Showing 6001 words to 9000 words out of 29601 words

Chapter 3 - KARA'IN INNA DELU Book Bye Maman Afrah.txt

20 Jan 2025

4299

dan na tuna kisan zuciyoyi ya kamata in ce"


"Inna ban fahimta, sai ƙara ɓatar da ni kike, kin ce kisan kai kin ce na zuciya...


"Na gama shiryawa" Cewar Maryam da ta ɗakko jakarta ta fito daga ɗaki dan duk abin da ake faɗa tana jin su.


"To uwa gwadaga babu inda zai je sai na gama faɗa masa abin da ke raina wato shi ne kika ɗakko wata shegiyar jakarki mai kama da zabirar aski, wai kin gama to sai dai ki jira shi ya gama shi ma"


"Haba Inna "Ta faɗa taa zunɓura baki tare da komawa ɗaki dan ta ga mijin nata ya saki baki cikin rashin fahimtar takamaiman abin da ke faruwa.


'Ɗan nan ina kai ka, kana jina, Maryma da Yayunta su ne suke so su daƙushe zuciyoyi guda biyu haka kawai fa dan na ce zan yi aure, saboda son tauye mimi haƙƙi da kuma neman dalili suke so su dakatar dani wai na tsufa, dan na tarasu na sanar musu tunda na kammala takaba in yi aure, ni ma in huta idan da rabon haihuwa ma ba sai a yiwa mai ɗakin naka ƙanwa ko ƙani ba, to fir suka ƙi yo daɗi ta musu ake lissafani cikin zawarawa bayan ga ƴan matan nan da zawarawa sun rasa mazajen aure amma ni Allah ya bani mijina a hannu amma dan kawai su shiga haƙƙina sai su ce babu maganar aure wai sai dai in zauna in ke sallah da salatin annabi kaar da can ba na yi. Ai gwara dai in mutu a ɗakin aurena, in banda ƙoƙari faɗawa mijin baya tariya, meye a ido banda ruwa, abu lami ba ɗaci ba, banda ma ɗaukan alhaki ɗanka ya hanaka sunnar ma'aiki, to shi ne na ce ko kai za ka mini WALI (Alwali) Cewar Inna tana kafe sirikin nata da ido dan shi tun daga lokacin da ta ambaci aure ya saki baki yake kallonfa dan har ta gama leɓɓansa bash haɗu ba suna nan a buɗe.


"Kai ko kaima mijin ta ce ne, yo ya za a yi in zaunar da kai ina faɗa maka magana sai ka saki baki sharam ya layar mai tafiya kana kallona, ko baka fahimci inda maganar ta dosa bane na maka gwari-gwari"




"Eh Inna haka ne dama ai"


"Sammani anya kuwa cikin hayyacinka kake ko dai ka farw shaye-shaye ne, ya xa a yi in taƙarƙare in zabgo maka bayanai rututu amma ka kasa bani gamshashshiyar amsa sai ka ce wai eh Inna haka ne" Ta faɗa tana mere baki tate da maimaita abin da ya faɗa ta hanyar kwaikwayar muryartasa.


"Ko ɗaya Inna babu abin fa nake sha"


"A'a yo ni ai ban ga alamar hakan ba, yo wannan ai ba shawara bace ba kuma mafita bace ka bani Allah na tuba wannan magana taka akwai ya babu kakar wajen uba, ina so in ji ka zage kana rattabo bayanai sai kwai ka ɓige da eh Inna haka ne, tashi ku je Allah bamu alheri dan na ga kai da matartaka halinku ɗaya bakwa son ƙaruwata tun da kuwa haka ne sai ko ka ga katin gayyata dan aure babu fashi ko ana ha maza ha mata.


Sammani kamar jira yake ya miƙe tsaye yana gyara zaman babbar rigarsa, dan shi gabaɗaya yadda kansa ya ɗaure da maganar Innar idan da a ce mahaifiyarsa ce ta zo da wannan maganar ai sai dai ya zauna ya yi ta girka kuka saboda bai san mafita ba a ce mace tsofai-tsofai da ke kina maganar ƙara aure daga mutuwar mijinki.


