Showing 12001 words to 15000 words out of 29601 words
kawo kansa wataran hana shi kaina nake dan sai in ke ganin kamar amanarka zan ci ashe kai kana can kana kashe arnan soyayya, kana kwashe awoyi da mace yo Allah na tuba ai duk ka gama lale komai da komai babu sauran abin da zan samu, ko wani sauran abin da zan mora, har nake zumuɗin cin amarci...
Tana cikin faɗa tana kuka, bata ankara ba sai hango wulgawar Abba da Baba ta yi sun fice dan ko ganin tashin su bata yi ba ficewarsu kawai ta gani.
Umaru, Sa'adu" Ta faɗa tana ware murya dan su dawo. Amma ko alamarsu bata gani ba.
"Shattu bisu ki kirawo mini su, ki ce wallahi idan basu dawo ba zan yi abar" Ta faɗa tana kallon aminiyar tata da gabaɗaya ita ma ranta a jagule yake da maganar Jauro.
"Ki bar maganar yin abar ke baki da aiki sai anbaton za ki yi abar, to meye ribarki in kika tsinewa ƴaƴanki?" Cewar Shattu tana kallonta.
"Ke ce miki aka yi Delun mahaukata ce ni, ai ba wai yin tsinuwar zan yi ba ina faɗa ne dan in samu cikar burina kin san tsinuwar ce kaɗai zan ambata a mini abin da nake so a zauna lafiya" Cewar Inna cikin raɗa dan kar su Abban ko suna kusa su jiyo ta.
"Yawwa ko da na ji" Bari in bi bayansu" Shattu ta faɗa tana ficewa da sauri dan kar kowannen su ya shige ɓangarensa.
Tana fita Jauro ya matsa kusa da Inna ya kamo hannunta ta ƙwace, ganin za ta ɓata masa lokaci ya haɗa duka hannun biyu ya riƙe ya shiga aikin lallashi tana ta zunɓura baki ta ce
"Haka kurum ka je kana cin amanar soyayya ta"
"Haba Delu fara kyakkyawa wallahi kina raina, kuma da kike maganar ba na tunaninki, wani lokacin ko ina kan masai(Toilet) Ina kashi sai in ji tunaninki ya hana ni sakat, ke ko sallah nake ma tunaninki nake"
"Ka ce ɓata sallarka kake"
"A'a ba haka bane ai ina cewa a'uzubillahi minashshaiɗanir rajimmm, in kori shaiɗan ɗin kawai dai ina so ki san irin yadda kika yi kane-kane a raina, ke ni fa akwai lokacin da Harɗon rugarmu ya aika a kirawo ni wai dabobina sun shiga gonarsa, tun da na doshi fadar tasa kawai sai na ga ya koma mini ke sak, kawai ke na gani a kan kujerar mulkin dan haka tun da na kalleshi sai nake sakin murmushin ƙaunayya aikuwa ya harzuƙa, ina zama yake faɗa kamar ya cinyeni ɗanye, ni kuwa tun da na sunkuyar da kai tunaninki kawai nake, dan haka faɗan da yake mini ma amon muryarki nake ji kina mimi kalaman soyayya dan haka ko da ya saurara da faɗan ya ce da kai fa nake Jauro ka ƙyaleni ai ina ɗago kaina ban san lokacin da na ce ina jinki Deluna"
Gabaɗaya Inna ta tuntsure da wata irin dariya sai ƙyaƙyatawa take ita ala dole Jauro yana tuna ta duk daɗi ya cika ta.
ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄
NA
MAMAN AFRAH
FCW💛
Page 1⃣1⃣➡1⃣2⃣
Abba ne ya yi gyaran murya ya fara magana kamar haka, dan ya ga abin na su Inna ya wuce gona da iri nema suke su ɗakko musu magana su ɗakko musu ruwan dafa kansu.
"Hana Inna wannan abu fa ba mai yiwuwa bane, saboda abin da zai iyu shi ake faɗa ta yaya ma haka zai faru a ce wai mu kama ɗakin taron shagali ai sai duniya ta zage...
