lasifika) Yana cewa in baki na yi saurin baki amma ni kike jirgani" Ya ƙarasa faɗa cikin raɗa-raɗa. Ta ji shi sarai amma sai ta masa banza.
"Bebi ka ce azumi kake" Ta faɗa masa ita ma cikin raɗa dan ta lura in ta zauna masa bayanin abubuwan da ke cikin cake ɗin ba ganewa za ta yi ba.
"Azumi fa kika ce Delu yo wane shegen ne zai yarda azumi nake, yo ni rabona sa azumi tin wancan shekarar, ko azumi nake saboda ket (Cake)Ɗin nan aradu na karya shi katsak sai dai in yi istigfari" Ya faɗa yana aikwa Inna wata harara dan ya lura kamar baƙinciki take ya ci cake ɗin.
"Amarya ke ake jira fa domin kowa yana son ganin kalar taki soyayyar" Cewar MC ganin amarya ta yi jinkirin bada cake.
Wani irin gyaɗa kai Jauro ya yi irin na kin dai ji ai ɗin nan. Inna kuwa wani kallo ta masa tare da ɗan danne gefen leɓenta ta saki wani murmushin yaƙe.
Wani irin hangame baki Jauro ya yi ganin za a saka masa cake aikuwa Inna tana zuwa bakin ta tura cake ɗin cikin bakin nasa tare da ƙara zungura shi da hannunta. Jauro kuwa da ya buɗe baki jin dirar wani tsatstsaman abu mai shegen ɗaci da wani warin kananzir sun baibaye masa baki, wani irin yamutsa fuska ya yi tare da zaro idanu dan gabaɗaya abun ya haɗe masa baki.
"Haɗiye mana Bebi" Cewar Inna tana sanya hannu ta haɗe masa leɓɓan bakin. Wani amai ne ya yunƙuro masa amma ganin Inna riƙe da leɓunansa ga idanun mutane a kansu dan kowa ya yi zaton duj cikin salon soyayya ne haka ya daure ya haɗiye dakyar yana neman yin amai aikuwa aka shiga tafa masa.
"Kai jama'a da kun san mai na ƙunsa a bakin nan nawa na haɗiya da baku tafa mini ba" Cewar Jauro a zuciyarsa kamar ya yi kuka.
Duk abin nan da ake Amna tana laɓe daga wani wuri tana kallonsu, dan ita ce ta je kicin ɗin Inna inda aka ajiye cake ɗin ta jiƙa bula lemo, ta yi amfani da sabon sirinji wajen zuba wa a jikin cake ɗin, ta jiƙa filajin mai yawa gabaɗaya ta ɗore a cikin cake ɗin daga ƙarshe ta ɗura kananzir duk da sirinji. Bayan ta je gidan su ƙawarta shi ne ta biyo ta wajen partyn na Inna domin ganin ya za ta kaya.
"Ba dai kin ce sai kin yi aure ba duk da iyayenmu sun hana ki kaɗan ma kika gani" Cewar Amna a zuciyarta.
Haka dai aka gama taro aka watse motoci suka maida su Inna gida.
Washe gari da yake a ranar ne za ta tare da yamma suka tafi gidan wata mai maganin mata duk da wanda Inna tasha wanda suka siyo daga kasuwa amma sai da ta ce Lantana ta raka ta dan tana so ta rikirkita ango haka suka je da Shattu da Inna da Lantana direba ya kai su. Cicciɓi aka dafawa Inna ta cinye, da ƴan shila aka ƙara mata da maganin matsi har da na gyaran nono, haka suka cake kuɗin mai kayan suka bata tun a mota Inna take ta sakin wani murmushi, Shattu ce ta gaji ta ɗan matsa kusa da kunnenta ta ce
"Wai ni kam Delu dariyar me kike?"
"Hmmm bari dai ke ai na fara tunano yadda ango zai rule saboda na sha gyara, kinsan Allah Shattu a gidan mai maganin nan da na shiga bayi fitsari tsabar matsin da aka mini ko yatsa bai shiga wurin nan ba, aradu ina jin Jauro sai ya ɗauka da budurwa yake tare, dan yanzu ma ɗan tofina jargaf yake ya jiƙe yadda kika san ƙorama haka na koma" Cewar Inna tana ƴar dariya yadda direba da Lantana da suke gaba ba za su ji ba. Hannu Shattu ta bata suka tafa suna sakin wata dariya irin tasu ta tsofaffi da su kaɗai suka san ma'anarta.
