Showing 54001 words to 56602 words out of 56602 words
Chapter 19 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt
d'insa a kirjinta, a haka bacci b'arawo ya sace Zaljameel.
Jawad kam ya kasa zaune ya kasa tsaye,sai juyi yake a kan bed ya kasa bacci, ya shiga damuwa bad'an kad'an ba, yanzu ya zai da Zaljameel, bazai iya jurar rashin ta a kusa dashi ba, gangar jikin sa ya saba dana Zaljameel, ga wani sha'awarta da yake ji, tabbas yasan ance bacci b'arawo ne amma baya tunanin bacci zai d'auke shi. Tashi yayi ya sauka main parlour ko zai ga alamun Zaljameel ta fito amma, duk wani da suka siya yana nan, gashi ya tabbata bata ci komai ba, gashi yasan halin Zaljameel da zuciya duk irin knocking d'in da yayi ba bud'e masa zatayi ba, murmushin k'arfin hali Jawad yayi, amma kuma yunwa itama ai bata bari ayi bacci, kwanciya yayi a kujerar main parlour yana tunanin Zaljameel.
Zaljameel kwance a bed sai juye juye take, da alama yunwa ke d'awainiya da ita, tun tana iya d'aurewa taga abin yaci tura, zumbur tayi ta mik'e ta fita neman abinda zata ci, dan bama ta gani sosai tsabar yunwa.
Tana sauka ta nufi ledojin da suka yi shopping, ta chocolate da ita cream take nema, Jawad kam yana jin takun Zaljameel ya sauke wata sanyayyar ajiyar zuciya, had'e da murmushi mai bayyanar da farin cikin daya samu kansa a ciki. Bata lura da Jawad ba, ta d'auka ledar ta fara duba cikin ta, chocolate d'in ta fito dasu ta baje a k'asa ta fara sha, ta d'auka ice cream shima tasha, sai da taji ta k'oshi ta huta sannan tayi fara k'ok'arin barin parlour, ji tayi an hugging d'inta ta baya, amma razane ta bud'e baki zatayi saka ihu Jawad yayi saurin juyo da ita ya had'a bakinsa da nata ya fara kissing, Zaljameel kam ganin Jawad ne yasa ta saki jiki tare biye masa itama, dan itama bak'aramin missing d'insa tayi ba, sai da yayi romancing d'inta yarda ya kamata har ya samu nutsuwa sannan ya cikata yayi hugging d'inta a kirjinsa yana jin sonta na k'ara ratsa shi. Zaljameel kam anyi luf a kirjinsa sai wani lumshe ido take kamar mai jin 3bacci, gaba d'aya Jawad ya mantar da ita b'acin ran da take ciki da salon soyayyar sa.
Kunnen ta Jawad ya kama da bakinsa ya cijeta kad'an, k'ara ta saki tana wani yarfe hannu na shagwaba, daga kai tayi ta harare sa, had'e da turo bcute lips d'inta gaba
"Ya Jawad mai nayi maka ka cijeni ?"
kallonta yayi itama shi take kallo, sun dau wajen 3mint a haka, sannan ta hura ma Jawad iska a ido.
" Ya Jawad wannan kallon fa? "
In romantic ya fara magana, yana shafa gashin kan Zaljameel, fuskarsa d'auke da murmushi.
" Zaljameel rashin ki kusa dani shine babban hukunci mai wuyar gaske da bazan iya jurar sa, bana tunanin zan iya cigaba da rayuwa a gaba bayan bana tare dake, ina sonki matuk'ar so"
Hannun ta ya kama ya d'aura a kirjinsa saitin zuciyarsa ji tayi tana bugawa da sauri da sauri.
Zuciyata na harbawa ne saboda ke kad'ai Zaljameel, zata iya tsaya da aiki a duk lokacin da kikayi k'ok'arin guje mata, a da na jure rashin ki Zaljameel amma a yanzu bana tunanin zan rayu idan bake.
Hugging d'insa Zaljameel tayi ta fashe da kuka, "please Ya Jawad kabar maganar nan, nima bazan k'ara barinka ba, na hak'ura na barka har sai lokacin da kaso mu koma ga parents d'in mu sai mu koma. Rik'e ta yayi sosai shima yana jin dad'in maganar Zaljameel, harshe yasa ya lashe hawayen ta.
" Its ok my baby kukan ya isa haka ko?, bana son ki k'ara yi mini asarar hawaye na kinji "
"Insha Allah my habibi, d'aukarta yayi chak ya nufi bed room d'insa, a ranar ma Zaljameel da Jawad an rab'ashe soyayya, sai dai bata sha wahalan na farko ba.
