Showing 9001 words to 12000 words out of 56602 words
Chapter 4 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt
 sa fulani, cikin murmushin sa wanda ba kowa ke ganin sa ya bata ansa, tana gaishe ki. Ina ansawa yareema jawad ta fada tana murmushi. Tayseer kam xama tayi ta xubawa yareema jawad ido cike da so da kauna. 
"Areef ne ya tashi bakinsa yak'i rifuwa dan farincikin ganin yareema jawad, hannunsa ya kama suka nufi part din areef. Xaune suke a palourn areef wanda a ka cika gaban yareema jawad da kayan tab'awa. Wallahi yareema jawad ka matuk'ar bani suprise, murmushi yareema yyi ai dama haka nakeso, eh ka kyauta. Kasan ku manya masu sarauta komai naku daban ne, hararasa yareema yyi yana murmushin sa mai birgewa. Areef xaka fara ko? Wallahi ynx sai na bar maku gidan ku, daria areef yyi tuba nake ranka ya dad'e suka sa daria gaba d'aya. 
"Areef ne ya kalli yareema jawad wanda ya lumshe idonsa yana xuba murmushi,yareema jawad da alamu a kawai wani abin farinciki daya sameka, bud'e idonsa yyi tar a fuskar areef still da smile a face d'in shi, a hankali ya furta baby xaljamil sun dawo nigeria, areef kaga xaljamil kuwa, ta girma sosai tayi wani kyau, wallahi xaka rantse cewa bata had'a jini da nigeria ba. Baki areef ya saki yana kallon yareema jawad duk da yasan akwai soyayya mai karfi da yareema jawad kewa xaljamil, amma daga ganin yarda yake nishadi da farinciki ya fara xargin wani abu. Kai masha Allah areef ya fada, gaskia naji dadi sosai yareema jawad, kace auren ka ya kusa kenan? Juice din da yareema jawad ya xuba a bakinsa ya fito dashi, yana hararar areef, god 4 bid, xaljamil ai kanwa tace, kana tunanin xan iya auren ta, tun ba yau ba kasan irin san dana kewa baby xaljamil amma ta yan'uwan taka ce kawai, murmushi areef yyi daya tuna wani abu, ok yareema jawad, gaskia na gane manufarka amma idan bbu damuwa inasan ka hadani da xaljamil mana,cup din hannun yareema jawad ne ya fadi a kasa wanda sai da ya fashe, duk ya wani rikice, cikin rawar murya ya kalli areef, wai, wai xaljamil kake so? Wani shu'umin murmushi areef yyi eh ya fadawa yareema jawad. 
Wata xufa ce ta lullube shi, da kyar yyi controlling temper d'insa ya kuma kallon areef, gaba d'aya yanayin sa ya sauya, sai da ya had'iyi wani yawu mai d'aci sannan yace, sai ka iya larabci kafin kaje, murmushi areef yyi kai nayi murna babban yaya dan dai larabci ai mun iya haxa da haxihi.wani kallo yareema jawad ya watsa masa wanda bai masan yyi ba.
SUMYNBASH CE💋
KUYI HKR DA WANNAN WALLAHI BA K'ARAMIN K'OK'ARI NAYI BA NAYI TYPING D'IN NAN, LUV U MASOYAN SUMYNBASH
 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
            YAREEMAH JAWAD 
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS 
         P. M. L. W 
A romantic love story 
           2017 
Story & written by 
           SUMAYYA SALEES SADEEQ 
PLX MY FANS UR PRAYER IS NEEDED IM SICK, PLX KU SANI A DU'A DINKU, INA KAUNAR KU A DUK INDA KUKE MASOYAN SUMYNBASH 💋💋💋💋
Chapter 13&14 
"Yareema jawad ji yyi gaba d'aya hirar ta ishe shi, dan haka ya mike yana duba watch d'in dake d'aure  a wrist d'insa, wata iska ya furxar sannan ya kalli areef, gaba d'aya yanayin sa ya chanja, xan wuce ya fad'a da sanyin murya, tashi tsaye areef yyi sannan ya kalli yareema jawad yyi murmushi, ok babban yaya muje na rakaka gida dan ina san na fara ganin my heart desire, ya fad'a yana shafa sumar kansa.
