Showing 1 words to 3000 words out of 56602 words

Chapter 1 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt

19 Feb 2025

3266

๏ปฟCopying and Compiled bay Umar Dalha.




๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ


YAREEMAH JAWAD


๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ




















BISSMILLAHIR RAHMAN ARRAHIM




INA GODIA GA ALLAH MAI KOWA MAI KOMAI DAYA BANI IKON SAKE DAWO MUKU A SABON NOVEL DINA INA FATAN XAKU KARBESHI HANNU BIBBIYU DAN KARUWA DA ABINDA KE CIKI.








GODIA MARA ADADI GA DUNBIN MASOYAN SUMYNBASH ๐Ÿ’‹DA WANDA NA SANI DA WANDA BAN SANI BA INA ALFAHRI DAKU A DUK INDA KUKE.








GARGADI


BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARINA BA. DUK WANDA YYI HAKAN ALLAH YA ISA.








WANNAN NOVEL DIN KIRKIRARRENE BANYI SHI DAN CIN XARAFIN KOWA BA, I DAN YAXO A IRIN RAYUWAR KI/KA BADA NIYA BANE.










INA ALFAHRI DAKU


AISHAT A MU'HD


NAFESAT ANKER


RAHENAT


UMMA ILA


SAFAH


SAEED BEBEJI


FATY AXLAND


MAMAN IHSAN




DAMA SAURAN WANDA BAN FADA BA DAN KUNA DA YAWA. ILUSM๐Ÿ’‹








SADAUKARWA GA




LATE ALHAJI SHAREEF KABEER FAMILIES

AND




ALHAJI SADEEQ IBRAHIM FAGGE












A romantic love story
2017










Story & written by โœ๐Ÿป


SUMAYYA SALEES SADEEQ












Chapter 1&2




Qatar






"Kyakkyawar budurwa ce kwance take a cinyar mom dinta tana kuka wanda daga gani kasan na shagwaba ne.






A hankali ta fara magana da muryarta mai dadi kamar ana busa sarewa,plx mom muyi xaman mu a qatar karmu koma nigeria. Daria mom tayi kai xaljamil rigima ta miki yawa, banda abinki ya xa'ai kice mu xauna a qatar bayan ga country dinmu chan asalinmu yake.






Kuma fashewa tayi da kuka, mom ni baxani ba sai dai ku tafi ku barni anan. Baki mom ta saki, eh lallai kina mace ba namiji ba, wane irin iyaye kika dauke mu?






Mikewa xaune tayi ta kama hannun mom, mom na miki alkawarin kula da kaina, kinsan bana daga cikin ballagaxaxxun mata, xan kare mutuncin kaina plx, ta fada tana share hawayen dake fuskarta.








Xaljamil mai yasameki wai? Ko kin fara shan wani abune, contract ne ya kawo dad dinki kasar qatar kuma ta kare dan haka dole xamu tafi nigeria nan da 2days kuma dake xamu tafi.








Maganar mom ta bata ran xaljamil, dan haka ta mike daga cinyar mom ta nufi dakinta tana rusar kuka,. Mom ce ta bita da kallo, sanye take da doguwar riga pink colour wacce taji adon stone, kanta bbu dankwali sai ribbon da tasa ta tufke gashin kanta daya xuba har gadon bayanta. Tana shigewa mom ta mike hade da sauke a jiyar xucia..




Dakin xaljamil ta nufa, kwance ta sameta tayi ruf da ciki tana kuka, da sallama mom ta shiga dakin ta xauna kusa da xaljamil.






Habibty mom ta kirata da sigar lallashi, a hankali ta dago kai ta kalli Mom da idonta jajir. Mom ce ta mata nuni data taso ta taho wajen ta, tashi tayi ta nufi jikin Mom ta shige jikinta tayi luf tana kuka. Mom ce ta fara lallashinta dan jin kukan xaljamil take har cikin ranta. Kiyi hkr habibty ki daina kukan nan bashi da amfani. Menene illa a cikin komawarmu nigeria? Kasar mu ce, dolen mu mu koma cikin ta.


