Showing 15001 words to 18000 words out of 29601 words

Chapter 6 - KARA'IN INNA DELU Book Bye Maman Afrah.txt

20 Jan 2025

4305

kike kuma wace jikartawa, ai Namna (Amna) Baƙinciki take da auren nan ko zama bata yi a gidan ba bare har a mata kwalliya" Cewar Inna dan ita tunninta mai kwalliyar tana nufin ifan ta yiwa Amna ne.


"Auren dole ne kenan" Cewar mai kwalliya dan ita kwai yadda Inna ke magana ne ya matuƙar birgeta dan tana son hulɗa da tsoffi ko ba komai ka sha dariya abinka.


"Ke wai maganar me kike ana maganar auren ƘARA'I na soyayya kina maganar dole, kula ki gama mini dan kar mu ɓata lokaci na ji an ce kwalliyar akwai ɗaukan lokaci"


"Wai Iya mai za a miki tukunna?"


"Yau ni na ga ikon Allah ɓatan nono a ƙirjin budurwa, ban da kudura ya za a yi a ɗakko ki ki mini kwalliya amma kina mini wani tambyar rainin wayo"


"Ita ce fa amaryar kuma ita aka ɗakkoki domin ki yiwa kwallyar" Cewar Lantana da shigowarta kenan, da sauri mai kwalliya ta tashi tana kallon Inna da mamaki dan ta lura cikin maganar da Lantana ta yi babu wasa ko ƙarya a ciki.


"Ita za a yiwa make up?"


"Ni na ga ƙarfin hali ɓarawo da sallama ke dai ba aikin kuɗi kike ba to ina ruwanki ko bango aka ɗakko ki ki yiwa ai kuɗinki dai kika sani" Cewar Inna tana kallon yarinyar dan ranta har ya ɓaci.


"Haba Iya yanzu tsofai-tsofai da ke zamki ce a yiwa fuskarki kwalliya wannan abu duk a yamutse kamar k...


"Ke! Idan ba za ki yi ba ki kama gabanki u nemi wata" Inna ta faɗa tana harararta, mai kwalliya dai ganin da gaske Inna za ta yiwa sai kawai ta zauna ta shiga fitar da kayan kwalliyarta sai da ta gama tsaf ta kama fuskar Inna ta fente ta tass kamar budurwar amarya, dan har gashin gira aka askewa Inna da za a zana jagira wajen kwalliyar baki kwa sun ɓata lokaci saboda yadda bakin nata yake guluf na tsofaffi haka aka buɗe ledar Inna aka
ɗakko wedding gown ɗin da suka siyo aka zige zip ɗin ta sanyata mai kwalliya ta rangaɗa mata ɗauri mai fanka sannanta sanya mata komai sai ga Inna ta fito a amaryarta.


Haka dai ta saka takalminta da yamma aka zo za a tafi ɗakin da aka kama har da wasu kayan Inna da Jauro suka tafi dan canjawa.


A bayan mota aka sanya su motoci huɗu ne suka tafi cike da mutane, ana zuwa ɗakin taron aka tarar da wasu mutanen a can ga kuma wurin zaman amarya da ango ya sha decoration yinƙurawa ya yi ya fito sanye yake da shaddarsa fara ƙal ta sha aiki sai Inna ma ta fito daga ɗaya ƙofar gabaɗaya sai kallo ya koma kansu...






ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄

NA






MAMAN AFRAH




FCW💛


Page 1⃣3⃣➡1⃣4⃣




Da yake ba wani tsaro aka saka a wurin ba duk mutanen gari sun shigo kallo musamman samari, yadda wurin ya tsaru kowa ya ɗauka zai ga amarya budurwa ango saurayi amma suna fitowa aka fara tozali da wata uwar furfura da ta yiwa Jauro ƙawanya a fuska ga wani aski da aka masa na zamani aka aske wani wurin wani wurin aka bar masa gashi sai ya zama kamar irin fataken nan wanda suka daɗe suna yawo basu samu gari a kusa ba. Inna na fitowa daga motar da yake rigar tata doguwa ce ta mata yawa ko ƙafar baka hangowa da takalminta mai tudu gashi kuma yadin satin ne aka yi ɗinkin da shi sai aka ɗora net aka sosai rigar ta mata yawa, tana fitowa kowa ya saki baki yana kallonsu banda ƴan ƙauyensu da dama sun san su waye amarya da angon.


