Showing 45001 words to 48000 words out of 56602 words

Chapter 16 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt

19 Feb 2025

6909

horn d'aya yayi gate man ya bud'e k'ofar ta sauri yana washe hak'ora, Jawad ya shiga da motor d'in ciki yayi parking. Da gudu gate man ya k'ara so kusa da Jawad ya zube yana kwasar gaisuwa, babu yabo babu fallasa Jawad ya amsa masa.




K'in fitowa Zaljameel tayi tana ta zare ido kamar shege a rabon gado, lol. Fincikota Jawad yayi ya nufi cikin gidan da ita, sai da ya danna password a jikin k'ofar sannan ta bud'e suka shiga k'ofar ta rufe da kanta.




Tsaye Zaljameel tayi tana k'arema gidan kallo, ya bala'in burgeta, yanayin ganin irin na turawa ne, ta shagala da kallon parlour taji an watso mata papers a jikinta, firgit tayi ta kalli k'asa inda suka zube ta kuma kalli Jawad dake zaune a 2cter ya yayi crossing leg yana ma Zaljameel wani irin kallo na kin shiga uku.






Gaba d'aya ya koma Yareema Jawad d'insa na asali, ya manta fara'a ballantana smiling, hankalin Zaljameel fa ya tashi, cike da izza Jawad ya fara magana.


"Keeeeee d'auka papers d'in nan kizo nan" ya nuna mata k'asa inda k'afarsa take.




"Kasan ta kalla ta kuma kalli Jawad, ganin babu alamun wasa a tare dashi, gasu a wani gida da bata son ta ina zata fita ba ballantana ta gudu yasa ta durk'usa ta d'eba ta nufi inda ya nuna mata sai dai ta kasa zama a k'asan kamar yarda ya umarce ta, dan Zaljameel itama akwai izza,hakan yasa take ganin bazata iya zama a k'asan k'afarsa ba.




Ganin bata da niyar zama yasa ya tashi tsaye yana zuba hannu a pocket yana kallon Zaljameel.




Wata iska ya fitar a bakinsa mai bayyanar da takaicin dake zuciyarsa ya fara magana "Zaljameel? Kinyi k'ok'ari sosai a abinda kika aikata, kuma na gane abinda kike nema, tun farko da kin fad'a mini da baki bamu wahala ba"


tsayawa tayi tana kallon sa dan bata gane inda ya dosa ba.


" Zan baki abinda kike nema Zaljameel, ciki kike buk'ata na miki ko, to zan miki kuma ke da gida sai kin samu cikin gaske Zaljameel" yayi wani killer smile ya kashe mata ido d'aya.




Cikin rawar murya Zaljameel ta fara magana "Ya... Ja.. wa.. d! Please karka mini haka, wallahi ni ba haka nake nufi ba, dan Allah kayi hakuri, wallahi na tuba, please ka maidani gida, wallahi zan janye abinda ya fad'a ma iyayen mu " ta fashe da kuka. Dana sanin abinda ta aikata, itakam Zahra ta cuceta data bata wannan shawarar, gashi bata taho da phone ba ballantana ta buga mata waya ta bata wani advice d'in. Upstairs Jawad ya shige ya bar Zaljameel na kuka.










SUMYNBASH CE 💋




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮




©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS


P.M.L


(We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers)




