Showing 24001 words to 27000 words out of 34045 words
Chapter 9 - KWARTON MANYA Book 3 end Writing by Maman Teddy .txt
rufe basa ko ganin gaban su...kashe mun ke zaiyi?? Ina bazai yiwu ba ,ga tukwicin saki ga kuma shi yana shirin kashe mun ke Sobreen?? Tabbas sai na kaisa kotu ,kotun ƙoliii kuwa, muje sobreen ,nemo mana keke mu hau yanxu zamu tafi kotun ƙoli....Ammin Sobreen ke tafe tana sambatu na mahaukata , wanda nesa na hango Sobreen tana gudu haɗi da ƙwala kirar sunan ta Ummma!! Amma ina gaba tayi tana shiga titi wannan abun hawa ya kauce mata ,wancenn ya kauce mata". Isowan Sobreen yasata saurin jan hannun ta tana kauda ita daga titin ,kana tace " Umma sati nawa da barin mu gidan Abba , muyi hakuri komai ya faru damu mu muka jah mawa kanmu". Tayi maganan tana goge hawayen fuskar ta , da tayi baƙi wannan farin fatan da ake ƙafulle dashi ya jeme ta lalace tamkar ba ita ba. Sobreen!! Taji an kirata cike da mmki ta juya ganin su Shema'u da Hjy Luba suma a wulaƙance ". Kunya ne ya kama Sobreen wanda yasata kasa haɗa ido da su sai sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana cigaba da zuban hawaye". Mai ya sameta ??? Hjy Luba tayi maganan tana nufar inda Mahaifiyar Sobreen take ta duƙa tana ta tsintar ledoji . Cike da Muryar kuka Sobreen take basu labarin sakin da mahaifin ta yayi mawa Umman nata , da kuma dukan da yayi mata tamkar zai kashe ta ....wanda ruɗun rabuwar su yasata haukacewa...... Salati Hjy Luba tasa tana rushewa da kuka , wanda suna tsaka da hakan ne Suka ga Umman Sobreen ta razana tana jah baya da cewa " Ni ne Alh nafi'u zai saki?? Bazai yiwu ba sai na kai sa kotun ƙoli tana maganan haɗi da fallawa da gudu tana nufar titi , bin ta sukayi suna cewa " Taimako a kamata a riƙe , amma ina tuni ta shige ma titin , wani babban moto ne yayo kan babban titin ,wanda jah baya su Hjy Luba sukayi suna sakin wani gigitaccen ihu ganin moton yabi takan Umman Sobreen.... Sobreen kuwa ganin hakan yasata zubewa wurin gwiwowin ta ƙasa tana tsaga ihu.... Mutane ne suka rufe wurin ciki harda Alh nafi'u mahaifin ta da dama yake neman ta ta bashi ƴar sa . Da ita kenan masa wato Sobreen ya ɗauki alƙawarin aura mawa koma waye koda kuturu ne".
[7/3, 16:01] Matar Doctor: *Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*
****
[7/3, 16:44] Matar Doctor: *Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*
Mutane kuwa daga masu kama kai sai masu ihu ganin irin daga dagan da Umman Sobreen tayi ta haɗe da kwalta , inalillahi wa'inna ilaihir raji'un shine kaɗai abun da Hjy Luba ke cewa " ruɗu iya ruɗu tashi ga a wannan rana .. Alh Nafi'u ne ya kama hannun Sobreen da take ihu kaman ranta zai fita ,yana jefa ta a moto yana jahh haɗi da barin wurin , don ko a jikin sa ganin wannan haɗari , cewa ma yake hakkin mahaifiyar sa ne , da ta raɓasu tsawon shekaru. Don haka can zai kai Sobreen garin Adamawa ta koya mata tarbiya kaman sauran ƴaƴan da ya saba gani.