Shattu ce riƙe da wani bokiti da aka zuba ganyen maina irin wanda ya yi yellow ɗin nan tana watsa musu a matsayin furanni dan Inna ta ce babu wani abu da ba za a musu ba sai dai ko idan mantawa suka yi da shi.


Tana watsa musu tana carara guda duk da mc ya ƙure kiɗa baka jin komai amma bata daina guɗar ba, Jauro ne ya riƙe hannunta irin yadda amarya da ango suke yi, matakala ce a wurin suna zuwa sun hau ɗaya biyu suna shirin hawa ta ukun rigar Inna ta taɗe ta aikuwa ta zame ta tafi za ta faɗi, da sauri Jauro ya tareta ashe shi ma rigar ta maƙalo da ƙafarsa aikuwa suka tafi a tare suka tiƙu da ƙasa ji kake tim sun faɗi ai gabaɗaya samarin nan da suka ziyarci wurin ba gayyata suka ɗauki wani uban ihu kamar an ci ball a gidan kallon ƙwallo. Gabaɗaya wurin ya kaure da ihu wasu har fito suke, da yake da suka faɗin Jauro ne a ƙasa ita kuma sai ta faɗa da rubda ciki a kansa, duk sai kunya ta rufe su, Shattu bokitin ganyen mainar da take watsawa a matsayin furanni ta ajiye tana sakin wani salati ta nufe su cikin azama tana faɗin.


"Ya subhanallahi, amarya da ango an sha ƙasa, yo dama ku da za ku shigo cikin mutane ai bakwa fito ba tare da kun sha lahaula ba, ko maganin baki saboda kallo, yadda kuka yi kyan nan ai sai ido ya kama ku kar fa ku manta duk taron nan saboda ku aka yi kuma kowa ƙoƙarinsa ya ganku wasu har ɗaɗɗage suke dan su hangi amarya da ango" Ta faɗa tana ƙarasawa wurinsu ta ce


"Sannu Delu sannu Jauro ai sai ku tashi ku karkaɗe jikinku domin ƙasa ba sirikar kowa bace da za ku ji kunyarta"Cewar Shattu tana miƙa hannu za ta ɗaga Delu dan yanzu ta gangara ƙasa daga kan Jauron, gashi taƙi tashi sai Shattun ta ce


"Ki tashi mana ku ƙarasa kan kujerunku na amare"


"Haba Shattu kin ji ƙirjina kuwa...


"Wane irin na ji ƙirjinki kuwa ke da kika faɗi ai ke za ki ji a jikinki dama" Shattu ta faɗa rai ɓace dan ta fi so Innar ta tashi saboda yadda idanu suka musu caaa






"Haba ina dalili dama ai laifin Lantana ne da bata saka an rage mini tsawon rigar nan ba ta barni ina yawo a ciki zulum-zulum kamar limamin masallacin juma'a zai yi kuɗuba...


"Wai Delu ki tashi mana banda ma ɗan adam ke da Allah ya taimake ki kika faɗa a kan Jauro da kan dakalin nan kika faɗa ai da kin ji a jikin ki" Cewar Shattu tana kama tsantsa ganin Delu ta ƙi tashi.