A romantic love story
2017


July 2017




Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ






Chapter 66&67








Jin takunsa tayi yana sakko wa, a hankali ta d'aga fuskarta da tayi ja saboda kuka tana kallonsa, kyau sosai ya mata, sanye yake da pink shirt and blue jeans ne a jikinsa ya d'aura p cap, fuskarsa d'auke da sunglass,sai tashin k'amshi yake.
ta shagala da kallonsa sai jin muryarsa tayi a kusa da ita, firgit tayi ta kalle sa, tsugunna wa yayi dab da ita yana kallon cikin idonta, itama zuba masa nata idon tayi,wani yarrr taji a jikinta, dan yau kallon na Ya Jawad na musamman ne, janye idonta tayi ta kalli gefe tana hawaye, duk da zuciyarsa bata masa dad'i ba ganin Zaljameel a ya nayi na tashin hankali, amma bai bari ta gane hakan ba ya fara magana "As you know Zaljameel yau ke amarya ce, ina son kisa ranki cewa yau aka kawo ki gidan Jawad, so kukan ya isa haka zan fita na siya abinda ake kaima amarya a daren farkon ta". Yayi wani murmushi ganin kukan Zaljameel ya k'aru, "Zaljameel!" Ya kirata, bata iya amsawa ba dan maganar da Jawad ya fad'a mata ta bala'in d'aga mata hankali, kallonsa tayi idonta na zubar da hawaye,"Ki tashi ki hau upstairs akwai room na farko ki shiga zaki samu duk abinda kike buk'ata a ciki, kinsan ya kamata ki shirya kanki kafin Angon ki Jawad yazo" yana gama fad'in haka ya mik'e da sauri y nufi hanyar fita, binsa tayi da kallo har ya fice.




Tashi tayi ta fara zagaye gidan, tana kallon kyau da tsari da yayi, upstairs ta nufa nan ma duniya ce, an zuba kayan decorating kamar ba kud'e ne yayi aiki ba, room d'in daya fad'a mata ta shiga, shima a tsare yake, ganin wardrobe ta nufa ta bud'e, ganin kaya an mace a ciki ya firgita Zaljameel, gaba d'aya English wears ne a ciki, tana son dubawa amma kyankyami ya hanata tab'a su, a zuciyarta ta fara magana, dama Ya Jawad dan iska ne, har room ya ware saboda mata, shine zai fake mata da abinda tayi itama ya raina mata hankali, wai tana buk'atar ciki? Eh lallai zaiga ciki Amma a jikinsa. Tsaki taja ta rufe wardrobe, zuciyarta taji tana harbawa da k'arfi, duk wani tsoro ya fita a ranta, murmushi tayi, "Ha Ya Jawad bazaka tab'a cin nasara akaina ba, ba kuma zaka tab'a samun kwanciya da ni ba ta dole, har sai ka firta da kanka kana buk'atar kuma kana d'auke tsantsar sona a zuciyarka.




Wardrobe d'in Zaljameel ta kuma nufa zatayi shahadar tab'a kayan, white top ta d'auka tana dubawa, daga ni ba'a tab'a saka ta ba hakan yasa hankalin Zaljameel ya kwanta ta kuma duba wani mini skirt ta d'auka shima sabone hakan yasa ta ajiyesu gefen bed ta rufe wardrobe d'in tunda ta samu na sawa.






Mirror ta nufa taga cream and lotion masu kyau da tsada, ga perfumes kala kala, harda powder da lipstick, ga eyeliner, abin ya d'aure mata kai, lallai a gaida Ya Jawad, yayi k'ok'ari wajen ajiyewa yan matansa abinda suke buk'ata.




Bakin ciki taji ya tsaya mata a rai, a hassale ta nufi bathroom danyin wanka.




Fes ta fito d'aure da towel a kirjinta, gashin kanta na d'igar da ruwa ta nufi mirror, bayan ta gama tayi make up sosai harda Eye Shadow, white top ta saka wanda bata da baya kuma ta gaba cibiyar ta a waje take, yellow mini skirt ta saka shima bai rufe mata cinya ba, ta gyara gashin kanta yayi baya ta fesa perfumes a duk wata gab'a ta jikinta ta fita parlour ta zauna jiran Jawad.




Kitchen ta l'eka taga fridge, bud'e wa tayi taga chocolate ice cream, cikin zumud'i Zaljameel ta d'auka ta nufi parlour ta zauna tayi crossing leg tana kallon film tana shan ice cream d'inta hankali kwance.




Tun tana jiran dawowar Jawad har ta gaji ta shanye ice cream d'in ga wani bacci ta take ji, bata son lokacin da bacci b'arawo ya sace ba.






