Showing 39001 words to 42000 words out of 56602 words

Chapter 14 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt

19 Feb 2025

6915

babu walwala, sosai yake jin feelings akan Zaljameel.




"Ya Jawad ci kani in tafi"


Sosai ran Jawad ya b'aci cikin zafin nama ya tura Zaljameel baya, sai da tayi tangal tangal sannan ta fad'a kan 3cter, wani k'ara Zaljameel kwalla dan a tunanin ta a k'asa zata fad'i, jinta a zaune yasa ta sauke ajiyar zuciya.




Nuna ta yayi da yatsa, "Keeeeee waya baki izinin fita a gidan nan ba tare da kin tambaye ni ba? Ko zaman kanki kike yi a gidan?"




Cikin b'acin rai ta mik'e tsaye, Ya Jawad, karka k'ara ce mini keee, you know my name, I'm Zaljameel bana son ka k'ara kirana dake kuma" ta fad'a tana harararsa had'e da murgud'a masa baki.




"Kuma fita basai na ganka ba zan fad'a maka, tayi rau rau da idanu, kamar zatayi kuka, na gaji da zaman nan wallahi,menene banbancina da mai zaman kanta d'in, iyaye na sam basu mini adalci ba, da basu had'a ni aure da wanda nake so ba, na rasa irin zunubin dana aikata da k'addara ta had'ani da kai Ya Jawad, yau zan tafi wajen Mom d'ina kuma karkasa rai zan dawo gidan nan " tana kaiwa nan ta mik'e tana goge kwallar dake fita a idonta ta d'auka handbag d'inta ta yi gaba.






Mutuwar tsaye Jawad yayi, komai na jikinsa yayi nauyi, yana kallon Zaljameel ta fita amma ya kasa tsaida ta. Ja da baya yayi ya zauna a 1 cter ya rik'e kansa daya ji yana sara masa,addu'oi ya fara karanta a ransa a hankali yaji zuciyarsa ta saki,a zuciyarsa ya fara magana




"Mai Zaljameel ke nufi da idan tatafi bazata dawo ba? Hakan na nufin ta barni kenan, No....ya furta da k'arfi, it will never happen Zaljameel, muna tare har mutuwa dan ita kad'ai zata iya rabani dake"




Cikin hanzari ya nufi part d'insa ya fara shiri ko ina zashi oho, a gurguje ya shirya cikin shadda mai tsadar gaske coffee colour, ya saka hula ya d'auka key na moto ya fita. Parking space ya nufa ya d'auka motornsa ya ja da k'arfi.




Tafiya take a nutse ta nufi part d'in Fulani dan yafi mata kusa, bayi nata tsayawa suna bajewa k'asa suna kwasar gaisuwa, Zaljameel kam da fara'a take amsa musu. Sosai ta fara gajiya, ba tayi tunanin akwai tazara mai yawa a tsakanin su ba shiyasa bata d'auka motor ba.




Jin mota tayi a bayanta tayi parking, juyawa tayi ganin waye, "Ya Jawad, mai ya kawo shi nan kuma?" bata k'arasa tunanin ta ba taji an kama hannun ta, cikin zafin nama ta fuzge hannun ta ta hararesa ta cigaba da tafiya, binta yayi da sauri yasha gaban ta, ya kuma kama hannun ta ya langwabar da fuska yana murmushi, har sai da beauty point d'insa suka lotsa.


"My wife Zaljameel" a furta in a romantic voice.


Yarda ya kira sunan Zaljameel ya tafi da ita, cuz Ya Jawad yafi kowa iya fad'ar sunan ta. D'aga idonta tayi ta sauke a fuskarsa, shima ita yake kallo, sai da suka dau mintuna a haka sannan Zaljameel ta d'auke idonta bata iya jurar wannan kallon, hannun ta ta fara k'ok'arin kwata amma Jawad yak'i sakin ta, a hassale ta fara magana!


"Ya Jawad cika mini hannuna let me go please, ko na maka ihu yanzun nan na tara maka mutane".


Dariya Zaljameel ta bama Jawad har sai da white teeth d'insa suka fita," ihu Zaljameel, Oya fara mu gani, banda abinki ai babu wanda zaizo cuz kowa yasan you are my lovely wife, so babu ma wanda zai taho cuz ansan wasa muke "D'aga kai tayi ta kalle shi ya kashe mata ido d'aya.
" Zaljameel muje rana na dukan mu" ya kalli sama.




Itama saman ta kalla,ta tab'e baki, "Ina ruwanka dani, ba rana ba ko ruwa ne ya dake ni mana ya fad'a zata tafi ya jawo ta jikinsa ya rungume, a razane ta fara k'ok'arin ture shi amma amma ta kasa. Kansa ya d'aura a k'afadar ta yana shin shinar k'amshin perfume d'inta dake saukar masa da kasala.




