Showing 15001 words to 18000 words out of 56602 words

Chapter 6 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt

19 Feb 2025

6905

dinsa yyi cikin da sauri. Office ya nufa ya ajiye laptop bag ya d'auki lab court ya saka, yana fita da sauri suka ci karo da peter, tsorata yyi da ganin yareema jawad a hospital kuma a shirye, kallonsa yareema jawad yyi "ina patient d'in?" jawad ya katsewa peter tunani. Duk wani singing da xa'ayi an gama dan haka yana shiga hand clove yasa a hannunsa ya fara operation d'in, bai d'au wani long time ba yayi nasarar cire baby girl a cikin matar.










"Yana fita ya tarar da mijin matar tsaye a kofar theater room d'in, da sauri yabi bayan yareema jawad yana tamayarsa a wane hali matarsa ke ciki,labari ya bashi matarsa ta haihu kuma baby girl, yyi gaba, ya bar mutun da rawa. Office dinsa ya nufa ya huta kafin yaje wajen director ya sanar masa tafiarsa Nigeria.










"Da kyar director ya yarda da tafiar jawad, dan yace ya sanar dasu ko salary d'in da suke basa ne yyi kad'an ya sanar dasu ko nawa yakeso xasu bashi, a hankali ya warware musu abinda ke faruwa, shima ba asan ransa bane tafiar. Sunyi ciwon rai dan samun doctor kamar jawad abu ne mai wuya.








"Bbu matsala doctor jawad amma ko ya koma yyi kokari ya dinga xuwa, ya amince da hakan ya kuma ji dadin yarda suka nuna masa kauna,










"Xaune yake a office d'in sa yana duba wani file, wayarsa ce tayi ringing, mai martaba ya gani dan haka da ladabi ya daga, sun gaisa nan yake masa tuni cewa yau Friday gobe ne ranar daya kamata ka dawo, "eh mai martaba insha Allah goben xan taho" to shi kenan Allah ya maka albarka "ameen yareema jawad ya amsa.










" A ranar Friday karfe 8:00pm aka hada dinner saboda tafiar yareema jawad, suna so su karramashi, duk doctors d'in hospital d'in sun hallara a wani babban waje da ake ji dashi a London, yareema jawad yyi farin ciki da hakan.










"Karfe 8:00pm yareema jawad ya bayyana a wajen, yyi masifar kyau, suit ce a jikinsa black, sai red longslip, black necktie ya saka, fuskarsa dauke da farin glass wanda ya karawa shigar sa kyau,wani daddad'an k'amshi ke tashi a jikinsa. Da takunsa na k'asaita ya karasa kan high table da aka tanadar masa, nan waje ya kaure sa tafi, raf-raf-raf, cikin farin ciki ya daga kai yana karewa mutanen dasukazo wajen, waxai gani, Zahra zahradden ya maimaita a xuciarsa. Sanye take da wani mini skirt orange,sai karamar riga mara hannu, ta saki gashin kanta a gadon bayanta, xaune take a cinyar wani bature sai wani shafa fuskarsa take tana wani narkewa a jikinsa, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shine abinda ya nana ta a xuciarsa. A hankali yaji kuncin da yakeji ya bar xuciarsa. Neman yareema jawad akai akan yyi jawabin godia da kuma sallama ga friends dinsa,tashi yyi ya karbi loudspeaker ya fara bayani, dum Zahra taji xuciarta ta buga jin murya yareema jawad, a hankali ta juyo da kanta tana kallon mai magana, shi ne ta fada a ranta, gaba daya ta tsure, Dan tabbas tasan ya ganta, tashi take kokarin yi daga cinyar baturen amma yaki barinta, haushi ne ya kamata ta fara kunkuni, "ynx Idan yareema jawad bai ganni ba wannan sai ya tuna mini asiri" duk abinda take jawad na kallonta yana murmushin mugunta. Da kyar ta samu ya cikata bayan ta masa rad'a a kunne akan tana da uxuri ne, tana tashi ta nufi high table Inda yareema jawad ke bayani, tana wani kwarkwasa da karairaya. Tunda ta tunkaro shi ya xuba mata ido yana kallonta cike da kyama, sai yatsina fuska yakeyi. Gaba daya Zahra tasha jinin jikinta da kallon da jawad ke mata, duba jikinta ta fara yi ko a kwai matsalar daya hango,a haka ta daure ta karasa kusa dashi, bude baki tayi xatayi magana yareema jawad ya tushe hanci yana kakarin amai, security ya fara kira yana nuna Zahra da hannunsa hancinsa da bakinsa a tushe, da sauri kam suka bayyana a wajen suka d'auki Zahra chak suka nufi waje da ita. Baturen da sukaxo yana gani ya basar dan a tunainsa ganin jawad yasa ta rabu dashi, ga kuma irin wulakancin daya mata dan haka ya nuna kamar bai Santa ba.wani murmushi yareema jawad yyi bayan mutanen wajen sun kewaye shi suna masa sannu.












