Showing 3001 words to 6000 words out of 29601 words

Chapter 2 - KARA'IN INNA DELU Book Bye Maman Afrah.txt

20 Jan 2025

4298

ne ƴaƴanki to dole ki haƙura" Baba ya faɗa yana kallonta, shi dai Abba tun da ya zauna bai kuma magana ba.


"Umaru, biyani nono na da na shayar da kai, aradun Allah gwara na sheƙa masa ruwa na yi kindirmo(Nono) tun da ni kake so na maka biyayya ba wai kai bane za ka mini biyayya ba"


"Ni ba haka nake nufi ba"


"Yo in ba haka kake nufi ba menene ba dai ni bace kake rainawa har muke faɗi in faɗa, to ni kuwa ni ce ƙofar shigarka aljanna, ka ga wannan ƙafartawa mai faso da kaushi kana ganinta kamar kofaton doki wallahi ita zan ɗaga ka shiga aljanna" Ta faɗa tana ɗage ƙafarta ta nuna masa.




Gabaɗaya sun kasa gane ta inda za su ɓullowa Innar kowa sai ya zuba mata ido tana ta taunar goro abinta, zuwa can, Abba Sa'adu ya zamo daga kan kujera ya nufi wajen Inna da rarrafe, shi ma Baba Umar sakkowa ya yi ya nufi wanjenta gwiwarsa a ƙasa yana rarrafe, Maryam ma ganin haka sai ta sakko daga kujera ta durƙusa a kan gwiwoyinta. Su duka kuka suka saka mata kamar ƙananan yara, Inna kuwa baki sake take kallonsu dan ko a jikinta kukan da suke ita dai aurenta na ƙara'i babu abin da zai sanya ta fasa.


Ai Inna ma sai gani suka yi bidik ta sakko ƙasan ta durƙusa kamar yadda suka yi gabaɗaya sai kowa ya tsayar da kukan da yake suka shiga kallonta. Fashewa ta yi da wani irin kuka mai jiniya wanda ya fi nasu su duka ukun, tun da ta ɓare bakinta bata rufe ba kuka kawai take zabgawa kamar wanda aka bata umarni. Yin nan take babu ƙaƙƙautawa sun rasa ma bakin magana.


"Inna menene" Maryam ta yi ƙarfin halin jefa mata tambayar cikin shaƙeƙƙiyar muryarra da bata fita sosai saboda kukan da ta yi. Maimakon Inna ta bata amsa sai kawai ta ƙara gudu da kuma ƙaran kukan nata.Tun suna lallashinta har suka yi shiru gabaɗaya tausayinta ya kama su dan su duk tunaninsu ko iyayenta ta tuna take kukan, falon ya yi tsit baka jin komai sai kukanta zuwa can.


"Dan Allah Inna ki daina kukan nan baki ji ba yadda duk kika karya mana zuciya, su kaka babu abin da suke buƙata sama da addu'a" Cewar Baba yana kallon Inna da tausayawa.
"Ba batun mutuwa bane ɗan nan, duk da an ce ana bikin duniya ake na ƙiyama amma yau dai iya duniyar ne"


"Ikon Allah, ba su kaka kika tuna ba dama" Abba ya jefa mata tambayar.


"Allah sarki Inna Baba Malam ta tuna ai dama ko ba komai akwai sabo sa...


Wani kallo da Inna ta bi Maryam da shi, shi ne abin da ya hanata ƙarasa maganar.


"Waye Malam kuma, in ce dai yanzu aka ambaci uwata da ubana na ce ba su nake yiwa kuka ba, kuma sai ki ce wani Malam" Ta faɗa tana ƙara rushewa da kukan.


"Dan Allah to Inna ki faɗa mana tun da duk abubuwan da muke zato ba su bane" Baba ya faɗa yana kallonta har lokacin su duka ukun sun akan gwiwoyinsu ciki kuwa har da Inna da ke da rasgar kuka.




"To ku yi shiru zan faɗa, tun da kun takurani"


"Allah sarki Inna" Suka faɗa a zuciyarsu suna jin wani daɗi dan duk tunninsu cewa za ta yi ta haƙura da auren tun da suna kuka shi yasa take kuka dan ta fasa auren.