Haka dai ya sanya hannu a aljihu ya ɗakko rafar ƴan ɗari biyu ya ajiye mata a gabanta ya ce


"Gashi Inna kya sayi goro"


"Ikon Allah yo kai kuma Sammani a yi haka, har da kuɗin goro kamar yadda aka saba ai da ka barshi a haɗu a gaba tunda ga abu nan ya taho kar wahalar ta yi yawa"


"Menene ya taho"


"Yo har ka tambaya ma kai da yanzu na gama baka labarin zan yi aure ai ko dan saboda haɗa gudunmuwa da ka bat na goron a haɗu a gudunmuwar fan wallahi biki zan karɓa babu babbba ba yaro ba ɗa ba siriki...


Kafin ta kai aya Maryam ta daɗe da ficewa saboda takaici.


"To Inna ai duk ba zai gagara ba" Cewar Sammani cikin ɗan jin nauyi.


"Allahu akbar kabiran to ai shikenan Allah nuna mana dama da na ga ba wani lokaci za a ɗauka ba" Shi dai ba sake cewa komai ba ya saka kai ya fice




Da dare Inna ta sanya aka kira mata mamar Amna da Mamar Abubakar, bayan sun zo sun gaisheta cikin girmamawa ta kalle su a shelaƙe ta ce


"Na kirawo ku ne dan in sanar da ku abin da baku sani ba, idan ma ku ne kuke sonnshiga tsakani na da ƴaƴana to ku sani watan komawarku gidajen iyayenku wato ƙauye za ta ɗauke ku"
Cikin rashin fahimta suke bin Inna da kallo wacce ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana musu kallon ɗai - ɗai


"Inna mai ya yi zafi kuma shi ba wuta ba"


"Kwa santa munfukan banza, wato kuna can ɗakunanku kun ƙule da mazajenku hankalu kwance ni ina nan a matsayin mai muku gadi yo Allah na tuba in ba dai dama su Umaru sun so su ja mini raini ba ya za a yi ina zaune da sirikai gida ɗaya amma a ce ina mazaunin bazawara kuma na ce zan yi aure suke neman hana ni, to tunda haka ne kowane ɗan banza zan sanya ya saki tasa matar su ma su zauna a gwauraye idan zaman haka da daɗi"


Tunda ta fara zuba suka saku baki cike da mamaki suke kallonta, dan sai ma yanzu suka fahimci inda maganar tata ta dosa.


"Inna wallahi bamu san da wannan maganar bama babu wanda ya faɗa mana Allah ne shaidarmu, mu ya za a yi mu hana sunnar ma'aiki abin da Allah ya halatta miki duk wanda zai hana ki ai bai so zaman lafiya ba" Suka haɗa baku wajen faɗa cikin girmamawa dan sun san kaɗan daga aikin nata ta sanya a mayar da su ƙauyen ko a a sake su baki ɗaya.


"Allah sarki ƴaƴan nan ku yafe mini wallahi duk zatona da haɗin bakinku"


"Wallahi babu Inna ai ciwon ƴa mace na ƴa mace ne kowace mace za ta so ta muti a ɗakin mijinta"




"Kai Allah sarki daman an ce mace ita ta san damuwar ƴar uwarta mace, da a ce ku ne na haifa da tuni an ɗaura mini auren ba za ku mini gardama ba amma wannan yarinya Maryama kai kamar kwakwa taƙi fir sai kuka take kamar matar marigayi, amma na san abin da zan yi ku tashi ku tafi Allah muku albarka" Ta faɗa tana share hawayen takaici.


"Amin Inna" Suka haɗa baki waje faɗa suka mata sallama suka tafi


WASHE GARI


Tunda garin Allah ya waye take ta saƙa da warwara tana son ta samu mafita dan dole auren take so a ɗaura mata. Sai da yamma ta fito lokacin babu kowa a waje ta fito tana ta waige-waige kamar marar gaskiya mai gadin ma yana bayi ta sulale ta bar gidan, titi ta tsallaka abinta tana ta saƙa abin da za ta faɗa idan ta je.


Masallacin juma'ar wanda yake unguwar ta nufa tana zuwa ta samu mutane a ƙofar daga can gefe zazzaune a bishiya suna hira, wurinsu ta nufa ta musu sallama suka amsa mata.