"Idan fa ban yi da gaske ba, ba zan taɓa samun abin da nake so ba gwara dai in tauna tsakuwa ko aya ta ji tsoro" Cewar Inna Delu a zuciyarta a fili kuma sai ta ce
"Yanzu Sa'adu ni kake faɗi in faɗa dani, ni kake cewa ba mai yiwuwa bane, haka zan tare a ɗakin sabon uban naka babu wani shagali kamar wacce ta yi auren ƙiyayya, yo in ba auren ƙiyayya ba a ina aka taɓa biki lami shataf babu wani ɗanɗano, ai ko auren ubanka Malam duk da ba son sa nake ba sai da aka ɗakko masu gurmi" Ta katse masa maganar tana kaiwa ƙarshen maganar tare da fashewa da wani kuka mai sauti kamar an kunna jiniya, tana fara kukan Jauro ya yi saurin ruƙo hannunta yake bata baki amma ko saurara wa da kukan bata yi ba ganin haka shi ma sai ya ɓare baki ya saki nasa kukan yana ƙwalawa da ƙarfi har wani jan birki yake sai kuma ya ci gaba.
Shattu ma bata yi ƙasa a gwiwa ba ta ƙarasa wajensu tana basu baki
"Haba amarya da ango ya da kuka kuma a ranar farincikin ku, ranar da kuka yi shekaru sama da hamsin kuna mafarkin samunta"
"Barmu mu yi kayanmu Shattu ɗan yanzu ni ka haifeshi baka haifi halinshi ba, in banda zamani mai sa wani ya ƙi uwarsa ya so wasu, zamani mai sanya ɗa ya baƙantawa uwarsa rai ya farantawa uwar matarsa rai, ta yaya za a ce kamar ni in haifi yaran na su girma su mallaki hanklin kansu amma su ƙi mini abun da zai sa ni farinciki" Cewar Inna tana goge hawayen takaici. Ganin haka sai Jauro ya miƙa goshinsa ya haɗa da goshin Inna a haka suke kukan kamar wasu tsuntsaye.
"Muke kukan a haka Bebi in gwara duk runtsi duk wuya mu zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya" Ya faɗa yana ƙara sautin kukansa.
Shattu ma ganin haka sai kawai ta mara musu baya dan ita ma tana ganin ba a barta a baya ba wani irin kukan tsoffi ta saki irin mai sanya ciwon kai lokaci guda. Sun cika ɗakin da koke -koke kamar gidan mutuwa, baka jin komai sai sautin kukansu babu mai lallashin wani.
Idan Inna ta bada sautin
"Yiiiiii"
Sai Jauro ya bada sautin
Yeeeee"
Ita kuma Shattu nata sauti
"Yeyiye-yiye" Kamar wata agwagwa haka suke kukan suna jan hanci.
Abba da Baba kawai kansu suka sunkuyar hannuwansu dafe da kansu.
"Ya Allah ka bamu ikon cin jarabawar nan" Cewar Abba a zuciyarsa.
"Kai ji nake dama bana ƙasar nan Inna ta yi aure da wataƙila ba zan ji takaici kamar haka ba" Cewar Baba a zuciyarsa yana jin wani damshi a fuskarsa hannu ya kai ya shafo ashe dai hawaye ne suke gangaro masa.
"Bari dai in tashi mu san inda dare ya mana yaran nan in basu ga da gaske nake ba babu abin da za su yarda su mana" Inna ta faɗa a ranta tana mai tashi ta nufi ɗakin har lokacin tana kuka mai sauti, su ma su Shattu basu bari ba an ma rasa sautin kukan wa za a saurara kamar wasu yara.
Ƙaran akwatunan da Inna ta ɗakko guda biyu su ne suka dakatar da kowa aka shiga kallonta har masu kukan ma ɗiff suka yi dan dama kukan sheƙiyanci ne. A kanta ta ɗora akwatin ɗaya yadda kika san irin inyamuran nan na Lagos masu ɗora daro a ka haka ta koma, tana janye da ɗaya akwatin a hannunta
"Kai wannan mata da shegen abu take kin ga ni ban samu shagalin biki ba za ta jaza mini komawa ruga bayan na yi sallama da zaman can" Cewar Jauro da bai san ma lokacin da kukan munafurcin da yake yi ya tsaya ba, banda faɗuwa babu abin da gabansa ke yi.
