Showing 1 words to 3000 words out of 59211 words

Chapter 1 - AJIYA A DUHU Book Complete Original billy.docx

04 Feb 2025

26254

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_

ب

ِ

س

ْ

م

ِ

الل

َّ

ه

ِ

الر

َّ

ح

ْ

م

َٰ

ن

ِ

الر

َّ

ح

ِ

يم

_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖0️⃣1️⃣

.......Ƙaddarorin rayuwa tamkar TASWIRA ce dake zane a takardar lissafin rayuwar kowanne ɗan adam, duk yanda ka so gogesu ko san kauce musu ba lallai ne ka samu makaman yaƙin ba balle GARKUWAR kare kanka daga isowarsu gareka ko mai gajartar tsahon shekaru ko yawaitarsu. A wasu lokutan mukanyi kuka ne da hawaye, sai dai kukan ZUCIYA shine mafi ciwo da ɗacin kuka da yafi kassara rayuwarmu da nasarorinmu a ɓoye ko a zahirance da bama iya mantawa. Dan a wasu lokutan har tambarin tabon da zamu iya ringa tunawa a lokaci bayan lokacin yake bar mana.

    A farkon haihuwar mu iyayenmu sune GARKUWARMU, dan sukan sadaukar da komai nasu ne domin lulluɓe RAYUWARMU da dukkan fatansu. Sukan rainemu da shauƙi da yaƙini har zuwa girmanmu. Hakan yake saka SOYAYYAR su bata taɓa iya goguwa a ZUKATANMU, sannan takan banbanta da irin kowacce soyayya da zata biyo bayanta. Koda hukuntamu sukai mukaji zafi mukai kuka wannan soyayyar tasu bata taɓa canja kanta a ZUKATANMU saboda su ɗin sune dai ɗaya tamkar da dubu a dukkan abubuwan dake zagaye damu na NASARA ko akasinta. 

      A lokacin da girmanmu ke ƙara yawaita sai TSUFA ya riskesu. Mu kuma ƘURUCIYA ta baibayemu. Sai dai me daga lokacin daka iya tantance ma'anar FARI da ƁAKI a yau ɗinka da gobenka littafin ƘADDARARKA kuma ya fara kenan da manyan zanukan layukan dake bayyana JARABAWOYINKA. Gwagwarmaya ta zama ƙawa ko abokin RAYUWARKA. Yaƙin ba yana farawa da gwagwarmayar RAYUWAR DUNIYAR kawai bane ba. Harda ta neman LAHIRA da zaɓama kai makoma ƙyaƙyƙyawa ko akasinta. Domin kuwa fara rayuwar girman na farawa ne da daidaiton mizanin ayyukan samun LADANKA da kuma ZUNUBI duk a bayyane kuma a rubuce ga wanda ya HALICCEKA. Iyayenmu kan gama gwagwarmayar ƙuruciyarmu, sannan su koma ta girmanmu babu gajiyawa saboda su ɗin na dabanne a cikin daban a garemu.

      A lissafin fara fahimtar kanka da tabbatar da WANENE kai, da wahala kaga babu armashin soyayyar ƙuruciya da takanyi kutse a ƙaddararka. Ba soyayyar bace ba kawai abar kallo ko zama daban a gareka ko wanda ke tare da rayuwarka. A yaya SOYAYYAR ta FARA? Ko ta ƙare? Ko ta kasance? Ko ta cigaba da wanzuwa? Itace madubin dubawarka ko masu juriyar bibiyar labarinka.

     ★ Ƴammata ne uku sanye cikin kayan hidimar ƙasa. Tsaye suke a bakin titi kowacce hannunta riƙe da hannun trolling alamar abin hawa suke jira. Dan suna ma ta ƙoƙarin tsaida napep amma mafi yawanci sai kaga akwai wani a ciki ta yanda bazai isa su ukun duk su shiga ciki ba. Cikin ɗan damuwa da ƙosawa ta tsakkiyarsu da bata da yawan fara'ar fuska ta ɗaga kai tana kallon sararin samaniya dake haɗa hadari. Ko kaɗan bata fatan ruwan nan ya taɓa ta. Dan hakan baya zama mai sauƙi a gareta shiyyasa tafi kowa damuwa da samun abin hawan nasu, daɗin daɗawa tafiyarsu mai nisa ce. Dan kuwa jihar Kaduna suka nufa.

