Showing 3001 words to 6000 words out of 56602 words
Chapter 2 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt
 aliyu da farouq auren ya'yan alhaji usman aysha da maryam, ba tare da bata lokaci ya amince ya kuma shaidawa sarki shi mai bada auren ya'yan ne. Sosai sarki yyi farinciki dan yasan aliyu da farouq sunyi dacen mata masu hankali da tarbiyya. 
Xaljamil ce ta kalli mom, su waye aysha da maryam, ni da kanwata mom ta bata ansa, gyada kai xaljamil tayi alamar gamsuwa, ok mom cigaba. 
Farouq da Umar sun yi na'am da xabin sarki dan haka sarki ya saka musu albarka ya kuma shaida musu ba dadewa xasuyi ba xaayi auren. 
Alhaji Usman da fara'arsa ya nufi gidan sa ya shaidawa matarsa hajia fatima, itama tayi murna dan tasan xumuncin su da fulani ya karu bayan amintaka ga kuma surukuta. 
Abbanmu ta bawa maman mu akan tasanar damu xabin daya mana, bbu musu muka amince dan bama iya yiwa mahaifan mu musu. 
Sosai aka fara shirye shirye a fada da cikin gida, bikin yayan sarki su biyu. Muna munyi shiri sosai dan mahaifin mu ya fitar damu kunya. Bayan bukukuwa na alada aka saka mu a lalle aka daura aure ko wacce aka kaita gidan mijin ta da aka gina a gidan sarki. Ni aysha aka aurawa aliyu kanwata maryam aka aura mata farouq. 
Sosai maxajen mu ke bamu kulawa ana haka maryam ta samu ciki, sosai gidan sarautar ya dauki murna har karamin biki aka hada a gidan nima nayi murna sosai haka ma aliyu. Cikin maryam ya shiga wata tara ta haifi danta namiji.. Mom ce ta kalli xaljamil data kara nutsuwa danjin yarda xata kasance, murmushi mom tayi a tunaninki wane irin budiri xaa yi da haihuwar baby boy a gidan sarki. Murmushi xaljamil tayi eh lallai kam tunda a samun ciki ma anyi bidiri ballantana a haihuwa. 
Ranar suna aka sakawa yaro suna jawad, anyi kade kade da bushe bushe irin na gidan sarauta an yi hawan dawakai duk saboda murna, sarki Abubakar yyi gayyata har abokansa na kasar waje a cikin su harda sarauniyar england, sarauniyar england 
? Xaljamil ta fada mamaki bayyane  a fuskarta. Kwarai kuwa kuma ta halarci wannan ranar, dan nima a ranar na fara ganinta. A jiyar xucia ta sauke eh lallai jawad dan gata, daria mom tayi gaskia kam dan gata, dan ya samu kyaututuka na gidaje da filaye  harda wanda ya dauki
 nauyin karatunsa har ya gama. 
 Tunda aka haifi jawad ka bashi kuyangu masu kula dashi, amma ni  a wajena yake wuni, ina kaunar jawad sosai ina kuma kula dashi kamar dan cikina. Hakan yasa maryam ta dauke kanta a kan jawad dan tana tausayamin na rashin haihuwar da banyi ba. 
  Jawad ya girma har an sakashi  askul amma ni shiru bbu ciki bbu alamunsa, mahaifiyata ma abin ya fara damunta duk da aliyu bai taba nuna damuwarsa akan hakan ba, amma ni kaina ina san naga na haifi baby na. 
Kwanci tashi bbu wuya a wajen Allah jawad ya kallama yana primary skul yana shirye shirye tafia secondry. A lokacin mai martaba ya bawa aliyu shawara akan muje kasar waje dan duba lapiyata ina haihuwa ko banayi, aliyu kam ransa ya baci har mai martaba ya lura da hakan ya kuma sanar da mai martaba bbu inda xamuje muna jiran ranar da Allah xai bamu. Sosai dad dinki ya kasa xaman nigeria, dan yana ganin kamar ina xaune ne a cikin damuwa saboda rashin kulawar da bana samu a gidan sanadiyyar rashin haihuwar da banyi ba. Muna xaman mu sai dad dinki ya samu aiki a qatar, da kyar mai martaba ya yarda, shiri sosai muka fara a tym din jawad na ss1. 