Zainabu kuwa sam bata farka ba sai wuraren 9:00am ,wanda da addu'a a bakin ta ta miƙe , tana kirar sunan Habab , sai da idon ta yaƙara buɗe wa ne ta tabbatar da mafarki tayi". Dafe ƙirjin ta tayi da yake harba mata da ƙarfi tana cewa " Meke shirin faruwa da Habab ?? Allah kasa mafarki ne ba gaskiya bane . Kasa nufar toilet tayi sai kawai nufan falon tayi don ganin Momy a wani hali take ciki don tasan jiya a kanta ta kwana". Cike da murmushi Momy take bin Zainabu da kallo da tayi wani dama² tayi kyau ta murje sai ƙiban ta take mai sukuni da natsuwa. Cike da harka Zainabu ta ke yin mata an tashi lfy? Kana ta nufi kitchen don taimaka mata aiki. A'a Zainab koma kije ki huta , na kammala komai ai , yanxu ke nake jira ki shirya kizo kiyi breakfast sai kisha maganin ki". Nisawa Zainabu tayi tana murmushi da mata sannu da aiki ,kana ta juya don ta watsa Ruwa ta sauya kayan jikin ta daga na barcin zuwa na zaman gida". Cike da jin ƙaunar Zainabu n Mom Salma kebin ta da kallo , tabbas abun da take hasashe hakan yake , juna biyun jikin ta na nan bai fita ba ,Allah kenan! Allah ya raba lafiya". Mom Salma tayi maganan tana cigaba da shirya dirnng area n. Motsin Zainabu ne yasata ce mata " Bismillah zauna dai da lura! To Momy". Zainabu tayi maganan tana zama a hankali duk jikin ta nauyin shi take ji a kwana biyu sai tana rinƙa jin ba daɗi a harshen ta ,kome xata ci bata jin daɗin shi....nan tafara break cike da gode mawa Mom Salma don iya girki da karamci ba baya ba". Gaskiya Mom Komai yayi daɗi". Zainabu tayi magana tana dariya. Dariya itama Momy tayi tana cewa " mashaallh to tun da Zee ta yaba saura ɗan ƙaƙƙwafi Habab! Ohhh!! Ɗazu fa Habab yazo gidan nan kina bacci tfy aiki ya kamasa a yau ɗin nan yanxu ma ina tunanin jirgin su ya ɗaga gasky". Wani irin bugawa ƙirjin Zainabu yayi , wanda sakin cup ɗin tea tayi tana cewa " Momy meyasa kika bar sa ya tafi?? Wallh tsoro nakeji nayi mafarki Momy ki kirasa ya dawo!!!. Ganin Zainabu ta ruɗe lokaci ɗaya yasa Mom Salma saurin dafata tana ɗan bubbaga kafaɗan ta da cewa " Shiiii... Ya isa ai zai dawo yace baifi 1 mount zaiyi ba , kuma mafarki Zainab ba gaskiya bane ba kinji ,Allah zai dawo maki da Habab lafiya inshaallh". Nisawa Zainabu tayi ji tayi komai ya fice mata a rai. A hankali ta ce " To Momy Allah yasa". Amin abun da Mom Salma tace kenan tana cigaba da matsar mata da irish gaban ta.
****
Kwana uku da tafiyar Habab Daddy da Kanshi yazo bikon Mom Salma ,wanda iyaye sun shiga cikin maganan sosai da ƴan uwa da suke ta zuruntu garuruwa kuwa ,wannan yasa don dole Mom Salma ta kuma amincewa , a satin a ka maida auren su da Daddy ,duk da ba wani taro akayi ba,manya ne a dangi suka taru...a kuma ranan Mom Salma da Zainabu da baki yaƙi rufuwa saboda farin ciki suka koma gidan Daddy. Da komai na gidan sai da aka sake , niko nace sabon gwamnati kenan shi aka kafa". A ɓangaren Zainabu ke zaune ,kula da gata iri iri take gani a wurin Momy da Daddy kowann su na ƙoƙarin ganin sun faran ta mata ,sun kawar mata da dukkan wani damuwa . Wanda a yanxu kusan wata ɗaya kenan da tafiyar Habab . A yau ne Zainabu ta shirya don zuwa gidan Umman ta ,wanda a yanxu idan kaga Zainabu komai na alamun masu ɗauke da juna biyu ya bayyana mata , gashi bai fara girma ba ,amma ya sata tayi kyau matuƙa ,duk da da hutu da kula irin na Mom Salma da take bata".
Farin ciki da taje gidan ba'a magana wurin mutan gidan da su Abba ,bana har da Sama'ila anan nan da ita ,wanda sosai taji daɗin hakan , Zainabu fah anyi hankali don har da tsaraba takai mawa su Umma da sauran yaran gida. Anan take jin ashe Habab sai da yazo sukayi sallama sannan ya wuce. Wurare n yammaci ta tattara tana komawa gidan Daddy. A falo ne take jin kukan mutane da magiya na ban haƙuri ,wanda yasata kutsa kanta cikin sauri , idon ta ne ya sauka akan Hjy Luba da Shema safiya dukan su a falon gaban daddyy ,gyefe guda kuma Mom Salma ce itama fuskar ta ɗauke da damuwa.........
*Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*
[7/4, 16:55] Matar Doctor: *Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*
Jiki a sanyaye Zainabu ta isa tsakiyar falon tana zama gyefen Adda Raliya da itama ke share ƙwallah ganin yanda Uwar tasu duk ta mozan ta ,duk da da halin ta amma kuma uwa uwace ! Zama Zainabu tayi a ƙasa a hankali tana jin yanda Safiya da Shema'u keba ma Alh Ahmadu Haƙuri harda Hjy Luba , wanda cike da Muryar girma Alh Ahmadu ke cewa " Ya yafe masu Allah shi yafe mana baki ɗaya". Jin hakan yasa Su Hjy Luba juyowa ga Momy da Zainabu da kanta ke a ƙasa suna bata haƙuri akan abubuwan da suka ai ƙata da yanda ta kori Momy da hannun ta duk don kishi da masifa". Cike da nuna komai ya wuce suka ce Allah ya yafema na baki ɗaya". Wani irin Zainabu taji ganin wai Hjy Luba ce take yi masu sallama zata bar gidan ita da su Safiya. , Wanda ganin hakan yasa Momy kallon Daddy tana cewa " Ya kuma zaka barsu su tafi? Don Allah dai kayi haƙuri akan komai mu ɗauke shi muƙaddari dama rubuta ce ne Allah ya tsara xaya faru. Maganganun Momy ne yayi tasiri a zuciyar Daddy , wanda sai da suka fita ne yake ce mawa Adda Raliya ta kai su ɗaya daga cikin gidajen sa na High low cost , ya bama Hjy Luba har muddan rai , su Safiya su zauna can , har Allah ya basu bazajen aure ,idan kuma auren nasu ya dai daita Alhmdullh". Ba Adda Raliya ce kaɗai tayi godiya ba , har da Zainabu da farin ciki yaki ɓoyiwu a fuskar ta , don ganin Hjy Luba a wannan hali ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba". Godiya sukayi ta mawa Daddy har ya shige side ɗin shi ,kana Adda Raliya ta fice da sauri don sanar mawa su Hjy Luba da kyautar da karamcin da Daddy yayi mata... Momy ne ta kalli Zainabu tana murmushi kana tace " Har kin dawo yasu umma?? Suna lafiya Momy sunce a gaishe ki". Cike da jin daɗi Mom Salma tace " to mashaallh ina gdy. Tun daga nan shiru ne ya biyo bayan su tsawon lokaci ,kamin Zainabu ta katse shirun da cewa " Momy wai don Allah nayi maki wata tambaya ,Allah yasa bazai ɓata maki ba , don a kan rayuwar ki ne Momy da na Habab!
Murmushi Mom Salma tayi kana tace " Haba ɗiyata faɗi maganan ki mana ? . Gyara zama Zainabu tayi tana kama hannayen ta kaman mai shirin bada labarin wani abu ,kana tace " Har yau Habab bai san daliln barinki gidan Daddy ba , anai meki an rasa , kin rabu dashi da Daddy ,wanda ada baya akan su ki rabu da komai naki ƴan uwa ƙasar ki da kowa naki ,amma Momy lokaci ɗaya da rana tsaka aka neme ki aka rasa wai meyasa??? . Nisawa Mom Salma tayi tana girgiza kai kurum na tana lumshe idon ta haɗi da buɗesu lokaci ɗaya ta fara tuno da komai na rayuwar ta da ya shuɗe". Zainab tabbas kaman yanda kikaji haka yake , Ni Asalinsa baturiya ce ta england , wanda acan nayi rayuwata da ƴan uwa na , Alh Ahmadu yazo ƙasar akan kasuwancin sa ne sanadin riƙon amanan sa yasa naji ya burgeni kuma har naso mu ƙulla mu'amala da shi ,wanda da ga hakan har addinin iyayena na bari na zaɓi na zauna dashi na bar ƙasa ta ,kuma iyayen shi basu taɓa nuna mun wani ƙiyayya ko hantara ba...sai dai ba mutaɓa samun ƙyaƙyatawa r mu'amala da Ita ba. Kullum a cikin yada mun da maganganu da gori tana kirana da tubabbbiya ,wanda hakan ke ɓata mun rai matuƙa , kullum ina hƙri don Ni macace marar son hayaniya bare faɗa ,aranan dana bar gidan ban taɓa mantawa a yammacin ranan ne Hjy Luba da ƙanwarta suka zo suka tsaya mun aka suka zageni zagin tijara da cin mutunci wanda fushin zuciya yasani barin gidan , a daren ,wanda a washe gari na bar Nigeria na sauka a ƙasar Japan na cigaba da rayuwata tsawon lokaci , duk da rayuwar bata mun daɗi kullum ina cikin kewa na ɗana da halin da na bar sa ,ga kuma mijina Wanda sanadin shi na shiga addinin Musulunci ,wanda zai kaini ga Allah da Manzon sa. A kullum ina hƙri da wannan rashin ashe mahakurci mawadaci yau gashi na dawo ina zaune da ɗana da kuma mahaifin sa...ga ƙarin sarika har ina gab da samun jika ta ƙare maganan tana sa dariya da gode mawa Allah. Cike da kunya Zainabu ta rufe idon ta tana miƙewa haɗi da shiga ciki da sauri. Dariya Mom Salma keyi sosai . Kana itama ta miƙe tana nufar ɓangaren Daddy"