       Fara tasowar iskar hadarin ta sata duban ƴan uwan nata idanunta na cika da ƙwalla. Sai dai kafin ta samu damar cewa wani abu wata jar mota tai parking a gabansu. Su duka idanu suka zubama motar, sai dai buɗewa da fitowar matashin saurayin dake ciki ya saka biyu a cikinsu sakin murmushi da mamaki. Yayinda ta tsakkiyar sun nan dai ta sake haɗe ƙyaƙyƙyawar fuskarta tana mai kauda kanta gefe. Shi kam saurayin nan gaba ɗaya hankalinsa na kanta. Ya ƙaraso gabansu dai-dai saitinta ya tsaya tare da faɗin, “Yanzu duk saurin da nake sai da kika nema guje min?”.

     Fuska ta sake haɗewa tana ɗan matsawa baya. Kansa ya ɗan sosa yana mai sakin murmushi. Hankalinsa ya maida ga sauran biyu cikin jifansu da harar wasa ya ce, “Amana batace dai haka ba friends. Kamar ni ina daku amma a so haɗa kai da ku a gudu min”.

     Dariya suka ɗanyi a lokaci ɗaya. Ta gefen damarsa mai ɗan jiki kaɗan ta bashi amsa da, “Ina ai bazamu taɓa yarda hakan ta kasance ba. Ko an gudu maka mu zamu kawoka har wajen ɓuyar RK. Amma ai mana afuwa mutuniyar taka ce ta addabemu da tafiyar sassafen nan. Kasan jiya ko barcin kirki batai ba saboda farin cikin zata koma gida taga Ammie”.

           “Ko dai tana farin cikin zata gudu daga Jos ta bar ɗan nacinta ba?”. Ya faɗa idonsa a kan budurwar tsakkiyar dai. Da sauri ta gefen haggunta ta amshe da “Haba RK kaima kasan ba haka bane sam”.

     “Humm Aneesa dama ai baƙya son laifinta ke tuni na fahimci haka. Duk ta inda aka ɓullo sai kin kareta. Ni dai yanzu ku shiga mota muje kunga ruwa na shirin sakkowa karya jiƙa min sarauniyata”. Kafin wani cikinsu ya bashi amsa a hankali ta fara jan akwatinta domin barin wajen. Saurin riƙo akwatin yay, hakan ya sata tsayawa cak batare da ta juyo ba. Zai yi magana Aneesa tai saurin girgiza masa kai tare da amsar akwatin. Babu musu ya sakar mata yaja da baya.

    Akwatin tai ƙoƙarin ƙara ja Aneesa ta sake riƙewa. Hakan ya sata juyowa a fusace zatai magana a zatonta shine sai taga Aneesa. Idanunta tai wani irin lumshewa da cizar gefen lips ɗin ta irin na takaicin nan kawai. Hakan ya saka Aneesa sakin murmushi dan tasan ta gama ƙurewa a fusata. “Kiyi haƙuri dan ALLAH” ta faɗa da sauri, bata jira amsarta ba ta cigaba da faɗin, “Kiyi haƙuri mu bisa _Maanal_, kalla garin nan ki gani hadari ne da akoda yaushe za'a iya fara ruwa. Kinfi kowa sannin illar da hakan yake miki. Kema kin san iyakarsa yace zai kaimu tasha ne kawai. Daga yau ne fa an rabu shike nan kuma. Dan ALLAH kada ki bari kuyi irin wannan rabuwar da shi. RK bai cancanci hakan daga gareki ba. Ko bazaki taɓa amince masa ba kada ki munana masa a yau ɗin nan da zamu rabu. Yanda baki wulaƙantasa ba a baya yanzu karki aikata. A rabu lafiya daga haka kuma bashi ke nan ba tunda ko lambarki dai yanzu bai da ita ballema kice zai cigaba da takura miki, ba kuma sanin gidanku yay ba idan kika cire sunan gari”.