"Dan Allah limamin masallacin nan nake nema" Ta faɗa tana kallon matasan da su ma ita suke kallo.


"Gashi can shi ne wanda yake fitowa daga cikin masallacin" Ɗaya daga cikinsu ya bata amsa. Nufar mutumin ta yi wanda zai kai Abba a shekaru rike yake da carbi a hannunsa sai ganin Inna ya yi ta nufoshi tana zuwa ta ce


"Gafar malam wajenka na zo"


"Ikon Allah to sannu iya ina saurarenki"


"Wallahi mijina ne Allah ya masa cikawa ...


"Allahu akbar kabiran Iya abinci kike buƙata" Ya katse ta,cike da tausayawa duk da bata yi kama da mai jin yunwa ba


"Haba ɗan nan wane irin abinci ana maganar babban abinci, aure ne nake so shi ne ƴaƴana suka hana ni, na ce bari na kawo maka sadakin ka ɗaura mini tunda ba haramun bane" Ta faɗa tana share hawaye tare da saka hannu a aljihun ɗan tofinta ta zaro kuɗi.




"Aure iya"


"Yo aure mana ɗan nan ku ma da kuke malaman kana tantama da maganar auren bare kuma wanda ba malamai ba"


"Ba haka bane Iya"


"To karɓi nan, ka kirawo matasan can na zaune su zo ku haɗu ku ɗaura mana aure"


"Ina angon"


"Yana can ƙauyenmu, yo ai yana so na ba sai yana nan ba duk abinda na zartar daidai ne"


"Iya ki riƙe kuɗinki mu je gidan ƴaƴan naki sai a musu nasiha su barki ki yi auren"


"To ba a ƙi ta mutum ba"


Haka suka ta shiga gaba yana binta ashe dai ya san gidan ya yi mamakin ganin gidan Alhaji Umar da Alhaji Sa'adu ne ashe mahaifiyarsu ce mai son yin aure tsofe-tsofe da ita.


Haka aka sha ɗauki ba daɗi da liman da su Abba da Hajiya Inna suna ta kawo hujjoji ita kuma tana ta sharar hawaye ta dage a kan za ta gudu ta shiga yawon duniya idan ba a ɗaura mata aure da Jauro ba a haka dai suka amince ba dan sun so ba sai dan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.


Ta dage a kan sai a gidan nan za ta zauna ita da Jauron haka suka amince ba dan ransu ya so ba. Bayan an daidaita da Jauro ya yi matuƙar jin daɗin zaman da za su yi a birnin Kano dan haka ya xe zai siyar da komai nasa dan su dawo nan da zaa ko Kande da ta tada ɓasa hankalin ba zai tafi ya barta ba Inna ta saka an bata inda za ta zauna a cikin gidan.


Dan haka aka tsayar da ranar ɗaurin aure Inna ta saka Shattu ta gayyato mata ƴan ƙauyensu dan su zo su sha bidiri.


Page 7⃣➡8⃣






RANAR ƊAURIN AURE


Zaune take a kan kujera mai mazaunin mutum biyu, sanye take da atamfa ja wacce aka yiwa kwalliyar manyan ganye koraye, riga da zani sai ɗankwalin atamfar da ta tufka uban gwaggwaro irin nasu na tsoffi, hannayenta sanye da awarwaraye ƙafar nan ta sha jan ƙunshi dagwal har wajen ƙwaurinta. Kwalli ta rambaɗa da janbaki kai har ma da jagira ta zana abinta jagirar tamkar wanda aka zana da muciya gashi ya haɗu da yamutsatstsiyar fuska. Shattu aminiyarta ce a kusa da ita, ita ma irin kayan Inna Delun ne a jikinta sai washe baki suke kamar wanda ka yiwa albishir da tafiya aikin hajj bana.


Mata ne cike a ɗakin ƴan ƙauyukan su, suna zazzaune a falon suna ta cin abinci wasu tuwon shinkafa da taushe sai rangaɗa hira suke ana yi ana suɗe hannu, da alama ma dai akwai abin da ke faruwa na fari ciki.