"Yareema jawad ji yayi kamar areef ya soka masa mashi, dan haka bai iya cewa komai ba ya d'auki hanyar barin palour, bayan sa areef yabi yana daria k'asa-k'asa. Yareema jawad shiga motar yyi yana jiran k'arasowar areef su wuce, areef na karasowa ya sunkuyo da kansa dai-dai yareema jawad fuskarsa d'auke da murmushi, babban yaya baxan samu damar binka yau ba, amma gobe xanxo xance wajen my heart desire dan Allah a gyara ni a wajen ta, wani k'ululun bak'in ciki ne ya a tukarewa yareema jawad a mak'ogaro, da kyar yyi murmushin da bai kai xuci ba, ya ansawa areef da ok. 
"A takaice suka yi sallama yareema jawad ya ja mota da gudu ya nufi gida. Wani shu'umin murmushi areef yyi wanda shi kad'ai yasan manufarsa da haka ya shige cikin gida. 
"Yareema jawad kam Allah ne ya kai shi gida, bai tsaya ko ina ba sai a part d'insa, a nan ya ajiye motar yyi ciki. Gaba d'aya ransa a b'ace yake kuma ya rasa dalilin b'acin ran, to mai yake shirin faruwa dashi ne. 
"Bala ya fito daga kitchen yaga shigowar yareema jawad a fusace, daga gani yasan bbu lpy, dan haka ya rud'e dan yasan abin sai ya shafe shi. 
"Yareema jawad bedroom d'insa ya nufa yana shiga ya cire kayan jikinsa ya saka na wanka ya nufi toilet, dan wani bala'in xafi yake ji da baxai iya jiran bala yaxo ya hada masa ba. 
 
"Da sallama bala ya shigo d'akin yana rarraba ido, jin saukar ruwa a toilet ya k'ara firgita shi, shikenan yareema jawad ya gaji da jirana har ya shiga toilet da kansa. 
"A gurguje bala ya kwashe kayan da yareema jawad ya cire ya nufi wardrob ya dakko masa wata red riga mai karamin hannu, sai wando 3quater black colour ya ajiye a gefen bed, da sauri bala ya fita ya nufi kitchen dan kar girkin daya d'aura ya k'one, dan wannan yafi masa komai tashin hankali saboda yareema jawad bayasan yaji k'auri ko kad'an ballantana ace abincin da xaici ne yake k'aurin. 
"Yareema jawad kam banda sakarwa kansa ruwa bbu abinda yake yi, a hankali yaji sanyin ruwan ya fara ratsa shi dan haka ya hak'ura ya fito d'aure da towel a waist d'insa. Wajen standing Ac dake d'akin ya nufa, a hankali ya kaita karshe dan yaji sauki a ransa,sannan ya dawo ya nufi dressing mirror. 
"Kayan da bala ya d'akko masa ya saka ya fada luntsumeman gadonsa yana kallon ceilling, knocking bala yyi sannan ya shigo d'akin hannunsa d'auke da tray, gaba d'aya yareema jawad ya tafi duniar tunanin da bai san ma abinda yake tunanin ba. Ranka ya dad'e bala ya fada cike da ladabi, firgigit yareema jawad yyi ya d'ago kai ya kalli bala,na'am bala akwai matsala ne? a'a ranka ya dade ga abinci na kawo maka, ok ajiye bala ya fada bayan ya lumshe idonsa. Jiki bbu kwari bala ya ajiye abinci ya fita daga d'akin yana naxarin yarda yareema jawad ya shiga damuwa irin haka, ko mai ya same shi Allah masani. 
"A bangaren xaljamil kuwa tana gama shan coffee ta fad'a wanka, tsayawa kallon kyau da tsarin toilet d'in,  gaskia dakin nan da toilet d'in nan sunyi masifar birgeta, dan a gidan su kad'ai xata iya bada labari. 
"Ta dad'e a bathtube sannan ta fito d'aure da karamin towel d kad'an ya rufe mata cinyoyinta, gashin kanta a jik'e alamar ta wanke shi,sai faman gogesa tak'eyi ranta duk a bace,duba d'adin tayi taga ba kayanta dan haka ta shiga rud'ani, ita ba sanin kan gidan tayi ba, nd batasan fita ta had'u da kowa,gashi ba'a sai mata layin nigeria ba ballantana ta kira mom. 
ido na xaro waje nace ok xaljamil dama bata janye k'udirinta ba?
