Showing 18001 words to 21000 words out of 29601 words
ke yi " Cewar Inna ƙasa-ƙasa.
"A'a Bebi kinsan dai yadda muka sha ƙasa ɗazu kuma lokacin ma da ƙafafunmu muke tafiya shegiyar rigar nan ta taɗe mu bare kuma a ce na ɗaga ki to wallahi yanzu dai muka ƙara shan ƙasa sai kuma yadda hali ya yi" Shi ma Jauro ya bata amsa a hankali, yadda suke maganar raɗa-raɗa sai ya ƙara baiwa mutane dariya su ala dole ango da amarya a haka suka ƙarasa suka zauna.
Kande da Karime da ke laɓe a cikin wani ɗaki suna hango duk abin da ke faruwa, gabaɗaya kishi ya baibaiye musu zuciya Karime mahaifiyar Kande uwar gidan Jauro ita ce ta kalli Kande ta ce
"Maza ɗauki kwanan shan manjan nan tun da sun zauna yanzu ne dai dai aiwatar da abin da a dace tsaffin banza da basa jin kunya" Ta faɗa tana ƙara ƙyallara idonta ɗaya da yake ido ɗaya gareta. Jan hanci Kande ta yi yare da sanya hannu ta share hawayenta ta ce
"Gaskiya Jauro ya iya cin amana ji yadda ya riƙo ta yana zubar mini da mutunci a idon mutanen ƙauye da rugagenmu " Ta kai ƙarshen maganar tana sakin kukan takaici da na kishi.
"Ki haƙuri ai sai inda ƙarfinmu ya ƙare yanzu dai ki je ki yi abin da n saka ki" Cewar mahaifiyarta. Haka ta fito ta nufi wajen da ya karaɗe da kiɗa wasu har sun fita suna cashewa Kande na zuwa bata yi wata-wata ba ta faki idanun mutane da yake kowa idanunsa na kan masu rawa ne amarya da ango kuma ana zaune da cake a gabansu da lemuka amma in ka kalli fuskar Inna yadda take shaining ɗin foundation ga gumin nan yana ta kwaranyowa shi kuma ango da dabbaren fuskar kashe uku a fuskarsa ga wacce ta mayar masa da gemu kala biyu. Ta bayan kujerarsu Kande ta zo ta ɗaga kwanon sha mai cike da manja ta shiga kwaranyawa a kan ango da amarya tun daga kansu har uban jikinsu bata dakata ba sai da ta juye musu shi tas...
Su Jauro an saki baki an maida hankali kan kiɗa ana kallon masu rawa da juyi basu zata ba basu tsammata ba sai suka fara jin zubar wani abu a jikinsu yana gangarowa har fuskarsu. Inna Delu ce ta juya bayanta dan ganin wanda ke musu wannan aika aikan amma sai ta ga wayam babu kowa, juyawa ta yi ga masoyinta abin ƙaunarta Jauro aikuwa ta yi mugun gani domin kuwa manjan ne ya masa sharkaf tamkar an tsoma kaza a ruwan zafi babu abin da ya so baiwa Inna Delu dariya irin yadda manjan ke zubowa ta gemun Jauron, gurbin idanunsa ne kaɗai ake gani a fuskarsa inda ba manja.
"Badaƙalar nan lallai yau zan nuna wa wanda ya mana wannan aiki wacece ni, tabbas dama a san mutum a san sana'arsa in ya bari a san ya daina, domin kuwa inda ba ƙasa nan ake gardamar kokawa" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuwa sai ta kalli Jauro da ya washe bakinsa gemun nan nasa har lokacin yana ɗigar manjan amma wai ita yake yiwa dariya kuma duk abin da ake babu wanda ya lura da abin da aka yiwa ango da amarya dan kowa hankalinsa ya karkata ga rawar da ake a wurin.
Deluna kin ganki kuwa, kin ga yadda kika koma kamar jemage ya faɗo daga sama" Cewar Jauro cikin sigar wasa.
