Showing 36001 words to 39000 words out of 56602 words

Chapter 13 - YAREEMA JAWAD 1 To end Book Complete Writing by SUMAYYA SALEES SADEEQ -.txt

19 Feb 2025

7770

damuwa, jiyay ya kasa d'aukar mataki a kanta, hakan yasa ya buga tsaki ya fita a dakin.




Wani tsalle Zaljameel tayi a bed d'in ta dire tana murna, "Yes, gaskia naji dad'in shawarar Zahra, Ya Jawad ka shiga uku, sai ka tattara kayanka kabar gidan nan dan bak'in cikin ni Zaljameel, wayarta ta d'auka ta kira Zahra ta bata labari abinda ya faru Zahra ma kam tayi murna da jin haka," yawwa Zaljameel wannan had'uwa ta farko kenan, saura ta biyu, nan Zahra ta kuma bama Zaljameel shawara amma bata bari naji ba.




A kunyace Jawad ya fita a part d'in Zaljameel cuz friends d'insa na main parlour a zaune basu shiga ciki ba, suna ganin sa suka fara tsokanarsa, "Kai mutumi na baka da dama, wato tsabar gajen hakuri briefcase d'in ma a bakin k'afa aka yarda ta, Areef ne mai fad'an haka sauran friends suka fara dariya suma.




Jawad bai iya cewa komai ba, cuz Zaljameel ta gama tayar masa da hankali, ba surutu yake buk'ata ba yana son ya huta ne kawai,zama yayi shima a parlour ya d'aura kansa a saman cushion yana tunanin Zaljameel.




Jin K'ofar part d'in Zaljameel ta motsa yasa Jawad bud'e idonsa tar dan tabbatar da hakan, jin tafiya yayi hakan yasa ya juya da red eyes d'insa suka had'a ido da Zaljameel! Sanye take da brown hijab mai hannu har k'asa, ta nufi parlour. A kusa da Ya Jawad ta zauna dab dashi tana murmushi, d'ago ido yayi ya maka mata harara Zaljameel ta maida masa da murmushi, Cikin sanyin muryar ta ta gaisa da friends d'in Ya Jawad, rintse ido yayi jin muryar Zaljameel na fita tana gaisuwa da friends, muryar matarsa a sadaka wasu suke ji, jiyay zuciyarsa na tafarfasa kamar zata cire, ganin yarda take musu murmushi Jawad yaji kamar ya rufe ta da duka ko zai huce. Mikewa tayi ta nufi kitchen dan had'a musu abinda zasu ci, cuz yanzu Anna bata fiya zuwa gidan ba, kuma kuyangun ma basu zama a gidan dasun gama aiki suke tafiya.














KUYI HAKURI DA WANNAN






SUMYNBASH CE💋🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L


We don't just entertain we touch the heart of the readers




A romantic love story
2017


July 2017




Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ






Chapter 55&56








Bayanta yabi sa kallo, duk da babban hijab d'in dake jikin Zaljameel bai hana mazaunan ta juyawa ba, cikin ziciyarsa ya fara magana "Yanzu haka zata d'auka abu ta kuma kawo wa friends d'insa bayan jikin ta na showing, tashi yayi yabi bayanta.


Tsaye take a kitchen tana had'a snacks da drinks, a landline ta kira d'aya daga cikin kuyangun ta dan ta jera mata kayan, tazo shiga Ya Jawad yazo shiga, hakan yasa tayi baya jikin ta ya fara b'ari kamar an sa mata shocking ta fara gaida Jawad, bai bi ta kanta ba ya shige kitchen d'in.




Jin mutum ya shigo yasa Zaljameel bata waiwayaba ba cux tasan tayi waya, magana ta cigaba, "Yawwa Lantana zo ki tayani had'a kayan nan mijina ne yayi bak'i, wani murmushi Jawad yayi ya nufi inda Zaljameel ke tsaye, ta baya ya zira hannunsa ya kama k'ugunta ya juyo da ita suna facing juna, sosai ta razana amma ta basar,!


