Showing 9001 words to 12000 words out of 29601 words
a ƙasan nonon nata sai ta maida nonon ya zamana shi ne a akan fanfas ɗin ɗayan ma haka ta masa tun da ta zubawa jikinta da fuskarta ido a mudubi take ta faman doka murmushi, walwala ta kasa barin fuskarta.
"Taɓ lallai na yi maida tsohuwa yarinya ni Delu ai za mu kwashi ƙara'i ta faɗa tana washe bakinta har haƙorin makkarta ya bayyana.
Hanyar fitowa daga ɗakin ta yi domin ta san yanzu Jauro yana dab da zuwa, tana fitowa hakan ya yi dai dai da wata uwar guɗa da Shattu ƙawarta ta carara ba komai ya kawo guɗar ba kuwa sai shigowar Jauro falon shi da abokinsa Mati. Tunda ya shigo yake wuwulga ido ya ga ta inda zai ga Delunsa.
"Shattu ina amaryar take?" Ya faɗa yana washe bakinsa.
"Baka gane ni ba" Cewar Inna Delu tana wani farrr da ido ita ala dole amarya.
"De, De,Delu" Ya faɗa idanunsa a waje baki sake yana nuna ta da yatsansa. Kowa ma na falon maida kallonsa ya yi kan Inna Delu ganin ɗaurin ɗankwali mai acuci gashi fanfas ɗin da ta saka ya ɗago da nonon nata sai suka hayo ƙirji hakan ya sanya ta zama kamar yarinyar mace dan sosai fandas ɗin ya yi ɗoɗar a cikin shaddar.
"Wallahi Delu kin fiye mini Kande sau miliyan" Cewar Jauro yana kallonta baki sake.
"Ai baka haɗa bama Jauro" Cewar Mati yana ƙarewa Inna Delu kallo a ransa yana rayawa ina ma a ce shi ne ya yi wannan dacen tsuntsu daga sama gashasshshe, dan ya matuƙar so a ce shi ne musamman ma da ya ji wai a binnin a wannan ƙerarran gidan Jauron zai zauna da Delun dan ɗaurewa ƙarya tsantsa ma har da ɓangaren da zai saka matarsa Kande dan Kanden ta tada badaƙala cewar ba zai tafi binni ya barta a ƙauye ba ita kuma Inna da yake so take yi tana ganin mijinta kullum sai ta saka aka gyarawa Kande wani ɗaki ciki ɗaya daga can gefe yake.Ita kuma Kanden saboda son zaman binni take gani ba za ta yi saki na dafe ba gwara dai ta zo ko a akurkin kaji ne ta zauna.
"Kai jama'a wallahi na tsinci dami a kala" Ya faɗa yana shafo farin gashin gemunsa.
"Ai yau sai ka biya mu kwalliyar nan Jauro ango" Cewar Shattu tana washe bakinta wanda ta tauna goro.
Baki ya washe ya ce
"Ai in kin ji biya ma ɗaya kenan, kar ki samu damuwa aminiyar amarya sha kuruminki, kwantar da hankalinki kamar kin kashe ɗan mutum, ko kamar tsumma a randa" Ya faɗa har lokacin idanunsa a kan amaryarsa. Nan aka shiga gaisawa da mutanen ƙauye da suka zo domin ɗaurin aure, da la'asar suka koma garinsu dan Inna ta ce sai nan da sati guda za su zo shagalin biki dan yanzu aure kawai aka ɗaura dan hankalinta da na Jauro ya kwanta.
Da daddare bayan sallar isha'i Inna ta aika aka kirawo mata Abba Sa'adu da Baba Umar a kan tana son magana da su, cikin bin umarninta suka taho a tare sa sallama suka shiga lokacin ta ɗaga waya za ta kara a kunne, sai da ta msa sallamar tasu ya musu izinin shiga sannan ta kara wayar a kunne
"Alo Jaurona ango" Ta faɗa tana wani murmushi tare da kashe murya kamar wata ƙaramar budurwa.
Daga ɗaya ɓangaren Jauro ya ce
"Amarya, amarya, amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida" Cewar Jauro yana waya dariya da sautin dariya ya karaɗe kunnuwan Abba da Baba, da yake bolum ɗin wayar a ƙure yake ana iya jiyo maganar tasa.