"Faɗi mana Inna" Cewar Maryam tana washe haƙora dan ita tafi su Abba shiga damuwa dan ta san matsawar dai Inna ta yi auren na to fa dangin mijinta sai sun rinƙa goranta mata a kan uwarta mai budurwar zuciya, shi kansa mijin nata ta san wataran zai iya mata gori.


"Zan faɗa ɗiyar nan" Cewar Inna tana ɗan kauda kai gefe tana ɗan murmushi.


"Dama, dama, dama"


"Dama me Inna" Cewar Abba haƙoransa a buɗe dan shi ma ya gama jango jirgin Inna cewa za ta yi ta fasa auren.


"Kai wallahi sai zan faɗa sai kuma in ji kunya ta rufe ni" Ta faɗa tana ɗan kallon ƴaƴan nata.


"Inna mu fa ƴaƴanki ne babu wata kunya" Baba ya ce shi ma yana ƴar dariya, tarw da kannewa ƴan uwansa ido dan ya san mahaifiyarsu ta fasa aure take son cewa.


"I LOBIYU (I LOVE U) Ta faɗa tana rufe fuskarta da hannunta.


Wani daɗi ne ya ziyarce su jin abin da ta faɗa, dan sun ɗauka ma sai ta ce tana son nasu sannan ta ce ta janye maganar auren.


"Wallahi kukan daɗi nake ɗiyan nan, duk lokacin da na tuna kalamar I LOBIYU (I LOVE U) Sai in ji wani daɗi da farinciki marar misaltuwa"


"Allah sarki Inna" Suka haɗa baki wajen faɗa.


"Wallahi ƴaƴan nan wannan kalma ce da Jauro ya faɗa mini tun ina budurwa, kalmar nan ce kullum ke kwaɗaitar da ni zuwa ga aurensa domin ina da yaƙinin zai rinƙa faɗa mini ita idan mun yi aure, dan safe da yamma zan ce masa yake faɗa mini saboda yadda take faranta mini rai, shi yasa nake kwaɗayin aurensa dan idan zai faɗi kalmar nan har wani gunna yake mata yadda za ta ƙara garɗi a bakinsa zuwa cikin kunnuwana, wallahi ya fi ubanku iya soyayya nesa ba ma kusa ba, ka san shi ubanku ban da Deluna babu wani abu da ya iya na jan hankalin mace, sai shigen son raya sunna kamar ɗan taure gashi babu wani armashi a gabatar da sunnar tashi, shi yasa kawai zama da shi alal larurati, yo ya zanyi tun da ya zame mini ƙarfen ƙafa, kullum sai dai yake rubutu yana bani wai dan ya zaunar dani a gidansa bai san ba tun da bai iya soyayya ba shi da sakainar kashi ɗaya suke a wuri...


Tunda ta fara wannan bayanin sai suka yi ɗif kamar babu kowa a falon, su duka banda lazimi babu abinda suke dan sun gama fahimtar lamarin Inna addu'a ce kawai za ta musu maganinsa. Haka suka tashi daga durƙuson da suka yi dan sun lura babu wani amfanin yin hakan, da haka suka mata sallamar za su je masallacin la'asar ita ma bata bi ta kansu ba sai dai ta sa nya a ranta ko ana ha maza ha mata aurenta da Jauro bbu fashi. Maryam ma haka ta tashi ta tafi ɓangaren matan gidan dan bata ma jin za ta cigaba da zama Inna tana ta maimaita zancen da bashi da kai bate ƙafa.




*DA LA'ASAR LIS*


Inna tana zaune a falo ta ɗora ƙafarta ɗaya kan ɗaya sai farantin kankana irin mai jan nan kuma mai yashi tana sha tana lunshe ido saboda zaƙi ga kuma sanyi da kankanar ta ɗauka.