" Ya Jawad kana buk'atar wani abu ne?, cikani please sai in d'auka maka" ta fad'a da wata irin murya da ita kanta bata san ta iya taba saurin sakinta yayi ya yayi kicin kicin da fuska, ita kam Zaljameel fuskarta d'auke da murmushi da har sai da beauty point dinta duka lotsa, ta zuba masa dara daran idanunta, saurin d'auke kai yayi daga kallonta, hannunsa d'aya yasa ya kama danyatsan ta ya murd'a har sai da yayi k'ara! K'as, ji tayi kamar ta saki ihu dan azaba.


Cikin wata irin murya mai wuyar fassararuwa ya Jawad ya fara magana, "Zaljameel baki jin magana yanzu ko? Waya baki izinin zuwa ki gaisa da su ballantana har ki had'a musu abinda zasu ci? Da chan da suke zuwa gidan ke kike basu?" Jin tayi shiru yasa ya kuma murd'a hannun, wata k'arar da bata shirya ba tayi dan azaba, hannun ta ta rik'e ta kalli Ya Jawad cikin muryar tausayi tace "Please Ya Jawad let me go, kaga munbar mutane a zaune, idan sun tafi ko ma menene sai ayi".


Tausayi ta bashi ganin yarda idonta yayi ja, hakan yasa ya cikata, bai fita a kitchen d'in ba sai da ta had'a komai a babban tray, Ya Jawad ya mik'a hannunsa ya d'auka d'aya sai da bisa da kallon mamaki sannan ta d'auka nata, jiran ta yayi suka fita tare.




Jerawa sukayi har k'afadar su na gogan ta juna suka nufi parlour, a center table suka ajiye! Mazauninsu nada suka koma,hannun ta Ya Jawad ya kama ya rik'e cikin nashi yana wasa da zara zaran yatsunta da suka sha jan lalle,ga wata azurfa mai kyau da ring na gold mai bala'in tsada,sosai tayi k'ok'arin kwacewa amma ta kasa hakan yasa ta hak'ura.




Zaljameel ta gama sarewa da al'amarin Jawad,Anya ba talala ya mata ba, gaskia kafin bak'in nan su tafi zata samu ta gudu kar reshe ya juye da mujiya.




Kallonsa tayi ta kuma sakar masa murmushi, adai dai kunnesa ta masa rad'a
"Ya Jawad ina son na shiga bathroom, please"


Kallonta yayi yaga ta wani b'ata fuska kamar gaske, a hankali ya cika hannun ta kamar bayaso, "Thanks Ya Jawad" ta fad'a ta nufi part d'inta da sauri.




"Chaiiii Jawad gaskia kunji dad'i kai da Zaljameel, a gaban mu ma baza'a hakura fa soyayya ba?"






Murmushi Jawad yayi ya lumshe idonsa yana shafar man's pride d'insa daya kwanta luf, "A bayan idonku kake so muyi?" Dariya Areef yayi a'a Romeo and Joliet kuyi sha'anin ku wallahi. Dariya friends d'in suka saka, Jawad kam hankalin sa na kan Zaljameel, smooth d'in hannun ta ya tuna kamar bata d'aukar komai dashi, a hankali ya furta "Kin had'u Zaljameel".






Su Areef basu bar gidan ba sai dare, Zaljameel kam bata k'ara fita ba, key ma ta zuba a room d'in dan kar ya Jawad ya shigo, wanka tayi ta shirya cikin wasu purple sleeping dress, yar yalolowa ce, mai siririn hannu, iya karta cinyar ta. Bayan ta gama shirya wa ta d'ane bed tayi dai dai abinta suna chat da Zahra har bacci ya d'auke ta.