SUMYNBASH CE💋




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮














®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS




P. M. L. W














A romantic love story
2017














Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ












Chapter 23&24














"A hankali yake amsa musu bayan ya gama kakarin nasa, d'aya bayan d'aya suka dinga tashi suna masa sannu. Xuciar yareema jawad fal farinciki dan yasan yyi wa Zahra abinda har ta mutu baxata manta dashi ba.










"Zahra security na fita da ita suka direta a gate d'in wajen suka yanka mata warning akan kar suga ta dawo cikin wajen,durkusa wa tayi a wajen ta fashe da wani kukan bakin ciki," lallai yau ta tabbatar yareema jawad baya santa, amma duk da haka baxata rabu dashi ba sai ta mallaki zuciarsa" Xama tayi a wajen tana jiran fitowar yareema jawad, dan tanaso suyi sallama dan taji yace gobe xai wuce a bayaninsa, Allah sarki Zahra.












"Sai 11:35pm aka tashi a dinner party d'in, bayan an bawa yareema jawad award da kyaututuka aka fara watsewa. Cikin tafiarsa ta k'asaita yake takawa shida Peter suna tafe suna hira, Peter yana bayyana jimaminsa na tafiar jawad, a hankali ya karasa jikin motarsa, kokarin budewa yake yaji an kama kafarsa, wani tsalle yareema jawad yyi yana kallon k'asa wani tsaki yaja na bacin rai ganin Zahra zahradden ce, tabbas banda shi d'in namiji ne to da bbu abinda xai hanasa ihu a wanna lokacin.












"Kuka take shabe shabe still hannunta a kafarsa, "please jawad ka taimakeni ka yarda da soyayya ta, ynx abinda ka mini daxu ka kyauta?? Ka tuxartani a cikin mutane, mai nayi maka?" ta cigaba da kuka. Wayyo yareema jawad jiyay kamar yasa k'afa ya hambare ta, wani k'ululun bakin ciki ne ya tukare masa xucia, wannan kalmar ta ina sanka data fita a bakin Zahra ta tafarfasa shi.






" Kallon ta yyi da sexy eyes d'in sa wanda sun koma ja dan tsabar bacin rai,wata iska mai xafi ya fitar daga bakinsa cikin husky voice ya fara magana "to hell with you Zahra, wallahi na tsane ki na tsani halinki, baxan taba soyayya dake ba dan bakya cikin type d'in matan da nake bukata nayi rayuwar aure da su ba, ba mu dace da juna ba, ina miki nasiha ki rabu dani tun muna mu biyu"








"Mik'ewa tsaye tayi ta kama k'ugu cik'e da fitsara ta kalli yareema jawad, "wallahi sai ka aure ni kuma sai ka so ni, ban taba neman abu na rasa ba, kuma baxan fara a kanka ba, ina sanka ya xama dole kaima ka so ni, kuma nima nigeria d'in xan taho, muyi ta achan mu k'are,I ayi auren mu mu xauna a chan ko jawad" ta masa dab dashi tana masa wani kallo.