After 3 month
Babu abinda ya chanja a son da suke ma juna, suna tattalin juna sosai, Zaljameel ta chanja tayi wani fresh tayi k'iba kad'an, tsaye suke a kitchen, suna h'ada lunch, dan Zaljameel tace bata yarda wata ta dinga ciyar da mijin ta ba da kanta zatayi, hakan yasa Jawad ya sallami mai masu girki.
Zaljameel sanye da gajeran wando na mata pink colour, sai wata black half best,ta d'aura apron akai, ta tufke kanta da ribbon, Jawad sanye da boxers, sai white singlet yana taya Zaljameel aiki,(shifati) take so tayi, snacks ne na larabawa, duk ta b'ata masa fuska da fulawa, shima ya zuba mata har jikinta, ta bishi zata rama ya d'iba fulawan ya zuba a jikin sa, dariya suka sa gaba d'aya. bayan ta gama h'ada sos taji zuciyarta na bala'in tashi, da gudu ta fita a kitchen d'in ta nufi toilet,bin bayanta Jawad yayi hankalinsa a tashe, amai tayi sosai kamar zata fito da kayan cikin ta, ta jigata sosai, bayan Jawad ya wanke mata ya d'auke ta suka nufi upstairs, a bed d'insa ya ajiyeta yana jera mata sannu, Zaljameel kam sai maida numfashi take, idonta yayi ja tsabar azaba.
In minute jikin Zaljameel ya dau zafi ta fara rawar sanyi, lura da hakan yasa Jawad ya lullube ta da blanket, dakinsa ya nufa ya d'auka first aid ya fara auna Zaljameel, ya bata treatment ya mata allurai amma da kyar dan sai da yayi da gaske Zaljameel ta bari akayi mata. Bacci mai nauyi ya d'auke ta .
Sai dai me, gaba d'aya Zaljameel bat son k'amshin girki, ko abinci Jawad ya dafa sai dai yaci shi kad'ai, batama son ganin sa, sai dai tayi ta fama da chocolate da ice cream, shine abinda idan Zaljameel tasha babu maganar vomiting,ga yawan bacci da take yi, kuma batason ko wane perfume sai na Jawad shi d'in ma ba shinshina shi take direct ba sai dai kayan da Jawad ya cire, shi zata d'auka ta rufa a fuskarta to anfi zaman lpy,ga zafin rai da take ji dashi, abu kad'an ke hassala ta.
Kasancewar Jawad kwararran likita ne yasa ya gane Zaljameel na d'auke da juna biyu sai dai banson kwana nawa bane ko wata nawa,dan bashi da kayan aiki wani private hospital ya kaita, anan aka shaida masa Zaljameel na d'auke da ciki na 3month. Kallon doctor d'in Jawad yayi, "Kana nufin nan da 6 month zan zama dady?" murmushi doctor yayi "Yes my brother, congratulations".
Jawad d'aga Zaljameel yayi sama yana juyi da ita, godiya yayi ma Allah daya masa wannan kyauta, haka suka nufi gida da tsantsar farin ciki.
After 6 month
Cikin Zaljameel yayi girma ya zama k'ato,ga watan haihuwar ta ya tsaya. banda tsokanarta babu abinda Jawad yasa a gaba, wai cikin ta kamar randa, Zaljameel kam dariya ma yake bata.
Kamar kullum, kwance suke a bed, bayan sunyi yan dabaru sun faranta ran juna coz cikin Zaljameel ya hana Jawad sakewa. Kwance take tayi tana kallon ceiling, fuskarta d'auke da fara'a, Jawad kam an samu akasin haka, dan wayar da Areef ya masa, akan rashin lpy grandfa, jikinsa yayi tsanani kuma babu sunan da yake ambata sai Jawad da Zaljameel. Hakan y tashi hankalinsa ya kuma sa ya fara kokarin janye k'udirinsa na sai Zaljameel ta haihu, ajiyar zuciya yayi to meya ma marabar tambe da fad'a, tunda Zaljameel d'in ma ai watan haihuwar ta ya tsaya, hakan yasa ransa ko yau Zaljameel ta haihu to tabbas daga hospital sai gidansu kuma zasu nufa direct. Zaljameel ta lura da yanayin Jawad ta kuma tambaye shi yace mata lpy, duk da tasan babu maganar lpy amma ta gyale shi dan bata son tirsasashi kuma itama taji abinda hankalin ta zai tashi.
Ta zuba masa ido tana kallonsa taji wani irin ciwon mara ya taso mata, batason lokacin data furta "innalillahi wa'inna ilaihi".
SUMMY NACE ALLAH SARKI ZALJAMEEL, YAU ZA'A D'AND'ANI ABINDA MOM TAJI.........🤧😰😭😔
SUMYNBASH CE 💋
COMPILER:AISHA AMINU SHUGABA.