"Angona kenan bada kan ka a sare ka je gida ka ce ya faɗi, ina ƙaunarka Jaurona"
"Ai kin zama mallakina yanzu Deluwa maƙwallaton zuciyata"
Gabaɗaya Abba da Baba kai kawai suka sunkuyar saboda tsabar kunyar da ta ziyarce su a ce uwarsu mahaifiyarsu ta yi sabon aure yau kuma tana wayar soyayya har da kalamai kamar wata farin shiga, ƙaramar yarinya ko nauyinsu bata ji.
"Ka zo ɓangarena za a yi magana kan shagalin bikinmu" Ta faɗa tana ƙara kashe muryarta har da wani lanƙwasa muryar kamar wani lauje.
"Yanzu kuwa" Ya faɗa yana kashe wayar ya taso zai taho.
Ajiye wayar ta yi har lokacin murmushi bai bar yamutsatstsiyar fuskarta wacce tun tuni tsufa ya yiwa kamun kazar kuku. Dakyar ta iya dakayar da murmushin, ta kalli ɗiyan nata ta ce bari Baban naku ya ƙaraso dan na fi so a yi maganar shagulgulan bikin namu a gabansa ko yana da wani tsare-tsaren shi ma"
Baki sake ƴaƴan nata suke kallonta fuskarsu fal mamaki.
"Umaru, Sa'adu wai ko bakwa son albarkar iyaye ne, ya ina maganar abin da zai saka ni farinciki kuna wani kauce kauce kamar wacce ta faɗi saɓon Allah, aure ne fa ba haramun ba sunnar ma'aiki" Ta faɗa tana kama haɓa cike da mamaki dan ita har ga Allah a kan gaskiyarta take.
Da sallama Jauro ya shigo wanda hakan ne ya katse musu maganar, amsa masa ta yi ya ƙaraso zai zauna a kujera mai zaman mutum ɗaya.
"Haba Jaurona matso kusan iyalinka mana ka zauna a nesa da ni" Cewar Inna da ke zaune kan kujera mai zaman mutum biyu, su Umar suna ƙasa daga gabanta, haka ya ƙaraso yana wani washe baki yana wani baza babbar riga kamar wanda ke baza buhu a kasuwar barkono. Kusa da ita ya zauna suka zauna da ita dab da juna da ido ya kafe ta yana mata wani kallon soyayya dan ya kasa ɗauke idanunsa daga kan ɗaurin ɗankwalin acuci mazan da ta yi sosai ta masa kyau.
"Barka da dare" Umar da Sa'adu suka faɗa, wanda hakan ne ya dawo da shi daga hayyacinsa daga kallon da yake yiwa uwarsu, amma bai ɗauke idanun daga kallonta ba, amsawa ya yi ba tare da ya kallesu ba har lokacin yana kallon Inna Delu.
"Kallon fa" Ta faɗa tana rufe fuska da tafukan hannayenta alamun kunya.
"Wallahi bana gajiya da kallonki Deluna, sosai ɗaurin nan ya miki kyau ya ɗauru sosai kamar an ɗaure itace da igiya ɗaurin ya zauna daram ga wani ɗan tozo da ya yi irin na yara, sai kika dawo mini ɗanya sharaf kamar kina budurwa sai yau nake ƙara jin haushi da ba ni na aureki ba, na so a ce ni ne nan na buɗe ki a leda lokacin kina sabuwa dadal, amma Allah bai yi ba sai yau da kike da shekara saba'in" Ya faɗa haƙoransa washe gabaɗaya talatin da biyun a waje.
ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄💄
NA
MAMAN AFRAH
FCW 💛
Pag 9⃣➡🔟
Wani daɗi ne ya lulluɓe Inna Delu jin irin yabon da angon nata ke mata, ƙuri ta masa da ido tana kallon fuskar nan tasa mai yalwar furfurar gashin baki da saje. Dai dai nan Shattu wacce ita kaɗai ce bata tafi ba saboda ita ce aminiyar Delu wai sai bayan shagali za ta tafi, shigowa ta yi ganin kallon da Delun ke jifan Jauro da shi sai kuwa ta carara wata uwar guɗa, guɗar da ta carara ce ta sanya Delun sanya hannu ta rufe ido.