"Mamaki ko al'ajabi xaiyi a maganar Zahra, tabbas yana ganin brain d'in yarinyar ya fara samun problem, bai tanka mata ba dan bashi da lokacin ta. Peter na tsaye a wajen kamar an dasa shi yana kallon yarda xa'ayi so dole, yasan wahalar da kanta kawai take dan yareema jawad ba sauraran ta xaiyi ba, ya sha gayyatarsa club dan su shana da yan mata amma yareema jawad yaki bashi dama, Peter har ya fara xargin ko yareema bashi da lapia ne?.












"Bude motarsa yyi ya shige, da sauri Zahra ta matso ta kuma fashewa da kuka, Dan Allah karka tafi, inasan ka sanar dani kana sona please, cikin xafin nama yaja motarsa ya bar wajen dan ko sallama baiyiwa Peter ba.








"Zahra kam durkushewa tayi a wajen ta cigaba da kukanta, Peter ma motarsa ya nufa y bar wajen.










"Sai da tayi mai isarta sannan ta Mike ta shiga nata motar ta bar wajen.






"Hawayen bakin ciki yareema jawad ke xubar wa, Zahra taci masa mutunci da baxai barta ba, "sai ya wulakanta ta, duk dunia ta rasa wanda ya mata sai shi"tsaki yaja ya daki steering motar da hannu biyu yana jin zuciarsa na kunci da d'aci. Yana isa gida ya fara hada kayansa a daren da sassafe ya nufi airport sai nigeria, Dan yana ganin xai samu sassauci a chan.












"Tsaki yaja dan ransa yaji yakuma baci lokacin daya dawo daga duniar tunaninsa, da kyar bacci barawo ya sace yareema jawad a wannan daren.












"Kiran sallar asuba ne ya tashi yareema jawad, wanda xai iya cewa a d'akinsa aka saka speaker d'in dan k'arar da yaji, a hankali ya bude ido yayi addua sannan ya shiga toilet, kamar yarda ya saba sai da yyi wanka sannan yyi alwala ya fito, a gurguje ya xira jallabiya dan yaji masjid suna neman su tada sallah, yana fita ya tarar da bala na jiran fitowarsa, durkusa bala yyi yana gaida yareema jawad, lpy yace ya d'auki hanyar fita bala na binsa a baya. Suna xuwa ana tayarwa dan haka suka shiga sahu. Bayan an idar ya fita daga masjid ya tarar d sarki mai murabus (grand fa) d'in sa a kofar masjid d'in. Charaf yyi ya rike hannun yareema jawad yana murmushi," xonan d'an nema, muje ka duba mini jikata"yareema jawad ne ya harare sa," kai dai tsohon nan rikicin tsofan ka ya isheni, naga alama ma akaina yake k'arewa, to baxani ba cika mini hannuna ".












" Sarki abubakar chanja rik'on da yyi wa yareema jawad yyi daga sakwasakwa xuwa da karfi, tuni xafin rik'on ya xagaye ilahirin jikin jawad, wata k'ara ya saki da bai masan yyi ba dan axaba, hhhhh yaji hannun maxan jiya. Da kyar yareema jawad ya tattaro jarumtarsa ya kalli grandfa ya wani b'ata rai kamar gaske , "kai tsohon nan bari mana, so kake ka karyani?" daria sarki abubakar yyi "ai Idan kaga na sakeka munje ka duba mini jikata" to xani"yareema jawad ya fad'a yana wani bata rai. Daria sarki abubakar yyi ya kalli jawad "akace bakaji" banxa yareema jawad ya masa suka d'auki hanyar gidan farouq a lokacin gari ya waye.










"Bala ne yyi knocking, farouq ne ya bud'e dan bai dad'e da shigowa gidan ba shima, ganin mahaifinsa yasa ya durkusa k'asa ya dunkule hannu yana gaida sarki, murmushi sarki abubakar yyi "tashi farouq" tashi yyi ya basu hanya suka shiga. A parlour suka xauna bala na tsaye a gefe, xamewa yareema jawad yyi daga kujerar ya gaida yayan mahaifinsa, cikin sakin fuska farouq ya amsa masa cike da kulawa.