Zaljameel ta gaji da ture Jawad tayi luf a faffad'an kirjinsa, idonta ya cika da kwalla dan kunya, tana ganin bayi ta bayan Jawad da sun biyo hanyar suka gansu rungume da juna sai su chanja hanya, takaici ya ishi Zaljameel, mai ya Jawad ke nufi da itane da zai mata haka a cikin jama'a.




"Please Ya Jawad ka cikani, kana gani mutane na kallon mu"






Sake matse ta Jawad yayi a jikinsa ya sauke ajiyar zuciya, Zaljameel najin yarda bugun zuciyarsa ke k'aruwa.




Cikin wani voice mai wuyar fassaruwa Jawad ya fara magana "Mutane na kallon mu" ya maimaita abinda ta fad'a! Hmm su mutanen ai sun san ba matar wani na runguma ba matata ce, so bana tunanin akwai damuwa anan"




Zaljameel kam al'amarin Jawad mamaki kawai yake bata, ace lokaci d'aya ya chanja, "muje moto Zaljameel in ba haka ba wallahi zan d'auke ki na saki da kaina, kallon sa tayi taga yarda ya zuba mata ido kamar zai cinyeta, a hankali ta lumshe idonta, zuciyarta na bugawa, bud'e idon tayi ta kalli Jawad, cikin sanyin murya ta fara magana" Ya Jawad cikani zan shiga basai ka kaini ni ba, Kallon ta yayi "Zaljameel you promise?" Yes i promise ".


Cikata yayi, yayi crossing hands yana kallon ta, Zaljameel kam tana fakar idon Jawad ta fara gudu tana dariya


" Wooooo Ya Jawad na maka wayo "




Dariya yayi yabi ta shima, taku kad'an ya kamata, d'aga ta yayi chak ya nufi moto da ita, ita kam sai dukan kirjinsa take tana k'ok'arin kwatar kanta amma ta kasa har ya kaita moto ya rufe ta ya zagaya bangaren driver ya zauna.




Kallonta yayi sai hakki take cuz ta dad'e batayi gudu ba sai yau, murmushi ne a fuskarta.




Baice da ita komai ba yaja moto sai part d'in Fulani dan nan yaga ta nufa.




Tun kan su k'araso an sanar da Fulani zuwan su, tasa an shirya musu abin motsa baki.




Jawad da kansa ya bud'e ma Zaljameel ta fita ya kama hannun ta, fuzge hannun tayi tana harararsa "Haba Ya Jawad meye haka wai, naga alama yau so kake kunya ta kashe ni" ta murgud'a masa baki.


"Ok d'aukan ki kikeso nayi ko bari na d'auke ki".




"A'a Ya Jawad ka bari mana"ta fad'a a shagwabe .




Maganar da tayi cikin shagwaba ya matuk'ar tafiya da Jawad, sexy eyes d'insa ya zuba mata ya kama hannun ta suka nufi ciki.






Rik'e da hannun Zaljameel Jawad yayi sallama parlour Fulani.




A kashingid'e take, sanye take da alkyabba ta mata kyau taci necklace and earing da bangles masu tsadar gaske.




Murmushi d'auke a fuskarta ta amsa musu, Zaljameel nata k'ok'arin kwace hannun ta amma Jawad yaki sakin ta, a waje d'aya suka zauna jikinsu na gogar juna.




Kunya ta lullube Zaljameel, Jawad kam ko a jikinsa. Bayan sun gaisa Fulani ta sake musu lecture akan zaman aure, sosai ta ratsa su suka mata sallama,Fulani tace ta kalli Jawad "
To mak'ale mata kaje waje ka jira ta zamuyi magana" sai da shagwabe fuska sannan ya fita badan ransa yaso ba. wata jaka Fulani ta bama Zaljameel ta fad'a mata kayan mata ne da aka kawo mata daga nijar da kula sosai wajen shansu, godia ta mata a fili aranta kam cewa take, "Haba Fulani, wanda nasha ma kafin auren ma ya isheni".




Part d'in Mom suka nufa. Motor Jawad na tsayawa Zaljameel ta bud'e murfin motar ta fita da gudu ko handbag d'inta bata d'auka ba dan zumud'i.




Jawad kam binta yayi da kallo yana kallon yarda take budirinta babu abinda ya dame ta, kai baka ce tana da aure ba.




Girgiza kai yayi ya d'auka handbag d'in ya rufe moto ya shiga ciki.