"Ikon Allah ga zara ga wata" Ta faɗa lokacin da ta shigo tare da ƙarasowa ta tsaya fuskarta da fara'a
"Wallahi Shattu ke dai bari garin daɗi ba kusa da wai kyankyaso ya leƙa masai ai ni ma tun shigowata nan gabaɗaya aminiyar taki ta kunce mini notin kaina ita kaɗai nake gani duk ta susutani da wani kallo wanda ko kwatarsa Kande bata iya ba, yo ina ma Kande ta iya kallon soyayya babu abin da ta iya idan tana kallona wani lokacin har cewa nake me na miki Kande? Ko na miki laifi ne? Sai ta ce me ka gani? In ce na ga kina hararata, sai ta ce ba harara bace kallon soyayya ne, to haka dai zan yi yaƙe amma ba wai dan na gamsu ba dan kawai gani zaki yi tana zare ido kamar wacce tsakuwa ta faɗawa ido can kuma sai ki ga ta gwale idon sai kuma ta runtse, da sauri nake nufarta in ce kawo in bushe miki idon naki in wani abu ne ya faɗa miki a ciki, sai ta ce ka jika Jsuro da wani abu duk a cikin kallon soyayyar fa ake har yanzu" Ya faɗa yana tuntsurewa da dariya har da ƙyaƙyatawa da ya tuno irin yadda matarsa take masa kallon soyayya bata iya ba.
"Taɓ ashe kana shan kallo"Shattu ta faɗa tana ƙilƙilewa da dariya.
"Ba ni da zara ido ba, gata da ƙwal ƙwalan ido kamar ƴaƴan carabke" Cewar Jauro har lokacin yana dariya.
"Amma ya na ga aminiyar tawa tana rufe ido?"
"Rabu da ita Shattu wai kunya ce take ji irin ta sabuwar amarya, wacce amare ke ji, ni zan cire wannan kunyar gabaɗaya, dan duk wayon amarya sai an sha man ta" Ya faɗa yana wani ƙallare ido ɗaya shi a dole ɗan duniya
"Aikuwa dai gwara ka cire kunyar nan"
"To ko in fara rage hanya yanzu" Ya faɗa yana ƙoƙarin kamo hannun Inna Delu.
"Ashsha, gyara kintsi da kyau ango"Cewar Shattu tana masa nuni da Abba da Baba da suke zaune a ƙasan capet kamar an dasa su kowanne kansa a kasa saboda tssbar jin nauyi da kunyar maganganun da su Jauron ke yi.
"La'ilaha illalahu muhammaddur rasuslullah S.A.W, an yi abin kunya yau wallahi Shattu na ma manta da yaran nan suna zaune, kin san dai ni idan Deluna tana wuri mantawa nake da kaina ma bare kuma wani" Ya faɗa hannunsa a haɓarsa.
"Haba angona ai wannan ba abin kunya bane ka san ai su ma ba yara bane, tun da har sun hayayyafa kuma waye cikinsu bai san soyayya ba wa ma ya san irin ƴar muryar da suke yiwa nasu matan, kuma ai dama an fi so ƴaƴa suke ganin iyaye na soyayya ba wai ƙiyyya ba dan yara tsanar uban da baya son uwarsu suke kuma suna jin haushin uwar da take uzzurawa ubansu sun fi so su ga ana zaman lafiya da nuna ƙauna ko ba haka bane Umaru" Cewar Inna Delu tana ƴar dariya kaɗan.
"Haka ne Inna" Cewar Baba Umar kamar ya yi kuka.
"Yawwa ɗan albarka, kai kuma fa Sa'adu ko ba haka bane?" Ta faɗa tana kallon Sa'adu da ya sunkuyar da kai ƙasa kamar zai kifa dan takaici.
Shiru bai bata amsa ba.
"Ba tambayarka ba nake Sa'adu ka watsa yina, kamar shara a bola"
"Allah baki haƙuri Inna, haka ne" Ya faɗa cikin ɗacin rai.