Cikin tane ya murd'a mata a cikin bacci, wani zabura tayi cuz bata tab'a jin ciwon ciki irin wannan ba, rik'e cikin tayi tana murk'ususu, a haka ta fad'o k'asa, ji tayi numfashinta na barazanar fita a jikin ta a hankali taja jiki ta nufi k'afa, sai da taje jikin kofar sai ta kasa mik'ewa tsaye ta jingina da k'ofar, kuka take sosai tana rik'e da cikin ta!


"Wayyo ciki na! Wayyo zan mutu Ya Jawad"




Kamar a mafarki yaji ihun Zaljameel, kwance yake a main parlour dan ya kasa shiga ciki, haka Bala ya gama nacin sa akan Jawad ya tafi part d'insa amma yak'i yayi kwanciyarsa a parlour.


Firgit yayi ya tashi zaune, "Please ya Jawad come and help....... Bata k'arasa ba yaji dif kukan da maganar sun tsaya.


Wani irin tsalle yayi ya dura ta bayan 3cter ya nufi room d'in Zaljameel, murda handle d'in yayi yaji shi a rufe da key!" Zaljameel! Zaljameel "ya fara kiran sunan ta a kid'ime, duk ilahirin jikinsa rawa yake," Zaljameel bud'e mini mana let me help you "dai dai nan numfashinta daya d'auke ya dawo, ta sauke ajiyar zuciya da yaji ta har kunnesa, ganin tsayuwar babu amfanin da zata masa yasa ya nufi d'akin Bala ya bashi spare keys, cikin magagin bacci Bala ya bama Jawad keys amma ya kasa tambayar sa mai ke faruwa.




Da gudu ya nufi room d'in ya saka key ya bud'e, jinta yayi jingine jikin door d'in a hankali ya tura harta bud'e, "Hannu Jawad ya d'aura akai ya furta" innalillahi wa'inna ilaihi raji'un "ganin Zaljameel kwance babu alamun numfashi a tare da ita.




Hawaye ne ya fara zarya a idonsa da gudu ya nufi inda first aid box yake dan bata taimakon gaggawa.




Allurai ya fara mata yayi mata duk abinda ya kamata na gaggawa, d'aukarta yayi chak ya kaita bed d'inta ya kwantar, tsaye yayi yana k'are mata kallo, "She look sexy ya fad'a a ransa".


Tundaga k'afarta Jawad ke k'arema ta kallo har fuskarta, idonsa ya sauka a kan cute mouth d'inta,sunyi pink dasu kamar ta shafa lipstick, idanunta a rufe eye lashes d'in ya kwanta luf ya kuma k'arama fuskar tata kyau. Zama yayi a gefenta yana shafa gashin kanta "I love you Zaljameel, please karki tafi ki barni, can't do without you my sunshine, kece farin cikina, burina bai wuce zuciyarki ta fad'a sona ba , ni Kuma na bayyana miki tsantar san da nake miki"
Peck ya bata a lips d'in ta y zauna ya d'aura kanta a cinyarsa yana shafa kanta a haka bacci b'arawo ya kwashe shi.




Asuba




Idon Zaljameel ya fara bud'ewa a hankali, jinta tayi jikin mutum mik'ewa zaune tayi jikin ta babu kwari, ganin Jawad tayi zaune yana bacci ga kanta a cinyar sa, tsorata tayi, "Mai ya kawo Ya Jawad d'akin ta?" a hankali ta fara resuming komai, "Omg" tace ta kalli Jawad, a zaune ya kwana saboda ita, wane irin matsayi gareta a zuciyar Jawad, kardai abinda Zahra ta fad'a mata gaskia ne? Ta rasa amsar tambayoyinta. Allah sarki Ya Jawad, sosai taji tausayin sa a ranta, man's pride d'in sa ta shafa tana murmushi dan yarda yake masa style yana burgeta, pillow ta saka a hankali ta kwantar da Ya Jawad.