Da gudu Zaljameel ta shiga, Mom zaune a parlour tana karanta newspaper taji mutum ya fad'o jikin ta, d'aga kai tayi tana murmushi cuz tasan babu mai mata haka sai Zaljameel, Rumgume ta Mom tayi itama tana murnar ganin Zaljameel.




Sallama Jawad yayi da handbag a hannun sa, ganin Zaljameel yayi zaune a cinyar Mom, "Inama ace Zaljameel a cinyar sa take a zaune bata Mom ba"


Zama yayi kusa da Mom ya d'aura kansa a k'afadar ta yana cin magani, ture Zaljameel Mom tayi ta d'aura hannun ta akan Jawad tana shafa sumar kansa. Zunburo baki Zaljameel tayi, tana b'ata rai, "Mom ture ni fa ki kayi a cinyar ki saboda Ya Jawad ko?".




Dariya Mom tayi ta jawo Zaljameel jikinta tana lallashi"Aa Zaljameel ba haka bane, kinsan Jawad shine first born,amma ai kema ina sonki ".




Gwalo Jawad ya mata yana murmushin mugun ta! B'are baki tayi ta fara kukan shagwaba, tashi tayi ta nufi d'akin ta tana buga k'afa.






Zaljameel na shiga room d'inta ta ganshi fes, babu abinda ya chanja yana nan a yarda ta barshi, k'amshi mai dad'i ke tashi. Wardrobe ta bud'e, kayanta suma suna nan, wani tsallen murna tayi! "Yes zama daram kenan a gidan nan"




Kayan jikinta ta cire ta nufi toilet danyin wanka.




Zaman parlour ya gundiresa, hirar da suke da Mom ba bajin dad'in ta yake ba, idonsa nakan d'akin Zaljameel ko zaiga fitowarta amma shiru, Mom ta gama lura da Jawad dan haka ta mik'e ta cewa Jawad tana zuwa.






Dad'i ne yake mashi tana shiga room d'inta shi kuma yabi bayan Zaljameel.




Murd'a handle yayi ya shiga, bai sameta ba sai kayanta daya gani a gefen bed ga kuma saukar ruwa a toilet, hakane ya tabbata masa wanka take yi.




Murmushi yayi" sai kace agwagwa" ya fad'a a hankali.




Zaljameel d'aure da towel a kirjinta tana brush a toilet, bayan ta gama ta d'auka k'aramin towel ta fara goge gashin kanta daya jik'e, fitowa tayi ta nufi mirror, ta jona hand dryer ta fara busar da kanta.




Yareema Jawad yayi suman zaune, ganin Zaljameel a haka, gaba d'aya notin kansa ya kunce, wata irin sha'awar Zaljameel ce ta motsa masa, kyan dirin Zaljameel ya tafi dashi. Bai san sanda ya mik'e ya nufi inda Zaljameel ke tsaye.


Bata san da zamansa a d'akin ba duk a tunaninta ita kad'ai ce.




Hannun sa ya zura ya sak'alo waist d'inta ya juyo da ita ta fad'a jikinsa, a razane ta dage zata saki k'ara da iya k'arfinta Jawad ya had'e bakinsa da nata..... 🙊














SUMYNBASH CE




💋🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮




©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L


(We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers)


A romantic love story
2017


July 2017




Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ




Chapter 60&61






Kissing d'inta yake cike da kwarewa,sun dau wajen 5mint Jawad na kissing d'in lips d'in Zaljameel kamar ya samu sweet, cire bakinta yayi daga nasa amma bai cikata ba, hugging dinta yayi yana sauke ajiyar zuciya, dan ba k'aramin d'aure wa yayi ba ya rabu da Zaljameel.


Zaljameel tayi luf a kirjinsa tana maida numfashi, cuz taji bak'on lamari a tare da ita, tunda take babu wanda ya tab'a kissing d'in ta sai Jawad.


Sake hugging dinta yayi yana ji kamar wani zai raba su. A hankali Zaljameel ke dawowa nutsuwarta, da k'arfinta ta tura shi, kasancewar jikinsa babu kwari yasa yayi baya, ya zuba mata sexy eyes d'insa yana kallon ta cike da sha'awarta.




A hankali y fara takowa ya nufi inda Zaljameel ke tsaye, hannu ta d'aga masa!


"Jawad dakata, karka kuskura ka matso kusa dani," tuf ta tufar da yawon bakinta, "Ka rasa abinda zaka mini sai ka zuba mini wannan bakin naka a cikin nawa. Runtse ido tayi cike da takaicin abinda Jawad ya mata." Jawad karka raina mini hankali, na rasa dalilin chanja warka lokaci d'aya, I know what I'm doing, i'm not a small gal I'm matured, so na riga na gane ka, I hate you Jawad, kamar yarda kaima you hate me, banson k'ara ganin ka, kaje ka auri wacce kake so ka huta da auren Zaljameel har abada".