"Wai ni Shattu har yanzu auren nan bai ɗauru ba, tun daɗewa aka tafi amma har zuwa yanzu ban ga ana shigowa da goro da alawa ba bare in tabbatar da zamana matar Jauro, karfa a yi mini sakiyar da ba ruwa, dan wallahi kwarankwatsa dubu matuƙar su Sa'adu rufata suka yi ba ɗaurin aure aka tafi ba, to a yau ɗin nan ba sai gobe ba zan ɗagawa kowannensu nono, tsinuwa kwa sai na tabbatar sun gama tsinuwa zan daina ja musu ita, ace na tara jama'a dan taya ni murna amma an shanya mu kamar wasu kaya a igiyar shanya"Inna Delu ta faɗa cikin raɗa dan kar mutane su fuskanci me ke faruwa, jikinta babu ƙwari dan duk ta gama sarewa daga samun cikar burinta.


"Haba Delu me yasa kike da gajen haƙuri ne? Ai duk gaggawar asara ta jira samu ko, sai ki bari ki ga gudun ruwan yaran nan amma ba wai kike ikirarin ɗaiɗaita musu rayuwa ba ta hanyar ambata musu tsinuwa bayan kin tursasa musu su aurar da ke, ai duk lalacewar naka nake ne, kuma naka sai naka daɗin zama sai bare, sannan ma ba da ni ba gaɗa a hurumi, in goyi bayanki da tsinewa ƴaƴan cikin ki yo Allah na tuba kika tsinewa su Umaru ina muka kama kuma" Cewar Shattu cikin ƙarfin hali dan ita ma gabaɗaya ta sare da ɗaurin auren aminiyar tata.


"Haba Shattu bakya tausayina yanzu a ce shekarata 70 amma sai yanzu zan yi auren soyayya, amma ina shirin rasa maƙwallaton zuciyata kuma marurun raina Jauro kina wata magana, na lura yaran nan kishin mataccen ubansu suke" Cewar Inna tana fakar idanun ƴan ɗakin ta share hawayen da ya taru a idanunta


"Ki dauri ki jure Delu, dan rabon kwaɗo ba ya hawa sama kuma duk nisan dare ai gari zai waye, in har kuna da rabon aure to za a ɗaura in kuma babu to sai...


"Bakin ki ya sari ɗanyen kashi Shattu, ai rabon aure ma kamar an yi an gama...




"Aure ya ɗauru, tsakanin Aisha (Delu) Tare da Jabiru (Jauro) A kan sadaki dubu hamsin lakadan ba ajalan ba" Maganar da wani maroƙi da ya shiga faɗa a lasifika




"An ɗaura, an ɗaura na zama matar Jauro Allah na gode ma" Cewar Inna Delu da ta tashi tsaye ta fara taka rawa tana waƙa, ita ma Shattun tsaye ta tashi suka shiga taka rawar a tare gabaɗaya falon ya karaɗe da guɗa kowa ƙoƙarin tofa albarkacin bakinsa yake na guɗar dan duk ɗakin kowa ya san cewa Delu tana mutuwer son Jauro haka shi ma yana ƙaunarta.

Shattu ce ta ɗakko ƴar pos ɗinta ta buɗe ta ɗakko ƴan biyar-biyar sabbi dal ta shiga liƙawa aminiyar tata tana yi tana cewa


"Alƙawari ya cika amarya, alƙawari ya cika amarya, in angonki ya shigo amarya ki yi masa fifita, amarya ki bashi ruwa ya sha, amarya alƙawari ya cika amarya" Tana yi tana mata liƙi ita kuma Imma Delu sai rawa take tana juyi, gabaɗaya matan falo ma tashi suka yi, suka haɗu da Inna ana ta rawa ana ranbaɗa guɗa ko hannu basu wanke ba da suke cin abinci.






Inna! Inna!! Inna!!!" Cewar Abubakar cikin ɗaga murya rai a ɓace yana wani muzurai da cin magani sai wani harare-harare yake yana musu kallon ɗaya saura kwata. Cikin kiɗima Inna da Shattu kai har ma da ƴan ɗakin da ke ife-ife da guɗa suka dakata kowa ya maida hanklinsa kan Abubakar ɗin da ya shigo kamar an koro shi.