Kuka xaljamil ta kara fashewa dashi, tana magana, Mom banasan nigeria a yarda nakejin labari rinta baxan iya xama a cikin ta ba.,i can't wallahi, qatar is my country, a cikin ta aka hanani, an mini takardar shedar ni yar kasa ce, ku barni a kasata mom please.




Baki mom ta saki tana kallon xaljamil cike da mamaki, ganin da gaske take batasan nigeria,. Xaljamil mom ta kira sunana, na'am ta amsa cikin sheshekar kuka.




Kinsan kuwa cewa ke jinin sarautace, da sauri xaljamil ta dago kai ta kalli mom fuskarta dauke da murmushi. Da gaske mom? Yea my habibty.da gaske, grand fa dinki sarkine. Murna sosai xaljamil ta fara, mai yasa baku taba fada mini ba ta tambayi mom? Murmushin nasara mom tayi, menene abin fada tunda nasan xakije ki gani. Tuni annurin fuskarta ya dauke, xanje na gani ta maimaita? Eh mom ta fada tana kallonta. Tinxuro baki tayi ni baxani ba, nama daina murna ma, inama a ce sarkin qatar ne kakana ai danaji dadi amma sarki a nigeria ai bama dadi sarautar.






Haba habibty gaskia bakisan nigeria ba, amma sarautar nigeria akwai dadi dan baki gani bane shiyasa, hmm mom duk yarda xaki yabi nigeria ba xata taba yi mini ba. Kuma ko xanje ba xan kalli kowa dan ina ganin su a tv bakake dasu ga muni,kinsan ban saba ganin bakake ba a cikin fafare na tashi fafaren ma larabawa larabawan ma na qatar ta fada tana kara hade rai. Rayuwata xanyi ni kadai a dakina, mom ce ta maka mata harara a karkashin gado habibty. Mom da gaske nake dan kwara ma kuce ba dani kuka xoba.,ko kuce masu bani da lpy banasan ganin kowa a kusa dani. Daria mom tayi, xaljamil kenan wallahi kyayi kya gama gujegujenki kuma daga karshe dole ki saki jikinki ba. Kuka xaljamil ta fashe dashi, mom ynx ba kya sona ko? Hararata mom tayi waya fada miki haka? Nina gani mana.Ina sanki xaljamil, yarda na haifeki haka nima mamana ta haifeni, kuma tanasona, tanasan ganina a kusa da, yaushe rabon dana gata, wallahi ba'a san raina nake xaune a qatar ba.




Idon xaljamil akan mom harta gama magana, cike da takaici xaljamil ta mike daga jikin mom ta shige toilet ta rufe. Tagumi mom ta buga tana tunanin yarda xaljamil ta bullo musu da da sabon alamari, duk da tasan laipinsune basu taba xiyarta nigeria ba tunda sukaxo qatar.













SUMYNBASH CE


๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ


YAREEMAH JAWAD




๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ










A romantic love story
2017






Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ










Chapter 3&4










Wacece Xaljamil








Kyakkyawa ce mai kama da larabawa, fara ce tas mai manyan idanu da dogon lashes, tana da dogon hanci da karamin baki, ga kuma beauty point wanda ke kara bayyanar da tsantsar kyan xaljamil. She is tall nd slinder a takaice dai xaljamil ta hadu.








Ta samu kyakkyawar tarbiyya daga wajen mahaifanta, tayi saukar alqur'ani mai girma, ta kuma kammala haddarsa, miskilace, bata da yawan magana, amma tana da barkwanci. A kasar qatar aka haifeta, anan ta taso amma bata da kawa balle aboki, ita kadai take rayuwar ta a skul. Ta kammala degree dinta a wata babbar university dake qatar, ta karanci anatomy. Xaljamil bata taba soyayya ba dan haka bata san so bama. Tana yiwa iyayenta biyayya bata taba kin yarda da abinda suka xo mata dashi ba sai komawarsu nigeria. Shiyasa mom takejin bbu dadi ganin yarda take masu biyayya kamata suma su mata abinda takeso sai dai bbu dama.