Aliyu ya kaini gida mukayi sallama da mamana da babana suka mini fatan alkhairi,.a daren na shiga wajen fulani da mutan gidan nayi Sallama dasu dan gobe da safe xamu wuce. Jawad kam xama yyi a part dina yana kuka wai saina tafi dashi qatar da Ni kaina saida nayi kokan rabuwa da jawad saboda shakuwar da suka yi kyar aka lallashe 
hi akan xamu dawo mu tafi dashi. 
Mom ce ta kalli xaljamil kinji yarda muka rabu da yareema jawad, a jiyar xucia xaljamil ta sauke mom ki cigaba ina jinki. Ok habibty! Da asuba muka bar gidan sarki aka kaimu airport, karfe 8:00 jirgin mu ya tashi sai qatar. A gidan nan muka sauka sai da muka huta sannan dad dinki ya tafi yyi reporting ya sanar da xuwansa. 
A kwana a tashi mukayi 3 month a qatar, rashin lapia na farayi sosai kamar baxan yi ba, hankalin dad ya tashi harda kuka, daria xaljamil ta fara harda rike ciki, eh lallai soyayya, hararata mom tayi eh ai kadan ma kikaji. uhum romeo nd juliet ta fada tana daria. Hmmmm mom tayi murmushi,, muna xuwa hospital doctor ya tabbatar mana da ina da ciki wata 2,wani tsalle dad ya biga a office din ya fara rawa, doctor din daria kawai yake masa. Kudin dake jikinsa gaba daya ya cire ya bawa doctor. 
Muna dira gida aliyu ya fara bige bigen waya yana sanar da yanuwa da abokanan arxiki. Mai martaba sai da yaxo qatar ya ganni shida fulani da maryam da farouq, amma baaxo mini da jawad ba dan kar ya makale,.
 Sallama dady yyi ya shigo pallon, duk da xaljamil taji dadin dawo warsa amma bata ji dadi ba dan tasan anan labarin xai tsaya. A gurguje suka shirya dan flight din ya kusa tashi suka nufi airport. 
SUMYNBASH CE 💋
 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
YAREEMAH JAWAD 
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS 
         P. M. L. W 
A romantic love story 
               2017 
Story & written by 
        SUMAYYA SALEES SADEEQ 
Chapter 7&8 
"Xaune suke a airport suna jiran a kira sunan su su wuce, dad ya gano wani friend d'insa ya tafi suna gaisawa. Xaljamil ta kalli mom fuskarta dauke da damuwa,murmushi mom tayi dan ta gane damuwar xaljamil,dan haka ta cigaba da bata labarin. 
Haka nayi ta renan cikin ki har na haife ki, dad d'inki yyi murna kamar ya mai da ke cikin sa haka yake ji, waya ya dauka ya kira gida ya sanar musu da haihuwar. Mai martaba da fulani sunxo ganin baby,kuka sosai yyi. Aliyu ashe dama xanga jininka kafin na bar dunia,dad ma sai da yyi kuka. 
Yareema jawad munyi waya dashi in kinga murnar da yyi xaki sha mamaki, har walima ya had'a a nigeria ya tara friends d'insa,su tayashi murna yyi kanwa. 
Haka nayi ta renan ki, muna baki kulawa ni da dad d'inki, bayasan yaji kinyi kuka ko kad'an ynx xakiga hankalinsa ya tashi. 
Jawad kam always muna waya,sai yasa a saka miki waya a kunne yana miki wasa ke kuma kina tuntsira daria. Daria xaljamil ta fara yi tana rufe fuskarta wai kunya. Daria mom tayi eh lallai kamata kiji kunya amma ta jawad, nasan xaiyi murna sosai da ganin ki, b'ata rai xaljamil tayi, ai mom xaiyi murnar sa ma ya gama d'an bbu ruwana dashi. Kallon ta mom tayi hmmmm xaljamil kenan. 
Sarki Abubakar Abdulaziz ya gaji da mulki dan dama lokacin da ya karbi mulki shekarun sa da yawa, gashi kuma y'a'yan sa sun girma dan haka ya yanke shawarar yin murabus. 