Jawad kam ya zama kamar an dasa shi a wajen, his brain has already stop thinking anything,banda kallonta babu abinda Jawad keyi.




K'ofa ta kalla," Get out Jawad I don't want to see you ".


Bashi da zab'i daya wuce ya fita a d'akin kafin zuciyarsa ta tarwatse, a hankali yaja k'afa ya fita a d'akin.




Bai tsaya yima Mom sallama ba cuz bazai iya magana ba a halin da yake ciki, bai bi takan motarsa ba ya nufi part d'insa haunkalinsa a tashe, dishi dishi yake gani a idonsa a da kyar yaje guda.


Yana shiga bai tsaya ko ina ba ya nufi bathroom, dan ruwa kawai yake buk'ata, jacuzzi ya nufa ya shiga ciki ya sakar ma kansa ruwa,a hankali ya fara dawowa dai dai da har ya fara tuna maganganun Zaljameel, Runtse ido yana jin zuciyarsa na masa rad'adi, a haka ya gama wankan y fito ya baje a kan bed.




Binsa Zaljameel tayi da kallon tausayi, fad'a wa kan bed d'inta tayi ta fashe da wani kuka mai ban tausayi," I'm sorry Ya Jawad, wallahi I love you, you mean alot to me, but ina son tabbatar da soyayyata a zuciyarka ta cigaba da kuka, sai da tayi mai isarta sannan ta tashi zaune, ko me ta tuna ta mai rubutashi da sauri ta nufi wardrobe,shiryawa tayi cikin wani black material, mai ratsin red, d'inkin riga da siket, veil ta yafa ta fita da sauri.




Itama bata bari Mom tasan da fitarta ta wuce da sauri, gidan ta ta nufa.


A hankali ta shiga parlour dan karsu had'u da Jawad, ganin baya nan yasa ta shige part d'inta tana sand'a, tana waiwaye harda tuntub'e a haka ta shige ciki ta saka key.






Zama tayi a gefen bed d'inta ta buga tagumi, Jawad ya shiga uku, wato girman kanshi da izza sun hanashi magana, tsaki taja ta jawo wayarta ta buga ma Zahra, tana fara ringing tayi picking kamar mai jira.




Zaljameel ta bama Zahra labarin yarda sukayi da Jawad,"Zahra kaina ya kulle, need your advice please ki taimaka mini.


Shiru Zahra tayi tana nazarin mafita, cikin sanyin jiki Zahra ta fara magana!


Zaljameel Jawad ya gama dake, ya kuma ruguza miki duk wani shiri da kike yi, karki manta kince tare kukaje wajen parent d'inku ya kuma nuna miki so a gaban so, Zaljameel a tunanin ki mai zaki ce musu su yarda?.




Gumi ne ya karyo wa Zaljameel, tabbas Jawad ya gama da ita, "Zahra solution nake nema please help me".




"Akwai mafita d'aya Zaljameel, amma tana da had' ari, amma idan kika bi yarda na nuna miki to tabbas zakiyi nasara"


"Insha Allah Zahra komai zai tafi dai dai fad'a mini"
korata Zaljameel tayi banji me Zahra tace mata ba.




A tsorace Zaljameel ta fito da ido waje, "Zahra kina ganin hakan zaiyi kuwa?"


"Kwarai kuwa Zaljameel babu matsala"






Ihun murna Zaljameel tayi ta fara had'a kayan ta a trolley.




Jawad tunda ya kwanta ya kasa motsi, a haka Bala ya same shi, cikin tashin hankali Bala ke tambayar Jawad ko lpy amma bai ce dashi komai ba, ya kawo masa abinci yak'i ci, hankalin Bala kam ya tashi ganin Yareema Jawad a wannan hankali, bai ankara ba yaga hawaye nabin fuskar Jawad. Tagumi Bala ya buga dan yasan duk abinda ke damun Jawad ba karami bane.



After one week


Zaljameel tayi doguwar mik'a tayi addu'ar tashi a bacci ta mik'e zuciyarta fes ta shiga bathroom, wanka tayi ta d'auka doguwar riga ta saka, batayi make up ba sai kyalli da fuskarta keyi, rub ta samu ta shafa a face d'inta nan da nan face d'inta yayi ja idonta ya fara hawaye, itama ta k'ara da nata kukan, hijab ta d'auka ta saka ta d'auka trolley ta fita.




A motar ta ta nufi part Fulani tana rusar kuka.




Tana zuwa kofar gida ta fita batare data rufe motar ba ta shiga tana wani irin kuka.




Fulani da mai martaba zaune

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login