Showing 27001 words to 27433 words out of 27433 words
Asabar aka daura Auren Amira kafin na
Ramlat a matsayinsu na matan Yusuf,
yayinda Kazrat kuma da Imran sunga
larabawa kam ba laifi. Gida babba ya gina
musu a g.r.a kowacce da fannninta 3
bedroom each, babu wacce zatasan me ake
ciki, kuma kowacce yabata mukullin mota,
dadin sa daya dukka su sunada ilmi, wayewa
da kuma hankali, donhaka kishin su bazai
basa matsala ba, Dakin Amira aka fara
tarewa kafin na Ramlat, (nidai tunda muka
kawo amarya aka bamu kudin sallamar mu
shikenan muka watse, details kuma Allah
yabar wa kansa sani). Nads tanata shirin
nata itama, wanda Farzan yafi ta gandoki,
sunfara event (shima ana kawo ashobe na
dauka namika wa tela na yamin dinki, don
muje musha rawa). Tabbas biki yayi kyau,
(mun ci mun goge wuya munkuma yi rawa),
biki ne na yayan manya shima, itakuma
gidanta na gida dubu aka kaita aka watse,
[1/1, 8:28 PM] Benaxir Omar: 6⃣9⃣HANNU
DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA BENAXIR
OMAR Dama Kazrat abuja aka wuce da ita,
donhaka masu zuwa sukaje Abdullahi
baisamu lafiya ba sai kusan wata biyu,
dakyar aka cire asirin jikin sa, a lokacin
yusuf ne kadai yaje malamin ya masa
bayanin cewa asiri ne sosai akayi , mai
kuma karfi wanda daya karye yakoma kansa.
Abdullahi yadawo abun tausayi Yusuf ne
yadaukoshi a mota suka dawo , Amira tasa
masa ruwan wanka yayi, duk tanayi tana
hawaye shima hawayen yake cike da
nadaman abunda ya aikata, bayan yayi
wankan suka shirya gaba daya don zuwa su
roki inna ko zata yafe mai, Inna kin kallonsu
tayi, saida Amira ta sha kuka, shima
Abdullahin kuka yayi tayi yana rike kafafunta
yana rokonta gafara dakyar ta amince da
sharadin zai biya diya, yakuma yi azumi, ya
amince anan yafara samun nutsuwa, Amira
suka tafi suka barshi. Zaman lafiya suna
kokarin yi daga Amira har Ramlat suna bada
hakkin zaman aure kowacce tana kishin ta
cikin aji da wayewa, shi kadai zai iya gane
hakan. Lalle mata biyu rahama ne, domin
shi kam yayi dace, Allah yakara hada kan su
ya kori shaidan , lokaci daya suka sami ciki,
(abun ba acewa komi sai godiyan Allah). Ni
dai Benaxir danaga nagama ganin labarin
nake cewa BISALLAM, Anan na kawo
karshen labarin , dafatan mundauki darussan
dake ciki, Ubangiji Allah yasa mu gyra, Na
sadaukar da Wannan littafin zuwa ga Hanifa
usman Maryam maleka Maman ahmad lagos
Hauwa mudi Ummi Aisha Luvly mimie Nd All
those dat have been by my side right from
day one, dukka masoya na wanda na sani da
wanda bansaniba , i love you all, Allah yabar
zumunci