      A hankali ta buɗe idanunta da suka gama kaɗawa, ga hawaye sun cika su zubowa kawai ya rage. Lips ɗinta ta buɗe zatai magana ruwa yay wani irin kecewa lokaci guda. Gaba ɗaya ta rikice. Har bata ma san Aneesa taja hannunta ta tura cikin motar ba itama ta shiga. Sai da taji babu saukar ruwan a kanta sai ƙararsa sannan ta farga ta ɗago kanta data cusa cikin ƙafafunta da sauri. Waigowar da zatai suka haɗa ido da RK daya wani zuba mata ido kamar zai cinyeta. Nata ta janye da sauri tana mai juyawa ta kalla ƙawayen nata. Da sauri Zeezah ta nuna Aneesa alamar babu ruwanta itace. Aneesar ma saita marairaice mata fuska alamar kartace komai dan ALLAH. Harara ta sakar mata tare da ɗauke kanta, sai kawai ta juya tana goge fuskarta da ruwa ya fara taɓawa da handkhachief.....

     Tunda motar ta fara tafiya babu wanda yay magana. Ga ruwa ana kwararawa kamar da bakin ƙwarya. Tuni wasu motocin ma sun koma gefen titin sun tsaya. Ganin sunzo sun wuce tasha yasa Zeezah yinƙurin yin magana. Da sauri RK dake kallonsu ta mirror yay mata alamar roƙon tai shiru. Haɗiye maganar tayi tana murmushi, sai kuma ta ɗan dubi Maanal da kanta ke sunkuye novel a hannunta alamar karatu takeyi, shiyyasa bata san wainar da ake toyawa ba ma.

       Shima dai RK ya raba hankalinsa biyu ne. Rabi ga tuƙi rabi a kallonta. Maanal ƙyaƙyawar yarinya ce kuma nutsatstsiya. Za'a iya kiranta tsaka tsaki a tsaho, a wani gurin kuwa ma wasu kai tsaye zasu kirata doguwar duk da ba shalleliya bace, sannan bata da wani jikin kirki. A duk wanda ya santa musamman a tsukun shekarun nan zai iya sakata a jerin miskilayen mutane. Bata da yawan magana, hakama bata da fara'a ko yawan walwala sam. Dan da wahala kaga murmushi ma a fuskar Maanal balle akai ga dariya. Akoda yaushe fuskarta ciɗin-ciɗin take. Hatta da magana ma sai taso take yinta. In har ba wani abu take mai muhimmanci ba to akoda yaushe zaka samu novel a hannunta tana karantawa. Hakan na nufin ita ɗin mayyar karance-karance ce. Dan zamu iya cewa ma yawan karance-karance nata ne yasa koda yaushe zaka samu idanunta da eyeglasses fari tas da mutane da yawa basa iya ɓoye mata cewar yana mata matuƙar ƙyau. Itama kanta tasan yana mata ƙyawun, dan takai tun ma tana sakashi domin karatu, har ya zame mata jiki akoda yaushe zaka ganshi tare da ita in har ba barci take ba ko wani abinda ba'a buƙatarsa. Sai dai kuma abinda kowa bai sani ba wani dalili ne daban ya ɗabi'antata da yawan daka gilashin akoda yaushe bawai dan karance-karance kawai ba, duk da a ɓangaren karatun ma yana bata gudummawa matuƙa........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)

2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)