"Yo ba gwara ni kamar jemage ya faɗo daga sama ba wallahi idan ka ga yadda ka koma kamar an tsamo ɓera daga ruwa" Ta faɗa tana tashi tsaye dan ta ji haushin maganarsa duk da wasa ya faɗa. Tashin amarya tsaye shi ya sanar da mutane halin da ake ciki kowa ɗaɗɗage yake ya hango amarya da ango dan ya tabbatar da ka ce na cen da ake, ita kuwa Delu bata damu da kallon da ake musu ba kawai so take ta ga wanda ya musu wannan ɗanyen aikin.
Iya ganinta bata ga kowa ba shi ma Jauro haka ya tashi yana dubawa amma ba a ga kowa ba Shattu ce ta kamo hanya daga mazauninta dan zuwa wurin aminiyarta amma kafin ta ƙarasa sai ganin Inna ta yi a fusace ta nufi wajen MC rigar nan sai rinjayarta take rana neman faɗuwa.
Inna na zuwa wajen MC ta warce lasifikar hannunsa shi kuwa saka mata ya yi dan kar ta goga masa manja ta taƙaita shi.
"Lallai yau na gane shayi ruwa ne, banda mutane baku da tsoron Allah ku da kuka zo cin arziƙi amma wadatar biki tsarki da romo shi ne har aka samu wani ɗan kan uwan da ya lalata mana kwalliyarmu saboda baƙinciki, to inason wanda ya yi wannan aiki ya sani an yi ba a yi bane wai rufe ƙofa da ɓarawo, in ma baƙinciki mutum yake to sai dai ya mutu mutu dan ni da Bebi Jauro mutuƙaraba takalmin kaza, kuma masu cewa tsoho da tsohuwa to ni banga tsofan Jaurona ba ganinsa make kamar saurayi ɗan shekaru ashirin, yo ai guntun gatarinka ya fi sari ka bani kuma...
Maganar Inna ta tsaya ne sanadin ganin wani saurayi mai ƙarfin hali, wanda ya zo har gabanta y tsaya yana mata video dan shi daga can inda yake videon ba ya ɗaukuwa shi yasa ya zo gabanta dan yau ya yi alƙawari duk wata lfr sadarwa sai ya ɗorata yadda ta yi jargaf da manjan nan, ko kwalliyar da aka mata ba a gani manja ya rufe ta ruf.
Kallo Inna ta ƙare masa ta ganshi sanye yake da garar riga irin mai farin nan tass sai baƙin wando, cikin sanɗa da ƙarasa gabansa shi kuma ya maida hankali cikin wayar dan da ya fara ganin tana matsowa a a cikin wayar sai ya ganta kamar aljana kuma bai yi zaton wurinsa ta nufa ba ya ɗauka ta kammala jawabin ne za ta bar wajen.
Inna Delu na ƙarasowa ta miƙa hannu cikin zafin nama ta damƙo wuyan rigar saurayin nan, saurayi na ɗaukan video sai ji ya yi an rafkoshi kamar wanda ɗan sanda ya kama ɓarawo, ɗago kan da zai yi aikuwa ya sauke su a kan Inna Delu da manjan nan sharkaf sai ɗiga take kamar wacce ta yi noman kwakwar manja.
Wani takaici ne ya lulluɓeshi ganin hannunta da manja amma ta kama masa riga, rigar ma fara, wani irin zabura ya yi zai fara mata rashin kunya, Inna kuwa hannu ta kai ta damƙo hannayensa ta haɗa wuri ɗaya ta damƙe dama ɗan siriri da shi kamar sandar rake, bakinsa dai ya buɗa zai fara magana aikuwa Inna ta saki ɗaya hannun nasa ta gwabje masa baki ta janyoshi ta wanka masa mari sannan ta kai masa kyawawan ranƙwashi guda uku.
"Allah ya isa n...
Ai kafin ya ƙarasa Inna ta janyoshi jikinta ta rungume sai da ta tabbatar rigarsa fara ta gama samun manja har fuskarsa marabarsu da Innar yanzu kaɗan ne dan shi ma kamar wanda ya shafa shuni amma na manja. Ihu aka ɗauka a wajen wanda har ya fi na lokacin faɗuwa da kiss ɗin su Inna...