"Allah sarki Jaurona da kana kusa da a baki zan ke baka irin na turawa, shi yasa na ƙosa mu yi auren nan dan mu yi ƘARA'I babu kama hannun yaro, amma dan ƙarfin hali ɓarawo da sallama yaran nan suna neman kawo mana cikas sabo...


Sallamar Abba, Baba, da kuma abokansu tun na yarinta wanda suke a ƙauyensu kafin yanzu su ma a Kanon suke zaune da iyalansu amma ƙauyensu ɗaya da su Inna, ita ma Maryam dama a hannun su Abba ta taso a Kano ta yi karatun ta da ta kammala fa samu miji sai aka mata aurenta, yanzu haka suna da ɗa ɗan shekara takwas.


Baki washe Inna ta amsa tana kallonsu, dan ita a ranta har ta gama ƙiyasta za ta faɗawa abokan nasu ƙudurinta na son yin aure da ƴaƴan nata ke son hana ta duk da ta nuna musu basu isa ba amma tana ganin idan abokan nasu sun faɗa musu ko su sa ji maganarsu tun da suna mata ganin ta tsufa, su sa banbance da sauran ta.


"Marhababin da su Rabilu sannunku da zuwa" Cewar Inna tana washe baki har kunne dan ta hango burinta na dab da cika tun da su Rabilu sun zo to tabbas faɗuwa ta zo dai dai da zama.


Bayan sun zazzauna suka shiga gaishe da Inna ta amsa musu tana musu faɗan basa son zumunci wai rabon da ta gansu tun da suka je yi mata gaisuwar Malam. Haka sai suka ɗan kare kansu a kan aiyuka ne suka musu yawa.




Bayan shiru ya ɗan gifta Inna tana raya ta inda za ta fara sai kawai ta ji Kamal ya fara gyaran murya ya fara magana.


"Inna dama mun zo ne a kan wata muhimmiyar magana, da su Umar suka same mu da ita, a kan mu zo ko Allah zai sa a sasanta mu shawo kan lamarin" Ya faɗa cikin ladabi yana kallon Inna wanda tun da ya farw magana ta wani yatsina fuska tare da mere baki tana kallonsa dan tun kan ya kai aya ta gama harbo jirginsa ta ƙyaleshi ne kawai ya ƙarasa dan kar ta katse masa hanzari.


"Haka ne Inna ai maganar aure ma bai taso ba, haƙuri za ki yi tunda kin ga yanzu Baba Malam ko cikon shekara ba a masa ba, babu zancen cikon shekara tun da ko wata biyar bai ƙarasa ba, kai koda ma a ce ya yi shekaru goma ne da rasuwa bai kamata a ce kin yi wani auren ba tun da kin riga kin manyanta, bare kuma a ce ko jimawa baki yi da kammala takaba ba wannan sai ya zama abin faɗa a wurin jama'a kuma ko ba komai ko dan ƴaƴanki ai kya janye maganar auren nan" Rabilu ya kai ƙarshen maganar a dai dai lokacin da Maryam ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama, amsa mata suka yi ta gaishe da su Rabilun ta nemi wuri ta zauna tana jin wani daɗi a ranta dan ta san dai magana ta ƙare tun da dai Inna ta ga abokan su Abba.


Tun da Rabilu ya ɗora daga inda




Kamal ɗin ya tsaya Inna ta yi tagumi da ɗaya hannunta ɗayan kuma tana riƙe da gutsuren kankanarta da ta riƙe mamaki ma ya hanata magana. Ganin da suka yi ta kifa uban tagumi duk tunaninsu maganar da aka yi ce ta shigeta har sun fara tunanin tsuntsunsu ya kama tarko.








Sai da Rabilu ya kai aya Inna ta ɗauke hannunta daga tagumin da ta yi, ta kai kankanarta ta saka a bakinta har da lunshe ido, sai da ta tauna ta haɗiye abinta ta suɗe yatsunta ta maida kallonta gare su ta ce


"Kamalu, Rabilu, kun gama jawabin naku, in ce dai duk a kan magana ɗaya kuka kwaso ƙafa kuka zo nan?" Kallon kallo aka shiga tsakanin su Baba da su Rabilu ita dai tun da ta jefa ayar tambaya bata sake cewa komai ba.