Jawad bai dawo gida yana part d'in Areef suna tattauna akan maganar, Jawad ya sanar ma da Areef Zaljameel na gidan sa, Areef ya tsorata da abinda yayi, amma d'aya fad'a masa dalilinsa nayin hakan Areef ya bashi goyon baya 100 percent,a haka sukayi sallama ya fice dan dama bai shigo da motor ba.








Fulani taji shirun Zaljameel yayi yawa, hakan yasa ta tura kuyangu su duba mata ita, sun dawowa da Fulani da labarin da yasa zuciyarta ta kusa tsaya wa, part d'in Mom ta aika a duba mata Zaljameel, Mom kam tace rabonta da Zaljameel ai ta dad'e, nan da nan labari ya karad'e masarauta akan rashin ganin Gimbiya Zaljameel, hankalin kowa ya tashi harda grandfa dan labari yaje garesa, gate akaje aka tambayi masu gadi ko sunga fitar Zaljameel suka ce a'a, duk wani sak'o da luko a gidan nan an duba babu Zaljameel babu alamun ta,Fulani kuka take sosai, ina Zaljameel ta shiga ita kam ta shiga uku, a haka a kayi report a duk wata station dake garin.




Mom ma abin ya d'aure mata, a lokacin ta d'aura fitar Zaljameel daga gidan sanadiyar kin goya mata baya da tayi, tayi watsi da ita gaba d'aya.




Dana sani mara amfani Mom keyi, itama taci kuka kamar ranta zai fita.




10:2pm




Jawad ya danna password ya shiga gidan, ganin Zaljameel kwance tayi dai dai a kujera tana bacci, skirt d'in da tasa ha dan dag'e har white pant d'inta Jawad ya gano, binta yayi da kallo mai cike da so da k'aunar Zaljameel, ga kuma sh'awarta data masa katutu, sai dai bazai tab'a kusantar Zaljameel ba tare da yarda ta ba, yayi alkawarin hakan, dama duk abinda ya fad'a mata barazana ce.






Step ya k'ara yaje dab da Zaljameel ya tsugunna yana k'arema beautiful face d'inta kallo, "make up d'in da tayi ya bala'in birgeshi,gashin kanta daya rufe mata fuska ya mayar gefe da hannunsa, baison lokacin daya bata peck a pink lips d'inta ba, ganin zata motsa yasa Jawad ja baya, ganin ta cigaba da bacci yasa, d'aukar ta yayi chak ya nufi upstairs da ita idonsa akan kirjinta daya cicciko kamar an hura balloon, wani sanyayyar ajiyar zuciya Jawad yayi ya shiga room d'in daya ware saboda Zaljameel. Kwantar da ita yayi a bed ya saka mata pillow, blanket yaja ya rufeta ya rage gudun Ac, parlour ya sauka ya d'auka ledar daya zo dasu ya nufi room d'in Zaljameel, baccinta take ba tare da damuwa ko kad'an ba a tare da ita, murmushi Jawad yayi ya ajiye ledojin ya d'auka memo yayi note ya ajiye a gefen ledar, "Idan kin tashi kici abinci, dan bana son ki wahala nafi so ki k'oshi tukunna kafin komai ya gudana a tsakanin mu ki samu abinda kike so" yana kaiwa nan ya fice a room d'in ya tafi nashi.






Room ne daya amsa sunan sa na Yareema Jawad, ya tsaru sosai ya kuma ji manya manya frames masu d'auke da pictures kala kala, pic d'in dana gani shi ya tsorata ni, pictures d'in Zaljameel ne manne tun tana k'arama har girman ta, duk ya cika dakin dasu, sai ma mai martaba da fulani, sai nashi wanda kana shiga yana kallo ka, akan doki yake yaci alkyabba da rawani yayi murmushi a pic d'in, sai da y gama bin pictures d'in da kallo fuskarsa d'auke da murmushi, ya shafa gefen fuskarsa ya furta, "I LOVE YOU MY NISFUL HAYAT"




Bathroom ya nufa yayi wanka ya chanja kaya ya d'auka key sai da ya lek'a Zaljameel sannan ya fita ya nufi gidan sarki.