Wani takaici ne ya turnuƙe saurayin ganin irin cakumar da Inna ta yiwa rigarsa, domin kuwa ta yiwa rigar wani irin ɗiban karan mahaukaciya.
" Zamani kenan mura ta tadda kwaɗo wallahi sai kin san wanda kika yiwa wannan riƙon kamar kin samu wuyan saniya, wallahi sai kin banbance tsakanin kiɗa da karatu" Cewar saurayin a ransa yana ƙiyasta irin cin mutuncin da zai yiwa Inna domin huce takaicin haushin abin da ta masa za ta sanya duk inda ya yi ake nuna shi.
Hannu ya sanya ya rungomo Inna, wani irin zare ido Inna ta yi dan duk tunaninta faɗe zai mata
"Wallahi sai na kai amarcina gidan mijina dan yanzu layin Jauro ne, na Malam ya wuce kai kuwa baka isa ka sha zuma ta ba" Cewar Inna tana ƙoƙarin ƙwatar kanta.
Kafin ta gama tantancewa sai ji ta yi ya sakata daga rungumar da ya mata ya finciki ɗaurin ɗankwalinta haɗe da hular gashin da aka saka mata, sai ga kan Inna a bainan nasi, gabaɗaya kan a ƙwaiƙwaye yake babu ma kitso saboda kan ba zai kitsu ba, duk ya zube, dan dama ƙawarta Shattu ke haɗawa da tsumma tana mata zanen hausa shi ne yanzu aka sayi hula za a yi ƙara'in biki da ita.Yana yin jifa da hula da ɗan kwalinya kama wuyan rigarta sai da ya daidaici saitin ƙirjinta ya kama ya yaga rigar har wajen saitin cibiyarta, tana ƙoƙarin kare wurin saurayin nan ya yi ido biyu da bireziyarta da ke shaƙe da fanfas ɗin yara, da alama ciko ta yi kuma cikon daban nonon da ban, dan haka ai bai yi wata-wata ba ya sa hannu ya fisgi hannun bireziyar duka biyu sai kuwa ta cire sai ga fanfas suna faɗowa kamar ƙwallon mangwaro na faɗowa daga bishiya, dan guda huɗu ne ragas ko ina biyu ta saka dan cikon ya yi tudu. Inna kuwa ganin fanfas a ƙasa a zube kuma jin wurin ya ɗauki ihu har da amsa kuwwa sannan sai ta ji nonuwan nata na reto kamar lilon wasan yara domin ya fito daga bireziya babu mafakar fakewa dan haka bata yi wata-wata ba ta durƙushe hannunta riƙe gam a ƙirjinta.
Jauro daga inda yake ganin abin da ke faruwa sai kuwa ya yi wani tsalle kamar jakican sai gashi ya yi dirar mikiya a gaban wasu ƙarafe da ake ajiyewa a wajen daga can gefe, guda ɗaya ya warto ya taho rai a matuƙar ɓace dan shi ba komai bane ya ɓata masa rai irin yadda saurayin nan ya rungume Inna tare da kai hannunsa jikin bireziyarta wannan ne ya tada masa wani kishi marar misali
Saurayin nan ganin irin yadda Jauro ya taho a matuƙar fusace kamar kumurcin maciji hakan ya sanya ya bawa kansa shawarar cika wandonsa da iska dan idan ya tsaya bafulatanin nan ya far masa sai ya kwanta asibiti in ma bai kai shi kushewa ba. Da mugun gudu ya bar wajen Inna yana haɗawa da tsalle, haka ma Jauro ya mara masa baya ɗauke da ƙarfen, a ransa yana raya wa a ransa cewa ba zai yiwu ba kura da aiki gardi da shan bugu. Yadda suka zuba a na kare kamar ibro ya biyo ƙulu Allah jkn rai, haka suka falfala kamar sun ci ƙafar kare. Wurin kuwa ya karaɗe da ihu MC kuwa sai cewa yake
"Jama'a a yi haƙuri wuri fa ya hargitse an samu wani saurayi ya kaiwa amarya farmaki, dan haka ango ya fusata ya ga ba zai iya haƙuri ba bare ya jure ya bi bayan saurayin sai yadda hali ya yi"
Samarin nan kuwa sai cewa suke
"Sai ka cimmasa ango ya za a yi kai baka ga amaryarka ba, shi ya gane maka, har da rungumeta ya yi kamar shi ne angon" Haka suke faɗa suna ihu, dan su zuga Jauro dan ko tarkar riƙe masa saurayin babu wanda ya yi niyyar yi dan dama sun fi so su ga yadda wasan zai kasance dan su sha dariya.