Mom ce ta sauke ajiyar xucia ta mike ta nufi dakinta dan gabatar da sallar magrib. A hankali xaljamil ta murda handle din ta fito daga toilet din kirjinta daure da towel tana kuma tsane gashin kanta da karamin towel. Dressing mirror ta nufa ta xauna ta fara shafa mayukanta masu kamshi, ta feshi jikinta da arabian perfume masu dadin kamshi.powder ta shafa a fuskarta ta nufi wardrob.








Sanye take da riga milk iya gwiwa da brown din wando pencil, ta dauke kanta da ribbon milk. Har ta xauna a dakinta taji tana san ganin mom dan haka ta mike ta nufi falo ranta a bace.








Mom xaune a falo tayi xirfi acikin kallon wani film da akeyi a mbc action mai suna v. Har xaljamil ta karaso inda take, a bayan kujerar da mom ke xaune xaljamil ta tsaya tana kallon itama. Kamshin turaraenta mom taji dan haka ta daga kai ta kalli xaljamil hade da sakar mata murmushi, bata rai xaljamil tayi ta nufi 1cter ta xauna ta cigaba da kallon film din batare da ta kalli inda mom takeba. Door bell aka danna da sauri xaljamil ta mike dan bude wa, dady ta gani dan haka ta buga tsallen murna tayi hugging dinsa, oyoyo dady! Daria dad keyi, kai xaljamil bakya girma ko? yanayin fuskarta ne ya chanja data tuna da dad ne ya bullo da barinsu kasar da take bala'in so, dan haka ta saki dad ta nufi dakinta da sauri.






Mom ce ta karaso tayi hugging dad hade da karbar briefcase din hannunsa, peck dad y bata a goshi jikinsa duk yyi sanyi, mai ya samu xaljamil?dad ya tambayi mom. Kasan na mata maganar xamu wuce nigeria gobe shine take bacin rai harda kuka wai baxata jeba,murmushin takaice dad yyi. Mom ce ta kama hannunsa ta raka shi dakinsa hade da taimaka masa har ya shirya, tare suka fito,Direct dakin xaljamil ya nufa.








Xaune take a gefen gadon ta ta buga tagumi tana hawaye, da sallama dad ya shiga dakin ya xauna kusa da ita,xaljamil ya kira sunanta, bata dago ba ta kallesa ba dan tafi jin haushin dad. Daga ta yyi chak ya nufi dining area da ita, sai kokarin sauka take amma dad yaki bata dama, sai da ya direta a kujerar dining sannan ya xauna shima,ba yarda ta iya haka ta xauna itama xuciarta na kuna.










Mom ce tayi sarving dinsu, xaljamil kam ta xubawa abincin ido kamar mai san tuna wani abu, jellop rice ne da taji hanta da kifi, daya plate kuma farfeson kazane. Sai juya shinkafar take da spoon, mom da dad sun lura da ko spoon daya bata ci ba, tausayin ta ya kamata, basu basa ganin ta a irin mood din ba, kullum cikin fara'a take bata fushi. Dad ne ya jawo kujerar xaljamil ta dawo kusa dashi, daukarta yyi ya daura a cinyarsa. Dago kai tayi ta kallesa bbu yabo bbu fallasa, dan ynx ta gama believing dad baya santa tunda ya kiyi mata abinda takeso.








Spoon din ya dauka ya fara bata a baki, a hankali take karba mata harta kusa cinyewa, mom na kallon su tana murmushi dan dad na bala'in san xaljamil baya bukatar ganin bacin ranta. Spoon din ta rike tayiwa dad alamar ta koshi ta hanyar girgixa masa kai.ajiye spoon din yyi ya dakko juice a glass cup ya fara bata a hnkl take sha harta gama.