"Bani amsa mana" Ta faɗa tana ɗan muskuwata a kan kujera.


"Eh Inna" Cewar Rabilu jiki ba ƙwari dan bai ga alamar akwai sauƙi a tattare da Inna ba.


"To duk cikinku babu wanda ya isa ya dakatar da ni, wato su sun kasa shawo kaina shi ne suka je sula taho daku, ku kuma kuka ɗakko ƙafa ya sillen kara, kai kana tura ƙeya kamar gafiya ta so shiga rami" Ta faɗa tana kallon Kamal da ya sunkuyar da kai tsabar ba ar da Inna ta masa.


"Kai kuma ka ɗauki fuska kamar farantin tallar kukar kaɗi, kana ɗaga dogon wuyanka mai kama da mariƙin lema "Unbrella) Tambayar da zan muku uwaku Talatu bayan mutuwar ubanku aure nawa ta ƙara?" Ta faɗa tana tsare su da ido, babu wanda ya tanka mata dan haka sai ta ɗora da cewa


"Tunda ba za ka bani amsa ba, dan na ga ba niyya ango ya kwana da wando, tun da kun ƙi magana kun ƙunshe baki kamar amaryar da bata kai budurci gidan miji ba, bari ni in baku amsar, Talatu bayan mutuwar ubanku sai da ta yi aure-aure, sai da ta ƙara aure uku rigis, fir taƙi zama a gidan mijin da ta aura na farko bayan mutuwar uban naku, taƙi zama ne kuwa dan bashi da kataɓus a wajen gabatar da sunna. Bayan ta fito daga gidansa ta sake sabon aure amma saboda mijin baya gamsheta(Gamsar da ita) Ta fito dan cewa ta yi shi da lagwanin fitila babu banbanci yo cewa fa ta yi abar tasa ce jalele kamar hanjin ɗan tsako. Sai a gidan mijin na uku ne ta zauna har yau tana can dan cewa ta yi zama daram ita da shi mutukaraba takalmin kaza yo ai a can ne ta samu abin da take so me ya hana ku hanata lokacin da take aure-auren ? Shi ne dan rashin ta ido ni kuka zo za ku mini sagegeduwa wato in ƙare a gantale ba aure, na zo a sadaka in koma a alakoro, to wallahi haka ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa dan aurena da Jauro kamar an ɗaura taminjau" Ta faɗa tana binsu su duka da kallo.


"Dan Allah Inna ba dan mu ba" Baba ya faɗa kamar zai yi kuka.


"Kai rufe mini baki, ba waɗannn ka ɗakko ba kana ganin kamar su za su saka ni abin da ban yi niyya ba, to duk cikinku babu wanda ya isa ya tauye mini haƙƙi, ni babu wanda na hana ya ƙara aure a cikin ku ko mata huɗu kuke so babu mai hana ku, amma duk wanda ya ce ni zai hana rawar gaban hantsi, to mu zuba shege ka fasa ɗan halak sai yanka, kuma duk wanda ya ƙara yunƙurin hana ni aure sai na saka ya saki matarsa ya zauna a gauro ya ji idan zama haka ba aure da daɗi" Ta faɗa tana miƙa hannu ta ɗauki kankan ɗaya ta kai bakinta har ruwan na gangarowa daga bakin nata ta saka harshe ta suɗe. Tun da ta yi maganaar sakin matansu sai duk suka shiga taitayinsu, babu wansa ya ƙara magana.


"Ke ma kuma in sak naki mijin ya sake ki sai ki dawo mu zauna a tare" Ta faɗa tana kallon Maryam da gabanta ya buga jin furucin Inna na saki.


Haka sai su Rabilu suka yiwa Inna sallama suka fice sumi-sumi su da su Abba, Maryam kuma bedroom ɗin Inna ta kwanra tana jiran mijinta ya zo ya ɗauketa su tafi, dan sun yi magana ya ce zai zo bayan magriba saboda ta gaji da abubuwan nan da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa, dan har alla alla take a gama maganar kafin mijin nata ya zo dan bata so ko ɓurɓushin maganar ya tarar a barta da abin kunya. Inna kuwa ko ta kanta bata bi ba dan ta yi alƙawarin babu wanda za ta saurarawa matsawar dai babu wanda zai goyi bayanta.