3 DUNIYAR MU (Huguma)

4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500

Book 2:-1000

Book 3:-1500

Book 4:-2000

0022419171

Access bank

Maryam Sani Gumi

Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷

1000CF

Nousaiba Lawali Maradi

Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_

ب

ِ

س

ْ

م

ِ

الل

َّ

ه

ِ

الر

َّ

ح

ْ

م

َٰ

ن

ِ

الر

َّ

ح

ِ

يم

_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

_________________

Aslm barkanmu da wannan lokaci

Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka

Mallaka Maganin sanyi

Maganin cire tumbiMaganin farin jini

Maganin matsiMaganin mata

Maganin sa ni’ima da dandano

Dulka Amare Set na gyran jiki

Set na amarya

Tabaje tsumin Gomba

Xuma kiba ta hips and Brest

Magungunan gyran Brest

Magungunan Karin hips

Maganin sliming

Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa

Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291

Idan maganin mata kikeso akwai

Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips

DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻

Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500

Garin bata gaban kishiya 500

Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500

Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500

Za a bakisu akan 3800

Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k

🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki

_______________

🅿️➖0️⃣2️⃣

.......Ganin tafiyar taƙi ƙarewa yasata kai hannu ta ɗan gyara eyeglasses ɗin tare da ɗagowa ta kalla titi, har yanzu ruwa ake zulawa, sai dai hakan bai hanata fahimtar har sun fara barin gari Jos ba. Da mamaki a karo na farko ta dubi RK da tunda ta ɗago ya kama kansa daga satar kallonta da yake yi. Kamar zatai magana sai kuma ta kauda kanta. Sake maidawa tayi ga book ɗin, sai dai ba karatun take ba tayi shiru ne kawai tana juya maganar da take son fitarwa. Sai da ta mula dan kanta sannan a hankali cikin sassanyar muryarta da take matuƙar zama mafi girman rowa ga masu son ji irinsu RK ta furta. “Bayan waccan tashar akwai wata ne a gaba naga mun wuce?”.

        Har cikin tsakkiyar kai yaji gajeren zancen nata. Sai da ya wani lumshe idanunsa ya fuɗe tare da sakin murmushi sannan ya bata amsa da, “Bazan iya saukeki a ko'ina cikin ruwan nan ba kiyi haƙuri sai a Abuja”.

      Ɗagowa tai kamar zata kallesa sai kuma ta fasa. Sake maida kanta tai ga buk ɗin kawai tana ɗan cizar gefen lips ɗinta. Murmushi ya ɗan saki shima dan ya fahimci wannan cizar lips ɗin nata takan yisa a duk sanda takai ƙarshen takaicin da har ta rasa abin cewa.

     “Kiyi haƙuri Please”.

  Ya sake faɗa a hankali. Bata tanka masa ba, sai ma sake maida kanta tai a karatun kawai. Shima sai yay gum da bakinsa ya maida hankalinsa gasu Zezaa tunda dai ya samu da alama ta haƙuran. Tanata karatunta suna hirarsu. Yawan sakkota a hirar tasu da dariyar da suke ya fara gundurarta, sai kawai ta manna Bluetooth a kunnenta ta ajiye book ɗin ta lumshe idanunta. A haka barci ya kwasheta tana sauraren karatun Alkur'ani data sanya daga bakin Gwani Abdullahi Zaria. Har suna gab da shigowa garin Abuja ruwan akeyi, har kuma lokacin Maanal barci take sosai dan sam batai isashen barci jiya ba. Addu'a yay tayi da fatan subar Abuja bata farka ba. Dan yasan zata iya tuburewa akan ya ajiyesu anan ɗin, aiko addu'ar tasa bata amsu ba. Dan sun wuce zuba kaɗan kuwa ta farka. Agogo ta fara kalla sannan ta juya tana kallon su Zezaah.

     “Muna ina ne yanzu?”..

  Ɗan kallon juna sukayi, sai Zezaah tai tsulum tace, “Mun fita a Abuja”.