"Tunda ga dakin ta fara sand'a, a hnkl ta murd'a handle d'in kofar ta lek'a, OMG! Xaljamil ta fad'a a fili, ganin kyau da tsarin palour d'in ya birgeta, ga sanyin Ac da ya had'u da airfreshner, sosai xaljamil ta bud 'e kofar hanci ta tana shak' a. Da sauri ta tuna abinda ta fito yi dan haka a hankali ta fara k'arewa palour kallo, wani murmushi ta saki ganin trolley d'insu a chan gefe, cikin sand'a da kallon hanya xaljamil ta k'arasa gaban trolley d'in.
" Duk abinda xaljamil ke yi mom na kallon ta ta window d'in d'akinta, sosai xaljamil ta bawa mom daria, hmmmm xaljamil kenan xakiyi ki gama. 
"A hankali xaljamil ta fara jan trolley d'inta tayi hanyar d'akinta,ji tayi an bankad'o curtain d'in palour, wani bugawa xuciar xaljamil tayi tana baraxanar fita daga kirjinta. Tsayawa chak tayi dan ta kasa d'aga k'afarta tayi. Batasan sanda hawaye ya fara fita a idon ta ba, shikenan yau ta shiga uku, ko wane irin mutun xata gani. 
"Aunty xaljamil! Nawal ta kirata, da gudu ta nufi xaljamil ta rungumeta ta baya, wata ajiyar xucia xaljamil ta sauke wanda sai da nawal taji, dan haka ta xagayo gaban xaljamil tana kallon fuskarta, OMG nawal ta fad'a aunty xaljamil waya saki kuka? Da sauri xaljamil ta fara goge hawayen fuskarta dan ta manta sun fito. Murmushi ta k'irkiro ta kama hannun nawal, bbu komai baby nawal xo muje cikin na shirya, ok my aunty. Xaljamil ta kama trolley d'inta ta shig'e da sauri dan kar tsautsayi yasa wani ya shigo. 
"Handdryer ta fara d'akkowa ta xura a socket ta fara busar da gashin kanta, nawal kam sai surutu take mata xaljamil na kwasar daria, a hankali taji kaunar nawal ta shiga ranta. 
"Bayan gashin ta ya bushe ta fito da mayukanta na shafa da gashi, sosai xaljamil ta gama da shafa ta kuma nufi trolley d'in ta dan chanja kaya, wata purple gown tasa wacce aka mata ratsi da yellow, abinka da farar fata sun bala'in karbar jikin xaljamil,ga rigar dai-dai ita bata mata yawa ba batayi kad'an ba. 
"Nawal sai yaba kyan da aunty d'in nata take, wallahi aunty xaljamil kinyi kyau, dama a kwai mata irinku  a duniar nan nawal ta fad'a hannunta a kan bakinta irin mamakin nan takeyi. Kamo hannunta xaljamil tayi tana tunxira daria, chiiiiiiiiiiii gaskia baby nawal xamu cire bakin ki mu aje  a gefe, ido nawal ta fito dashi, i'm sowi my aunty kinsan haka uncle jawad yake fad'a? Ji tayi gaban ta ya fad'i a xuciar ta ta mai-maita jawad, badai wanda mom d'inta ta bata labari ba? Gaba d'aya ta shiga tunani, indai shine ta nasan ganin sa, amma ya yake, bak'i ne ko fari, mai kyau ne ko mummuna, a hankali labarin mom ya dawo mata, yareema jawad kyakkyawan gaske ne, au my aunt na manta sarki mai murabus ynx yace mini xai taho duba ki, nasan ma yana hanya kinsan ya xama old man tafiar sai a hnkl. 
"What! Xaljamil ta fad'a da karfi wanda sai da nawal ta tsorata, kallon aunt d'in nata tayi, aunty xaljamil layin? Idonta ne ya kawo kwalla dan haka hankalin nawal ya kuma tashi, my aunty ki fad'a mini mana, xaljamil kam banda innalillahi wa'inna ilaihi rajiun bbu abinda take nanatawa  a xuciar ta. Dabara ce ta fad'o mata dan haka tayi wa nawal rad'a a kunne, daria nawal tayi hhhhhh my aunt karki samu matsala. 