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
YAREEMA JAWAD
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
(We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers)
A romantic love story
2017
August 2017
Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ
Chapter 85&86
END
A GURGUJE PLEASE
Ganin sakin fuska a tare da iyayen nasa yasa hankalinsa ya d'an kwanta, tashi yayi tsaye ya nufi inda suke tsaye ya durk'usa gaban su, cikin sark'ewar murya wanda yaci kuka kuma yana cikin tashin hankali Jawad ya fara magana "Dan Allah dan Annabi kuyi hak'ur" Dad bai bari ya k'arasa ba ya d'ago Jawad,"tashi son, ba wannan ne ya kawo mu hospital d'in nan ba, ya jikin Zaljameel"?.
Waiwayawa yayi ya kalleta ya sakar mata murmushi, itama murmushin k'arfin hali ta masa,"da sauk'i Dad! Allah ya k'ara sauk'i? "Ameen suka amsa har iyayen mata.
Zahra kam baki har kunne, ita ta kawo ma Sarki da Dad babies d'in suka d'auka, an musu kud'uba da sunan Mom da Fulani, Maryam da Aysha kenan.
Zaljameel na samun taimakon doctors, hakan yasa ta warware da wuri, Fulani da Mom dama hospital suka dawo da zama suna kula da d'iyarsu.
Ana gobe suna aka sallami Zaljameel, dama already Zahra ta gama shirye shiryen shagalin suna, ranar suna mai jego da babies sunyi kyau, ana ta yaba kyawun yaran wasu suce kyan uwarsu sukayi wasu suce baban su, coz a tsakanin Yareema Jawad da Zaljameel kowa ji yake da kyau babu na kushewa.
Anyi suna lpy anci ansha kunsan abu na manya.yara sun samu gift kala kala harda kyautar gidaje aka basu, kowa ya watse.
Grandpa ya watssake, murna kawai yake na ganin jikokinsa da akayi, yana godiya ga Allah, sai dai ga dukkan alamu Zaljameel da Jawad basu wahala ba, a duk inda sukaje. Bayan suna iyayen da yaran suka had'a meeting.
Bayan an zauna anan iyayen ke tambayar su yarda suka had'u, cikin jin kunya da danasani Jawad ya bayyana musu shi ya d'auke Zaljameel, ya kuma sanar dasu irin k'aunar da yake mata. Zaljameel ma ta bada labarin k'aryar da tama Jawad, inda take bayyana musu a lokacin ma Jawad bai tab'a kunsantar ta ba.
Iyayen su da grandfa kansu y d'aure, lallai anyi chakwakiya ba k'arama ba, sunyi masu nasiha sosai suka kuma saka musu albarka da yaran su, taro ya watse.
AFTER 3 MONTH
Zaljameel kwance a part d'in Mom tana danna wayarta, cikin sand'a Jawad ya shiga parlour,Zaljameel bata san da zuwansa ba sai ji tayi an d'aga ta sama, a tsorace ta saki k'ara, tana k'ok'arin kwacewa, riketa Jawad yayi, yana dariya, "Kai my darling, a gaskiya tsoron ki yayi yawa" Harararsa Zaljameel tayi, ta fara k'ok'arin kwace kanta "ni cikani, haka kurum ka tsorata ni" ta turo baki.
"Haba maman Hanan da Hanfa, kiyi hakuri mana "Jawad ya shawo kan princess d'insa ya zauna a kan three sitter ya d'aura kan Zaljameel a cinyarsa suna jirar su ta soyayya
"Zaljameel yaushe zamu koma gidan mu ne, nifa gaskiya hak'urina ya fara k'arewa"
Harararsa tayi tana murmushi, "Kaji ka mijina ai ni naxo kenan babu inda zan sake zuwa kuma".
"Wallahi kam baki isa ba, dan kinga nayi shiru bance a bani matata ba, shiyasa kika samu bakin magana ko? ".
Kallonsa tayi" Sannu mai mata ".
" Yawwa" Jawad ya amsa yana dariya.
Yarda tayi dariyar ya tafi da Jawad, bai san lokacin daya h'ada bakinsa da nata ba ya fara kissing,Zaljameel kam an manta a ina ake aka biyewa miji coz itama tayi missing d'insa.
Mom ce ta fito daga bedroom tana jijjiga Hanfa data dame ta da kuka zata kawo wa Zaljameel ta lallasheta dan ita kad'ai ke iyawa da rigimar Hanfa, turus tayi ganin Jawad da Zaljameel an lula wata duniyar, da sauri tayi baya ta koma d'akin tana jin haushin fitowar da tayi, lallai yaran nan babu kunya a tattare dasu, kwara ta had'a ma Zaljameel kayanta su tafi tun ba'a mata mai gaba d'aya ba a gida.