"Ke kike ganin na faɗa kan Jauro, amma ni na san inda na faɗa, yadda na bugu a ƙirjinsa ankan ƙashin haƙarƙarinsa baki ji ba kamar wanda na faɗa kan duwatsun wuta, har sai da na gwammace a kan dakalin na faɗa, yo ƙirjinsa babu tsoka ko ƙwaya sai ƙashi kamar ƙashin kan saniya, yadda kika san baya cin abinci" Cewar Inna tana kai hannu fuskarta ta shiga cire ganyayen mainan da suka lilliƙe mata a fuska wanda Shattu ke watsawa a matsayin furanni, da yake zafi ake fuskar nan ta yi jargaf da gumi fawundation ɗin da aka mata kwalliya da ita duk ta haɗu da gumi ya gangaro har bakinta jagirar ta haɗe da ƴar uwarta fuskar nan ta miki kamar an shafa mata jan ɓurjin bulo, tana cikin cire mainan da yake yanzu a zaune take dakaka shi kuma gogan har yanzu bai tashi ba dan shi kaɗai ya san irin azabar da yake ji, tana cire maina sai wani ƙwaro ya hau fuskar aikuwa ta sanya hannu ta dakeshi daga fuskar ta da sanya hannu ta murtsuke fuskar dan ji ta yi kamar ƙwaron ya cije ta a fuskar duk wanda ya kalli amarya sai ya yi kamar ya shiɗe saboda dariya sosai foundation ɗin ta mata kaca-kaca da fuskar.


"Delu kin ganki kuwa" Shattu ta faɗa tana tuntsurewa da dariya, banza ta yiwa Shattu dan ita bata ma san kwalliyar ta caɓe ba, gabaɗaya ma jin jikinta take kamar an sheƙa mata ruwa saboda gumi ga zafi da kuma nauyin rigar.


"Kamani Delu, ɗago ni, ki taya ni in tashi wallahi allon bayana kamar zai rabe a biyu, wannan wane irin daɓe (ploring) Ne suka yiwa wurin nan wallahi yadda kika san ƙarfe wajen ya daɓu sosai sun samu ma'aikatan gini wanda basu da ha'inci da kuma yashi na kirki marar algus da ƙasa, simintin da suka yi amfani ma da alama irin mai luwai-luwai ɗin nan ne.






Tunda ya fara magana Inna da ke zaune take jifansa da wata ƙatuwar harara, ita takaicinta ma ɗaya yadda ta ji ƙirjinsa babu komai banda tarin ƙasusuwa, wani kishi ne ya turnuƙeta dan tana ji a ranta cewa duk Kande ta lale tsokar wajen shi yasa ta ji saura ƙashi, baƙincikinta ɗaya shi ne babu abin da za ta samu a wajen na amarci.


"Kai wannan mutum akwai ayar tambaya a kan ka wallahi ka ce wai Kande kana ɗan yin sunna da ita saisa -saisa amma gashi duk ta lale tsokar jikinka sai ƙashi wato ma kullum a nan take aaɗora kanta" Cewar Inna a ranta wani kishi na turnuƙeta a gefe ɗaya kuma wata ƙwalla na cika idanunta a fili kuma ta ce


"Zaka tashi da kan ka ka kama hannun nawa irin yadda ake yiwa amaren mu ƙarasa kujerar zaman namu ko kuma zaka tsaya jiran gawon shanu ne har sai na ɗaga ka, to in kuwa haka ne wallahi iska na yawo da mai kayan kara dan ko yatsanka ba zan kama ka tashi ba, banda ragwanta mai makon da zan faɗin daka taro ni ka mini irin ɗaukan da namiji ba indiye ke yiwa ba indiya wato ɗaukan jarirai kar ka bari na kufce daga hannunka yadda za a tafa mana amma shi ne kai ka faɗi ni ɗin ma na faɗi gashi nan maimakon a mana tafi ihu ake mana, zaka bar mini abin gori son a je a baiwa Kande labari take goranta mini" Cewar Inna har lokacin bata daina jifansa da harara ba.


"Haba Delu bakya ganin mutane suna kallomu, a bainan nasi fa muke in banda ma ƙaran kiɗan nan ai da sai kowa ya ji abin da kike cewa...