SUMYNBASH CE💋




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮




©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L


(We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers)




A romantic love story
2017


August 2017






Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ




Chapter 68&69






Gidan sarki Jawad ya nufa, hankalin sa kwance, tun a gate ya lura da yanayin masu gadin gidan yasan babu lpy, tsayawa yayi suka gaida shi, a dak'ile ya amsa ya tambaye me ke faruwa, d'aya daga cikin su ya bama Jawad labarin b'atan Zaljameel, baice dasu komai ba yaja motarsa da k'arfi ya k'ure speed ya nufi part d'in Fulani. Cikin tashin hankali Jawad ya shiga parlour yana kiran Fulani, Ammi nah! Ammi nah!, zumbur Fulani tayi ta mik'e daga zaunen da take tana kuka ta nufi inda taji muryar Jawad, har tuntub'e tayi ta fito.




Tsaye ta tarar da Jawad ya rik'e kansa yana hawaye, sororo tayi tana kallonsa dan ita ta gama believing Zaljameel na tare da Jawad, to mai yasa taga yana kuka.




Inda take tsaye Jawad ya nufa ya rumgume Fulani ya fashe da kuka, "Fulani wai Zaljameel ta b'ata, wannan wane irin tashin hankali ne yazo mana da rana tsaka, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ya Allah ka bayyana mini Zaljameel" ya kuma fashewa da kuka.




Duk da haushin da Fulani keji na Jawad sai da ya bata tausayi, amma ta dake, a zafafe ta ture shi a jikinta, tana nuna sa da yatsa, "Kul Jawad, karka kuskura ka k'ara zuwa kusa dani, bana son ganin ka Jawad, har kana da bakin kuka saboda rashin ganin Zaljameel, gaskia Jawad rashin kunyar taka takai, duk abinda ya samu Zaljameel da hannun ka a ciki Jawad, wallahi indai kaga na sakar maka to Zaljameel ta dawo gare ni da dan dake cikin ta, tun wuri Jawad, tun raina bai b'aci ba ka dawo da Zaljameel, nasan kai ka d'auke ta.




A razane Jawad ya d'ago ya kalli Fulani, sosai kirjinsa ya buga dan yayi tunanin asirin sa ya tuno, amma ya basar.




"What?! Fulani what are you saying, kina nufin nasan inda Zaljameel take? Ba haka bane Fulani, nasan nayi kuskure na korar Zaljameel da nayi wallahi Fulani ina son Zaljameel ina kuma son abinda ke cikin ta dama sharrin shed'an ne, amma bani da sa hannu a b'atan ta "Jawad ya durkusa ya cigaba da kuka.




Binsa Fulani tayi da kallo, Jawad na kuka, abinda ta dade bata gani ba kenan, a kalaman sa ta tabbatar da gaskiar sa, to ina Zaljameel ta shiga, shine tambayar data damu Fulani,ja da baya tayi ta zauna a karagarta jin kanta na juyawa. Jawad ta kalla, "Jawad! Kamar yarda na fad'a maka baka fa sauran sakewa a gidan nan in har Zaljameel bata dawo ba, na d'aura maka alhakin neman Zaljameel duk inda ta shiga a duniyar nan" tana gama fad'in haka ta mik'e tabar Jawad a durk'ushe, mik'ewa yayi ya fita, direct part d'insa ya nufa zuciyarsa fal farin ciki, Allah ya taimake shi shima zai bar gidan, dan dama yana ta tunanin yarda zai dinga zirga zirga daga gidan sarki zuwa gidansa inda ya ajiye Zaljameel, room d'insa ya shiga ya kira Bala akan ya had'a masa abinda yake buk'ata.