Bbu wanda ya kamata a bawa mulki sai dadyn ki Aliyu, dan yafi farouq shekaru ya kuma fishi wayo da sanin makamar mulki, dan haka mai martaba ya bugawa Aliyu waya akan ya baro qatar xa'a masa nadin sarauta, dadyn ki bayasan mulki dan yace yana da hadari dan haka yace ya ce ya hkr a bawa farouq. Ba haka sarki yaso ba amma dan kar farouq yaga baya san a bashi mulkin yasa ya janye bawa aliyu ya daura farouq. 
Ajiyar xucia xaljamil ta sauke, fuskarta d'auke da murmushi, mom wato da tuni dad ne sarki? Yea xaljamil mom ta bata amsa. Gyada kai tayi na gane. Mom ki cigaba mana, hararta mom tayi, haba xaljamil mai kike san ji a tarihin rayuwar ki bayan wannan. 
Murmushi tayi har sai da beauty point d'inta ya lotsa, hakane mom wannan ma thanks alots, I really appreciate. Ko? Mom ta tambaye ta. Yea ta fad'a tana murmushi. Kiran sunan su aka fara dan haka suka nufi jirgi. 
Tafiar 4 hours sukayi a sararin samaniya, suka sauka a proudly nigeria. 
Gaban xaljamil ne ya shiga fad'uwa, baiwar Allah duk ta rud'e dan haka ta rike mom sosai a jikinta. Mom ma rike ta tayi dan taji jikin xaljamil har rawa yake, kiyi du'a mom ta rad'a mata a kunne. 
Bayan wasu lokuta kalilan aka bud'e masu kofar jirgi, nan aka fara fita, still xaljamil rike take da mom har suka sauka a jirgi suka fito farfagiyar wajen.
Xaljamil sai raba ido take dan airport d'in ta mata kyau, wata irin magana taji a wajen kuma bata mutun d'aya ba. Fadawa ne suka xube a gaban d'an sarki Abubakar Abdulaziz, sai kayi d'an sarki jikan sarki,Allah yaja xamanin ka ranka ya dade. Hannu dad ya d'aga musu nan suka dawo kan mom itama suka fara mata kirari, gaishe ki gimbiya aysha, gaba salaman baya salaman. Murmushi mom tayi ta d'aga musu hannu. Xaljamil da Tunda taji maganar nan hankalin ta ya tashi ta kuma runtse idonta tana hawaye kirjinta na bugawa da karfi. Kamar an tab'a dan haka da sauri ta bud'e idonta, tar suka bud'e akan fadawa da suketa bud'e babbar riga,wata kara xaljamil ta saki dan ba karamin tsorata tayi ba ganin fadawan nan, gasu bakake munana ga kuma wasu kaya da bata taba ganin su ba. A hankali numfashinta ya d'auke, ta sulale kasa ta fadi sumammiya. Tofa. 
Fadawa kam tun daga ihun da tayi suka rikice, mom ce tayi kan xaljamil tana jijjigata amma ina ta suma, dad cikin tashin hankali ya dauki xaljamil ya xura a cikin motocin da aka xo d'aukarsu,shiga yyi mom ma ta shiga duk sun rikice. da gudu driver ya d'auki hanyar gidan sarki, wanda kafin su karasa har xance yaje wai gimbiya xaljamil ta suma. 
Ina xaka kaimu naga ka d'auki hanyar gidan sarki? Aliyu ya tambaya cikin tashin hankali. Gida muka nufa ranka ya dad'e, a'a hospital xamu wuce. Ba fadan ne ya russunar da murna, Allah ya taimakeka kasan yareema jawad ya dawo d'axu mai martaba yace  a kaita gida. Ajiyar xucia dad yyi ok muje, mom kam fuskarta ta jike da ruwan hawaye, Dad ne yake ta lallashinta. 
Kofar fada ta cika makil duk anyi jigum jigum,, harda mai martaba Abubakar da sarki farouq sun kasa xaune ballantana tsaye. Motar na tsayawa sarki farouq da kansa ya dauki xaljamil ya nufi part d'in da aka tanadar musu. Mom da dad ma suka bi bayan su. 