"Kin mini dai dai gwara ki tarki tafiya ko sa saduda su sakko" Cewar Shattu a ranta.
Cikin hanzari Jauro ya tashi ya karɓi akwatin kan Inna ya sauke ta ƙasa sannan ya koma ya zauna yana share hawaye, amma a baɗini hawayen baƙincikin barin binni ne dan ya ga Delu da gaske take tun da har ta ɗakko akwati.
"Ku taso mu tafi mu bar musu gidansu" Cewar Inna tana saurin dafe kanta jin ɗaurin ɗankwalin na neman faɗuwa.
Wani zillo gaban Jauro ya yi jin maganar da ta ratsa kunensa a kiɗime ya ɗago yana kallon amaryar tasa ji yake kamar ya ce su haƙura da shagalin su tare a haka amma kuma ya ga babu fuska a wajen Inna.
"Ni dama a shirye nake aminiyata dan dai nan da garinmu ko a ƙafarmu ma isa daga yanzu zuwa sulusun dare kan gari ya waye" Cewar Shattu da ta ɗauki akwati ɗaya.
"Bebi taso ka ɗauki ɗayar"
"Ga samu ga rashi wayyo ni Jauro duk na ɗaga dabbobina da shanaye da gonaki na siyar yanzu idan na koma gorin jama,a ma ya ishe ni" Cewar Jauro a zuciyarsa yana tuna washe garin ranar da Inna ta dawo binni aka ɗakko shi har za a ɗaura aure aka fasa shi ne da ya koma ya siyar da duka kadarorinsa.
"Ina zamu???" Cewar Jauro har lokacin yana zaune a kujera dan ko maganar tafiyar ma baya ƙaunar ji.
"Ka taso mana, baka gani yanzu dare ne kuma akwai gidan casu a garin nan akwai kwalob (Club) Akwai gidan karuwa kai sai inda muka zaɓa sai mu je mu yi casunmu in yaso daga can sai mu koma rugarku mu yi rayuwar aurenmu a can tun da nan an gagara kama mana gida a sirri ai sai mu je inda ƴan iskan duniya suke in yaso tunda su suna gudun maganar, a ce sun kamawa uwarsu ɗakin taro an yi shagali ai a ce an ga uwarsu a gidan rawa " Cewar Inna tana saurin ƙara dafe kanta jin kofin da ta yi acuci zai gangaro aikuwa dai an yi rashin sa'a dan ya faɗo ji kake ƙwal, ya faɗowa Abba a tsakiyar kansa da babu hula.
Wani kallon mamaki suka bi Inna da shi, ganin kofin da ya faɗo daga cikin ɗankwalinta, shi Abba ba ta faɗo masa da ya yi ba yake kawai ta yadda aka yi uwarsa tsofai-tsofai ta saka kofin yake dan sun fahimci babu makawa acuci maza ta yi.
"Haɓɓasa aminiyar gaskiya ne ba a bori sa sanyin jiki ai gwara ki gwangwaje ki yi ƙara'in ki" Shattu ta faɗa tana kallon Inna.
"Acuci maza ne, kuma babu wanda na cuta dan mijina na yi kuma ya yaba ɗaurin ɗankwalin" Inna ta faɗa tana juyawa ta kalli Jauro ta ce
"Ko baka yaba ɗaurin ba Bebi"
Wani takaici ne ya turnuƙe zuciyar Jauro dan shi gabaɗaya hankalinsa ya ɗugunzuma ga tafiyar da ta ce za su yi cikin ƙarfin hali ya daure ya ce
"Eh ya miki kyau"
"Yawwa Bauti (Beauty) Jaurona ko a maida kofin cikin ɗankwalin?"
"Barshi kawai ai a haka ma kin yi kyau" Ya faɗa yana jin tamkar ya hau Inna da duka dan ya lura shirin tafiyar da take ba wasa a ciki.