Mik'ewa tayi ta nufi toilet, sai a lokacin ta tuna da irin yanyin kayan dake jikin ta, kunya ce ta kamata ta shige toilet da sauri kar Ya Jawad ya farka.wanka tayi da alwala ta fito sad'af sad'af dan kar Jawad yaji takunta ya tashi.




Jallabiya ta zuba ta saka hijab ta shimfid'a prayer mat ta tada sallah.




Bayan ta idar ta zauna adkar, bayan ta gama ta fara karatun Al'qur'anil kareem, kira'a mai dad'i ta keyi, cikin bacci Jawad yaji muryar Zaljameel na karatu, a hankali ya bud'e idonsa tar, inda Zaljameel take ya kalla, sosai ta masa kyau, hijab d'in ya karb'eta.


Yunk'urawa yayi ya tashi tsaye zai bar room d'in yaji k'afarsa ta rik'e, ta masa tsami, ba shiri ya koma ya zauna. Zaman da yayi ya ja hankalin Zaljameel ta kallo wajen, ganin yana ya mutsa fuska yana kallon k'afarsa yasa tana kai Aya ta tsaya, tashi tayi a ajiye Al'qur'an d'in ta nufi bed inda Jawad ke zaune.




Had'e fuska yayi ya kalleta, "Lafiya" yace da ita ganin tana kallonsa, "lafiya lau Ya Jawad, gani nai kana kallon k'afarka ko lafiya?"


"Eh lafiya lau" ya fad'a yana k'ok'arin mik'ewa tsaye, sauri yayi ya zauna dan azaba.




"Sannu Ya Jawad" Ko kallonta baiyi ba ballantana ya amsa mata, hakan ne ya bata haushi amma ta basar cuz ya mata mutinci itama.




"Ko zan iya taimaka maka".


"A'a babu buk'ata" Zaljameel fa ta fara hassala, hakane ma yasa ta kyale Jawad ta hayewarta bed d'in ta gefe d'aya chan ta kwanta sai dai bacci ya gagari idonta, tasan Jawad ba buk'atar taimakon ta amma shegen girman kansa bai barinsa.




Tana sak'e sak'e a kwance bacci ya d'auke ta.




A hankali Jawad ya taka ya nufi part d'insa, wanda Bala ya gaji da jiransa k'ofar d'aki ya nufi masjid.




Bathroom ya shige yayi wanka yayi alwala ya fito, k'afar ta saki hakan ya bashi damar saka Jallabiya ya tada sallah a gida dan jam'i ya wuce shi.






Zaljameel zaune a gaban dressing mirror, ta yi light make up, sanye take da k'arama riga ash colour mai hannu d'aya, tana da tsaga a gefen cinya, kusan rabin breast d'in ta a waje yake, kama gashin ta tayi ta tufke, yunwa take ji hakan yasa ta nufi dining room.




Zaune yake a dining table yana yin breakfast, ya shirya cikin wata orange shirt and black tree quarter, sai tashin k'amshi yake yi. Gaban Zaljameel ne ya fad'i "anya zata iya zama cin abinci bayan ga ya Jawad a zaune?"


Why not? D'aya zuciyar ta bata ansa. Dake zuciyarta tayi ta nufi dining d'in tana tafiya mai d'aukar hankali harta k'arasa.




K'amshin perfume d'in tane ya mata sallama, basar wa Jawad yayi ya cigaba da cin abincinsa, kujera taja ta zauna tayi crossing leg, da k'afarta Idon Jawad yayi tozali, wani takalmi ne mai bala'in tsini yana da igiya an d'aure ta sama,ga cinyoyinta sai kyalli suke, gaba d'aya ya kare mata kallo bai bari ta lura. Jiyay zaman wajen ya isheshi abincin ma ya k'oshi.