"Habubakar kar dai ka ce mini maroƙin nan ƙarya yake ba a ɗaura ba ya karaɗe gida da sanarwa? Idan kuwa har ƙarya yake to wallahi sai na ɗaureshi daga shi har danginsa har sai igiya ta yi saura, a kan ɗaga mini hankali da ya yi" Cewar Inna cikin tashin hankali, burinta kawai Abubakar ɗin ya bata amsa bata ma lura da manyan ledojin hannunsa.


"Oho miki, gashi in ji Abba" Ya faɗa yana dangwarar mata ƙatuwar ledar goro, alewa, da kuma dibono wacce Abba (Sa'adu) Ya bashi ya kawo mata saboda ta ce matsawar ba a sayi goro da alewa da dabino an raba a wurin ɗaurin aure ba sai ran kowa ya ɓaci.


Juyawar da Abubakar zai yi aikuwa Inna taku ɗaya biyu ta yi fisgoshi, ji kake ƙiii ta maido dashi baya ta hanyar riƙo wuyan rigar jikinsa, sai da ta kawo shi gabanta sannan ta damƙe wuyan rigar da hannu ɗaya, ɗaya hannun ta dunƙule ta dage ƙarfinta na tuwo ta duma masa dundu a baya sai da ta masa dundu kifi uku sannan ta ce




"Ko ubanka Sa'adu ya yi kaɗan ya yiwa goron ɗaurin aurena da Jauro wannan dangwararwar yo Allah na tuba ba gwara ka ce Inna kwanta a ƙasa ba idan na kwanta ka fisgi ƙafata riiii har sai ka dangana ni da ƙofar gida, ai sai ya fi mini sauƙi a kan yadda na ji da ka yiwa goro da alewar ɗaurin aurenmu da Jauro riƙon sakainar kashi tare da dangwarar da su kamar an maka dole" Ta faɗa tana sakin rigarsa da ta riƙe wanda wurin gabaɗaya ya cukurkuɗe kamar an fito da rigar daga bakin kura.


Wani takaici ne ya rufe Abubakar ganin abin da kakarsa mahaifiyar ubansa ta masa a cikin mutane, dama ransa a matuƙar ɓace yake na auren da ta yi, dan abin kunya tsofe-tsofe da ita duk ta yi yaba amma wai za ta yi auren ƘARA'I. Wani irin kumburo baki ya yi yana wani huhhura hanci ya juya yana wani fisfisga ya fice daga falon.




"Au ko da na ji, she dai an ɗaura wallahi har gabana ya faɗi" Cewar Shattu tana buɗa ledojin.


"Rabu dashi ɗan kan uwa, an ɗauremu ni da Jauro, mugun hali ne irin na uwarsa, baƙinciki suke da auren sun fi so na zo mutuwa ana cewa matar marigayi ce haka kawai ai gwara a ce ka mutu da mijinka duk da ba a san gawar fari ba" Ta faɗa suna ɗaukar ledojin shiga rabawa mutanen da suke falon, dan dama duk daga ƙauyensu suke Shattu ta gayyato mata su, haka suka shiga rabawa mutane bakin Inna dan dama duk tsofaffi ne bakin Inna har kunne yau dai burinta ya cika, ɗaki ta shiga ta ɗakko wata shadda ƴar ubansu ta saka ta cakara ɗaurin ɗankwali har ta yi gwaggwaro ta koma ta ware ta ɗauki wani kofi a cikin ɗakin ɗan ƙarami da shi ta ɗora a tsakiyar kan nata tare da ɗaura ɗankwalin a kan kofin mudubi ta kalla aikuwa ɗaurin ya mata yadda take so.


"Ai gwara dai yau ɗaya in yi ƘARA'I in yi ɗaurin ɗankwali irin na yaran ƙauyenmu da suke wanda ake cewa a cuci maza"Cewar Inna tana dubawa ta ga ya yi kamar yadda yaran ke yi. Ƙaramar lokar mudubin ɗakin ta janyo ta ɗakko fanfas na yara guda biyu, jimƙe ɗaya ta yi ta ɗaga bireziyarta ta saka fanfas ɗaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login