"Jin an fara murd'a handle d'in d'akin xaljamil yasa nawal da xaljamil suka kashewa juna ido, da gudu xaljamil ta haye gadonta ta runtse Idonta ta fara hawaye dan dama xaljamil hawayen banxama fita yake a Idonta ballantana na kare kai, nawal ce ta koma kusa da xaljamil data d'aura hannunta a kan cikin ta tana kiran, wayyo mom cikina! Mom cikina. 
"Kofar d'akin aka turo da karfi, sarki Abubakar ne mai murabus da matarsa fulani da itama d'aga so kafar ta tayi ta taho duba xaljamil. 
"Ganin xaljamil na juyi tana kiran cikinta yasa hankalinsu gaba daya ya tashi, harda mom dan batasan plan bane, innalillahi wa'inna ilaihi rajiun shine abinda sarki keta mai mai tawa, mom da fulani ma haka, sarki ne yyi karfin halin tambayar nawal, tun yaushe take haka? Ynx bbu dad'ewa ta fada tana jan majina. Sarki mai murabus ne ya kalli bafadan sa da suka xo tare kira mini yareema jawad, rissinar dakai yyi bani da ita ranka ya dad'e. Ok kira mini farouq maxa a waya da sauri ya kira mai martaba sarki farouq ya sanar dashi halin da ake ciki, cikin rawar murya farouq ya ansa bari na kira jawad d'in. 
"Wayar yareema jawad ce ta fara ringing, kamar baxai duba mai kiran ba sai kuma ya dauka wayar ya duba, mai martaba ya gani dan haka yyi saurin dagawa dan ta kusa yin missed call. 
"Hello! Yareema jawad ya fad'a cikin kasalalliyar murya, sannu jawad ashe dama baka koma ka sak'e duba jikin xaljamil ba, ynx baba ya kirani akan gata chan tana ciwon ciki, haba jawad mai ya sa kake haka, xaljamil ce fa, xaljamil d'in jawad amma naga kamar baka damu da ciwon nata ba.
"Sunan da mai martaba ya fad'a yareema jawad ya maimata a hnkl, jawad d'in xaljamil, ji yyi tsigar jikinsa ya tashi, he is speechless dan haka, bari naje ya fad'a wa mai martaba, yawwa jawad nima gani nan.
" Jiyay gaba d'aya hankalinsa ya tashi, a gurguje ya dauk'i first aid box ya chanja shigarsa xuwa blue jeans, labcourt d'insa ya xira ya fita da sauri. Ba wai wani sauri chan ba, amma a yarda yareema jawad ke taka k' asa kamar baya so na tabbar cewa sauri yake. 
SUMYNBASH CE 💋
 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
           YAREEMAH JAWAD 
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS 
         P. M. L. W 
A romantic love story 
             2017 
Story & written by 
           SUMAYYA SALEES SADEEQ 
   NAGODE SOSAI DA ADDU'AR KU MY FANS ALLAH YA BAR XUMUNCI ❤💋
Chapter 15&16 
"Da sallama ya shiga part d'in, ba kowa a palour dan haka direct d'akin xaljamil ya nufa, ganin yarda take juyi tana murk'ususu yareema jawad yaji hankalinsa ya tashi, da sauri ya k'arasa gaban ta ya fara bud'e first aid box, sarki mai mirabus da fulani da momy suka fita dan barin yareema jawad yyi aikinsa. 
"Nawal na gefen xaljamil tana ta mata sannu, xaljamil  idonta a runtse yake tana hawaye. A hankali yareema jawad ya fara duba xaljamil, kallon ta yareema jawad yyi dan ya fara xargin ciwon cikin da xaljamil keyi na k'aryane kawai pretending ne.idan ran jawad yyi dubu sai da ya b'aci, dan haka ya tattara kayansa ya fice daga d'akin ransa a b'ace. Yana fita ya dan saisaita yanayin fuskarsa sannan ya karasa inda su sarki mai murabus suke xaune duk hankalin su a tashe, jawad ya ake ciki? Jiyayi gaba d'aya sun bashi tausayi, lallai yarinyar xata gane kurenta. Murmushin takaici jawad yyi eh na mata allurar bacci sai dai ku bari gobe kwaxo ku ganta. Shikenan yareema jawad Allah ya bata lpy, bai amsa ba yasa kai ya fice daga palour xuciarsa da bak'in cikin xaljamil. 