Sai faman keta gudu suke Jauro da saurayin nan, dan saurayin na fita ya sha wata uwar kwana bai bi kan titi ba sai ya keta wata unguwa shi kuwa Jauro ya take masa baya dan Jauro tun daga ƙofar wajen taron ya sille takalmansa dan ba ya jin gudun zai yiwu da takalmi, ga farar rigar nan da ta sha manja fuskar nan ban da idanunsa a fuskar babu inda manjan bai taɓa ba amma a haka yake zabga gudun famfalaƙi sai ƙara haɗa gumi yake. Saurayin nan kuwa sai waiwaye yake idan ya hango tazarar da ya bawa Jauron sai ya ƙilƙili da dariya amma dan ƙarfin hali Jauro ba ya ganin tazarar da ya bashi kawai burinsa ya same shi ya kwantar da shi da ƙarfen nan.
"Wallahi ba zai yiwu ba aradun Allah, ina zan yarda mai ɗakko katifar amarya da ban mai morarta ma da ban" Ya faɗa a ransa yana ƙara wuyar gudu dan ya ga ya ɗan fara taddo saurayin duk da duk inda suka gifta sai kallonsu ake.
Sai da suka kusa zuwa wani wuri inda akwai taron jama'a saurayin ya rage zabga gudun sai da ya bari Jauro ya kusa ƙarasowa sai ya ware murya ya ce
"Ihu mahaukaci jama'a duka yake kun ga da ya damƙe ni yadda ya ɓata mini riga da manjan jikinsa, ai mutane na jin furucinsa sai kowa ya fara guduwa wasu suna shiga gida suna rufewa dan ganin yanayin jikin Jauro ga manja a jikinsa da fuskarsa ga babu takalmi ga ya riƙo ƙarfe kowa sai ya fara ta kansa a ƙarshe dai ya ma rasa inda saurayin ya yi dan ya ɓace masa ga mutane sai kiransa suke mahaukaci ba wanda ke sauraronsa bare ya faɗa musu lafiyarsa ƙalaw.
Daga ƙarshe dai ya zo wucewa zai koma wajen taron, ta wani ƙaramin lungu sai ji ya yi, ƙum an sakar masa wani ƙaton bokitin fanti a kansa, daga saman wata katanga yana ɗagowa ya yi ido huɗu da saurayin nan shi da wani abokinsa, kan ka ce kwabo sun diro daga katangar kamar wasu birrai sun sheƙa a guje, haka ya yi ta danƙara musu Allah ya isa, har da ɗan kukansa ya matse a hanya dan kansa har ya yi wani ƙaton ƙullutu a tsakiyar kan nasa.
A hanyar dawo wa yana tafiya amma wani ƙululun baƙincikin kishin abin da aka yiwa Delunsa na runguma da taɓa bireziyarta, da kuma bokitin fantin da ya sha a tsakiyar kai duk su ne suka haɗe masa goma da ashirin .
"Gaskiya mutanen birni basu da kara, yanzu wannan da a ce a rugarmu ne abin nan ya faru da kowa sanda zai ɗakko a bi kwarton nan da ya rungume mini amarya, amma a nan sai ihu suke babu wanda ya yi kataɓus bare ya taimaka mini, sai ni kaɗai gashi a ƙarshe sun rafka mini bokiti kamar wanda aka aiko su duk da akwai gashin furfura a kaina amma sai da bokitin ya mini illa" Cewar Jauro a ransa lokacin da ya taho a hanya har wani ƙwallar takaici ne ya taru a idanunsa dan ba a taɓa ce masa ko da taɓi-taɓi ba amma yanzu gashi an kira shi mahaukaci sanadin ƘARA'IN aurensa da Delu. A haka ya ƙaraso bakin get ɗin inda ya watsar da takalmansa, a hannu ya ɗauka dan haushi ma ya hana shi ya saka a ƙafarsa.