Sun d'au dogon lokaci a haka sannan Jawad ya kyale Zaljameel, yana maida numafashi, "Gaskiya Zaljameel ki fara shirin tafiya, dan zanyi magana a bani matata" yana gama fad'in haka ya fice a parlour, binsa tayi da kallo tana jin sonsa da k'aunar sa na ratsa duk wani sassa na jikinta, sai a lokacin taji kukan Hanfa, dan haka da sauri ta nufi dakin Mom.
AFTER 5 YEARS
Tun daga nesa zakaji hayaniyar su a field , sanye suke da sport wears, Zaljameel da Hanfa iri d'aya, Jawad da Hanan iri d'aya, kowannen su da P cap a kansa. Basketball suke bugawa, sai dai Jawad yafi Zaljameel ci hakan yasa Hanfa da Zaljameel ke jin haushin su, ita kam Hanan murna ta isheta team dinsu yafi nasu Hanfa sai kwalo take mata.
Jawad ya sake bugawa yaci,dama shine bugawar k'arshe, aikan yaci, wani ihu suka saka shida Hanan suna murna, Jawad ya d'aga ta sama, "Bravo my Dad we deed it" ta bashi peck a kumatu.
Zaljameel da Hanfa sai cika suke suna batsewa. Jawad yaje inda Zaljameel ke tsaye tana ta harare harare, "Haba Queen of beauty, wannan fushin bai dace dake ba, ayi zuciya a iya basketball" ya lakace mata hanci.
"Bazan iya ba d'in, amma dai kasan nima akwai inda nake winning ba, zaka gani in mun had'e a cricket sai na kaika k'asa ".
" Yes haka ne Mom a time d'in mu zamu musu dariya Wallahi "rumgumeta Zaljameel tayi," kad'ai bari my Hanfa, losers zasu zama ".
" Losers," Hanan ta maimaita, "ai mu mun daina wasan cricket coz babu dad'i basketball yafi dad'i shi zamu dinga yi ko dady"hakane my proudly Hanan ".
"Momy we are feeling hungry a bamu abinci mana"Jawad ya fad'a ya wani shagwabe fuska.
Dariya ya bama Zaljameel, suka nufi cikin gida zuciayrsu fal farinciki,sun jera suna tafiya Jawad ya mata rad'a," Zaljameel yaushe zaki bamu Baby ne "hararsa tayi," Baby kuma? Gasu Hanfa da Hanan nan ai sun ishemu ".
Zaljameel na ajiyewa Hanfa da Hanan suka d'auka," A'a mom Wallahi bamu isa ba muna son bro or sis please ".
Dariya Jawad da Zaljameel sukayi coz basuyi tunanin yaran sunji mai suke cewa ba. D'urkusa Jawad yayi ya kama yaran," Yawwa babies ashe kuma Kuna so, "eh dad muna so" to ku kwantar da hankalinku baby ya kusa zuwa "yeeee suka shige parlour da gudu suna murna.
Zaljameel kam cikin ta ta shafa, coz ita tasan akwai ciki a jikinta sai dai bata son months d'in ba,d'aukar ta Jawad yayi suka shiga parlour suma suna hirar su mai dad'i.
END, THEY LIVE HAPPILY.
JINJINAR BAN GIRMA GA:
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS, A ZAHIRIN GASKIYA BANI DA KAMARKU, U ARE SPECIAL TO ME GUYS.
AISHAT A MUHAMMAD KE TA DABAN CE A ZUCIYAR SUMAYYA, INA MATUK'AR ALFAHRI DAKE MY TWINNY.
ZAHRA BUKAR(AUNTY CUTE) KEMA TAWA CE KUMA ANA MUGUN TARE.
KAWALLIYA HAPSAT MUSA(INDON KAUY'E, BAN MANTA DAKE BA ALWAYS KINA RAINA.
AISHAT AMINU SHUGABA U ARE SUCH A DARLING, KE D'IN TA DABAN CE YAR UWATA TA JINI, INA TAYAKI MURNAR ENGAGEMENT D'IN KI, ALLAH YA KAIMU LOKACI MISHA BIKI💃🏻
SUMYN BASH NOVEL
YAREEMA JAWAD FANS
FUTHUHATUL KHAIR1&2
ZEE&HUSSY NOVELS
ONLINE HAUSA WRITERS
WASH HANNUNA WALLAHI KUNA DA YAWA WAD'ANDA SUKA DACE NA JINJINA MUSU, AMMA KUNA RAINA, ZUCIYAR SUMAYYA NA HARBAWA NE SABODA KU MASOYANA.
WALLAHI I SOO MUCH LOVE YOU ❤💛💚💙💜🖤
KU CIGABA DA BINA A SABON NOVEL D'INA DAZAN FARA IDAN NAYI SABIWAR WAYA.
NIHLAH
NIHLAH
NIHLAH 💖💖
Karku bari a baku labari.
SUMYN BASH CE💋