"Part d'insa ya nufa, yana shiga palour bala ya tashi da sauri ya karb'i first aid box d'in. Barka da xuwa ranka ya dad'e, yareema jawad bai kalli bala ba dan gaba d'aya ransa a b'ace yake, bedroom d'insa ya nufa yana takun k'asaitarsa. Bala na biye dashi a baya, suna shiga bala ya cirewa yareema jawad labcourt a ajiye a cikin wardrob. 
"Xama yareema jawad yyi a kan carpet tare da bawa Bala umarnin xuba masa abinci. Durkusa Bala yyi ya jawo tray d'in ya fara xuba masa,jellop spagetti wanda taji kayan lambu,sai farfeson kaxa, mixed fruit d'in da Bala yake had'a masa dan bayasan shan ko wane irin juice, xuba masa yyi ya ajiye, tashi yyi ya koma gefe. 
"Kamar bayaso haka ya dinga cin abincin, har ya kammala, Bala ya tattare wajen ya gyara komai.Pajamas bala ya dakkowa Yareema jawad ya ajiye a gefen bed ya masa sai da safe ya fita. Kayan ya saka ya haye luntsumeman gadonsa, yana runtse idonsa ya tuna alkawarin da yyi wa nawal na ice cream, tunawa yyi yana dashi a fridge dama saboda ita yake ajiyewa, nd kuma yana san kara ganin kyakkyawar fuskar xaljamil, duk da dai ta b'ata masa rai d'axu.
"Tashi yyi ya cire pajamas d'in ya xira jallabiya, wayarsa ya dauka ya kira layin momy, bugu d'aya ta d'aga kiran, hello yareema jawad wallahi fushi nake dakai, wato ta xaljamil kawai kake ka manta momy ko? Murmushi yareema jawad yyi yana shafa sajen fuskarsa, i'm sorry momy na kinsan mara lapia na bukatar a bashi kulawa shine kawai amma kun kwanta ne? A'a dan dad d'in naka ma bai dawo ba yana chan wajen sarki farouq da mai martaba. Daria yareema jawad yyi cike da kasaita, eh lallai baxaki ganshi da wuri  ba. Nawal ta tafi ne? A'a tace tare da xaljamil xata kwana dan fulani taxo duba xaljamil amma nawal taki binta, murmushi yareema jawad yyi eh lallai yarinyar nan wai menene manufarta ne? Momy gani nan. Ok sai kaxo. 
"Fridge ya bud'e ya ciro rubar ice cream guda biyu ya nufi part d'in su xaljamil, da sallama ya shiga palour, mom na xaune tana kallon labarai a aljaxeera, cike da fara'a ta amsa ya shigo ya xauna a gefen momy. Hira sosai sukeyi suna daria abin sha'awa. 
"Xaljamil da nawal xaune a bed suna hira, aunty xaljamil dan Allah ki tashi muyi pillow fight, haba nawal ki bari sai gobe mana, plx aunty ki tashi muyi, nawal ta bata fuska kamar xatayi kuka, karki mini kuka tashi muyi. 
"Yes, dats my aunty, tashi tashi suka dauki pillow suka fara guje guje a d'akin, daria suke sosai xuciar su cike da nishadi. 
"Yareema jawad ne ya kalli momy, mom ina su nawal? Tana d'akin xaljamil, ok bari naje na dubata,mikewa yyi ya nufi d'akin, tun kan ya bud'e d'akin yaji hayaniyar su, nawal ta biyo xaljamil da gudu ta nufi hanyar k'ofa yareema jawad ya murda handle d'in ya bud'e, da sauri xaljamil ta durk'ushe a wajen ta rike cikinta. Baki da hanci yareema jawad ya bud'e yana kallon xaljamil cike da mamakin wannan alamari,nawal kam da gudu ta nufo jawad ta rungume shi, I miss u sooooooo much uncle jawad,