Kallonsa Zaljameel tayi ta lumshe idonta a hankali tana jin wani abu game da Ya Jawad a zuciyar ta amma ta rasa gane menene. Cikin sanyin muryar ta ta furta "Ya Jawad ina kwana" bai kalleta ba ya amsa da lafiya lau ya mik'e zai bar wajen "Thanks Ya Jawad for saving my life" Chak ya tsaya, juyowa yayi ya kalle ta yana wani yatsina, "Ki gode ma Allah bani Jawad ba" yayi gaba abinsa fuskarsa babu annuri, a ziciyarsa kuwa murna ce ta kamashi wanda indai ya cigaba da tsayuwa a nan to tabbas Zaljameel zata gane shi, part d'insa ya nufa.














SUMYNBASH CE💋




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L


(we don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers)




A romantic love story
2017


July 2017




Story & written by


SUMAYYA SALEES SADEEQ




I DEDICATED DIS PAGE 2 MY FANS, NGD ALLAH YA BAR K'AUNA YA KUMA BARMU TARE #ONE ❤




Chapter 58&59








After one month




Zaman Zaljameel da Jawad bai chanja ba, suna nan a yarda sai ma abinda ya k'aru, Zaljameel gaba d'aya ta fita harkansa, duk wani hanya da zai had'asu dashi ta daina, ta koma life inta a part d'inta, shima wannan shawarar Zahra ne.






Kwance take a sofa, sanye take cikin wata doguwar riga mara nauyi red ta kama jikinta, gashin kanta baje a bayanta, dama Zaljameel ba mai son yawo da d'ankwali bace,Babu make up a face d'in ta! powder kawai ta shafa sai lip balm mai k'ashin strawberry. idonta na kallon ceiling, She missed her Mom, cuz tunda aka mata aure 2 month kenan bata k'ara sa Mom a idonta ba cuz fushi take da ita, amma yau kam bata ganin zata iya kwana bata sa Mom a idonta ba.




Mik'ewa tayi ta fad'a bathroom dan sake wanka. Shiryawa tayi cikin wani lace dark blue mai tsadar gaske, an mishi ratsi da yellow,yellow veil ta yafa a k'afadar ta ta d'auka handbag black da wani shoe mai tsini shima black. Mirror ta kuma kalla taga yarda tayi kyau, ita kanta tasan tayi kyau dan yau make up d'in nata na mussamman ne, sake fesa tsaddaddun perfume tayi ta nufi parlour tana takawa a hankali.






Sai da ta gama kashe selfie sannan ta nufi hanyar fita, da happiness a heart d'inta, cuz zata ga Mom da Nawal.




Har ta murd'a handle zata fita taji an daka mata tsawa "Keeeeee" Duk da tasan waye hakan bai hanata tsorata ba, cux bata sa rai yana gidan ba.


Handbag d'in ta saki a k'asa tsabar tsorata da tayi, jikinta har rawa yake! Had'e fuska tayi ta kalli Jawad! " Harararsa tayi ta tura cute lips d'inta gaba" haba Ya Jawad! Meye haka?tsorata ni fa kayi".




"Meye haka" ya maimaita a ransa, lallai Zaljameel ta gama raina sa. Cikin zafin nama ya k'arasa kusa da ita ya janyo ta ta fad'o jikinsa da k'arfi, gashin kanta ya rike data fito dashi bata saka shi a d'aurin taba ya ja, wata k'ara Zaljameel ta saki ta runtse idonta tana jiran hukuncin Ya Jawad.




Sosai ya shagala da kallonta, ganin yarda tayi masa kyau dama gashi ya kai wajen 2 weeks bai ganta, kewarta ya dame shi, har wata rama yayi, hannun sa yasa ya fara zagaya mata a face, face d'insa ya had'a dana Zaljameel hancinsa da nata suna gogar na juna,tana jin saukar numfashin sa. wani yarrr Zaljameel taji a jikinta haka Jawad, so yake yayi kissing d'inta amma ya kasa, zuciyarsa na ingizashi amma yana tuna abinda zai je yazo, jin shirun da Zaljameel taji yasa ta bud'e idonta d'aya tana kallon Jawad, k'arema fuskarta kallo yake,face d'insa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login