Har cikin part d'in ya kaita ya nufi d'akin da aka tanadarwa xaljamil, a kan gadon ya ajiyeta. Wayarsa ya d'auka ya kira jawad, bugu biyu ya d'aga cikin rissinawa. Sarki farouq ne ya lullube shi da fad'a, jawad kana ina haka? Gashi har sun karaso baka xo ba. Gani ya fad'a bayan ya murd'a handle d'in dakin. 
OMG! Phone d'in hannuna naji tana baraxanar rabuwa da hannuna, da sauri na rike ta dan gano muku rahoton abinda na gani. Kyakkyawan guy na gani wanda xan iya ranteswa baiyi kama da d'an nigeria ba, fari ne dogo yana da dan jiki amma ba sosai ba, sumar kansa a gyare sai kyalli take, wani kamshi mai dad'i ne ya doki hancina. Sanye yake da labcourt fuskarsa dauk'e da farin glass. Sarki farouq ne ya juyo ya kalli shi, jawad mai kake jira? Da sauri ya karasa jikin gadon sannan ya basu umarni su fita ya dubata, mai martaba Abubakar ne ya kalli jawad, kaci gidan ku, ina kakeso muje ina ganin jikata a cikin wannan yana yin. B'ata rai jawad yyi ya kalli iyayensa Aliyu da farouq, murmushin mugun ta yyi sannan ya juyo alamar xai bar wajen, sarki Abubakar ya kalla ok xoka dubata. Sarki Abubakar ne ya kalli jawad dake kokarin fita daga d'akin,da sauri ya riko hannunsa kai tsaya mana, idan ka tafi waxai duba kanwar taka, murmushi jawad yyi wanda ya kasheni a  xaune. gaka a tsaye, yau naga ja'irin yaro bari mu fita sai ka dubata. Duk da suna cikin tashin hankali sai da suka murmusa.Fita sukayi gaba d'aya suka rufe kofar. 
Yareema jawad ya mai da hankalinsa ga kallon xaljamil,kallon fuskarta yake tayi kyau sosai kamar mai bacci, a hankali ya dawo kan pink lips d'inta masu kyau da fasali, wow beautiful ya fad'a yana wani shu'umin murmushi yana shafa sumar kansa.dama haka yarinyar nan ta koma?gaskia ta girma sosai. Jawad ka duba ta mana xuciar sa ta tuna masa abinda yaxo yi. 
Sosai ya fara dubata, baisha wahala ba xaljamil ta farfado a hankali ta bud'e idonta tana salati,lumshe ido jawad yyi jin daddadar muryar xaljamil. Fes ta bude idonta ta d'aura su akan jawad, gaban ta ne ya fad'i ta ganin balarabe a gaban ta, a hankali take bin d'akin da kallo, eh lallai tabar nigeria, ganin haduwar dakin. Idonta ta sauke akan jawad da ya xuba mata ido yana kallonta. Doctor ina Mom da dad dina ko basu biyo mu qatar din ba? Kallon ta yyi da mamaki amma bai ce komai ba. Doctor suna nigeria ko?duk da larabci ta tambaye shi., jawad kam yyi mutuwar tsaye, muryar xaljamil ta gama tafia dashi.shiru ya mata ya fara ra, idon xaljamil ya kawo kwalla ta fara yarfa hannu cike da shagwaba xatayi kuka,jawad na kallon ta ya dake yana kara yaba siffar xaljamil a xuciar sa, kukan da take niyar yi ta kara masa kyau. Plx doctor bana san allura ta fad'a da larabci, ganin ya nuna kamar bai jitaba ranta ya fara baci, wannan wane irin mutun ne? Tund'a xu nake tambayarsa ya mini banxa. Ko baya magana ne? Xuciar ta ta bata. 
Jawad na gama hada allurar ya juyo ga xaljamil da ta fara kuka ma, Mom dad kawai take kira, jawad bai daina kokarin tsira mata allura ba dan haka ta rike hannunsa tana kuka mara sauti. Kallonta ya tsayayi gani xata b'ata masa lokaci yasa ya kwace hannunsa, sexy eyes d'insa ya xuba a cikin na xaljamil yana kallonta, gaba d'aya ji tayi jikinta yyi sanyi. Cikin lion voice d'insa ya mata magana, ki tsaya kar kiji ciwo, da larabci ya fad'a mata, wayyo Allah, xaljamil gaba d'aya mutuwar kwance tayi, jin voice d'in jawad, batasan tym d'in da jawad ya juye mata allurar ba. Magani ya ajiye mata a gefe ya kwashi tarkacensa ya fita daga d'akin. Ido xaljamil ta bishi dashi tana yaba kyawun gayen .