"To kun dai ji daga bakin uban naku wanda aka yi ɗaurin dominsa" Ta faɗa tana gyara ɗaurin ɗankwalin ba tare da ta ɗauki kofin ba ta , juya abinta Shattu na bin bayanta da akwatin, ganin haka ne Jauro ya yi ta maza ya tashi ya ɗauki ɗaya akwatin yana jin babu daɗi a ransa, suna dab da fita daga falon Baba ya ce
"Ku dakata Inna mun ji za a muku duk abin da kuke so a kan dai ko je gidan rawa" Ya faɗa kamar ya saki kuka.
"Eh mun amince" Abba ma ya faɗa ba dan ransa ya so ba.
"Kayyasa in ka ji ana ba zan iya ba to bai samu mutum ba" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ce
"A'a ku barshi kawai"
"Dan Allah Inna ki yi haƙuri" Abba ya faɗa cikin sanyin murya yana tsaye a gabansu.
"Ke ko Delu ki haƙura mana kuma babu kyau dai fushin uwa a kan ɗanta kuma Allah ma yana son mai haƙuri" ,Jauro ya faɗa yana wani karyar da kai fuskar nan tashi duk hawaye shaɓe-shaɓe
"Haba Delu ki yi haƙuri mana" Shattu ma ta sanya baki.
Dakyar aka shawo kan Inna ta aminci suka dawo da akwatunan nan kowa ya zauna Inna Delu ta ce
"Ni dama ba wai wani abun a zo a gani na ce ku yi ba ƴaƴan nan, yanzu kuɗi nake so ku bani gobe masu ɗan gwaɓi da direba a kai mu kasuwa mu siyo ƴan kayayyakin amarci sannan kuma ranar tariyar a kirawo mai kwalliyar amare (make up) Ta mini kwalliyar in fito rangaɗaɗau a amaryata, sai kuma a ɗauki motoci a kai jama'a can a ɗauki me kiɗa (DJ) A kai shikenan fa daga wannan" Ta faɗa tana kallon Abba da Baba da suka rasa bakin magana.
"To Inna za a miki duk abin da kike buƙata, idan har kika fasa tafiya" Baba da Abba suka haɗa baki wajen faɗa.
"Yawwa ƴaƴan nan ko da na ji ubangiji ya libga muku albarka ku wanye da duniya lafiya" Cewar Inna tana washe baki, Abba ya fito da 100k ya bata haka ma Baba shi ma 100k ya bata na siyayyar da ta ce za ta je haka suka rinƙa jero musu godiya da sanya musu albarka su dai haka suka amsa amma ba dan ransu ya so ba.
Washe gari tun da sanyin safiya Inna ta aika aka kira mata Lantana mai aiki, haka suka sanya ta a gaba wai za ta raka su siyayya, cikin zumuɗi Lantana ta yarda, da yamma haka suka ɗumguma Inna, Shattu da Lantana a baya Jauro da direba a gaba haka direba ya ɗau hanya Lantana ita ce mai faɗa kusu inda zai kai su suna cikin tafiya su Inna sai aikin washe baki suke.
"Tsaya, tsaya direba" Cewar Inna da ƙarfi tamkar wanda ta hango wani mugun abu ya tunkaro su da sauri direban ya taka birki ya ɗan gangara gefen titi yana tambaya ko lafiya.
"Haba ɗan nan aiulafiya ce ta fito da mu kalli can wancan shagon na tsallake nake so ka kaimu kalli wata mata can ta saka kayan indiyawa ni ma irin nata nake so, Lantana ce ta fashe da dariya ta ce
"Inna wannan fa mutunmutumi ne ba mutum ba kayan siyarwa ne aka saka mata dan masu siye su ga yadda kayan yake yi a jikin mutum"
"Allahu akbar kabiran lallai komai yana binni wallahi, gaskiya Delu idan kika saka kayan nan har sai na kusa suma" Cewar Jauro yana kallon Inna Delu da bakinta ke buɗe kamar gonar auduga.