"Momy xaune a bedroom ta jiyo muryar mai martaba, dan haka ta sako hijab d'in ta dan kwasar gaisuwa, bayan ta gaida shi sarki abubakar y kuma sa musu albarka. Nan ya tambayi jikin xaljamil sukace da sauki. Sarki abubakar ne y kalli jawad da yake ta cika yana batsewa"wannan ja'iriin yaron na sako a gaba ya duba mini jikata"daria sukai gaba daya banda jawad daya makawa grandfa harrara.








"Farouq ne ya kalli mom"ta tashi ne? "eh ta tashi ita da nawal" ok jawad ka fara shiga kafin mai martaba ya tashi shima y shigo. Tashi jawad yyi ya kuma makawa mai martaba harrara gaba daya suka sa daria, "xan kamaka ne jawad a hannuna xaka maimaita" daria yyi ya shige ciki.












"Xaune take a kan prayer mat, hannunta d'auke da alqur'ani mai girma tana karatun ta a bayyane, suratu yusuf take karantawa, murda handle d'in yyi yaji ana karatu, baiyi tunanin kunnensa gaskia ya fada masa ba sai da ya bude kofar dakin ya shiga, chak y tsaya ganin ta sanye cikin pink hijab mai hannu, daddad'an muryar ta da yarda take fitar da harufan had'e da tajweed ya birgeshi, ji yyi inama su dawwama yana jin wannan daddad'an karatun nata mai sanya nutsuwa, ji tayi kamar ana kallonta dan haka ta daga ido ta kalli kofa, idonsu sune ya had'e wani irin shock yaji aa jikinsa ganin idon xaljamil, ita kuma da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa, dan wani nauyi da kunyarsa take ji ganin daya mata suna pillow fight d nawal alhali tace cikin ta ciwo.










"Yareema jawad ya lura da yanayinta na kunyar da takeji dan haka dan ya kara bata wata kunyar ya xuba mata ido yana kallonta, a hankali taji voice d'in sa ya daki kunnenta, "mai ciwon ciki y jiki? Fatan ya daina ciwon?" wayyo xaljamil ji tayi kamar k'asa ta tsage t shige ciki don kunya, ita kam duk rashin kunyarta ai baxata ansa masa ba. Nawal ce t fito daga toilet, da gudu ta nufi jawad, hannayensa ya bude ya dagata sama, kamar wata baby,kiss ya mata a baki had'e da shafa gashin kanta, "I missed u soo much uncle jawad" missed u 2 baby nawal. Hugging d'in sa ta kara yi,xaljamil na kallon su sai taji sun birgeta inama gaba daya yan gidan kamarsu daya da wadan nan kyawawan da taji dadi , sosai ta shagala da kallonsu tana murmushi har beauty point dinta ya lutsa, yareema jawad na kallonta dan shima nashi hankalin na kanta.












"Xaljamil ji tayi an turo kofar dakin da muryar da taji ance grandfa din ta ne, da idonta ta rufe ruf tayi k'asa da kanta, gaba d'aya jikinta ya d'auki bari kamar maxari, kallonta yareema jawad keyi da mamaki da kuma San sanin damuwar xaljamil, "Wato jawad a wajen nawal ka shiririce baka duba mini jikata ba, da turanci grandfa ke magana dan an fada masa xaljamil bata jin hausa, jin tturancin tayi wani iri dan haka batasan lokacin d ata bude idonta ba tana San ganin tsohon, duk da ta gane mai yake nufi amma turancin nasa na yan da ne. Idonta tar akan tsohon, kamar su daya da dadyn ta farouq, shima fari ne amma dad ya fishi fari tana tunanin tsofane da ranar nigeria ta maida shi haka,duk abinda take yareema jawad na kallonta,mamaki duk ya ishesa, ji tayi soyayyar grandfa ta shiga ranta ganin yarda ya damu da ita, tausayinsa ne ya kamata yarda ta dinga pretending bata da lapia duk hankalin sa ya tashi, tabbas da tasan haka yake da bata wahalar dashi ba.