Mamaki bayyane a fuskar Bala, ganin yarda Yareema Jawad ya nuna halin ko in kula da b'atan Zaljameel, sanin halin Jawad bayason shishigi a lamarinsa yasa Bala ya kama bakinsa, ya had'ama Jawad kayansa ya fita kawo masa dinner.




Washe gari






Ana idar da sallar asuba Jawad ya bar gidan. Gidan sa ya nufa ransa fes zaiga Zaljameel.








Horn yayi gate man ya bud'e masa, parking motar yayi ya shiga ciki,sai fara'a yake.






Tunda Jawad yabar gidan Zaljameel bata tashi ba, baccin ta kawai take cikin kwanciyar hankali.




Jawad na shiga upstairs ya haye, ya nufi room d'in Zaljameel, yarda ya barta haka ya same ta,sai dai ta yaye blanket d'in, tayi d'ai d'ai tana bacci, gashin kanta ya rufe mata fuska. Murmushi Jawad yayi ya nufi bed idonsa na kanta, duba ledar daya kawo mata yayi, komai na nan,hakan ne ya tabbatar masa da Zaljameel bata farka ba, juye juye Zaljameel ta fara alamun zata tashi a bacci, hakan yasa Jawad ya fita a room d'in da sauri, yana fita Zaljameel na bud'e ido, gani tayi gari ya waye hakan yasa tayi du'a ta mike ta shige toilet.




Wanka tayo ta fito tayi sallah ta nufi mirror tayi shafa da light make up ta nufi wardrobe, sai a time d'in ta lura da kayan gaba d'aya new ne, hankakinta ne ya kwanta hakan yasa ta kuma duba kayan ta d'auka wata red gown mai k'aramin hannu iya gwiwa, ta gyara kanta, zama tayi a sofa ta buga tagumi dan ta fara jin yunwa, idonta ne ya sauka a kan ledojin da Jawad ya ajiye ga kuma paper kamar an bar Note, tashi tayi ta nufi wajen, letter d'in ta fara karantawa sannan ta fara bud'e kayan, gas chicken ne guda biyu, sai yoghot guda biyu shima,d'ayan kuma kayan chocolate ne da sweet,murmushi Zaljameel tayi, "Ha Ya Jawad kenan, ana so ana kaiwa kasuwa". Sai a time d'in ta tuna bacci ya d'auke ta ne a parlour, to waya kawota kan bed, "Ya Jawad" ta fad'a tana murmushi, tashi tayi ta nufi kasa ko zata ga kitchen, ta dan gasa chicken d'in a macro wave.






Jawad zaune a parlour yana watching film a mbc bollywood , Bajrangi baijaan, film d'in ya masa kyau ya bada duk wani attention nashi, hannun sa d'auke da hot coffee yana sha.




Jin k'amshin turaren Zaljameel yasa Jawad juyawa da sauri, itakam bata lura dashi ba ta fara neman kitchen, ganin ledar dake hannun ta yasa Jawad gane inda take nema, murmushi yayi ya mik'e ya nufi inda Zaljameel ta nufa cuz ba hanya bane. Tafia take tayi tana zare ido, cuz ta fara ganin kamar tabi wrong way dan ta rasa kitchen, wani door Zaljameel ta bud'e tana lekawa taga duhu, gashi tana ganin alamar mutun a ciki, gani tayi kamar mutun d'in ya nifo ta, ai da sauri daja door d'in ta kwalla k'ara ta fara neman hanyar gudu,gudu take sosai tana kuka tana kiran Jawad "Ya Jawad! Ya Jawad! Please need ur help. Ji tayi tayi karo da mutun wata razanar niyar kara Zaljameel ta kwala ta fara k'ok'arin kwace kanta, hugging d'inta Jawad yayi yana shafa bayan ta" Relax Zaljameel its me Jawad ".


Jin muryar Jawad yasa Zaljameel ta kara shigewa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Shafa bayan ta Jawad ya cigaba dayi, ji tayi wani yarr a jikinta haka shima, fara kokarin kwace kanta tayi amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login