"Yo su ji mana abin kunya ai ni gaba na bashi ba baya ba, tunda dai suka ga faɗuwarmu mai kuma ya rage, ai komai aka yi da jaki sai ya ci kara in banda ma abin kirki bai gaji kare ba in ya yi ma zaginsa ake, ta yaya za a ce amarya da ango sun sha ƙasa, musamma ma ni amarya, ai amarya ko ta buzuzu ce sunanta amarya a wajen ango" Ta faɗa tana ƙara sharɓuno fuskar zuwa lokacin fuska ta kwaɓe kwaɓ kamar wanda aka yiwa bango flasta da kashi.


Jin maganganun Inna Jauro ya yi ta maza ya miƙe zaune, kamar wanda aka janyoshi ya sake komawa ya kwanta lifet, dakyar dai ya tashi zaune yana yatsina fuska alamar shi kaɗai ya san abin da ya ji.


"Kai Bebi na doku a ƙasan nan yadda kika san ba faɗuwa na yi ba, kamar wanda muke dambe aka samu wanda ya fi ƙarfina ya ɗaga ni sama ya niƙa ni da ƙasa wallahi haka na ji" Ya faɗa, yana ƙoƙarin miƙewa dakyar a dai dai nan ne Lantana da ta koma gida domin ɗakkowa amarya gwaggwaron da za ta yi amfani da shi in za ta canja kaya da magriba ta dawo cikin sauri ta nufi wurin suka kama Inna ita da Shattu suka ɗaga ta tsaye hakan ya yi dai dai da tashin Jauro tsaye aikuwa ya miƙa hannu zai kama hannun Inna ta janye tana ɓata rai.


"Na gano ki aradun Allah na gano ki Delu wannan ihun ne da ake mana yake ɓata miki rai amma yanzu zan sa a mana tafi" Cewar Jauro yana matsawa saitin fuskar Inna ya miƙa dogon bakinsa mai kamar na jaɓa, wanda yake da adon gemu fari fat, ya kaiwa Inna wani kiss a kunci, yadda ya buɗe bakin ba ƙaramin wuri bakin ya ci ba a wajen yin kiss ɗin dan sosai ba kuma haɗe kuncin ma baki ɗaya d yake ƙaton baki ne da shi, yana mata kiss ɗin wanda sai da aka yi kamar a haɗo da fatar kuncin dan Inna har haƙoransa ta ji sun gatso fatar amma saboda yadda ya shammace ta da kuma tafin da wurin ya ɗauka shi ne abin da ya bala'in birgeta.






..ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄

NA






MAMAN AFRAH


FCW💛


Page 1⃣5⃣➡1⃣6⃣

Yana ɗago fuskarsa wajen ya ƙara kacamewa da ihu da tafi, ihu amma irin ma an burge mutane, kowa gemun ango yake bi da kallo dan ya koma kala biyu sama fari na furfura ƙasan kuma na foundation dan kiss ɗin da ya yiwa amarya Delu gabaɗaya ya gogo foundation a ƙasan gemu, hatta bakinsa da ya doɓara wajen yin kiss ɗin kamar akuya ta ci dusa dan foundation ɗin ce da ta haɗu da gumi ya danɓarota. Shi kuwa Jauro da bai san abin da ake yiwa dariya ba tunaninsa duk kiss ɗin da ya yi ne ya burgesu, dan haka sai ya shiga washe baki.


"Aikin banza ashe ma abu ƙanƙane zan yi ku daina ihun ku koma yi mana tafi, da kun ɗauka indiyawa ne kaɗai suka iya hiss (kiss) Da nuna soyayya ga mace to ni ma da nake rugage gashi nan na yi abin da na caje muku ƙwalƙwalwa, ai dama da rashin kira karen bebe ya ɓata kuɓa da rashin tayi ake barin araha" Cewar Jauro a zuciyarsa.