"Ai Bebi yau kaya sai mun siyo har dana banza dan kaima sai ka gaji da zaɓar naka" Cewar Inna tana kallon Jauro.
"Direba yi aikin ka kawai" Cewar Shattu tana ƴar dariya. Haka direban ya gangara ya je ya samu wajen parking ya ajiye motar su kuma suka fita su duka suka barshi a motar yana mamakin halin tsofaffin nan.
Ƙaton shago ne wanda ya haɗa komai da komai kayan mata kananan kaya dogayen riguna babu abin babu na maza da mata. Tun da suka shiga kallo ya koma sama.
Hular gashi, rigar amare gown, pakistan, dogayen riguna, rigunan bacci da rigunan bacci wanda basu kai ƙasa ba, bireziya mai ƙoƙo, sarƙa da ɗankunne takalmi mai tudu pos ta amare. Su ne kayan da Inna ta ɗakko Lantana na taya ta zaɓe.
Wandunan jeans, shirts, combos, glases pacing cap , wanduna tiri kwata, su ne kayan da aka zaɓarwa Jauro, sai murna yake zai dawo yaro ɗanye sharaf, shagon aski suka shiga aka yiwa Jauro askin zamani na samari
Daga nan kasuwar ƴan kayan maganun mata suka je suka kwaso kayan mata na amare wai za a ci amarci Jauro kwa sai washe baki yake zai kwashi ganima. Haka suka dawo gida niƙi-niƙi da kaya.
Tun da suka fito suna tsaye ana fiddo kayan sai ga Abubakar kallo ɗaya ya musu ya ɗauke kai.
"Kai fitsararren yaron nan baka da kunya kana ganin kakanninka amma ka ɗauke kai sai ka ce ka ga wasu bare, to wallahi ka shiga taitayinka, zo ɗauke mana kayan kanshiga da su" Cewar Inna cikin faɗa-faɗa dan ta lura Abubakar ɗin ba ya son cigabanta kwata-kwata yana ta zumɓura baki ya ɗauki ledojin ita ma Lantana ta ɗauki wasu suka shige ɓangaren Inna domin zuwa su ƙara kashe kwarkwatar idanunsu.
Bayan kwana huɗu
Yau ta kama alhamis ita ce ranar da za a yi shagalin bikin Inna da Jauro dan haka juma'a kuma za ta tare dan haka yau gabaɗaya wanda suka gayyato daga ƙauye sun hallara tun safe sai hada hadar ake yi masu kiɗan ƙwarya da aka ɗakko su sai aikin kiɗa suke masu rawa na yi su dai masu gidan wato sirikan Inna duk suna ɓangarensu abin duniya ya ishe su saboda abin da surukarsu ke yi hatta Abba da Baba tunda suka fita da safe basu dawo gidan ba sai dai sun bawa Inna komai da za a buƙata hatta hall da dj babu abin da baa ɗakko ba sun ajiye motoci da direbobi dan kawai su faranta mata, Amna ma gidan su ƙawarta ta tafi dan haushi da yake yanzu suna hutun makaranta ne.
Misalin ƙarfe biyu da rabi mai kwalliya ta zo da kayan kwalliyarta haka ta zauna jiran fitowar amarya a ɓangaren Inna a falon sai mutane da kowa je sabgar gabansa.
Inna ce ta fito daga ƙuryar ɗakinta (Bedroom) Hannunta riƙe da leda, mai ɗauke da kayan da za ta yi amfani da su.
"Ƴar nan ina fatan dai kin ƙware wajen yin ƙyalin(kwalliya) Nan na zamani dan ranar nan a TV na ga ana yiwa wata amarya baki ga yadda jagirar ta zanu ba raɗau kamar ka sace amaryar ka zangaya da gudu" Cewar Inna tana kallon yarinyar.
"Kar ki damu Iya in sha Allah idan na gama zaki yaba kwalliyar da zan yiwa jikarki" Mai kwalliya ta faɗa tana dariya, dan ita tunaninta amaryar da za ta yiwa kwalliyar jikar Inna ce .
"Wace magana