ƘARA'IN INNA DELU
Page 1⃣7⃣➡1⃣8⃣
A fusace ya shigo wurin yana shigowa ya yi wurgi da ƙarfen hannunsa rai a matuƙar ɓace. Yana shigowa idanunsa suka sauka a tsakiyar kan furfurar amaryarsa kan nan kawai yake hangowa tana daga durƙushe Shattu da Lantana suna ta faman ta tashi amma kunyar yadda rigarta ke a ɓarke ga babu bireziya dan hannun ɗaya bireziyar ma ya maƙale a jikin ɗankunnenta, ga ihun da wajen ya karaɗe wurin ranta in ya yi dubu ya ɓaci yadda gashin kanta da ta san ko kitson kirki babu a jiki dama hular gashin da aka saka ita ce rufin asirin kan sai kuma saurayin nan ya cire mata dan ya kunyata ta a gaban jama'a.
"Ya Allah kai ka san karatun kurma, ranar ƘARA'IN nan da na ci buri a rayuwata, tun da aka ɗaura auren nan ko barcin kirki bana yi sabo da ɗoki amma a ce yau tun daga farkon shigowarmu muka sha ƙasa ni da ango na anya ba hannu aka saka mini ba, wani ɗan hana ruwa gudu, wato sa'idinawa wanda ana ruwa suna irgawa" Cewar Inna a ranta zuciyarta na ƙuna.
"Jama'a ku kauce, ku jaye ga ango nan da ƙarfin gwiwarsa ya dawo daga filin dagar ya je ya ɗauki fansa ya dawo" Cewar MC a lasifika.
"Ka ji ɗan jaraba, in banda dai neman magana fansar me na ɗauka in banda jikina da ya faɗa mini, kan nan nawa kamar na ɗauki duron kananzir, ai ba dan ba dan ba da na ce wannan ƙara'i ban ji daɗinsa ba" Ya faɗa a ransa lokacin da ya ƙaraso wajen yana aikawa MC wata muguwar harara kamar dai shi ya ce ya bi bayan saurayin.
"Ɗan tsoho ƙyamus-ƙyamus ba ni na ce ka yi auren ƙara'i ba kuma ba ni na saka ka bin saurayin nan ba, ka ga kuwa ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Ya faɗa a ransa yana saki wata ɓoyayyar dariya.
Cikin hanzari Jauro ya nufi inda su Shattun da Inna da Lantanar suke. Su Kande da Karima kuwa sun daɗe da cikawa rigarsu iska dan tun lokacin da ta watsa manjan ta shige ƙasan kujerun da ke wajen shi sa ba a ganta ba, bayan hankalin mutane ya koma wajen Inna da saurayin sai ta fito suka silale suka fice daga wajen, daga nan kuwa garinsu suka koma dan dama Jauro ya ce sai ranar da amarya za ta tare za ta dawo gidan da zama.
Yana zuwa Shattun cikin sanyin murya ta ce
"Yawwa ango, ka ganta nan sai fama muke da ita ta ƙi tashi" Wani haushin Shattu ne ya cikawa Jauro ciki da ta kirashi da suna ango, dan shi a yadda jikinsa yake a damule da manja kai da cillukutu ko abokin ango bai ci a ce an kira shi ba bare ango, gashi ji ya yi kamar ya zabgawa Shattu da Lantana mari da suka bar Delunsa a wajen ai da ko cicciɓarta sun yi sun kaita wani ɗaki.
Hannu kawai ya miƙa ba tare da ya ce uffan ba, Delu da ke durƙushe kanta a ƙasa sai ji ta yi an sure ta an yi sama da ita, sosai ta tsorata dan tunaninta wani ne cikin samarin wurin a sure