"Allah sarki uwa da ɗa kenan ashe kuwa maganar taki haka ne Delu, gaskiya babu wanda ya fi uwa fahimtar halin da ƴaƴanta ke ciki" Cewar Jauro yana washe baki.
"Yo ai su ma murna suke sun yi sabon uba ka ga basu da maraici kenan, shi yasa na ce mu zauna a nan ɗin kusa da su ko ba komai ma ke ɗauke musu kewa, kuma idan suna ganinka za suke mantawa da mutuwar mahaifinsu" Cewar Inna tana kallon fuskar Jauro dan ita tafi ƙaunar gemun fuskarsa fiye da komai yadda ya tashi ɗin nan ziyat ya fi tafiya da ita.
"Amarya mai daɗin tuwo amarya mai maganar siga" Cewar Jauro yana ƙara gyara zamansa, idanunsa kafe a kan Inna Delu.
"Allah gamu gareka ɓarawo a hannun mata" Cewar Abba a zuciyarsa dan ji yake kamar ya zura da gudu.
"Allah mun gode maka haƙiƙa baka ɗorawa bawa abin da ba zai iya ba" Baba ya faɗa a ransa.
"Kuna birgeni wallahi haƙiƙa kun matuƙar dacewa da juna, na so kun auri junanku tin a samartaka, sai dai Malam Lawwali ya muku shigar sauri" Cewar Shattu tana neman wuri ta zauna.
"Ke dai bari Shattu ai tuna baya shi ne roƙo" Cewar Jauro yana ɗan jijjiga kai, dan idan ya tuna Malam ne ya fara sanin Inna Delunsa a matsayin mace sai ya ji ransa na ƙuna amma babu yadda zai yi dan ƙaddara ta riga fata.
"Haka ne Shattu ya za a yi da ƙaddara, ai banda tuna baya wai gyartai ya ci sarauta" Cewar Inna Delu tana jin haushi a ranta.
"To ai yanzu kun auri junanku sai ku yi koma menene dan wuri bai ƙure muku ba" Shattu ta faɗa tana dariyarsu ta tsofaffi.
"Ai fa za ku gani, dan za a kashe arnan soyayya har ma dana ƙaunayya"Jauro ya faɗa yana jifan Inna Delu da wani kallo.
Hannu ta sanya ta ɗan rufe fuskarta tana murmushi.
"Allah nuna mana"
"Amin, ai idan aminiyar nan taki ta rufe fuskar nan tata baki ji ba yadda nake ji, ba ƙaramin tsumani take ba sosai nake ganinta kamar budurwa ɗanya sharaf, ƴar shekara sha biyar" Cewar Jauro yana dariya, gabaɗaya Inna Delu da Shattun ma dariyar suka sanya, hatta Abba da Baba sun ɗan murmusa a ransu amma murmushin na takaici ba wai na jin daɗi ba.
"Inna ko mu tafi ma yi maganar da safe" Cewar Umar yana wani ɗan ɓata rai dan ya ga abin nasu ba na ƙare bane gwara su basu wuri sa fi sakewa su yi maganar duk da yanzun ma ba wai sun fasa maganar bane kuma ko sakaya wa basa yi.
"Oh ni Delu, na ga ikon Allah faɗa da mai gari ranar sallah, yo Allah na tuba banda ƙarfin hali ɓarawo da sallama, yanzu Umaru in kirawo ka wato ba za ka iya jira in gama abin da nake ba shi ne har ka ƙagauta kana so ka tafi ka yi uzurinka da ya fi nawa, ko soyayyar da sabon uban naka yake nuna mini kke baƙinciki? Wato kana taya ubanka marigayi kishi ko, Yo in ba baƙinciki ba menene a ciki ɗan ƘARA'IN da zan yi a sauran rayuwata shi kake yiwa baƙinciki in ka yi haƙuri dai nawa ma ya rage mini a rayuwar, tunda dai wanda zai je sama ya taka leda ai ya ci ƙarfin tafiya, ni da nake da shekaru saba'in aikuwa idan da saura ma kaɗan ne, kai idan ka tafi ɓangaren naka wa ya san me za ka yi wato kana sauri ka tafi wajen matar so, waccen ƙeƙashashshiyar matar da ciyar da ita da hana ta abinci babu banbanci abu kullum a rame kamar raƙumin dawa, kullum jikinta jiya i yau, sai shegen ɗaga kai kamar ƙadangaruwa da haɗe rai fuskar nan kamar faten wake, tana tafiya tana tura baki yadda kika san bakin jaɓa"
Tun da Inna ta fara faɗa babu wanda ya tanka daga Abba har Baba kowa kai ya cigaba da sunkuyar da kansa.