Dab da magriba wata mota golf da Kande ta iyo shatar ta tun daga garinsu aka ɗakko mata kayanta, ita da wata budurwa ƴar ƙawarta mai suna Balaraba suka taho motar ce ta ƙaraso gidan aka ƙarasa da ita ɓangaren da aka ce za ta zauna dan Jauron ne ma ya raka ta sai kuma aka saka almajirai suka kwashe kayan.
*DARE*
*JAURO*
Sanye yake da shadda mai babbar riga hannunsa riƙe da kedoji guda biyu, haka ya je ɗakin Kande da ke zaune ita da Balaraba suna zumɓure-zumɓuren baki, da sallama ya shiga amma babu wanda ya amsa sai dai abin da ya lura da shi tun shigarsa Balaraba ke satar kallonsa tana masa wani kallo da ya kasa gane na menene. Haka dai ya ajiye musu ƙaramar leda mai tanƙwashen kifi ɗaya rak ya musu sallama babu wanda ya tanka masa ya fito ya nufi ɓangaren amarya Delu dan Inna ta ce babu wani wanda zai haɗa ta da wata kishiya ya musu kashedi dan haka ma bai tarka ba.
Yana shiga falon da sallama Shattu ce da ke cikin ɗakin ta amsa masa, suka masa iso a kan ya ƙarasa cikin bedroom ɗin haka ya ƙarasa ya same su Inna zaune a bakin gado lulluɓe da mayafi kanta a sunkuye, ƙafar nn da hannu ta sha ƙunshi, Shattu da Lantana sun saka ta a tsakiya.
Cinikin baki aka yi ya biya Shattu da Lantana suka musu sallama suka tafi ɓagaren su Lantana. Bayan fitarsu ango ya miƙe ya cire babbar riga ya matsa yana yiwa amarya daɗin baki ya buɗe fuskar.
"Allahu akbar, lallai Allah ya yi halitta a nan kin ganki kuwa Delu duk duniya babu wata mace da ta fiki kyau da matsayi a wurina"
"Har Baba Asabe?" Cewar Inna tana wani fari da ido.
"Haba Bebi idan ana dara ai fidda uwa ake, ya za a yi ki haɗa kanki da uwata"
"Allah huci zuciyarka ai na ji ka ce duk duniya yo ai na ɗauka har ita"
Banza ya mata yana jin babu daɗi a ransa, amma babu yadda ya iya tunda dai yau yana so ya kwashi ganimar amarya.
Hannun Inna ya kamo ta janye da sauri.
"Haba Bebi ya haka kuma? Bayan na biya sadaki"
"Ka biya sadaki ko dai an biya maka, wallahi kana taɓa ni na ji wani yammm "
"Duk ɗaya ne ai tun da dai mijinki nake, yo ai yammm ɗin da kika ji alamar lafiyarmu ƙalaw ne "
"Haba Jauro ai tun ranar aure aka gwadamu aka ce babu mai ƙanjamau"
"Ba wannan lafiyar ba, lafiyar gabatar d sunnar aure"
Hannu ta sanya ta rufe idanunta alamar kunya, haka dai ya kama hannunta suka zauna a ƙasan ɗakin, har sun zauna Jauro ya ce su cire kayansu dan kar su yi ƙarnin kifi.
"Ki...ki...kifi fa ka ce?"