BAYAN MAGRIBA


Zaune suke a falo su uku Inna tana kan sallaya ta miƙe ƙafafunta tana jan carbi dan tun da ta idar da sallar magariba bata tashi daga wurin ba. Sai Maryam da Amna da suke cin abinci a falon suna hira abinsu, bayan sun kammmala Amna ta kwashe kwanukan ta kai kicin ya cewa Maryam


"Aunty bari in je zan yi karatu"


"To my Amna a yi karatu da yawa, sai yaushe za ki je gidan nawa kuma?"


"Sai dai idan na samu lokaci dan yanzu makarantar boko da islamiya babu hutu amma zan zo"


"To Allah taimaka ya baku sa'a sai kin zo ɗin ina zuba ido" Cewar Maryam tana kallon ƴar wan nata. Fita Amna ta yi wanda hakan ya yi dai dai da shigowar mijin Aunty Maryam ɗin sa sallama cikin ɗan sakin fuska Inna ta amsa masa saboda ta san ko ba komai idan zai tafi yana bata kuɗi sababbi Inna kuwa akwai son sabon kuɗi dan wano lokacin ma sai ta yi ta ajiyarsu kamar wanda za ta rataya a wuya wai bata son kashe sabon kuɗi
ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄


NA




MAMAN AFRAH




FCW


Page5⃣➡6⃣


Ƙarasowa ya yi ya zauna Inna tana ta washe baki tare da masa marhabin. Bayan ya gaisheta take tambayarsa ɗan gidan Maryam ɗin yake sanar da ita ai daga makaranta gidan mahaifiyrsa ya wuce.


'Yo ke ko ruwa bakya kawo masa ba kika zauna kina wani zumu-zumu da baki kamar shazumamu ya samu sikari" Cewar Inna da ta lura da ɓacin ran da maryam ɗin ke yi tun shigowar mijin nata ita dai ta san dalilinta ma yin hakan. Ruwan ta tafi ta ɗakko masa a plate ta kawo masa tare da masa sanju da zuwa cikin sakin fuska ya amsa yana ɗaukan ruwan ya tilla ya sha ya mayar da ledar kan plate ɗin da yake pure water ne.




"Wannan matar taka ta koyi mugun hali wallahi"


"Mugun hali kuma Inna?"


"Eh mana kai vaka lura sa muzuran da take ba tun shigowarka ai ko idanunta ka kalla za ka ga sun yi luhu-luhu, to kuka ne ta yi ta garƙawa kamar da ranar sa ubanta Malam ya bar duniya"


"Subhanallahi mai ya yi zafi Inna" Ya tambaya da mamaki.


"Maza Maryama ki yi ta hararata amma wallahi harararki ba za fa hana ni faɗin abin da ke raina ba" Cewar Inna tana wani gatsina fuska.



Jin haka Maryam ta tashi fa sauri ta shige ɗaki dan ta san yun da Inna za ta fara magana babu mai taka mata birki sai ta ida amma dai ta san yau abin kunya ne ta gama ja mata a wajen mijinta


"Inna idan laifi ta miki ai sai ki ja mata kunne...


"Yi shiru ɗan nan bakinka alekum, ai ba zan yi ƙasa a gwiwa ba wajen faɗa maka komai da komai ba in yaso ko addu'a ce sai ka taya ni a kan Allah ya mini mafita ya ganar da yaran nan gaskiya gaskiya ce ƙarya kuma ɓata ce" Ta katse shi tana rattabo bayaninta.


"Yarinyar nan Maryama da ƴan uwanta ne suke son yin kisan kai...


"Subhanallahi, kisan kai fa Inna amma dai na tattabara ko?"


"Kai dallah ja can, ana maka maganar mutane kana ɓaganar tsuntsaye, to bari na maka gwari-gwari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login