Dad ne ya dauketa ya nufi falo da ita, 3cter ya direta shima ya xauna yana haki alamar ta masa nauyi, tuntsire wa tayi da daria tana kallon dad da yake ta yamutsa fuska. Baki ta tunxiro gaba cike da shagwaba, kai dad yaushe nayi nauyi haka, daria dad yyi ynx habibty bakiga irin abincin da kika ci ba.dad dan kadanne fa, eh na tuna habibty batacin abinci da yawa suka saka daria. Mom na xaune a dining tana kallon su,farinciki ya kamata, tashi tayi ta nufi falon ta xauna a gefen xaljamil suka saka ta a tsakiya suna bata labarai na daria. Tuni xaljamil ta manta abinda ke damunta, ta saki jikinta da iyayenta ta kuma kara tabbatar da kaunarsu agareta , dole ta hakura da kudirinta ta faranta ransu kamar yarda suke faranta mata. Hannu tasa tayi hugging dinsu tana jin kaunarsu na ratsata. Ba karamin dadi mom da dad sukaji ba ganin ta saki ranta,hira sosai sukeyi, mom ce ta duba a gogon dake manne a bangon dakin tym din da ta gani yasata fito da ido waje, omg kunga tym ta fada musu, a tare dad da xaljamil suka duba, 12:58am. Mikewa sukayi a tare suna daria, dad lokaci ya shammace mu hira tayi dadi xaljamil ta fada tana daria, eh lallai kam. Har cikin room dinta suka rakata sannan suka nufi nasu dakin cike da nishadi.










Xaljamil bata kwanta ba sai da ta tabbatar ta gama shirya kayanta a trolley na tafiarta nigeria.








8:55am




Xaljamil ta gama shirinta cikin arabian gown light blue, wacce taji stones, ta rufe gashin kanta da pink veil, light make up tayi ta feshe jikinta da arabian perfume sai tashin kamshi takeyi. Ta nufi pallow, bata tarar da mom a pallon ba dan haka ta nufi dakin. Da sallama ta shiga dakin Mom, Mom na gaban wardrob tana fito da kayanta tana shiryasu a trolley. Mom ce ta dago kai fuskarta dauke da murmushi ta amsa sallamar xaljamil. A nitse ta karasa dakin ta durkusa har kasa ta gaida mom, dafa kanta Mom tayi habibty kin tashi lpy? Lpy lau mom. Mikewa tayi ta nufi wardrob ta fara taya mom fito da kayan, mom ce ta kalleta, habibty ki barshi xanyi ki shirya naki kayan kema dan dad dinki na dawo wa daga company xamu wuce, Daria xaljamil tayi ai tun dare na hada nawa kayan mom.






Ok mom tace suka cigaba da hada kayan,bayan sun gama mom ta shiga wanka xaljamil kuma ta kwashi kayan ta kai pallow ta ajiye. Dakinta ta nufa ta fito da nata kayan ta ajiye ta xauna jiran fitowar mom.




Mom ce ta fito a shirye cikin arabian gown black tayi rolling kanta da black veil fuskarta bbu kwalliya sai powder da ta shafa, a hankali ta tako har inda xaljamil ke xaune ta rufe mata ido, wani ihu xaljamil ta saki dan ta tsorata, kamshin turaren mom taji dan haka ta saki ajiyar xucia, mom ta fada tana murmushi, daria mom tayi ta cika idon xaljamil. Kama hannunta tayi suka nufi dining dan yin breakfast,suna xama wayar mom ta fara ringing, hannu tasa ta dauka, murmushi tayi ganin mai kiran nata dan haka ta daga da sallama. Hello jawad! Mom kin manta dani wallahi ya fada kamar xaiyi kuka, daria mom tayi haba dai ni na isa na manta da my one nd only son, kana raina jawad, nayi missing contact dina shiyasa bama waya, ok mom na gane. Mai martaba ya dameni saina koma nigeria da aikina , munyi waya da ammi naji ance dad ma yau xai dawo ya gama contract din daya juyi, eh wallahi an jima xamu biyo flight na karfe 2.ok Allah ya kawo ku lpy. Tunda suka fara maganar xaljamil ke kallon mom, bata ji hirar da sukayi ba tasan yaran su mom ne amma ita bataji daga larabci sai turanci.taji dai mom tace my one and only son, dama tana da da bayan ni, duk a xucia ta ke maganar. Bye mom bye son sukayi sallama.