Xaune ya tarar da iyayensa a pallo sun buga tagumi suna jiran feed back. Murmushi yyi ya kalli sarki mai murabus da ya buga tagumi shima, ganin jawad yasa suka mike suna tambayarsa ya jikin nata? Ta farfad'o amma tana bukatar hutu dan haka basai kun shiga ba ku bari sai anjima idan tayi bacci ta tashi. 
Sarki Abubakar da kyar ya tafi, sarki farouq ma ya wuce, xasu dawo anjima. Jawad na fita ya nufi part dinsa.
 Uncle! Uncle!tsayawa yyi chak, murmushi yyi ba tare da ya juya ba dan yasan wacece, da gudu ta karaso ta rungume kafarsa ta baya. Da fara'arsa ya juyo ya d'auketa y chillata sama, daria suka sa gaba d'aya. 
Nawal ya furta yana kallon fuskarta, uncle ta fad'a tana murmushi, kinyi nauyi mai fulani take baki? Daria nawal tayi, bbu abinda take bani. Hancinta ya lakace au haka kikace ko? Saina fad'a mata. Hannu tasa ta tushe bakinta, la! Uncle karka fad' a mata plxxxxx, murmushi yyi ok chanja xancen ki. Fulani na bani abinci mai dad'i, harda ice cream da chocolate ma tana bani. Daria sosai jawad keyi kai nawal kin cika surutu, haka kowa yake cewa ta fada tana kokarin sauka daga jikinsa, ina xaki xaljamil? Ya fad'a yana kallonta, d'ago kai nawal tayi tana kallon jawad cike da mamaki, uncle! Wacece xaljamil. Sai lokacin ya tuna abinda ya fad'a,, tabarbarcewa yyi ya sauke nawal, oppsss I mean nawal ok? Gyada kai tayi tana murmushi. Uncle! Na'am nawal, bari naje na duba aunty na mai irin sunan daka fada ynx, sun dawo daga qatar fulani tace bata da lpy? Eh haka jawad ya fad'a bayan ya tuna kyakkyawar fuskar xaljamil. Ok nawal kiyi sauri kije ko? Inasan naje nayi wanka xan fita unguwa. Ok uncle karka manta ice cream ni da aunty na, shafa kanta yyi insha Allah baby nawal. Da gudu ta nufi part din Mom dan duba xaljamil. 
SUMYNBASH CE
 🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
           YAREEMAH JAWAD
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS 
          P. M. L. W 
A romantic love story 
                  2017 
Story & written by 
             SUMAYYA SALEES SADEEQ 
Chapter 9&10 
"Cike da takun k'asaita da isa ya ke tafia har ya karasa part din sa, bayi na ganin sa suka fara xubewa suna k'wasar gaisuwa, ransa kam duk ya gama b'aci dan ya tsani wannan haya niyar. Bai tanka musu ba ya shige ciki. 
"Rantsan tsan palour ne wanda yaji kayan alatu, ya hadu iya haduwa wanda idan kana ciki xaka iya manta cewa a nigeria kake. 
Cike da k'asaita ya nufi bedroom d'insa, yaxo shiga Bala kuma yaxo fita, dan haka Bala da sauri ya matsa baya kamar wanda aka tsikarawa shocking. Hannunsa ya dun k'ule ya kalli yareema jawad yana murmushi, ranka ya dad'e yareema jawad, d'an sarki jikan sarki, gaisheka magajin sarki, gaisheka............ Is ok jawad ya  buga masa wata tsawa mai raxanar wa. Da sauri Bala ya kama bakinsa ya tsuke yana jiran irin hukuncin da xa'a yanke masa. 
"Cike da b'acin rai yareema jawad ya kalli bala, cikin lion voice dinshi ya