"Ƙyale shi aminiya tun da dai kin auri Jauro yau kar ki bari wani abu ya ɓata miki rai ko ki yi ɓacin rai a ranar farincikin ki, ranar da kika daɗe kina dakon ta, ranar da muka daɗe muna jiran zuwanta ranar da ta zama rana mai matuƙar tarihi a cikin rayuwarku ke da angonki" Cewar Shattu da ta taso daga mazauninta ta zo gaban Inna Delu ta dafa kafaɗarta.
Wani daɗi ne ya rufe zuciyar Inna a take ta washe baki kamar gonar auduga ta ce
"Haka ne aminiyata ta gaban goshi, ai dama komai nisan dare gari zai waye kuma duk nisan jifa ƙasa zai dawo, sannan matar mutum kabarinsa, ban taɓa tunanin nesa za ta zo kusa ba, na daina faɗar abin da zai sosa raina ko kaɗan a ranar nan abin alfaharina"
"Yawwa ko ke fa, ai ni da kina faɗan ma kawai kallonki nake Deluna dan sai na ga babu banbanci da dariyarki da ɓacin ranki kowanne kyau kike a ciki, kin san ke kyakkyawa ce" Cewar Jauro yana kallonta
"Bari zuga ni Jaurona ai ni kaina na san da hakan tun da har ka ce kana sona ina budurwa yadda lokacin ka yi tashen kyau kamar amita bacas (Aminta bacha) Na indiya yanzu ma har na tsufa amma kana nan a kan bakar ka to na tabbata ina da kyau na nunawa sa'a"
"Ai har gobe ke ce tauraruwata Delu, ko Kande kawai ƙaddara ce da bin umarnin iyaye ya sa na aure ta, amma wallahi ba da niyyar na ci amanarki ba, dan ko yanzu sai in iya ƙidaye miki sau nawa na taɓa zuwa wajenta a matsayin miji, tafi kawo kanta kin ga ni kuma ai ba na ce a'a ba ko dan in sauke nauyinta kar in shiga haƙƙinta take mini kallon ragon namiji shi yasa nake ɗan yarda amma kaɗan-kaɗan ba da yawa ba, wallahi Delu kwarankwatsa dubu bana wuce awa bakwai ina yin sunna da Kande" Jauro ya kai maganar yana sakin kuka dan shi sai yake ga kamar Delu za ta ce kusantar Kanden ma cin amana ne.
"Awa bakwai fa ka ce Jauro" Cewar Inna tana dafe ƙirji.
"Haka na ce Delu, idan kuma ƙarya nake miki Allah yafe mini, wataran ne ma daga farkon dare muke kaiwa asuba, kin ga kuwa wannan ai duk ba wani abu bane ko?" Ya faɗa cikin karya murya yana karkarta kai shi a dole ta yarda dashi.
"Awa goma da wani abu Jauro, sai ka ce wani bunsuru, yo Allah na tuba in ba ɗan taure ba waye zai yi sama da awa goma yana gabatar da sunna" Cewar Shattu cikin ɓacin rai da taya aminiyarta kishi.
"Aradun Allah saisa-saisa nake yi Shattu" Ya faɗa yana share hawaye dan shi har ga Allah gani yake kamar ma ya ɗakko ruwan dafa kansa ne Delun za ta ce ta fasa, shikenan zai rasa zaman birni ya ga samu zai ga rashi, sannan zai mutu da son ta a ransa.
"Rabu da shi Shattu yo ko ɗan taure ne yake awoyin nan ai a sara masa ba wajen kaifin ba, haƙiƙa ka ci amana ta Jauro, kake daɗewa haka kana sunna kenan baka da lokacin tunani na ma, ni ina can a gidan Malam ko yaushe ina tunaninka, ko Malam ɗin ne ya