Haka rayuwa yayi ta tafiya , kullum Zainabu na fama da lallaulayin ciki don sai da cikin ya fara girma ne sannan take jin jikin ta , yanxu kusan 5 mount kenan , tun da Habab ya tafi Basu taɓa waya ba ,kullum in ya kira wani abu zai gifta tsakanin su ,wanda shikenan Muryar natan da baxaiji ba kenan , don bacci ne take yawon yin shi ,shi kuma duk idan yaji tana bacci sai yace Mom ta rabu da ita basai an tashe ta ba. Tun Zainabu na nuna rashin damuwa ta , har tafara tunani ita dai har ga Allah tsoro n aikin soja takeyi musamman irin nasu Habab ɗin ... Zaune take a falo cikin atampha brown tayi ɗinkin doguwar riga ,don juna biyun jikin ta ya fito sosai duk wani siffa ta mai cike ya bayyana mata , gaban ta dafaffan ƙwai ne a bowl da Mom Salma ta kawo mata , don a yanxu kullum ta samata sai ta ci shi , kunsan abunka ga likita musamman in abu nasu. Ruwa tasha tana ƙara vol ɗin tv da take kallo . Bin Agogan falon take da kallo ganin har 5:pm Mom Salma bata dawo ba ,don tace " bazata daɗe ba". Amma kuma har yanxu shiru.
Can taji horn ɗin motoci wanda yasata nisawa a zuciyar ta tana cewa" Momy ta dawo kenan , miƙewa tayi daga tsaye don ta yi mata " Barka da dawowa , wanda dai dai tana isa falon ne tafara jin takon sa wanda take jin sa da kuma ganin sa a mafarkin ta na kullum idan ta kwanta . Bugun zuciyar ta ne ya ƙaro jiyo ƙamshin sa wanda baya taɓa bace mata koda kuwa sunyi nisa da juna. A hankali ta ɗago da idanun ta da suka kosa da ganin sa , tana watsa su akan fuskar sa ,wanda yake fitar mata da Annuri yana sakin mata ƙasaitacciyar murmushi n sa ...mmki ne yasata tsayawa cakk ta kasa motsawa , Mom ne dake gyefe itama tana murmushi tace mata " Suprice!!! Dariya Zainabu tasa wanda kamin tayi magana Habab ya da yayi mata ƙurr yana bin ta da kallo ,gani tayi ƙiba tayi kyau ga ciki a gaba ,da bai san dashi ba , wani irin farin ciki ne ya ninnku a zuciyar sa ,wanda cikin sauri ya ware hannayen sa biyu yana kirar ta da take gare shi".
Tsayawa tayi tana kallon sa idon ta na ciko da ƙwallah , a zuciyar ta cewa take " Ji yanda yayi kyau yaƙara wani kamala , hummm wata uku a haɗu da tafiyar sa to da wacce macen ma ya zauna can, don Nasan Habab bazai taɓa iya kwana ɗaya ba tare da yayi Sex da mace ba....tana wanna n tunanin ne taji ya rungume ta yana dariya , haɗi da jan kumatun ta da suka yi suɓu³ dariya tasa tana ƙara shige masa , wanda ba ko kunya , Habab ya ɗaga ta cakkk yana juyi da ita , dariya take yana ƙyaƙyatawa ,ita ko Momy cewa take kuyi hankuli dai da Bbyn?? . Diree ta yayi yana kama hannun ta yana rungumota a tare suka zauna a falon , itama Mom Salma tana zama a ɗaya daga kujerun falon.
*Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*
*Mmn teddy*
[7/5, 08:37] Matar Doctor: *Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*
Ko wannen su ka kalli fuskar sa zaka ga yana ɗauke da matsanancin fara'a , musamman Momy da a kullum take mafarkin ganin familyn nata cikin wannan yanayi...Ita dai Zainabu tun da ta zauna ba tace masa komai ba sai Mom ce take ta jan sa da firar tafiyar tasa har zuwa dawowan sa". Kusan minti sha biyar suna firar sai dai hankalin sa na akan Zainabu da tayi shiru yawan zuban ta ya ragu ,kodon cikin jikin ta ne ? Tunanin da yake kenan kamin ya miƙe daga tsaye yana cewa " Momy yau fah zamu koma da Zee gidana , mun bar gidan Daddy daga yau .... Saurin kallon sa Mom tayi cike da mmkin wani gidan kenan ,ita ma Zainabu a wannan karon shi take kallo , kaman wanda ya bincika zukatan su ne ya cigaba da cewa " Gidana da Daddy yace " Bazan koma