Inna ma ganin abin da ango ya mata ya ɗau hankalin jama'ar wurin dan ta lura mutanen gari ma sai ƙara tuttulowa suke kamar wanda ake faɗa musu su zo dan yanzu gabaɗaya hall ɗin ya cika maƙil. Ganin haka ya sanya Inna ita ma ta nufi fuskar Jauro dan ya mayar masa da martani aikuwa sai da ta doɓara masa bakinta a wuri uku goshi, kan hanci da kuma kunci. Wani uba ihu da tafi ne ya karaɗe wajen wasu ar da tsalle suke, samari da ƴanmata duk sun fito da wayarsu suna ɗaukan hoto wasu video, su kuma nago da amarya sai daɗi ya cika su ganin kowa son ɗaukan hotonsu yake.




Samari kuwa gani suke sun samu comedy dan wasu videon ma a status za su ɗora wasu kuwa a facebuk wasu a wasu kafar sadarwar dan wanda basu gani ba su ga wannan abu mai kama da almara.


Yadda ake ihu abin har ya so basu mamaki sai dai basu san ba fuskar jauro ce ta bada wani irin abin dariya, dan duk inda Inna ra masa kiss wuraren nan guda uku goshi hanci da kunci sai ya yi abin powder fuskar ya fito a wuraren sai duskar ta zama kamar yadda ake yiwa mota idan za a sake mata fenti a saka mata farin abu yi tabbare tabbataren nan, haka fuskar ta yi da foundation sosai ya koma kamar wanda zai je tashe na iya duba-duba sammadara wanda ake da watan azumi. Lantana ma ta haɗe da ƴan tafi da ihu bata lura da yadda fuskar ango ta koma ba, bare kuma Shattu da ke ta aikin watsa ganye kamar wanda aka ce da ganyen ne auren zai ɗauru.


Wani daɗi ne yake baibaye Inna da Jauro idan suka ga wulgawar yellown ganyen mainan nan hakan ba ƙaramin faranta musu rai yake ba sannan suna ƙara tabbatar da cewa su amare ne. MC ne ya fara magana bayan an kashe kiɗan da ya karaɗe wajen.


"Amarya da ango muna muku barka da zuwa wannan waje, sannan muna baku haƙuri a kan faɗuwar da kuka yi wacce sanadinta ya haifar da wata salon soyayya da kuka gabatar mai ɗinbin tarihi a rayuwar aurenku da duk wanda ke wajen nan ya ga yadda kuka nunawa duniya irin yadda kuke son junanku" MC ya kai ƙarshen maganar yana cewa


"Dan Allah a tafa musu" A take wajen ya karaɗe da tafi da kuma ihu. Sosai zugar nan da aka yiwa amarya da ango ta shiga kunnuwansu shi kuma MC ya yi hakan ne dan ya fasa musu kai amma a zuciyarsa cewa yake


"Allah wadaran naka ya lalace cewar jakin dawa da ya ga an laftawa jakin gida kaya, banda budurwar zuciya mai sa raƙuma ta auri ɗan tsako ya za a yi tsofai-tsofai da ku, amma ku zo ku kama hall dan shagalin bikin ku, ai Allah raba bawa da wahala wai gwauro a teburin mai shayi" Ya faɗa a ransa a fili kuma ya ce


Dan haka yanzu amarya da ango za su ƙarasa wajen zaman su, su zauna dan mu fara gabatar da abin da ya taramu" Ya kai ƙarshen maganar yana ƙarewa wanda ke zaune kallo wanda duk yawanci ƴan ƙauye ne kuma tsofaffi sai matasan mata haka dan duk samari da ƴan matan ƴan cikin gari ne kumabya tabbatar kallon ƙwaƙwaf ne ya kawo su ba wai gayyatarsu aka yi ba.


Hannun dama Jauro ya kai ya riƙo ƙugun Inna tare da riƙe hannunta da ɗaya hannun nasa kamar yadda jiya da dare ya ga wani actor ya yiwa budurwarsa a film ɗin india. A haka suka nufi kujerar tasu, Shattu na aikin watsa musu ganyen maina.


"Wai bauti (Beauty) Ka ɗauke ni mana yadda indiyawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login