"Sarki abubakar ne ya kalleta, ganin tana daria, murmushin jin dadi yyi yana kallonta, kamarsu daya da farouq sai dai ta debo momy ta wani wajen, "masha Allah jiki yyi sauki xaljamil" murmushi tayi ta daga kanta alamar yea, hannunsa ya bude alamar taje ya rungumeta, a nitse ta tashi ta ajiye alqur'anin hannunta ta nufi grandfa, tana murmushi, Hugging d'inta yyi sai ga hawaye a fuskar sarki mai murabus. Nawal da jawad na tsaye suna kallon su, mom da dad suka shigo d'akin suma, sukaga xaljamil rungume a jikin sarki abubakar, dad'i ne ya kamasu suma mom harda hawaye.












"Allahu akbar ashe xan ji dumin jikata a jikina kafin na bar dunia, Allah ya raya ki xaljamil ya baki miji na gari " ameen suka amsa harda nawal.
















SUMYNBASH CE 💋


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮










Pure moment of life writers


p. m. l. w












A romantic love story
2017






July 2017










Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ




Alhamdulillah I'm back, fatan munyi axumi lpy, ina wa dukkan musulmai barka da sallah, fatan anyi lpy, and sai naxo karb'ar happy sallah na😁
















Chapter 27&28












A fusace yareema jawad ya nufi part d'insa, banda tafasa bbu abinda xuciarsa keyi, banka k'ofar shiga part d'insa yyi da k'arfi, bala dake xaune yana kallo ya mik'e a firgice yana duba hanya, ganin yareema jawad a fusace yasa ya tattaro nutsuwarsa yabi shi da idanu, jawad kam baibi takan bala ba ya nufi bedroom. Jikin bala yyi sanyi dan yasan ba k'aramin abune ke tafarfasa ran yareema jawad ba, bai kammala tunanin abinda ya samu jawad ba yaji an sake banko k'ofar, da sauri bala ya juya dan ganin mai shigowa, areef ne fuskarsa d'auke da murmushi, wajen bala ya nufa "ina sarkin rigimar yake?" nuni bala ya masa da hannu xuwa d'akin jawad, dan haka da sauri ya nufi d'akin.






"A tsaye ya taradda yareema jawad, sai safa da marwa yake, bak'in ciki da takaicin zaljameel ya masa katutu a xuciya, tunanin yarda xai ladaftar da ita yakeyi, dole sai ya ganar da ita ynx ba a Qatar take ba a Nigeria take, baisan da shigowar areef ba sai jiyay ya dafa kafad'arsa, yasan waye dan haka yak'i juyowa, wani bak'i yaji xuciarsa tayi ganin areef, duk shi ya jaxa masa wannan b'acin ran, da bai ce xaije duba zaljameel ba ai da haka bata faru ba.








"Haba yareema jawad dan sarki guda d'aya tilo, yareema mai jiran gadon mulki, "cikin lion voice jawad ya bugawa areef wata tsawa," is ok areef, please leave me alone, mai kake buk'ata kuma bayan jawowa dakai aka b'atan rai"harara ya kuma makawa areef sannan ya xauna a gefen bed d'insa, dafe kansa yyi dan jiyay yana sara masa, bayasan b'acin rai shiyasa baya shiga sabgar kowa. Murmushi areef yyi ganin yarda yareema jawad yad'au xafi, dan haka ya yanke shawarar tafia ya bashi waje ko ya samu sanyin xucia.






"Natafi jawad sai gobe"areef ya fad'a bayan ya nufi k'ofa, jawad bai d'aga kansa ba ballantana areef yasa rai xai tanka masa, fita yyi yaja k'ofa. Bala na tsaye bakin k'ofa yakasa shiga d'akin, ganin areef ya fito yasa shi gyara tsayuwa, yallabai mai ya samu uban d'akina, murmushi areef yyi, "kasan jawad d'an rigima ne sai da lallaba, so shida zaljameel ne yarinyar uncle aliyu," nan areef ya kwashe labarin abinda ya faru ya fad'a ma bala, ajiyar xucia bala ya sauke "na gode yallabai, ynx ina xakaje?" gida"areef ya fad'a yana tafia,"ka gaida gida yallabai "ok bala nagode".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login