        Da mamaki Maanal dake kallon titi ta ce, “Mun fita fa? Wannan ba hanyar suleja bace? Ko nan ba madalla bane?”. Yanda ta ƙare maganar tana kallon RK ya sashi ɗan sosa goshinsa yana furzar da iska. Sai kuma ya jinjina mata kai ganin ta wani tsaresa da idanunta dake matuƙar firgita masa lissafi. Kanta ta ɗauke tana faɗin, “To Alhamdullah sai ka sauke mu a dikko kawai ai zamu samu motar Kaduna a wajen”.

       Sosai fuskarsa ta nuna damuwa. A marairaice ya ce, “Haba miya rage Baby, tunda mukazo nan can ma bazai gagara ba. Kiyi haƙuri mu ƙarasa, ina Abuja ina Kaduna”.

     Yanda yake mata magana kamar zai yi kuka yasa haushi ya sake kamata. Mutumin nan sam baya ganewa, ta rasa mi kuma zata masa ya gane ɗin. Duk yanda taso hanasa kaisu kadunar hakan bai yiwu ba. Dole tana ji tana gani ya ɗauki hanya. Hankalinta ta sake maidawa akan novel ɗinta ta sharesa. Sai su Zeezah ne keta hirarsu da shi. Yanzun ma ko sun sakkota bata tankawa. Suna isowa Kawo tace ita anan zata sauka. Yi yay kamar bai jita ba. Cikin ɓacin rai ta juya tana kallon su Neesa. Cikin jin haushi, duk da muryar tata na fita ne da sanyinta da nutsuwa ta furta, “Malamai kusa ya saukeni anan tunda naga da sawarku yake komai”.

           Kafimma su bata amsa RK yay saurin faɗin, “Sorry Baby babu ruwansu. Ni dai fatana sai na direki har ƙofar gida dan ALLAH”.

   Yanzu kam harara ta zuba masa. Ya wani lumshe idanu da buɗewa a lokaci guda ya saukesu a kanta. Da tasan ta'asar da harar nan ke masa data tausaya masa ta bari. Ganin dai zata kife da shi yay ƴar gyaran murya yana wani marairaice fuska. “Please ki tausaya min hararar nan illa take min”. Ya faɗa a wani irin hankali kamar mai raɗa har yana ƙoƙarin ɗan matso ta. Janye jikinta tai ta lafe a murfin tana rumtse ido da ƙarfi. Daga haka bata sake magana ba. Su Neesa ne suka shiga nuna masa hanya har anguwarsu Maanal ɗin data kasance cikin manyan anguwannin da kadunawa ke ji da su (Ina da tambaya?, wai Kaduna akwai anguwanni masu ƙyau dan ALLAH ko sai sun zo Kanon mu suke gani kawai😂🥱🤪🤪. 🏃🏃🏃Bari na ware kafin ƴan Kaduna su maidani awara yau ɗin nan kun san bazazzage ba sauƙi🤣😘). Dai-dai ƙofar wani katafaren farin gate da akaima ado da golden suka tsaya. Ya wani sauke ajiyar zuciya yana kallon gidan da ƙyau. Eh lallai ashe itama ƴar masu kuɗi ce. Dan gidan nan kam dai ya kai a kirashi gida.....

        Fitar Maanal a motar ta sashi saurin katsewar tunanin sa. Shima da sauri ya buɗe ya fita. Dai-dai tana ƙoƙarin buɗe booth. Shine yay saurin sakko mata da akwatin ta. Ya juya da nufin sauke nasu Neesa taja kayanta. Su Aneesa da suka gama fahimtar mi take shirin yi duk suka fito. Magana Zezaah tai yunƙurin mata tai mata wani kallo na babu ruwanki da ni taja akwatinta tai gaba. Sai da tai ɗan taku uku zuwa huɗu ta juyo ta kalla RK daya zama kamar gunki a tsaye. Idanunta dake cikin gilashi ta ɗan lumshe ta buɗe a kansa. “Mun gode da ƙoƙarinka. ALLAH yabar zuminci. Amma zan baka haƙuri dan ALLAH karka cigaba da wahalar da kanka, kamar yanda na faɗa maka gaskiya tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login