Mom ce ta kalli xaljamil data buga tagumi, murmushi mom ta mata, sannan ta fara bata labarin hirar da sukayi da jawad dan tasan bataji ba. Jawad ta maimaita a ranta,suna mai dadi.








Mom wanene jawad xaljamil ta tambaya tana shan xaxxafan tea din data hada. Murmushi mom tayi yareema jawad kikasan jin labarinsa, yea ta gyada kai ok bari mu gama breakfast.














SUMYNBASH CE
๐Ÿ’‹ ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ?๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ


YAREEMAH JAWAD


๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ










A romantic love story
2017








Story & written by




SUMAYYA SALEES SADEEQ











Chapter 5&6














Xaune suke a pallow xaljamil ta xubawa mom ido tana jiran jin labarin yareema jawad. Daria mom tayi xaljamil kin cika san labari amma inasan kafin kisan jawad ki fara da sanin asalinmu gaba daya dan anan ne xaki samu labarin yareema jawad cikakke. Ajiyar xucia xaljamil ta sauke tare da gyara xamanta dan jin labarin. A hankali mom ta fara bata.










Asalinsu








Babbar masarauta ce wacce duk nigeria ba'a taba masarauta irin wannan ba, masarauta ce mai ixxa da kasaita, suna da arxiki wanda su kansu basu san iyakarsa ba, amma sun fi kauri a noma. Suna da gidajen gonaki a wajaje daban daban.






Kakanki alh Abubakar Abdulaziz ya samu sarautar a hannun mahaifinsa, bayan rasuwarsa, mutane da yawa sun yi kokarin a daura su akan karagar mulkin amma yan majalisar sarki da waxiri suka ga bbu wanda ya chanchanta sai kakanki alh Abubakar Abdulaziz da daya tilo ga sarki Abdulaziz, saboda yana da ilimin addini dana boko, kowa yyi amince da nadin waxiri dan haka a ranar da sarki Abdulaziz y rasu a ranar aka nada Abubakar grand fa dinki.











Mai martaba Alhaji Abubakar Abdulaziz yana da mata hajia aminatu wacce ake kira da fulani, ita kadaice matar kakanki yayanta maxa biyu farouq da aliyu sun tashi cikin kulawa a wajen mahaifansu har suka kammala karatunsu wanda sukayi a kasar waje. Dad dinki Aliyu shine babba sai farouqkaninsa, bayan kammala karatunsu mahaifinsu ya bijiro masu da maganar aure, dukkansu a lokacin basu da wata budurwa dan haka suka bawa mai martaba damar xabar musu matan aure. Mai martaba yyi farinciki da xabin da suka bashi dan haka ya kira Alhaji usman akan ya nasan ganinsa. Baiyi kasa a gwiwa ba ya nufi gidan sarki dan amsa kiran amininsa.






Xaljamil ce ta kuma gyara xamanta ta kalli mom fuskarta dauke da murmushi da alama labarin yana matukar birgeta, mom ki cigaba bana san dad ya dawo baki karasa mini ba, daria mom tayi ok bani ruwa a fridge sai mu cigaba. Da sauri xaljamil ta mike ta nufi fridge ta daukowa mom ruwa ta taho da cup ta xuba mata ta mika mata, karba mom tayi ngd xaljamil, aiki nane mom na kula dake ta fada tana murmushi.


Mom na shanye ruwan ta ajiye cup din a gefe,mom wanene Alhaji Usman aminin sarki? Murmushi mom tayi, mahaifi nane. Ok nagane xaljamil ta fada tana jiran mom ta cigaba.




Alhaji Usman ya je kiran da sarki ke masa, bayan sun gama hirar su ta abokai mai martaba ya nemawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login