"Eh mana kifin amarci"
"Haba Bebi yanzu tsakaninka da Allah kifi ne a matsayin kazar amarya duk yadda muka ci burin ranar nn" Ta faɗa tana zumɓura baki. Haƙuri ya shiga bata haka suka cire kaya ita sai ta saka rigar bacci mai ƙaramin hannu shi kuma ya zauna da gaeran wando kawai. A baki yake bata tana bashi sun yi nisa wurin cin kifin suna korawa da lemon kwalbar da ya sako guda biyu sai kawai Inna ta haɗiyi ƙaya lemon ta sha amma ƙaya ta ƙi gaba ta ƙi baya, tun abin kamar wasa ya koma ba na wasa ba, ganin Inna riƙe da maƙogwaro tana ta ƙolon amai, hakan ua sanya Jauro cewa
"Bari dai in je ɓangaren su Umaru ko za a samu gayan tuwo ki samu ki haɗiya ƙayar ta wuce" Yana faɗa bai jira cewar Inna ba ya fita da sauri dan gabaɗaya ma a ruɗe yake. Haka ya ƙarasa ɓangaren Baba daga shi sai gajeran wando tiɓi-tiɓi dan wandon ya kama shi, yana zuwa ya shiga doka ƙofar da uban ƙarfi Baba da matarsa har sun kwanta suka ji ana ta bugun ƙofa kamar za a ɓalla, haushi ya sanya Baban ƙin tasowa ya buɗe dan gabaɗaya zuciyarsa a dagule take haushin wai yau mahaifiyarsa ke tarewa sai wani rawar ƙafa take wai ita amarya wannan abun shi ke ci masa tuwo a ƙwarya. Matarce ta tashi tana wani yamutsa fuska ta sauko ƙasa dan a sama ma suke.Tana zuwa bata tambayi waye ba ta buɗe ƙofar Jauro da ke jiran a buɗe ƙofar yana ganin an buɗe sai kawai ya afka ciki, ita kuma bata tsaya ta tantance waye ba dan kallan tsoro ta masa tunaninta ma ko wani kwarton ne dan ganinshi tuɓe sai gajeran wando bai ƙarami ɗaga mata hankali ya yi ba.
A sukwane ta juya tana sakin ihu kwarto, ta haura sama dan step bibbiyu take tsallakewa tsabar a ruɗe take. Jauro kuwa haushinta ma ya ji dan haka ko ta kanta bai bi ba sai ya nufi kicin zai dubo tuwon san shi amaryarsa ce a gabansa ba zai tsaya dogon surutu ba ya je ya rasa ta.
Baba kuwa jin ihun matarsa da kuma kiran kwarto da take sai ya tashi ya ɗakko wata sanda wadda ya tanada saboda irin ranar nan dan haka kafin ta shigo ɗakin ma ya fito da gudu ɗauke da sanda, a bakin ƙofa suka yi kiciɓis ta shige ɗakin da gudu a ruɗe alamar a tsorace take, tana shiga shi kuma ya iyo ƙasan a sukwane, yana sakkowa falon ƙasan ya hango Jauro ya bashi baya ya nufi ƙofar fita, ganinshi da gajeran wando ya tabbatar masa da kwartancin ya zo, dan haka cikin sanɗa ya lallaɓa ya saukewa Jauro sanda a gadon baya, sai ga Jauro ya zube a reran hannunsa riƙe da gayan tuwon da ya ɗakko a kicin zai kai wa Inna taimakon gaggawa. Zubewar Jauro ta yi daidai da saukar idon Baba a akan fuskar Jauro idanu ya zaro ganin mijin mahaifiyarsa kuma angon wannan rana.
"Baba Jauro" Ya faɗa cikin tashin hankali yana jefar da sandar ya nufe shi, hakan ya yi dai dai da sakkowar matar Baban daga sama tana ɗari-ɗari.
"Alhamdulillah dear ka rafka masa sandar" Ta faɗa tana ƙarasowa inda aka baje Jauro. Banza Baba ya mata dan ya san yau sai ta Allah tunda ya rafke angon mahaifiyarsa tunanin da yake a gefe guda ma shin mai ya kawo shi ɗakin.
"Lah ashe bayan kwartanci har da satar tuwo ya zo" Ta ce lokacin da ta ƙaraso wajen idanunta a kan tuwon da ya faɗi daga hannunsa.
"Mijin Inna ne fa" Ya faɗa yana fito da wayarsa daga aljihunsa ya shiga kiran Abba. Haɓa ta dafe tana jinjina abin a ranta yanzu haka za su rayu da waɗannan tsofaffin a gida ɗaya suna abu kamar yara ƙanana a ce har da gajeran wando zai shigo musu sashen su.
"Ka zo ɓangarena yanzu" Haka Baba ya cewa Abba lokacin da ya ɗauki wayar dan shi ma yana kwance bacci ya kasa ɗaukansa abin duniya duk ya ishe sa.
Yana zuwa ya ga abin da ke faruwa ruwa aka ɗakko aka shiga sheƙa masa ya farfarɗo yana cewa
"Bebi dama ba za mu rayu tare ba, a daten farkonmu ashe zan mutu ko amarcin bamu fara ci ba" Ya faɗa yana sumbatu, su kuwa kowa jinin jikinsa ya sha. Sai da ya dawo hayyacinsa suka masa kama-kama suka nufi sashen Inna dashi sun doshi ɓangaren Innar sai ga Inna ta fito tana ɗan tari tare da